Isra'ila na shirin faɗaɗa samame ta ƙasa a Gaza

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, Ahmad Tijjani Bawage and Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. An kama tsohon minista a Kenya kan zargin cin hanci

    Najib Balala

    Asalin hoton, Getty Images

    An kama tsohon ministan yawon buɗe ido a ƙasar Kenya tare da kai shi kotu bisa zargin cin hanci da rashawa.

    Ana zargin Najib Balala, da wasu tsoffin jami'ai da amfani da kuɗi fiye da kima a aikin gina kwalejin yawon buɗe ido.

    Sai dai ya musanta amfani da ofishinsa wajen biyan wasu kuɗaɗe ba bisa ka'ida ba da suka kai $21m, a cewar jaridar Nation ta ƙasar.

    Shi ne tsohon minista na farko da aka kama tun bayan zaɓen shugaban ƙasar da ya bai wa shugaba William Ruto nasara a shekara da ta gabata.

    Mista Ruto ya zo kan mulki da alwashin cewa zai yaƙi cin hanci, wanda aka daɗe ana kallon a matsayin matsala a ƙasar.

    Mista Balala ya rike mukamin ministan yawon buɗe na tsawon shekara 12 a cikin gwamnatoci uku a ƙasar, inda ya sauka a 2022 lokacin shugaba Uhuru Kenyatta ya bar mulki.

    Ya bayyana a gaban kotu a garin Malindi tare da tsohuwar sakatariyar dindindin a ma'aikatar yawon buɗe ido, Leah Gwiyo.

    Ita ma ta musanta zargin da ake yi mata, in ji jaridar Nation.

    An ba da belin dukkansu biyu kan $6,400.

    Ana sa ran sauran waɗanda ake zargi za su bayyana gaban kotu a ranar 28 ga watan Disamba.

  2. Faransa ta haramtawa ɗaliban Najeriya tafiya da Iyalensu

    France parliament

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar dokokin Faransa ta zartar da dokar hana ɗaliban Najeriya da da na sauran ƙasashe shigowa da iyalansu ƙasar.

    Bayan da aka amince da wani sabon lafazin ƙudurin, wannan matakin ya sami goyon baya daga jam'iyyar Renaissance ta shugaba Emmanuel Macron da kuma jam'iyar National Rally ta Marine Le Pen.

    Manufofin shige da ficen da aka yi wa kwaskwarima na tsaurara matakai kan haɗuwar dangi, ta hana 'yan ci-rani damar samun waɗansu ababen more rayuwa, da kuma haramta tsare yara ƙanana a wuraren tsare mutane.

    Sai dai kuma shugabanni daga kashi ɗaya bisa uku na yankunan Faransa sun bayyana ƙin aiwatar da wasu muhimman matakai na doka.

    Musamman ma, wani ɓangaren dokar yana banbance tsakanin 'yan ƙasa da baƙi, gami da waɗanda ke zaune bisa doka a Faransa, dangane da cancantar samun waɗansu fa'idoji..

  3. Isra'ila na fuskantar matsin lamba kan matsalar rashin agaji a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Yayin da aka kammala kaɗa kaɗa ƙuri'ar Majalisar Dinkin Duniya kan yunƙurin kai agaji Gaza, matsin lambar da Isra'ila ke fuskanta kan taimakon jin kai da ke shiga yankin na ƙara ƙaimi.

    Ƙungiyoyin ba da agaji na ƙasa da ƙasa sun kwashe makonni suna gargadi game da mummunan halin jin kai a yankin.

    Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta gano a ranar Alhamis cewa kusan mutane 500,000 suna fuskantar "mummunar yanayi",

    Ta ce ɗaukacin mutanen yankin kusan mutane miliyan 2.2 na fama da matsananciyar ƙarancin abinci.

    Tsirarun manyan motocin dakon kaya sun kwashi makonni suna shigo da kayan agaji zuwa Gaza daga Masar, amma a baya-bayan nan shirin samar da aminci na Majalisar Ɗinkin duniya ya kiyasta cewa kashi 10 na abincin da ake bukata a halin yanzu ne ke shiga yankin.

