Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Usman Minjibir, Umar Mikail and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah Ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Kwastam ta kwace hodar iblis da kuɗinsa ya kai dala miliyan 150

    Cocaine

    Asalin hoton, AFP

    Jami'an kwastam a Senegal sun ce sun kwace hodar iblis fiye da tan guda a kan iyakar kasar da Mali.

    Sun ce wannan shi ne kwace mafi girma da ƙasar ta yi a kan kwaya.

    An sanya hodar iblis ɗin a cikin leda aka kuma naɗe ta sannan aka saka a cikin wata babbar mota wadda aka tsayar da ita a kusa da garin Kidira.

    An kiyasta kuɗin hodar iblis ɗin zai kai kusan dala miliyan 150.

    Senegal na iyaka da ƙasashen da suka haɗ da Guinea da Mauritania da kuma Guinea Bissau wanda dukkansu sun yi fice a wajen da ake tsayawa da kwaya idan an ɗauko ta daga ƙasashen Latin Amurka da kuma Turai.

    A watan Nuwamba, sojojin ƙasar ta Senegal suka bankaɗo kusan tan uku na hodar Iblis daga cikin wani jirgin ruwa a gaɓar ruwan ƙasar.

  3. Amurka da Iraqi sun ce za su taimaka don magance rikicin Gabas Ta Tsakiya

    Biden

    Asalin hoton, EPA

    Shugaba Biden da kuma Firaiministan Iraqi, Mohammed Shia-al-Sudani, sun yi alkawarin taimaka wa wajen dakatar da rikicin Gabas Ta Tsakiya daga yaɗuwa.

    Tattaunawar da shugabannin biyu suka yi a fadar gwamnatin Amurka, an shirya ta ne domin a mayar da hankali a kan kiran da Bagadaza ta yi na janye dakarun Amurka daga Iraqi.

    Sai dai tattaunawar ta mayar da hankali a kan karuwar zaman ɗar-ɗar bayan harin da Iran ta kai wa Isra'ila a yankin Gabas Ta Tsakiya.

    Mataimakin Firaiministan Iraqi, Muhammad Ali Tamim, wanda shi ma ke Washington ya gana da sakataren harkokin wajen Amurkan Antony Blinken, kuma ya yi gargaɗin fuskantar mummunan tashin hankali a yankin.

    Dukkaninsu sun amince su yi aiki tare wajen dakile ayyukan 'yan kungiyar IS a Iraqi.

  4. Gobara ta ƙona shaguna da dama a kasuwar Yola

    Gobara a kasuwar Yola

    Asalin hoton, Others

    Wata gobara ta tashi a kasuwar garin Yola da ke karamar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa, tare da ƙona shaguna da dama.

    Gobarar da ta afku ranar Litinin, ta kuma janyo wa ƴan kasuwa yin asarar kayayyakinsu.

    Wani ɗan kasuwa mai suna Ali Kachalla wanda shi ne shugaban ƴan kasuwan na garin Yola, ya shaida wa BBC cewa ɓarnar da gobarar ta yi ba zai misaltu ba.

    Ya ce ta ƙona kusan kashi 80 cikin ɗari na kasuwar.

    "Gobarar ta ƙona kayayyaki da suka kai dubban miliyoyi. Da farko mun ɗauka wuta ce ta janyo gobarar, amma bayan washegarin yau mun gano cewa har da iska da tsawa a cikin abin da suka haddasa ta," in ji shi.

    Kachalla ya ce mutane daga ko'ina ne suka kawo musu ɗauki.

    Ya kuma ce jami'an kashe gobara sun makara wajen kai ɗauki, saboda lokacin da suka iso wutar ta gama yin ɓarna.

    Ya ce mataimakiyar gwamnan jihar, Farfesa Kaletapwa Farauta ta ziyarci kasuwar da safiyar Litinin domin jajanta musu, inda ta ce gwamnati za ta taimakawa ƴan kasuwar da abin ya shafa da kuma yin binciki domin gano musabbabin tashin gobarar.

  5. Me ke faruwa da Adam A. Zango?

  6. Gwamnan Gombe ya miƙa ta'aziyyarsa kan rasuwar ƴan uwan Maidalan Gombe a hatsarin mota

    Gombe

    Asalin hoton, Ismaila Uba Misilli

    Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya miƙa ta'aziyyarsa ga Maidalan Gombe bisa rasuwar ‘yan uwansa shida a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Azare zuwa Gombe, a ranar Asabar.

