Shugaban Falasɗinawa Abbas ya ɗora alhakin 'kisan yaran Gaza' a kan Amurka

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Asuba ta gari

    Nan za mu rufe wannan shafi na rahotonni kai-tsaye a yau Asabar.

    Za mu kawo wasu a wani shafin daban gobe Lahadi.

    Da fatan za mu kwana lafiya.

  2. Sama da rabin mazauna Gaza na fama da yunwa

    Khan Younis

    Asalin hoton, Reuters

    Babban jami'i a hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya yi gargadin cewa rabin al'ummar Gaza na fama da yunwa, yayin da tara cikin mutum 10 ba su cin abinci a rana.

    Mataimakin shugaban hukumar samar da abinci ta MDD, ya ce kayan abinci da aka samu sun yi kadan saboda yanayin rikicin da ake gwabzawa a wasu yankunan Gaza sun hana kayan agaji shiga.

    Wakilin BBC ya ce daga arewa zuwa kudancin Gaza, sojojin Isra'ila sun ragargaje ko'ina.

    Cikin dare an kai wadanda suka ji raunuka daga harin sojin Isra'ila asibitin Naser.

    Kungoyoyin agaji sun ce da dama daga cikin mutanen da harin bm bai kashe su ba, za su iya mutuwa saboda tsananin yunwa.

  3. Shugaban Falasɗinawa Abbas ya ɗora alhakin 'kisan yaran Gaza' a kan Amurka

    Mahmoud Abbas

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Mahmoud Abbas ne jagoran Hukumar Falasɗinawa ta PA a ƙarƙashin jam'iyyar Fatah - wadda ke mulkin yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, ban da Gaza

    Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya zargi Amurka da tafka laifukan yaƙi sakamakon gagarumin goyon bayan da take bai wa Isra'ila a yaƙin da take yi a Zirin Gaza.

    Bayan ta ƙi amincewa da ƙuri'ar tsagaita wuta a Gaza wadda Kwamitin Tsaro na MDD ya bukata, Abbas ya ce ya ɗora alhakin zubar da jinin yara ƙanana da mata da kuma tsofaffin Falasdinawa kan Washington.

    Ma'aikatar lafiya a Zirin Gaza ƙarƙashin Hamas ta bayyana cewa sama da farar hula 17,700 ne suka rasa rayukansu tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba.

    An kaɗa ƙuri'ar neman tsagaita wutar ce bayan Babban Sakataren MDD Antonio Gutteres ya yi amfani da damarsa ta Aya ta 99 don neman Kwamitin Tsaron ya ɗauki mataki kan yaƙin.

  4. Al'ummar Gaza na gab da ɓalɓalcewa - MDD

    Gaza

    Asalin hoton, Ashraf Amrah/ UNRWA

    Bayanan hoto, Ɗaruruwan Falasɗinawa ne suka taru a ƙofar ofishin ajiyar kayayyaki na UNRWA da ke Gaza

    Hukumar bai wa Falasɗinawa agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce al'ummar da ke rayuwa a Zirin Gaza na gab da "aukawa cikin ɓalɓalcewa".

    Cikin wani saƙo a dandalinta na X, UNRWA ta ce "muna aiki da sauran abokan aiki wajen rarraba 'yan kayan da suka rage a hannunmu, amma fa saura su ƙare".

    "Idan UNRWa ta gaza, to aikin taimaka wa Falasɗinawa ma ya ƙare," kamar yadda ta bayyana.

    Hukumar ta kwana biyu tana gargaɗi game da yanayin da ake ciki a Gaza, wanda ta bayyana shi da "bala'i".

  5. Bournemouth ta kunyata Man United a Old Trafford

    Man United

    Asalin hoton, PA Media

    Manchester United ta yi rashin nasara a hannun Bournemouth da ci 3-0 a wasan mako na 16 a gasar Premier League ranar Asabar a filin wasa na Old Trafford.

    Dominic Solanke ne ya fara cin kwallo a minti na biyar da take leda, haka suka je hutu ana cin United 1-0.

    Da suka koma zagaye na biyu ne Bournemouth ta kara ƙwallayen a raga ta hannun Philip Billing da kuma Marcos Senesi.

    Wannan ne karon farko da aka ci United kwallo uku ko fiye da haka a Premier League a Old Trafford a wasa tsakaninta da wadda take cikin 'yan 10 na karshe a teburi.

    Wannan shi ne karon farko da Bournemouth ta ci wasa a mako na 16 a Premier League, bayan da ta kasa yin abin kirki a 2019/20 da kuma a 2022/23.

  6. 'Yanzu kuɗi ba su da daraja a Zirin Gaza'

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Sashen Larabci na BBC ya yi hira da mazauna Zirin Gaza, waɗanda hare-haren Isra'ila suka raba da muhallansu.

