Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. Maguire ne gwarzon ɗan wasan Premier na watan Nuwamba

  2. Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kaɗa kuri'a kan kiran tsagaita wuta a Gaza

    Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi taro nan da ‘yan sa’o’i domin kada kuri’a kan ko za a yi kiran tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza.

    Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya dauki matakin da ba a taba ganin irinsa ba na yin amfani da sashe na 99 na kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya.

    Babu wani da ke da mukami irin nasa da ya ɗauki irin wannan mataki a cikin shekaru da yawa.

    Matakin dai ya bai wa babban sakataren damar gabatar da duk wani lamari da a ra'ayinsa zai iya yin barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasashen duniya" a gaban majalisar "

    Hadaddiyar Daular Larabawa ta shirya wani daftarin kudiri da za a kada kuri’a, tana bukatar kuri’u akalla tara na goyon bayanta.

    • Tawagar ƙwararru ta MDD ta buƙaci Isra’ila ta tsagaita buɗe wuta a Gaza
    • Isra'ila-Gaza: Me ya sa wannan yaƙi ya zama daban da sauran
  3. Boye takardun kudi da mutane ke yi ne ya janyo karancin naira – CBN

    Babban Bankin Najeriya, CBN, ya yi gargadi game da boye takardun naira da ya ce wasu 'yan kasar na yi, lamarin da kuma ya janyo karancin kudi a hannun jama'a da ake fama da shi a baya-bayan nan.

    A zantawarsa da BBC, darakta mai kula da rassan babban bankin Najeriya, Shehu Alhaji Goringo ya kawar da duk wata fargaba, inda ya dage cewa babu wani karancin takardun naira a kasar, don haka mutane su daina shiga rububin cire kudi a bankunan kasuwanci.

    Ya ce bisa umarnin da kotu ta bayar za a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun naira 200 da 500 da 1,000 tare da sababbi har Illa masha Allahu.

    Ya ce a yanzu, babu batun wa'adin daina amfani da tsofaffin kuɗin a Najeriya kuma akwai wadatattun kuɗaɗe.

    Haka kuma daraktan na CBN ya shawarci 'yan kasar su rungumi karin hanyoyin musayar kudi kamar na laturoni da na dijital ciki har da tsarin aika kudi ta wayar salula.

    Ga karin bayani a tattaunawarsa da wakilin BBC Bashir Zubairu Kasarawa.

    • Yadda za ku gane jabun sabon kudin Najeriya
    • Ya za a yi da tsoffin kuɗin da za a sauya a Najeriya?
    Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar domin sauraron hirar
  4. Halin da ake ciki a Khan Younis bayan hare-haren Isra'ila

    A ƴan kwanakin nan, an samu ƙaruwar yaƙi a birnin Khan Younis da ke kudancin Gaza.

    A farkon yaƙin, an nemi Falasɗinawa su fice daga wajen saboda luguden wutar da ake a arewacin Gaza.

    Amma yanzu, mutane suna ficewa daga Khan Younis zuwa Rafah, kusa da iyakar yankin da Gaza.

    Ga wasu hotuna na baya-bayan nan daga Khan Younis bayan da Isra'ila ta lalata gine-gine da dama.

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

  5. An ɗaure ɗan Najeriyan da ya damfari mutanen ƙasashe 13

    EFCC

    Asalin hoton, X/EFCC

    Wata babbar kotu a Abuja, babban birnin Najeriya ta samu wani mazambaci, Eze Harrison Arinze, da laifin damfarar mutum 34 a ƙasashe 13 kuɗin da ya kai $592,000.

    Waɗanda ya damfara sun fito daga Burundi da Cameroon da Coasta Rica da Jamus da Ghana da Hungary da India da Rwanda da Singapore da Afirka ta Kudu da Uganda da Amurka da Zimbabwe.

    Hukumar yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta'annati, EFCC ce ta gurfanar da Arinze gaban mai shari'a J.K Omotosho kan laifin da ya shafi yin sojan gona.

    Arinze dai ya amsa laifinsa bayan da aka karanto masa uhumar da ake yi masa.

    Lauyan mai gabatar da ƙara Christopher Mshelia ya nemi kotu ta yanke wa wanda ake tuhuma hukunci.

    Mai shari'a Omotosho ya yanke wa Arinze hukuncin shekara uku a gidan yari da zaɓin biyan tara ta naira miliyan 3.

    A baya-bayan nan, Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ya ce abin damuwa ne yadda kashi 70 cikin 100 na ɗaliban Najeriya ke aikata zamba ta intanet.

    • Amurka na tuhumar 'yan Najeriya da zamba
    • Yadda EFCC ta kama ɗan takarar majalisa ɗauke da naira miliyan 326, da dala 610,500
  6. Putin zai sake tsayawa takarar shugaban ƙasa karo na biyar

    Putin

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce zai sake tsayawa takara karo na biyar kamar yadda rahotanni daga kafafen yaɗa labarai suka bayyana.