    Gwamna Inuwa, wanda ya halarci jana’izarsu tare da Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dr Abubakar Shehu Abubakar III, da sauran ɗaruruwan jama’a, ya ce rashin ‘yan uwa a irin wannan yanayi abu ne mai ciwo.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Ismaila Uba Misilli ya fitar, gwamnan ya ce wannan abin bakin ciki da ya faru na rashin, ya shafi ɗaukacin al’ummar Gombe.

    "Muna miƙa sakon ta'aziyyarmu ga Maidalan Gombe da kuma iyalan waɗanda suka rasa ƴan uwansu. Rasuwar 'yan uwa guda shida a cikin irin wannan mummunan hatsarin mota ba rashi ne ga dangin ku kaɗai ba, ya shafi al'ummar Gombe baki-ɗaya," in ji gwamnan.

    Ya kuma yi addu’ar Allah ya ji kan mutanen da suka rasa rayukansu a hatsarin motar, ya kuma saka musu da Aljannar Firdausi.

    Gombe

    Asalin hoton, Ismaila Uba Misilli

    Gombe

    Asalin hoton, Ismaila Uba Misilli

  7. Shagunan sayar da magani a Laberiya na sayar da magungunan sata na agaji - USAid

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kusan kashi 90 cikin 100 na magungunan da ake sayarwa a Laberiya sun kasance waɗanda aka sata ne daga cikin wanda ƙungiyoyin agaji ke bayar wa, in ji Hukumar Raya Ƙasashe ta Amurka (USAid).

    A karshen mako ne daraktan hukumar ta USAid Jim Wright ya ce irin wannan aikin zamba ya hana 'yan ƙasar Laberiya samun taimakon magunguna masu muhimmanci.

    "Ba za mu yarda da wannan ba. Wannan yana nufin cewa magani yana samuwa ne kawai ga marasa lafiya waɗanda ke da isassun kuɗi saye, ”in ji Mista Wright.

    Bayan bayyana hakan, ƙungiyoyin farar hula shida na ƙasar Laberiya sun kaddamar da wani gangamin na ƙasa da nufin sanya ido kan yadda ake raba kayayyakin jinya da kuma wayar da kan jama'a cewa magungunan da aka bayar kyauta ne kuma bai kamata a sayar da su ba.

    Mista Wright ya yi kira da a kara kaimi, ciki har da hukunta waɗanda suka aikata laifin sata da sayar da kayayyakin kiwon lafiya da aka bayar.

    Har yanzu hukumomin Laberiya ba su ce uffan ba game da wannan batu.

  8. 'Muna fatan taron da ƙasashe ke yi a kan Sudan a Paris zai kawo karshen rikicin ƙasar'

    Gwamnatin Faransa ta ce tana fatan taron da ƙasashen duniya ke yi a kan Sudan a Paris, zai kawo karshen rikicin ƙasar da aka shafe kusan shekara guda ana yi.

    Ministan harkokin wajen Faransa, Stephane Sejourne,ya ce al'ummar Sudan su ne rikicin ke shafa.

    Ya ce yaƙin da ake yi tsakanin sojojin gwamnati da kuma dakarun RSF ya janyo babbar asara.

    Faransa ta shirya taro tare da Jamus da kuma Tarayyar Turai domin a tara kuɗaɗen da ake buƙata don taimakawa ƙasar da kuma bayar da goyon baya ga ƙoƙarin shiga tsakanin da ake yi.

    Yaƙin da ake yi ƙasar ya raba miliyoyin mutane da muhallansu sannan ya jefa ta cikin yanayi na matsananciyar yunwa.

  9. Yadda tsutsa ta janyo wa manoma asarar Naira miliyan 500 a Kano

    Tsutsa

    Asalin hoton, Ismai’l Bagwai

    Wasu manoman a karamar hukumar Bagwai na jihar Kano, sun koka kan yadda tsutsa ke lalata musu amfanin gona.

    Manoman sun ce sun yi asarar amfanin gona da ta kai kusan Naira miliyan 500.

    Sun kuma ce tsutsar ta shafi kusan hekta 1000 na gonakinsu.

    Wani manomin tumatir, Bello Idris ya ce suna cikin wahalhalu kan yadda tsutsar ta addabe su.

    ''Za mu nome tumatir mu sayi taki 50,000, mu kuma sayi maganin feshi 10,000 da man fetur amma duk a banza,'' in ji shi.