    Cikinsu akwai Khaled, wanda ya ce an tilasta masa sauya wurin ɓuya har sau shida tun bayan fara yaƙi tsakanin Hamas da Isra'ila.

    "Babu wani wuri guda ɗaya tal da yake da aminci," kamar yadda ya yi bayani, yana mai cewa babu ruwan sha ko abinci, ko kuma gas ɗin girki.

    Hatta waɗanda ke da kuɗi a hannunsu ba za su iya amfani da su ba, in ji shi, saboda ƙarancin abubuwan da za a iya sayen.

    "Waɗanda ba su mutu ba saboda hare-hare za su iya mutuwa saboda rashin abbubwan da rayuwa ke buƙata. Lamarin bala'i ne kawai," a cewarsa.

    Wani mutumin ya bayyana cewa ya sauya wurin zama sau huɗu, kuma yana cikin waɗanda aka tilasta musu barin arewacin Gaza a farko-farkon yaƙin.

    Yanzu yana zaune asibitin European Hospital da ke Khan Younis a kudancin Gaza, inda ya ce mutane na fama da yunwa.

    "Farashi ya yi mummunan tashi kuma mutane ba su ma da kuɗin da za su iya sayen wani abu," in ji shi.

  7. Yi wa doki wanka da ziyarar Malala cikin hotunan Afirka

  8. Labarai da dumi-dumi, Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce an kashe Falasɗinawa 17,700 zuwa yanzu

    Ma'aikatar lafiya ta Zirin Gaza ƙarƙashin Hamas ta fitar sabbin alƙaluman mutunen da ta ce hare-haren Isra'ila sun kashe.

    Jami'ai a yankin sun ce zuwa yanzu mutanen da aka kashe sun kai 17,700 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

  9. Liverpool ta koma ta dayan teburin Premier kafin wasan Arsenal

  10. NNPCL ya gano haramtattun bututan mai fiye da 4,800 a Najeriya - Mele Kyari

    Fetur

    Asalin hoton, X/Mele Kyari

    Kamfanin man fetur na Najeriya ya ce ya gano bututan mai haramtattu har 4,800 zuwa matatun mai daban-daban a ƙasar.

    "Mun gano sama da 4,800 na haramtattun bututan mai. A tsakanin tsawon kilomita 100, ana iya samun ƙunshin fayif 300," in ji shugaban kamfanin na Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL), Mele Kyari, lokacin da ya bayyana a gaban kwamatin majalisar dattawa ranar Juma'a.

    "Saboda haka, ko da an samar da man, ba za a iya isar da shi da ƙarfin da ya dace ba, kuma yawansa ma zai ragu."

    A cewar shugaban na NNPCL, wasu mutanen daga maƙwabtan ƙasashe kan je su jona bututai ba bisa ƙa'ida ba a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur.

    Lamarin na zuwa ne kusan shekara ɗaya bayan kamfanin ya gano haramtattun bututai 295, abin da ke bayyana irin asarar da Najeriya ke yi saboda satar mai.

    Shekara biyu da suka wuce Kyari ya ce ƙasar na yin asarar gangar mai 200,000 a kullum, wanda darajarsa ta kai dala miliyan 13, saboda lalata bututai da kuma satar man.

  11. 'Yan sandan Landan sun kama mutum a wurin zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa

    Landan

    Asalin hoton, Reuters

    A Birtaniya, dubun dubatar magoya bayan Falasɗinawa ne suka yi maci a tsakiyar birnin Landan don neman a tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila take yi a Zirin Gaza.

    'Yan sanda sun ce yayin da ake fara zanga-zangar, sun kama wani mutum ɗauke da kwali mai rubutun wani saƙo da ke kwatanta Isra'ila da gwamnatin Nazi ta Jamus.

    "An kama shi ne saboda zargin ta'azzara tunziri ta hanyar kalaman wariya," a cewar rundunar 'yan sandan a shafinta na sada zumunta.

    Haka nan, an yi irin wannan zanga-zanga a wurin taron sauyin yanayi na COP28 da ke gudana a Dubai.

    Landan

    Asalin hoton, Reuters

  12. Isra'ila ta zargi Hamas da amfani da makarantu da masallatai don shirya hare-hare

    fg

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Isra'ila sun zargi Hamas da amfani da ''gine-ginen fararen hula'' wajen shirya tare da ƙaddamar da hare-haren rokoki zuwa Isra'ila

    Sun ce ƙungiyar na amfani da makarantar UNRWA da wani masallaci a Beit Hanoun da ke arewacin Gaza wajen kai hari kan sosjojin na Isra'ila.

    Daraktar yaɗa labarai na UNRWA, Juliette Touma ta shaida wa BBC cewa ba za ta iya tabbatar da wannan iƙirari ba, saboda a cewarta Isra'ila ta yi luguden bom a kusa da yankin.

