Shugaban Falasɗinawa Abbas ya ɗora alhakin 'kisan yaran Gaza' a kan Amurka

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Babu abin da ake ji a Rafah sai ƙarar hare-hare - MDD

    e

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Yau da safe kenan lokacin da jami'ai na ƙoƙarin kashe wuta a wani gida a Khan Younis

    Wani jami'in Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijirar Falasɗinawa ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA, daga birnin Rafah na kudancin gaza, ya ce fararen hula cikin 'mawuyacin hali' a yankin.

    Yayin da yake bayyana abin da ya gani a lokacin da ya je wata cibiyar rabon tallafi a Rafah ranar Juma'a, Tom White ya ce ''babu abin da ke kake ji a birnin sai ƙarar hare-hare''.

    Ya ce tsagaita wuta na da matuƙar muhimmanci, domin kuwa a cewarsa ''a Rafah akwai ɗaruruwan mutanen da ke kwana a waje, muna fuskantar ƙarancin ruwan sha, duk wanda ka gani a gefen titi na neman abincin da zai bai wa 'ya'yansa su ci''.

    "Gidajenmu sun cika da mutane, za ka samu daruruwan mutane na amfani da ban ɗaki guda ɗaya''.

    "In ma bom bai kashe su ba, to cutuka za su kashe su, saboda yadda mutane ke kwana a kan tituna."

    Ya kuma ce ya samu labarin cewa jiya da daddare an kai hari kan gidan da suka sauka a lokacin da suka je cibiyar.

  2. Ra'ayi Riga: Kan harin Tudun Biri

    Shirin Ra'ayi Riga na wannan makon ya duba harin jirgin sojojin Najeriya kan masu Maulidi a garin Tudun Biri, wanda hukumomi suka ce 'kuskure' ne.

    Me ya kamata a yi don bi wa waɗannan mutane haƙƙinsu, kuma waɗanne matakai ya kamata a ɗauka domin hana sake faruwar hakan?

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  3. Ba a gina matatun mai don rage farashin fetur ba - NNPCL

    d

    Asalin hoton, NNPCL/X

    Bayanan hoto, Shugaban NNPCL, Mele Kyari

    Shugaban babban kamfanin mai na Najeriya NNPCL, Mele Kyari ya ce ba rage farashin man fetur ba ne babban maƙasudin gina matatun mai a ƙasar ba, sai dai ya ce wataƙila hakan ka iya faruwa.

    Mele Kyari ya faɗi hakan ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin tsare-tsare da kasafin kuɗin majalisar dokokin ƙasar bisa gayyatar da majalisar ta yi masa.

    Shugaban na NNPCL ya kuma ce ayyukan sabbin matatun za su inganta tare da haɓaka samar da man fetur a ƙasar cikin shekarar 2024, ta yadda ƙasar za ta zama babbar mai fitar da man fetur a shekara mai kamawa.

    Ya kuma sake jaddawa cewa a yanzu kamfanin ne ke gudanar da harkokinsa ba tare da samun tallafin sisin kobo daga gwamnatin tarayya ba.

    A ranar Laraba ne dai majalisar dattawan ta bai wa shugaban na NNPCL wa'adin sa'o'i 24 da ya bayyana a gabanta, yayin da a baya ya sha yin watsi da gayyatar da kwamitocin wucin-gadin majalisar ke yi masa, kan yadda kamfanin ya kashe naira tiriliyan 11 wajen gyara da kula da matatun man fetur na ƙasar tsakanin shekarar 2010 zuwa 2023.

    A shekarar 2022 ne dai gwamnatin tarayya ta bai wa kamfanin cin gashin kansa, domin haɓaka tare da inganta harkokin man fetur a ƙasar.

    A lokacin da yake gabatar da jawabi bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban ƙasar cikin watan Mayu, Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, lamarin da ya haifar da tashin farashin man a faɗin ƙasar.

    Wani abu kuma da masana ke cewa ya janyo hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar, wadda ta fi kowacce yawan jama'a a nahiyar Afirka.

  4. An yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin rai da rai a Amurka

    An yanke wa wani matashi a jihar Michigan ta Amurka hukuncin ɗaurin rai da rai ba tare da saki ba bayan samunsa da laifin harbe wasu ɗalibai huɗu a 2021.

    Ethan Crumbley, na da shekara 15 a lokacin da ya yi harbin da wata 'yar ƙaramar bindiga wadda aka yi zargin cewa mahaifinsa ya ba shi ita a lokacin bikin kirsimeti na shekarar.

    An zargi malaman makarantarsa da nuna halin ko in kula da halayyar yaron.

    Da yake jawabi kafin yanke hukunci a kotun, Ethan Crumbley ya nemi afuwa a kan abin da ya aikata.

  5. An soki Amurka kan daƙile ƙudurin tsagaita wuta a Gaza

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Kungiyoyin kare hakkin bil-adama sun soki Amurka kan matakin da ta ɗauka na daƙile wani ƙudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya buƙaci a gaggauta tsagaita wuta a Gaza.

    Amnesty International ta ce matakin ya nuna rashin mutunta girman wahalhalun da fararen hula ke ciki.

    Haka kuma ita ma ƙungiyar agaji ta likitocin Doctors Without Borders, ta bayyana ƙuri'ar a matsayin cin zarafin bil'adama.

    Amurka ta ce ba ta goyon bayan tsagaita wutar saboda a ganinta wannan ƙuduri ba shi da ''daidaito sannan kuma yana kauce wa gaskiya''.

    Shima jakadan Amurka a kwamitin Robert Wood, ya ce ƙudurin zai bai wa ƙungiyar Hamas damar ƙara kai hare-hare kan Isra'ila.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a wannan safiya, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kada ku manta da tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.

    Ku biyo mu...