    Ya yi kira ga gwamnati da ta kawo musu ɗauki da kuma gano inda matsalar take.

    Haka-zalika, shi ma Sama'ila Bello mazaunin karamar hukumar Dawakin Tofa, ya ce tsutsar na lalata musu amfanin gona cikin lokaci kankani.

    "Muna so gwamnati ta taimaka mana a duba a ɓangaren iri ne ko maganin feshi ne ba a sayar da mai kyau," in ji Bello.

    Amfanin gona

    Asalin hoton, Ismai’l Bagwai

    Amfanin gona

    Asalin hoton, Ismai’l Bagwai

  10. Uba ya rasa ƴaƴansa uku bayan da mota ta buge su a Nasarawa, Mansur Abubakar, BBC News

    ..

    Asalin hoton, ABU UWAIS

    Bayanan hoto, Yaran su kaɗai ne ƴaƴan Abu da Fatima Uwais

    Wani uba ya shaida wa BBC irin tashin hankalin da yake ciki bayan da wata mota ta kaɗe yaransa mata uku abin da ya yi sanadin mutuwarsu a ranar Asabar.

    Yaran - ƴar shekara goma da takwas da shida - sun bar gida cikin murna kasancewar suna annashuwar bikin ƙaramar sallah, in ji Abu Uwais.

    "Sun sa sabon kaya da takalmin da na siya masu, kuma suna murnar fita," ya ƙara da cewa.

    An kama direban motar kuma zai bayyana gaban kotu, in ji ƴan sanda.

    Za a tuhume shi da tuƙin ganganci sakamakon haɗarin da ya janyo kisa a garin Toto da ke jihar Nassarawa, a cewar ƴan sanda.

    Mutanen da suka fusata da lamarin sun ƙona motar direban.

    Uwais ya shaida wa BBC cewa shi da mai ɗakinsa, Fatima, sun rasa gaba ɗaya ƴaƴan da suka haifa.

    Musulmai a Najeriya sun yi bikin ƙaramar sallah a ranar Laraba sai dai iyalai sun ci gaba da shagulgulan sallah har a ranakun ƙarshen mako - har da iyalin Uwais, sai dai shagulgulan wannan iyalin ya zo ƙarshe da mutuwar yaran.

    Uwais ya faɗa wa BBC cewa yaran nasa sun kai ziyara gidan kawunsu, suna tsaye a ƙofar gida "lokacin da direba da ke gudun wuce ƙima ya buge su bayan da ya doki turakun wutar lantarki."

    Yana gida lokacin da aka kira shi a waya ana faɗa masa ya yi sauri ya je asibiti.

    "Kawai an faɗa mani na je asibiti, sai da na isa na ga abin da ya faru, kuma na shiga tashin hankali," in ji Uwais.

    Nusaiba, mai shekara 10, ta mutu a asibiti, yayin da Rumasa'u ƴar shekara takwas da Nana Maryam ƴar shekara shida, sun mutu take a wurin haɗarin.

    Nusaiba tana cikin masu ƙoƙarin ajinsu yayin da ƙannenta suma suke da ƙoƙari a makarantarsu, kamar yadda mahaifin nasu suka ce.

  11. Sojojin Najeriya sun kama 'mai sayar wa ƴan bindiga makamai' a Taraba

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, @DefenseNigeria

    Rundunar Sojin Najeriya ta kashe wani ɗan bindiga tare da kama wani mutum da ake zargi da sayar da makamai ba bisa ƙa'ida ba a wani samame da dakarunta suka kai jihohin Benue da Taraba.

    A samamen, sojojin sun daƙile yunƙurin sace mutane kamar yadda daraktan yaɗa labarai na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana a sanarwar da ya fitar.

    A jihar Taraba, sojoji tare da haɗin gwiwar ƴan sintiri sun kama mutumin da ake zargi da sayar wa ƴan bindiga makamai ba a tashar mota ta Jalingo.

    Kamen nasa kuma ya sa an kama wasu mutanen da suke gudanar da ayyukan tare, in ji sanarwar.

    Rundunar ta kuma gano wasu bindigogi ciki har da ƙirar gida, da mota ƙirar Peugeot, da wayoyin hannu biyar, sai kunshin alburusai, da kuma babur, a cewarta.

    A wani samamen na daban, sojojin sun daƙile yunƙurin sace mutane a garin Zaki-Biam da ke ƙaramar hukumar Zaki-Biam na jihar Benue, inda yayin musayar wuta sojojin suka kashe wani mai garkuwa da mutane tare da ƙwace ƙaramar bindiga da kuma tarin alburusai.