    Amma ta jaddada cewa dole a kare makarantu a koyaushe ba za a taɓa amincewa a yi amfani da su don ayyukan soji ko faɗa ba.''

  13. An kashe ɗan Isra'ila da ake garkuwa da shi a Gaza

    Daya daga cikin Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da shi a Gaza, Sahar Baruch ya mutu.

    An kashe matashi mai shekara 25 a Gaza, kamar yadda dangin iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su daga kibbutz suka bayyana a cikin sanarwar da suka fitar.

    “Za mu buƙaci a dawo mana da gawarsa a wani ɓangare na kowace yarjejeniyar musayar fursunoni da za a ƙulla a nan gaba. Ba za mu daina ba har sai kowa ya dawo gida,'' in ji sanarwar.

    Labarin mutuwar matashin na zuwa ne bayan da mayaƙan Hamas suka fitar da wani bidiyo ranar Juma'a da ke nuna irin ɓarnar da suka ce harin da Isra'ila ta kai a yunƙurinta sakin fursunonin ya haddasa.

  14. 'DSS za ta fara amfani da makaman da jami'anta suka ƙera'

    d

    Asalin hoton, DSS

    Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya (DSS) ta ce nan ba da jimawa ba za ta fitar da makaman da jami'anta suka ƙera.

    Darakta Janar na hukumar, Yusuf Bichi ne ya bayyana haka ranar Asabar, a wajen bikin yaye tawagar jami'an da suka samu horo na musamman kan tattara bayanan sirri a Abuja babban birnin ƙasar.

    Bichi ya ce nan ba da jimawa ba, DSS za ta fara ''ƙera abin da za ta yi amfani da shi, sannan ta yi amfani da abin da ta ƙera''.

    Ya ƙara da cewa ''daga cikin makaman da hukumar ke shirin fitarwa, har da jirage marasa matuƙa''.

    Daraktan hukumar ya kuma ce DSS za ta ci gaba da tallafa wa cibiyar nazarin harkokin tsaro ta ƙasar domin samun nasarar yaɗa iliman da za su taimaka wajen tabbatar da tsaro a ƙasar.

    Ya kuma yi kira ga jami'an da suka yaye da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen kare ƙasar daga ayyukan ɓata-gari.

  15. 'Mun shafe kwanaki babu ruwan sha da abinci a Jabalia'

    .

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Sojojin Isra'ila da ke kai hare-hare a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia.

    Ayyukan tallafi a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza na ci gaba da taɓarɓarewa.

    Cikin kwanaki biyar da suka gabata, tankokin yaƙin Isra'ila sun yi wa sansanin ƙawanya, inda dubban mutane ke cikinsa.

    Wakilin BBC ya ce ya samu saƙon kar-ta-kwana daga wani mazaunin sansanin da safiyar yau Asabar, wanda a ciki ke cewa sun shafe kwana biyar babu abinci,babu ruwan sha.

    Kuma gomman irin waɗannan saƙonni sun ishe wasu gidajen radiyon da ke aiki a kudancin Gaza, kan yadda sojojin Isra'ila ke ci gaba da kai samame sansanin 'yan gudun hijirar na Jabalia.

    Wani ɗan gwagarmaya da ke sansanin mai suna Islam Badr, ya aike da wani saƙon sautin murya da a ciki ke cewa: ''A yanzu da misalin ƙarfe 8;00 na safiyar Asabar, Sojojin Isra'ila na ci gaba da kai hare-haren boma-bomai sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia''.

    Kawo yanzu babu wani tallafi da ya kai arewacin Gaza ko birnin Gaza tun bayan katse yarjejeniyar tsagaita wuta.

  16. Jakadiyar Amurka za ta gana da Tinubu da Ecowas kan matsalar Nijar

    d

    Asalin hoton, X/Tinubu/ Others

    Mataimakiyar sakataren harkokin ƙasashen Afirka ta Amurka, Molly Phee ta ziyarci Najeriya domin shiga tsakani kan rikicin shugabancin Nijar, wadda ke ƙarƙashin mulkin soji tun ranar 26 ga watan Yuli.

    A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta nuna cewa Ms Phee za ta tattauna da shugaban Najeriya Bola Tinubu, tare da shugabannin ƙungiyar Ecowas kan rikicin siyasar Nijar.

    Sanarwar ta ce an tsara ganawa tsakanin jakadiyar Amurkan da shugabanin ƙasashen ƙungiyar Ecowas ranar Litinin 10 ga watan Disamba domin tattauna batun.

    “A lokacin ziyarar tata, za ta tattauna da shugabannin Afirka da Yamma, kan yadda Amurka za ta tallafa wajen maido da mulkin dimokraɗiyya a jamhuriyar Nijar, tare da inganta tsaro da zaman lafiya da ci gaban yankin, da kuma tabbatar da dimokraɗiyya a yankin sahel,'' kamar yadda sanarwar ta nuna.