    A halin da a;ke ciki, Isra'ila na sanya ido kan duk wani taimako da man fetur da ake kaiwa Gaza.

  4. Mai ɗakin ɗan jarida Jamal Khashoggi ta samu mafaka a Amurka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta bai wa mai ɗakin ɗan jaridar nan Jamal Khashoggi wanda aka kashe a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Instanbul, mafakar siyasa.

    Khashoggi ya mutu ne a Oktoban 2018 kuma hukumar leƙen asirin Amurka ta ce tana ganin Saudiyya na da hannu a kisan marigayin.

    Hanan Elatr, mai ɗakin Khashoggi na fargabar tabbacin tsaronta abin da ya sa ta je Amurka a Agustan 2020 domin neman mafaka.

    BBC ta yi nazarin wasu takardu da ke nuna an ba ta mafaka ta dindindin ranar 28 ga watan Nuwamba.

    "Tabbas mun yi nasara," in ji Ms Elatr, muryarta na rawa. "Eh, sun kashe Jamal kuma sun lalata rayuwata, amma tabbas mun yi nasara."

    Fiye da shekara uku ke nan da Ms Elatr ta nemi samun mafaka a Amurka. Ta ce rayuwarta za ta kasance cikin haɗari idan ta koma Masar - ƙasar da ta fito ko Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa - gidanta na fiye da shekara 25.

  5. An amince da ƙudurin MDD kan kai agaji Gaza

    UN Security Council

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayan kwashe kwanaki ana jinkiri - kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ƙaɗa ƙuri'a kan yaƙin Isra'ila da Gaza.

    Mambobi goma sha uku ne suka kaɗa kuri'a - ciki har da Birtaniya.

    Amurka da Rasha sun ki kaɗa ƙuri'a amma ba su yi amfani da hurumin da suke da shi na kin amincewa da ƙudurin ba.

    An yi wa lafazin ƙudurin inda aka cire batun yin kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa - kuma a maimakon haka an yi kira da a samar da yanayin da hakan zai iya faruwa nan gaba.

    Rasha ta soki sauyin - tana mai cewa da gaske MDD za ta bai wa Isra'ila cikakken 'yancin walwala don ci gaba da tafka ta'adi a Zirin Gaza.

    Moscow ta gabatar da gyare-gyare don komawa zuwa lafazin ƙudurin na farko. Amma Amurka ta hana wannan yunƙurin.

    Jakadiyar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Lana Nusseibeh ta kare ƙudurin, duk da ta amince da cewa ba haka aka so ba.

    Ƙudirin ya kuma samar da wani tsarin MDD na yadda za a kula da rarraba kayan agaji.

    Da farko Washington ta yi gudun cewa hakan zai kawar da ikonda Isra'ila ke da shi kan aikin tantancewar - amma ƙudurin ya bayyana cewa zai kasance cikin tattaunawa da dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.

    Mambobi da dama sun lura cewa a karshe tasirin ƙudurin na ƙunshe ne a yadda aka aiwatar da shi a kasa - da kuma ko zai magance batun matsanancin jin kai a Gaza da ke ƙara ta'azzara.

  6. Hotuna: Yara na duba ɓaraguzai yayin da motocin kayan agaji ke jira a wajen Gaza

    Ga wasu sabbin hotuna da muka samu daga Gaza.

    Yayin da aka mayar da hankali wajen ganin kayan agaji ya shiga Zirin Gaza, hotuna sun nuna Falasɗinawa da dama na rayuwa cikin wahala.

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Motoci ɗauke da kayan agaji ke bin layi don shiga Gaza a mashigar Kerem Shalom - wani yanki da yake da iyakoki biyu: ɗaya tsakanin Zirin Gaza da Isra'ila, ɗaya kuma tsakanin Zirin Gaza da Masar.
    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Cikin Zirin Gaza, yara Falasɗinawa na bincike cikin ɓaraguzai bayan lugudan wutar Isra'ila a Rafah
    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

  7. An damƙe wata mata bisa zargin daɓa wa wani matashi wuƙa a Kano

    NIgeria police

    Asalin hoton, AFP

    Rundunar 'yan sanda a Kano ta kama wata matar aure mai suna Hafsat Sirajo mai shekaru 24 bisa zargin kashe wani matashi mai suna Nafiu Hafizu da wuƙa.

    Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel, ya gabatar da wanda ake zargin tare da wasu mutane biyu a gaban manema labarai a ranar Juma’a.

    Gumel ya ce Hafsat, wata mazauniyar Unguwa Uku da ke ƙaramar hukumar Tarauni, ta amsa laifin kashe mamacin ta hanyar daɓa masa wuƙa.

    Ya ce an kama mijinta, Dayyabu Abdullahi mai shekaru 38 da kuma mai gadinsu Malam Adam mai shekaru 65 bisa laifin taimakawa wajen ɓoye gawar don ɓoye laifin kisan kai.

    Hafsat ta shaida wa manema labarai cewa direban da ke zaune tare da su ya yi ƙoƙarin hana ta kashe kanta inda ya ƙwace wuka a hannunta.

    “Na ɗan yanke a hannuna sai ya ce in je in canza tufafina. Ina fitowa daga banɗaki na hango shi kwance sai na ɗauki wukar na daddaɓa masa,” inji ta.

    A halin da ake ciki, mahaifin marigayin, Malam Hafizu Gorondo, yana zargin cewa ma’auratan sun haɗa baki ne don kashe ɗansa saboda wasu maƙudan kuɗaɗe da yake bin mijin matar.

    Ya ce ɗansa ya shaida masa gazawar Dayyabu wanda shi ma abokin kasuwancinsa ne ya biya shi bashin N25m.

    ‘Yan sandan sun ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin bayan kammala bincike.

  8. Babban mai bincike na CBN ya zargi Emefiele da sace biliyoyin kuɗi

    CBN

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani rahoton bincike da manyan jaridun Najeriya suka samu kwafinsa ya bankaɗo yadda ake zargin tsohon gwamnan babban bankin ƙasar, Godwin Emefiele cewa ya buɗe asusun ajiya har guda dari biyar da casa`in da uku a ƙasahen Amurka da Birtaniya da kuma China.

    Rahoton wanda, shugaban hukumar bincike kan lamurran da suka shafi kuɗaɗe ta Najeriya, Jim Obazee ya jagoranta, ya bayyana cewa Emefiele ya buɗe waɗannan asusun ajiyan ne ba tare da amincewar kwamitin daraktocin bankin na CBN ba.

    An kuma gano cewa tsohon gwamnan bankin ya ɓoye fiye da fam miliyan ɗari biyar a cikin wasu asusun ajiya na ƙasar Birtaniya kaɗai.

    Rahoton bankaɗar wanda aka miƙa wa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba, ya bayyana cewa tsohon gwamnan babban bankin na CBN ya buɗe waɗannan asusun ne ajiya a mabambantan bankuna da ke Amurka da Birtaniya da kuma China.

    Rahoton ya bayar da shawarar a tsare wasu jami’an CBN da suka yi aiki da Emefiele da wasu na daban da ke da hannu dumu-dumu wajen aikata manyan laifuka masu alaƙa da badakalar kuɗaɗe.

    Idan dai za a iya tunawa, a watan Yunin wannan shekara ne shugaba Tinubu ya kafa wani kwamitin binciken babban bankin ƙasar da kuma dukkan ma'aikatansa ƙarƙashin shugaban hukumar binciken lamuran da suka shafi kuɗaɗe ta Najeriya, Jim Obazee.

  9. 'An yi wa sanarwar Fafaroma ta saka wa masu neman jinsi ɗaya albarka mummunar fahimta'

    Gamayyar limaman ɗarikar Katolika a Najeriya ta ce an yi wa sanarwar da fadar Fafaroma ta fitar na cewa ya amince limaman ɗarikar su saka wa masu neman jinsi ɗaya albarka, mummunar fahimta.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta Catholics Bishop Conference of Nigeria ta ce albarkar da ake nufi albarka ce ta gama-gari irin wadda ake iya saka wa kowaye ba tare da la’akari da zamansa salihi ko fasiƙi ba.

