An kama tsohon minista a Kenya kan zargin cin hanci

Asalin hoton, Getty Images
An kama tsohon ministan yawon buɗe ido a ƙasar Kenya tare da kai shi kotu bisa zargin cin hanci da rashawa.
Ana zargin Najib Balala, da wasu tsoffin jami'ai da amfani da kuɗi fiye da kima a aikin gina kwalejin yawon buɗe ido.
Sai dai ya musanta amfani da ofishinsa wajen biyan wasu kuɗaɗe ba bisa ka'ida ba da suka kai $21m, a cewar jaridar Nation ta ƙasar.
Shi ne tsohon minista na farko da aka kama tun bayan zaɓen shugaban ƙasar da ya bai wa shugaba William Ruto nasara a shekara da ta gabata.
Mista Ruto ya zo kan mulki da alwashin cewa zai yaƙi cin hanci, wanda aka daɗe ana kallon a matsayin matsala a ƙasar.
Mista Balala ya rike mukamin ministan yawon buɗe na tsawon shekara 12 a cikin gwamnatoci uku a ƙasar, inda ya sauka a 2022 lokacin shugaba Uhuru Kenyatta ya bar mulki.
Ya bayyana a gaban kotu a garin Malindi tare da tsohuwar sakatariyar dindindin a ma'aikatar yawon buɗe ido, Leah Gwiyo.
Ita ma ta musanta zargin da ake yi mata, in ji jaridar Nation.
An ba da belin dukkansu biyu kan $6,400.
Ana sa ran sauran waɗanda ake zargi za su bayyana gaban kotu a ranar 28 ga watan Disamba.





