    Kamfanonin dillancin labarai a Rasha sun ce Putin ya yi magana ne kan ƙudurinsa yayin wani taro da aka yi a Moscow.

    Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan da jami'ai suka ayyana 15 zuwa 17 ga watan Maris ɗin 2024 a matsayin ranakun zaɓen shugaban ƙasa.

    Putin ya kasance kan shugabanci fiye da kowa tun zamanin Josef Stalin sannan idan ya sake cin zaɓe, zai kasance shugaban ƙasa har sai 2030.

    Kakakin Fadar gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov tun farko ya ce mutane da dama suna son Mr Putin ya ci gaba da shugabanci sai dai ya danganta da shi idan ya yi sanarwar.

    • Ukraine ba ta shirya wa zaman lafiya ba - Putin
    • 'Yadda Putin ke son ya ci gajiyar yaƙin Isra'ila da Gaza'
  7. Hunter Biden na fuskantar tuhuma kan zargin kauce wa biyan haraji

  8. Za a yi jana'izar Falasɗinawan da sojin Isra'ila suka kashe, Yolande Knell daga Birnin Ƙudus

    Ana sa ran yin jana'izar Falasɗinawa shida da aka kashe a samamen da Isra'ila ta kai sansanin ƴan gudun hijra na al-Fara da ke kusa da Tubas a arewacin Gabar Yamma da Kogin Jordan.

    Sojojin Isra'ila zuwa yanzu ba su ce komai ba da aka nemi jin ta bakinsu game da harin.

    Shaidu a sansanin sun ce dakarun Isra'ila na musamman sun kutsa sansanin da sanyin safiyar Juma'a.

    Wani mutum ya ce an harbe ƴan uwansa bayan da ya buɗe ƙofa domin duba abin da ke faruwa.

    A cewar jami'ai a Falasɗinu, Falasɗinawa 263 sojojin Isra'ila suka kashe a Gabar Yamma da Kogin Jordan tun bayan da aka soma yaƙi a Gaza.

    • Daga ina Hamas ke samun kuɗi?
    • Isra'ila-Gaza: Me ya sa wannan yaƙi ya zama daban da sauran
  9. An kuɓutar da mutum 133 da ake zargi an yi safararsu a Afirka ta Kudu

    Afirka ta Kudu

    Asalin hoton, AFPCopyright

    Ƴan sanda a Lardin Limpopo a Afirka ta Kudu sun Kuɓutar da mutum 133 da ake zargin an yi safararsu.

    Kafar yaɗa labarai ta SABC ta ruwaito cewa mutanen da suka haɗar da yara da manya an same sune cikin wasu ƙananan bas-bas guda 10.

    Wannan ne karo na uku da irin haka ke faruwa tun ƙarshen makon da ya gabata.

    A Ranar Lahadi ne hukumomi a Limpopo suka kama fiye da ƙananan yara 400 da aka shigar da su Zimbabwe ba tare da wani babba a tare da su ba.

    Hukumomin Zimbabwe sun musanta rahoton inda suka ce yara 124 ne kaɗai.

    Ƙungiyar Save the Children ita ma ta ƙaryata iƙirarin Afirka ta Kudu cewa an sato yaran ne inda ta ce ba wai an kasi su Afirka ta Kudu bane domin yin aikatau.

  10. An kammala yaƙin neman zaɓe a Masar

    Masar

    Asalin hoton, Reuters

    An kammala yaƙin neman zaɓe a Masar gabanin zaɓen yini uku da za a fara daga gobe, Asabar.

    Shugaba Abdul Fattah al-Sisi yana neman wa'adi na uku duk da alƙawarin da ya yi a 2018 cewa ba zai sake tsayawa takara ba.

    Ya hau kan karagar mulki ne shekara 10 da suka gabata sakamakon juyin mulkin da aka yi.

    Ana kallon biyu daga cikin ƴan takarar shugaban ƙasar, Hazem Omar da Farid Zahran a matsayin makusantan al-Sisi abin da ya sa wasu ke kallon zaɓen a matsayin bogi.

    Sai dai yaƙin da ake a Gaza mai maƙwabtaka ya shafe batun zaɓen a ƙasar Afirka ta uku mafi yawan al'umma.

    Al'ummar ƙasar na fama da matsin rayuwa saboda taɓarɓarewar tattalin arziki.

    Ana hasashen Shugaba Sisi ne zai yi nasara da kyakkyawan rinjaye, kamar yadda aka yi a zaɓuka biyu na baya.

  11. 'An kashe mutane da dama bayan harin Isra'ila a Gabar Yamma da Kogin Jordan'

    ..

    Asalin hoton, ZAIN JAAFAR/AFP via Getty Images

    Sojojin Isra'ila sun harbe Falasɗinawa shida a wani sansanin ƴan gudun hijra da ke arewacin Gaɓar yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye kamar yadda ma'aikatar laiya ta Palasɗinu ta bayyana.