    Sanarwar ta ƙara jaddada cewa dokokin ɗarikar ba su sauya kan cewa auren jinsi ya saɓa wa dokokin ubangiji ba.

    Ku latsa ƙasa don sauraron tattaunawar da Haruna Shehu – Tangaza ya yi da Rabaran John Joseph Hayep, shugaban ƙungiyar Kiristoci reshen jihar Kaduna.

    Bayanan sautiLatsa sama don sauraron rahoton
  10. Kotun ƙoli ta tabbatar da zaɓen gwamna Peter Mbah na Enugu

    Peter Mbah

    Asalin hoton, PETER MBAH/FACEBOOK

    Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da zaɓen da aka yi wa Peter Mbah na jam'iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Enugu a zaɓen gwamnan jihar na watan Maris.

    Kotun ta yanke wannan hukunci ne a zaman da ta yi yau Juma'a.

    A lokacin zaman nata, ɗaukacin alƙalai biyar na kotun sun yi watsi da ƙarar da jam'iyyar LP da ɗan takararta na gwamnan jihar, Chijioke Edeoga suka ɗaukaka suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen na ranar 18 ga watan Maris.

    Kotun ta bayyana cewa babu wata hujja ƙwaƙƙwara da aka gabatar wadda zai sanya ta ta soke hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara da kuma na kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar ta Enugu, waɗanda dukkanin su suka tabbatar da nasarar ta Mbah.

    Sakamakon zaɓen gwamnan na jihar Enugu da Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta fitar dai ya nuna cewa Peter Mbah shi ne ya lashe zaɓen da ƙuri'u 160,895.

  11. Ƴan sanda a Kano na neman ƴan daba 72 ruwa-a-jallo

    CP Muhammad Hussaini Gumel

    Asalin hoton, facebook/Abdullahi Haruna Kiyawa

    Bayanan hoto, CP Muhammad Hussaini Gumel

    A jihar Kano, jami'an 'yan sanda sun ayyana neman wasu mutum saba'in da biyu ruwa a jallo bisa zargin aikata laifin fashi da makami da aikata daba.

    Mutanen suna cikin tubabbun 'yan daba 623 da suka mika wuya ga 'yan sanda a kwanakin baya, karkashin shirin zaman lafiya da yi musu afuwa.

    'Yan sanda sun ce sun gano wani da ya mika kansa a baya, a yanzu yana jagorantar gungun wasu matasa suna tayar da hankalin mutane a unguwanni da dama ciki har da yankin Dala.

    Kwamishinan ƴan sanda a jihar ta Kano, CP Muhammad Hussaini Gumel ya ce wadanda ba su fandare ba za su taimaka musu su zama masu amfani a cikin al’umma:

  12. Falasɗinawa za su fuskanci matsalar yunwa idan aka ci gaba da yaƙi – MDD

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Al'ummar Falasɗinu kusan 500,000 na fuskantar mummunan yanayi kamar yadda hukumart samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana.

    Ta ce Falasɗinawa za su ci gaba da fuskantar haɗarin yunwa idan aka ci gaba da yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas.

    Hukumar ta ce galibin al'ummar yankin da suka kai miliyan 2.2 na fama da ƙarancin abinci.

    "Babu wani da ya tsira daga yunwa a Gaza," in ji Cindy McCain daga hukumar samar da abinci ta MDD.

  13. Isra'ila na shirin faɗaɗa samame ta ƙasa a Gaza

    Isra'ila ta bayyana kudirinta na faɗaɗa yaƙin da take ta ƙasa a tsakiyar Gaza.

    Ta ba da umarnin mutane su fice daga Al-Bureji inda ta nemi su nausa kudancin yankin.