    Ziyarar Ms Phee Najeriya na zuwa ne watanni huɗu bayan da sojojin Nijar ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani suka kifar zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum.

    Juyin mulkin na ranar 26 ga watan Yuli ya sha suka da Allah wadai daga ƙasashen duniya, yayin da ƙasashen Yamma suka nuna goyon bayansu ga ƙungiyar Ecowas da ta AU, waɗanda suka nuna adwarsu ga juyin mulkin.

    Inda ƙungiyar Ecowas ƙarƙashin jagorancin shugaban Najeriya Bola Tinubu ta ƙaƙaba wa Nijar jerin takunkuman karya tattalin arziki, don tilasta wa sojojin mayar da shugaba Bazoum kan karagar mulki.

  17. Lafiya Zinariya: Cutukan da uwa za ta iya yaɗa wa jaririnta

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  18. Mene ne ya faru a kwamitin tsaro na MDD?

    c

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, António Guterres ya ce mutanen Gaza na cikin tsananin “neman sa'ida”

    A jiya ne kamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kaɗa ƙuri'ar neman gaggauta tsagaita wuta a Zirin Gaza.

    Kafin kaɗa ƙuri'ar - wadda ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa tare da wasu ƙasashe 97 suka buƙata - babban sakataren MDD, António Guterres ya ce al'ummar Gaza na cikin halin ''neman sa'ida''

    A lokacin ƙuri'ar, ƙasashen 13, sun amince da matakin, yayin da Birtaniya ta ƙaurace wa ƙuri'ar, sai kuma Amurka da ta ƙi amince wa matakin, ta hanyar amfani da matsayinta na wadda ke da kujerar dindindin a kwamitin, ta kuma hau kujerar na-ƙi.

    Yayin da yake jawabi bayan ƙuri'ar, jakadan Amurka a kwamitin ya ce ''mun ɗauki matakin ne saboda an yi watsi da kusan dukan buƙatunmu''.

    Ita ma Birtaniya - wadda babar ƙawar Amurka ce - a nata ɓangare ta kare matakin ƙaurace wa ƙuri'ar da cewa ta yi hakan ne saboda ''ƙudurin ya gaza yin Allah wadai da hare-haren da Hamas ta kai Isra'ila ranar 7 ga watan Okotoba .

    Matakin na Amurka ya sha Allah dawai daga ƙasashe da dama ciki har da China da Rasha, yayin da Gwamnatin Falasdinawa ta kira matakin da ''koma-baya a tarihi'', tana mai cewa ''matakin zai yi sanadin kisan ɗaruruwan mutane''.

    Kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya dai ya ƙushi ƙasashe biyar masu kujerun dindindin da suka haɗar da Amurka da Rasha da Birtaniya da Faransa da kuma China, sai kuma ƙasashe 10 marasa kujerar dindindin da ake sauyawa bayan wasu shekaru.

    Kuma dole ne sai duka ƙasashen biyar da ke da kujerun dindindin a kwamitin sun amince da ƙuduri kafin a zartar da shi.

  19. Hotunan yadda aka wayi gari a kudancin Gaza

    Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare zuwa kudancin Zirin Gaza, a ƙoƙarinta na fatattakar mayaƙan Hamas.

    ga wasu daga cikin hotunan yadda aka wayi gari a yau Asabar

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wani mummunan hari ta sama ya faɗa Khan Younis, birnin mafi girma a kudancin Gaza
    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Haka kuma da safiyar nan ne wani harin makami mai linzami ya faɗa kan wata makarantar renon yara a birnin Rafah da ke kusa da kan iyakar Masar
    z

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wasu ƙananan yara da suka jikkata a yau sun je asibitin Nasser da ke Khan Younis
    x

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A jiya ne Amurka ta ƙi amincewa da wani ƙudurin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya buƙaci a tsagaita wuta a Gaza.
  20. Gane Mini Hanya: Matsalar wutar lantarki a Najeriya

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin

    Wani abu da ke ɗaurewa ‘yan Najeriya kai shi ne yadda har yanzu kasar ba ta fi ƙarfin wutar lantarkin da za ta wadatar da al’ummarta ba duk kuwa da cewa ta kwashe fiye da shekara 60 da samun ‘yancin kai.

    Al’amarin ya kai ga yadda kididdigar dumbin kudaden da gwamnatocin kasar suke kashewa kan fannin na neman kubcewa masu bin diddigi.

    A yanzu haka dai za a iya cewa wuraren da suke samun wutar lantarki awa 24 a kullum a mako guda ba su da yawa.

    Usman Minjibir ya yi mana duba dangane da batun karancin wutar lantarkin a Najeriya ga kuma rahotonsa na musamman.