    • 'Muna rayuwa cikin zulumi sakamakon hare-haren ƴan bindiga'
    • Maris: Watan da aka sace daruruwan mutane a Najeriya
  12. APC ta dakatar da Abdullahi Ganduje a matakin mazaɓa

    ..

    Asalin hoton, APC Nigeria/X

    Jam'iyyar APC reshen mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano ta dakatar da shugaban jam'iyyar naa ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje nan take.

    Mai bai wa jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a a mazaɓar Ganduje ne Haladu Gwanjo ya sanar da dakatar da shugaban jam'iyyar a wani taron manema labarai da aka yi a Kano ranar Litinin.

    Gwanjo ya bayyana cewa matakin dakatar da Ganduje daga jam'iyyar ya faru ne saboda zargin da gwamnatin Kano take masa na aikata rashawa da wadaƙa da kuɗaɗe.

    A cewarsa, mambobin jam'iyyar sun yanke shawarar dakatar da shugaban APC na ƙasa ne bayan ƙuri'ar yanke ƙauna da aka kaɗa a kan shi saboda gazawarsa wajen wanke sunansa daga tarin zarge-zargen da aka yi masa na rashawa da cin hanci.

    Zarge-zargen dai sun haɗa da wani bidiyo da aka yi ta yaɗawa wanda a ciki ake zargin sa da karɓar cin hanci daga ɗan kwangila.

    Gwanjo ya bayyana cewa matakin ya fara aiki daga yau ɗin nan - 15 ga watan Afrilu.

    Sai dai bayanai na nuna cewa ba a yi sallamar da yawun shugaban jam'iyyar mazaɓar ba.

  13. Yadda aka kuɓutar da ragowar ɗaliban jami'ar Gusau daga hannun ƴan bindiga

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan uwa da iyayen ɗaliban jami'ar tarayya ta Gusau da ke jihar Zamfara da aka yi garkuwa da su sun tabbatar da sakin ragowar ɗaliban da suka rage a hannun ƴan bindiga.

    Sun ce tun a ranar Juma’ar da ta gabata aka saki rukuni na farko kafin daga bisani a sako sauran da yammacin ranar Lahadi.

    A watan Satumban bara ne ƴan bindiga suka yi awon gaba da ɗaliban daga ɗakin kwanansu da ke wajen jami'ar.

    Yar uwar wani mutum da ya nemi a sakaya sunansa na cikin ɗaliban da aka sako ranar Lahadi kuma ya shaida wa BBC cewa tun bayan da aka sace ɗaliban suna magana da su ta waya lokaci zuwa lokaci.

    Ya ce "ranar Juma'a an saki mutum uku, da aka sako su babu ƴar uwata a ciki, ranar Lahadi kuma, wasu daga cikin yaran sai suka kira iyayensu mata suka yi magana da su cewa an karɓo su, ga su a hannun jami'ai cewa za a tafi da su Gusau." in ji shi.

  14. Su wane ne masu fafutukar kafa ƙasar Yarabawa zalla a Najeriya?

  15. Likitoci na son babban sufeton ƴan sandan Kenya ya nemi yafiyarsu

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Wasu ƙungiyoyin farar hula da masu rajin kare haƙƙin bil adama a Kenya sun buƙaci shugaban ƴan sandan ƙasar ya nemi yafiyarsu bayan da ya yi alƙawarin ɗaukan mataki kan ma'aikatan lafiyar da ke yajin aiki.

    Gamayyar ƙungiyar likitoci sun tsunduma yajin aiki ranar 14 ga watan Maris saboda rashin biyan su albashin da ba a biya su ba da jan ƙafar da gwamnati take wajen aika likitoci masu neman ƙwarewa da sauran buƙarunsu.

    Babban sufeton ƴan sanda Japphet Koome a ranar Lahadi ya zargi ma'aikatan lafiya da zama matsala ga al'umma bayan da suka rufe tituna da hura usur yayin zanga-zanga abin da ya janyo marasa lafiya da ke asibitoci suka rasa samun nutsuwa.

    Gamayyar ƙungiyar da wasu ƙungiyoyin farar hula da na kare haƙƙin bil adama sun buƙaci mista Koome da ya janye kalamansa tare da neman afuwarsu saboda kalamansa ko kuma su shigar da ƙara a kan shi.