    Tun farko, ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta ce sojojin Isra'ila suna ci gaba da tsare takwas daga cikin ma'aikatanta da aka kama yayin wani samamen cikin dare da aka kai kan sansanin Jabalia a arewacin Gaza.

    Gaba a yau kuma, ana sa ran kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya zai kaɗa ƙuri'a da ta yi ta fuskantar tsaiko kan shigar da kayan agaji zuwa Gaza da kuma ƙoƙarin samar da yanayin ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta.

  14. An kafa kwamatocin yaƙar satar ɗanyen mai da inganta tattalin arzikin Najeriya

    ...

    Asalin hoton, @stanleynkwocha_/X

    Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima da gwamnonin ƙasar sun kafa kwamatoci kan satar ɗanyen mai da kuma na harkokin tattalin arziki.

    An ɗauki matakin ne a taron majalisar tattalin arziki ta Najeriya karo na 138 wanda aka yi ta intanet ranar Alhamis.

    A cewar sanarwar da mai taimaka wa mataimakin shugaban Najeriyar kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya fitar, kwamatocin za su kasance ƙarƙashin shugabancin gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdurrazak da takwaransa na jihar Imo, Hope Uzodinma.

    Ya ce an yi taron ne bayan tattaunawar da aka yi game da matsalolin da suka shafi tattalin arziki da kuma nazari kan tsare-tsaren magance matsin tattalin arziki na gajere da dogon zango.

    Kwamitin inganta tattalin arzikin yana da alhakin samar da tsarin kula da batun cire tallafin mai da bijiro da tsarin kare tattaunawar albashin ma'aikata da batun hauhawar farashin kayayyaki da sauran lamuran da suka danganci tattalin arziki.

    Mambobin kwamitin sun haɗa da gwamnan jihar Gombe mai wakiltar arewa maso gabas da gwamnan Legas mai wakiltar kudu maso yamma sai gwamnan Akwa Ibom mai wakiltar kudu maso kudu da gwamnan Anambra mai wakiltar kudu masu gabas da gwamnan Neja mai wakiltar arewa ta tsakiya da gwamnan Kaduna mai wakiltar arewa maso yamma.

    ..

    Asalin hoton, @stanleynkwocha_/X

    A ɗaya ɓangaren, kwamitin da aka kafa wanda zai kula da ɗanyen mai da magance satar shi zai zama a ƙarƙashin jagorancin gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.

    Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da gwamnan Ogun mai wakiltar Kudu ta yamma da gwamnan Plateau mai wakiltar arewa ta tsakiya sai gwamnan Rivers mai wakiltar kudu maso kudu da gwamnan Borno mai wakiltar arewa maso gabas sai gwamnan Jigawa mai wakiltar arewa maso yamma da gwamnan Abia mai wakiltar yankin kudu maso gabas sai ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare da ministan kuɗi da gwamnan babban bankin ƙasa sai shugaban kamfanin NNPCL da shugaban hukumar raya yankin Neja Delta, NDDC da manyan hafsoshin tsaro.

  15. An dakatar da likitan da ya naushi mara lafiya yana tsaka da yi mata tiyata

    ...

    Asalin hoton, WEIBO

    Hukumomin China suna gudanar da bincike a wani asibiti inda aka samu wani likita da ake zargi da naushin mara lafiyar da yake tsaka da yi wa tiyata.

    An ga lamarin ne cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta a China, lamarin da ya fusata al'ummar ƙasar.

    Asibitin na Aier China ya dakatar da likitan tare da korar shugaban asibitin da lamarin ya faru a 2019.

    BBC ta tuntuɓi asibitin domin jin ta bakinsu.

    Bidiyon ya nuna yadda likitan yake naushin mara lafiyar a ka sau uku yayin da yake tiyata a idonsa.

    Aeir China da ke tafiyar da asibitocin ido da dama, ya ce lamarin ya faru ne lokacin wata tiyata a asibitinsa da ke Guigang a kudu maso yammacin China.

    Mara lafiyar mace ce ƴar shekara 82 kuma yayin tiyatar saboda allurar kashe zafi da aka yi mata, ta sa a lokuta da dama ta yi ta motsa kanta da kuma ƙwayar idonta, kamar yadda wata sanarwa daga asibitin ta bayyana.

    Hukumomi a yankin sun ce mara lafiyar ta ji rauni a goshinta. Kuma ba ta jin wani yaren sai na garinsu sannan ba ta gane gargaɗin da likitan yake mata ba a harshen Mandarin, lamarin da ya sa likitan ya yi yadda yake so da ita a lokacin gaggawa.

    Bayan tiyatar, asibitin ya nemi afuwa tare da biyan yuan 500 - kwatankwacin dala 70 a matsayin diyya, a cewar ɗan matar wanda ya yi wa kafafen yaɗa labaran ƙasar bayani.

    Ya kuma ce mahaifiyarsa a yanzu ba ta gani da idonta na hagu, sai dai babu tabbacin ko hakan ya faru ne saboda lamarin da ya faru.

    A jiya Alhamis ne aka sanar da korar shugaban asibitin na Guiyang da kuma dakatar da likitan - wanda shi ma babban jami'i ne a asibitin saboda take ƙa'idojin aiki.

    Duk da lamarin ya faru a Disambar 2019, batun ya fito fili ne a wannan makon bayan fitacciyar likita a China, Ai Fen ta wallafa bidiyon tiyatar da na'urar CCTV ta naɗa.

    Dr Ai, wadda ke cikin tawagar likitocin da suka ankarar da jama'a kan ɓarkewar cutar korona a Wuhan, ta wallafa bidiyon a shafinta na Weibo inda mabiya sama da miliyan biyu suka kalla.

  16. Gini ya danne mata biyu da jariri a Legas

    ..

    Asalin hoton, Lagos State Government

    Hukumar kashe gobara da kai ɗaukin gaggawa ta jihar Legas ta ce yanzu haka tana ƙoƙarin ceto wasu mata biyu da jariri waɗanda gini ya rufta ma wa a unguwar Ebuta Meta da ke birnin Ikko.

    A cikin wata sanarwa da shugabar hukumar, Margaret Adeseye ta fitar a safiyar yau Juma'a, ta ce sun kai ɗaukin ne bayan samun kira na neman ɗauki daga wani gida a layin Herbert Macaulay Way a unguwar ta Ebuta Meta da misalin ƙarfe 9 na safe, inda aka sanar da su game da rugujewar ginin mai hawa ɗaya.

    Yayin da ake ƙoƙarin aikin zaƙulo waɗanda suka rage ƙaƙashin ɓaraguzai, an samu nasarar ciro wata mace ɗaya wadda ba ta jigata ba.

    ..

    Asalin hoton, Lagos State Government

  17. Falasɗinawa kusan 400 aka kashe cikin kwanaki biyu – Hamas

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas da ke Gaza ta ce kusan Falasɗinawa 400 aka kashe a Zirin Gaza cikin kwanaki biyu da suka gabata.

    Hamas ta ce a jumulla mutum 390 ne suka mutu, wasu ƙarin 734 suka jikkata.

    Tun bayan ɓarkewar rikicin ranar 7 ga watan Oktoba, ma'aikatar lafiyar ta ce fiye da mutum 200,000 aka kashe.

    BBC ba ta iya tantance ikirarin yawan Falasɗinawan da suka mutu ba.

  18. Yau ne wa'adin ficewar dakarun Faransa daga Nijar ya cika

    ...

    Asalin hoton, Gwamnatin Nijar

    A yau Juma'a ne wa'adin da aka bai wa dakarun Faransa na su fice daga Jamhuriyar Nijar ke cika.

    Sojojin Nijar da suka hamɓarar da mulkin Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yuli ne suka bai wa sojojin na Faransa umarnin kwashe nasu-ya-nasu daga ƙasar.

    Faransa ta soma janye dakarunta 1,400 daga Nijar a watan Oktoba.

    Akwai ƙasa da dakarun Faransa 200 da suka rage a Nijar kuma ana sa ran za su bar ƙasar a yau ko kuma zuwa ƙarshen shekarar nan.