    Sun yi alƙawarin ɗora laifi kan mista Koome idan wani abu na rashin daɗi ya faru da ma'aikatan da ke yajin aiki.

  16. Ƙasashen yamma sun nemi Isra'ila ta guji tashin hankali

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Hankali ya karkata ga Isra'ila kan yadda za ta mayar da martani kan harin jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da Iran ta kai mata sai dai ƙawayenta sun buƙaci ƙasar da ta guji ɓarkewar rikici.

    Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock ta ce Isra'ila ta yi nasara a faɗanta da Iran kuma dole ne a kaucewa rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya nemi a kwantar da hankali inda ya ce ƙasarsa za ta yi duk mai yiwuwa don hana ɓarkewar rikici.

    Tun farko kuma sakataren harkokin wajen Birtaniya, David Cameron ya shaida wa BBC cewa yana tunanin Isra'ila tana da hujja ta mayar wa Iran martani sai dai ya buƙaci ƙasar ta yi taka tsan-tsan ta kuma yi tunani a kai.

  17. Shugaban ƙasar Chadi ya fara yaƙin neman zabe

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Deby, ya fara yaƙin neman zaɓensa na shugaban ƙasa a ranar Lahadi, gabanin zaɓukan da za a gudanar da nufin tafiyar da ƙasar bisa tsarin mulkin farar hula na dimokuraɗiyya.

    Shugaban zai dai fuskanci wasu ƴan takara tara a zaɓen da aka shirya yi a ranar 6 ga watan Mayu, ciki har da firaminista Sucés Masra da aka naɗa.

    Shugaban ya kuma miƙa saƙonsa na farko a taron yaƙin neman zaɓensa a babban birnin N'Djamena.

    Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, yayin da yake jawabi ga taron, shugaban wanda tsohon soja ne, ya jaddada ƙudirinsa na cika alƙawuran da ya ɗauka.

    Deby ya bayyana alƙawuran yaƙin neman zaɓensa, inda ya mayar da hankali wajen inganta matakan tsaro da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar Chadi.

    Hasashe dai ya dabaibaye takarar Mista Déby, inda da dama ke sa ran zai samu nasara a zaɓen, ko da yake wasu ƴan adawa sun soki tsarin zaɓen da cewa "almara ce."

    An kashe babban abokin hamayyarsa, madugun ƴan adawa Yaya Dillo a wata musayar wuta da jami'an tsaro a ranar 28 ga watan Fabrairu inda gwamnatin ƙasar ta danganta mutuwar tasa da zargin hannunsa a wani mummunan hari da aka kai kan hukumar tsaron ƙasar, lamarin da ya musanta.

    Haka kuma kotun tsarin mulkin ƙasar ta kuma haramta wa wasu 'yan takara 10 takara a watan da ya gabata, ciki har da wasu masu sukar lamirin gwamnatin ƙasar.

    Da farko dai shugaba Deby ya yi alƙawarin miƙa mulki bayan watanni 18 ga mulkin dimokraɗiyya bayan hawansa mulki a shekarar 2021, bayan rasuwar mahaifinsa.

    Amma daga baya ya ɗage zaɓen har zuwa wannan shekarar, lamarin da ya janyo zanga-zangar da jami'an tsaro suka dakile da karfin tsiya.

    • Mohamat Idriss Deby: Kalaman shugaban kan yiwuwar tsawaita mulkinsa sun tayar da kura a Chadi
    • Mahamat Idriss Déby Itno: Abin da ba ku sani ba kan ɗan Idriss Deby wanda ya zama shugaban Chadi
  18. Hauhawar farashi ta kai kashi 33.20 cikin 100 a watan Maris

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙididdiga a Najeriya ta ce hauhawar farashi ta kai kashi 33.20 cikin 100 a watan Maris.

    A shafinta na X, hukumar ta ce hauhawar ta ƙaru ne daga kashi 31.7 cikin 100 na watan Fabarairu.

    A cewar hukumar, wannan ya nuna hauhawar farashi ta ƙaru da da kashi 11.16 cikin 100 a watan Maris ɗin 2024 idan aka kwatanta da yadda yake a watan Maris na 2023 da ya kasance kashi 22.04 cikin 100.

    Kazalika ƙididdigar da NBS ta fitar ta nuna cewa hauhawar farashi a Maris ɗin 2024 ta kai kashi 3.02 cikin 100 saɓanin kashi 3.12 cikin 100 da aka gani a watan Fabarairu.

    Hakan na nufin a watan Maris, ƙaruwar farashin kayayyaki ba ta kai wadda aka gani ba a watan Fabarairu.

    Hauhawar farashi a watan Maris ta faru ne a lokacin da matakan da babban bankin Najeriya ke ɗauka na ɗaga darajar naira kan kuɗaɗen waje suka fara tasiri.

    A makonnin baya-bayan nan darajar naira ta ƙaru a kan dala da fiye da kashi 40 cikin 100 daga kusan naira1,900 kan kowace dala zuwa kusan naira1,100 duk dala ɗaya.

    Sai dai duk da farfaowar da darajar naira take, har yanzu ba a soma ganin saukar farashin kayayyaki ba a kasuwa.

    Najeriya ta fuskanci hauhawar farashin da ba a taba gani ba a baya-bayan nan sakamakon faɗuwar darajar naira da kuma janye tallafin mai da gwamnati ta yi.

    Sau biyu babban bankin ƙasar na ƙara kuɗin ruwa a bana a ƙoƙarin daidaita farashin kaya.

    • Ƙarin hauhawar farashin da aka daɗe ba a gani ba na gigita ƴan Najeriya
  19. DSS ta kama makusanciyar El-Rufai kan sukar gwamna Uba Sani

    ...

    Asalin hoton, DSS

    A ranar Lahadi ne jami’an tsaro da ake kyautata zaton jami’an tsaron farin kaya (DSS) ne suka kama wata mutuniyar El-Rufai kuma ‘yar siyasa da ke jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Aisha Galadima.

    Ana zargin kamen na da nasaba da wani saƙo da ta wallafa a shafin sada zumunta na facebook da ta yi wasu kalamai marasa daɗi ga gwamnan jihar, Uba Sani.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa majiyoyi sun nuna cewa Galadima ta bayyana rashin amincewarta da kalaman Sani na baya-bayan nan game da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.

    Kamar yadda shaidu suka bayyana, an kama ta ne a unguwarsu da ke unguwar Tudun Wada da ke Kaduna a ranar Lahadi da yamma kuma wasu abokane sun bayyana cewa an kashe wayar ta bayan kama ta.

    Sai dai kuma da aka tuntuɓi babban sakataren yaɗa Labarai na Gwamnan, Muhammad Lawal Shehu, ya ce bai da masaniya game da kamen, kuma ya buƙaci ƙarin haske kan lamarin daga hukumar tsaro ta DSS

    “Ba a sanar da ni cewa an kama wata ba da ta yi wasu kalami marasa daɗi gwamna Sani Uba ba, amma duk da haka, ya kamata a tuntubi hukumar ta DSS game da wannan batu, maimakon gwamnatin jihar Kaduna,” inji shi.

    • Ina aka kwana a alƙawuran da aka yi wa mutanen Tudun Biri?
  20. Ambaliyar ruwa a Tanzaniya ta kashe kusan mutum 60 cikin mako biyu

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Kusan mutum 60 ne suka mutu tun farkon wannan wata sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da ambaliyar ruwa da ta afka wa sassa daban-daban na ƙasar Tanzaniya kamar yadda gwamnatin ƙasar ta bayyana.

    Ambaliyar ta yi mummunar ɓarna musamman a yankin gaɓar tekun ƙasar inda ɓarnar ta shafi dubban gonaki, kamar yadda Mobhare Matinyi, kakakin gwamnatin ƙasar ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

    Mista Matinyi ya jaddada tsananin halin da ake ciki a yankin gaɓar tekun, inda ya bayyana cewa mutum 11 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar.

    Ya ƙara da cewa adadin waɗanda suka mutu sakamakon ambaliyar ya kai 58, yayin da aka samu ƙarin asarar rayuka a wasu yankunan.

    Abin takaici in ji shi shi ne yadda wasu ‘yan makaranta 8 suka rasa rayukansu a lokacin da motar bas ɗinsu ta nutse a cikin ruwan saman da ya mamaye yankin arewacin ƙasar a ranar Juma’ar da ta gabata.

    Watan Afrilu dai shi ne ƙololuwar lokacin damina a Tanzaniya kuma a bana an sami ruwan sama mai yawa idan aka kwatanta da shekarun baya.

    Makwabciyar ƙasar Kenya ma ta fuskanci mamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, inda rahotanni suka nuna cewa aƙalla mutum 13 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu kusan 15,000 suka rasa matsugunansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

    • Ambaliyar Ghana: ‘Ruwa ya cinye gida da gonata'