    An yi wa janyewar tsari mai kyau sannan an yi shi lafiya bisa goyon bayan sojojin Nijar da ke mulki.

    Zuwa yanzu, babu wata jayayya daga ɓangarorin biyu.

    An girke sojojin Faransa a Nijar a wani ɓangare na yaƙar ƙungiyoyi masu iƙirarin Jihadi.

    A baya-bayan nan ne kuma Faransa ta sanar da rufe ofishinta na jakadanci a Nijar saboda rashin damar samun aiwatar da ayyukanta tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar.

    A cikin wata wasiƙa da jakadan Faransa na Nijar ɗin ya aika wa ma'aikatan ofishin ya ce hukumomi sun kasa amsa kiraye-kirayen neman ba da damar ci gaba da ayyukan ofishin.

  19. Ƴan sanda na binciken ɗan bindigar da ya kashe mutum 14 a Czech

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Ƴan sanda a Jamhuriyar Czech na gudanar da aikin bankaɗo abin da ya janyo ibtila'in harbin kan mai uwa da wabi mafi muni a ƙasar inda wani ɗalibi ya buɗe wuta a wata jami'a da ke tsakiyar Prague, lamarin da ya halaka mutum 14 da raunata 25.

    Shugaban Czech Petr Pavel ya roƙi haɗin kan jama'a inda ya ce bai kamata a yi amfani da kashe-kashen ba a matsayin wata dama ta sukar ƴan siyasa da yaɗa labaran ƙarya.

    Tuni hukumomi a ƙasar suka ayyana gobe Asabar a matsayin ranar makoki.

    Mr Pavel ya bayyana kaɗuwarsa da takaici kan yadda aka samu asarar ran mutane ta wannan hanya.

    An yi amanna ɗan bingidagr wanda 'yan sanda suka ce an hallaka shi, ya kuma kashe mahaifinsa sannan ana ganin kila shi ya kashe wasu mutum biyu a makon da ya gabata.

    Ƴan sanda sun ce ɗan bindigar mai shekara 24 ɗalibi ne a jami'ar kuma babu wasu bayanai da suka nuna cewa an taɓa samun sa da hannu a aikata wani laifi duk da cewa ƴan sandan sun ƙara da cewa an gano tulin makamai da alburusai.

    An bayyana sunansa a matsayin David Kozak.

    Kafin harbe-harben, ƴan sanda sun samu rahoto cewa ana tunanin wanda ake zargin yana kan hanyar zuwa Prague daga wani gari da ke kusa da nufin halaka kansa.

    Ƴan sanda sun kwashe mutane daga wani gini na jami'ar inda ake tunain ɗan bindigar zai halarci karatu sai dai daga baya an kira su zuwa wani gini na daban.

  20. Alƙaluman marasa aikin yi a Najeriya ya ƙaru in ji NBS

    ..

    Asalin hoton, GETTY IMAGES

    Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta ce an samu ƙari kan yawan mutanen da ba su da aikin yi zuwa kashi 4.2 cikin 100 a cikin watanni shida na farkon shekarar 2023 daga kashi 4.1 cikin 100 a watanni ukun farko na shekarar nan.

    NBS ta bayyana haka ne a alƙaluman da ta fitar game da yanayin ayyukan yi a bana.

    A cewar hukumar, rashin aikin yi a tsakanin maza ya kai kashi 3.5 cikin 100 yayin da a ɓangaren mata ya kai kashi 5.9 cikin 100 a watanni shidan farko na 2023.

    Rahoton ya kuma nuna cewa a tsukin watanni shidan na farko, yawan masu aikin da bai kai su biya buƙatunsu ba ya kai kashi 11.8 cikin 100, inda alƙaluman ya yi ƙasa daga kashi 12.2 cikin 100 na watanni ukun farko na 2023.

    "Game da alƙaluman matasa masu aikin yi ƴan tsakanin shekara 15-24 ya kai kashi 7.2 cikin 100 a tsukin wata shidan farko na bana.