    Ta yi iƙirarin cewa an kashe sune a sansanin al-Fara kusa da Tubas.

    Kamfanin dillancin labarai na Palasɗinu, Wafa ya ce mutane da dama sun ji rauni.

    An dai samu ƙaruwar tashin hankali a Gabar yamma da kogin Jordan tun bayan soma yaƙin Isra'ila da Hamas ranar 7 ga watan Oktoba.

    Ofishin kakakin rundunar sojin Isra'ila ya ce yana nazari kan rahoton.

  12. Gobara ta tashi a sansanin Jabalia yayin da yaƙi ke daɗa ƙazanta a Gaza, Rushdi Abu Alouf daga Istanbul

    Sojojin Isra'ila sun ci gaba da yin luguden wuta a sansanin ƴan gudun hijra na Jabalia da ke Gaza yayin da tankoin yaƙin Isra'ila ke nausawa tsakiyar sansanin.

    Ɗan jarida a yankin Hossam Shabat, wanda ke ba da rahoto kan halin da ake ciki a arewacin Gaza, ya ce a wani saƙon murya da ya karaɗe shafukan sada zumunta: "tankokin yaƙin Isra'ila sun zagaye mu, suna luguden wuta kan wani sansani da ke titin Abu Zaitun a sansanin ƴan gudun hijra na Jabalia da ya zma gida ga mutum 15,000 da suka ɗaiɗaita.

    "An shafe fiye da sa'a uku ana ta kai munanan hare-hare kuma motocin ɗaukan marasa lafiya ba za su iya kai wa wurin ba: Duka asibitocin da ke arewacin Gaza ba sa aiki.

    "Gobara ta tashi a gine-gine da dama da ke sansanin, lamarin da ya jefa dubban mutanen da suka rasa gidajensu, suke samun mafaka a makarantun Majalisar Ɗinkin Duniya cikin firgici."

  13. An kama mutum biyu kan zargin damfarar mutane da annobar kuɗin cizo

    Kuɗin cizo

    Asalin hoton, REUTERS

    Ƴan sanda a Faransa sun damƙe mutum biyu bisa zarginsu da damfarar tsofaffin mutane wajen biyan maƙudan kuɗaɗe domin kare su daga ƙwarin kuɗin cizo.

    Ƴan sanda a Strasburg sun ce mutanen suna zuwa gidajen tsofaffin ne inda suke kiran waya na bogi sannan su zabga kuɗi kan kayan kula da ƙwarin.

    Sun ƙara da cewa mutum 48 aka damfara ta wannan siga, galibinsu mata da shekarunsu suka zarce 90.

    A watannin baya-bayan nan, an ga ƙaruwar ƙwarin kuɗin cizo a sassan Faransa.

    Lamarin ya haifar da damuwa a ƙasar inda manyan jami'an gwamnati ke aiki domin magance matsalar.

    Hukumomi sun ce ƴan damfarar da ake zargi suna kiran mutane ne su faɗa musu cewa an samu ɓarkewar ƙwarin a inda suke.

    A cewarsu, mutanen suna zuwa gidajen ne da sunan ma'aikatan lafiya inda suke amfani da maganin feshi suna yaudararsu.

    Kafin su tafi kuma, suna basu wani mai da suka ce zai kare su daga ƙwarin.

    Ana karɓar tsakanin euro 300 da euro 2,100.

    Ƴan sandan sun kuma ce sun samu ƙorafe-ƙorafe har tare game da ƴan damfarar.

  14. Kusan kashi 20 na al'ummar Afirka na fuskantar matsalar yunwa - MDD

    MDD

    Asalin hoton, AFP

    Wani sabon rahoton da cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya uku da hadin gwiwar ƙungiyar Afirka suka fitar ya nuna cewa kusan 'yan Afirka miliyan 282, kusan kashi 20 na al'ummar nahiyar ne ke fama da matsalar ƙarancin abinci.

    Rahoton haɗin gwiwar ya kuma nuna cewa yawan mutanen da ke fama da ƙarancin abinci sun ƙaru da miliyan 57 tun bayan ɓarkewar cutar covid, lamarin da ya haifar da taɓarɓarewar matsalar abinci a nahiyar.

    "Mafi yawan al'ummar Afirka – kusan kashi 78 ko fiye da mutum biliyan guda – ba sa samun lafiyayen abinci, idan aka kwatanta da kashi 42 da ke samun hakan a faɗin duniya, kuma adadin na ci gaba da ƙaruwa," in ji rahoton.

    Rahoton ya kuma alaƙanta rashin samun lafiyayen abincin kan matsalar ƙarancin abinci da aka fuskanta a 'yan shekarun baya-bayan nan, musamman a Yammaci da Gabashin Afirka, wanda ya sa ba ma talakawa kaɗai ba, har ma da masu dama-daman ba sa iya samun lafiyayyen abinci.

    Hukumomin sun kuma ce kusan kashi 30 na ƙananan yara 'yan ƙasa da shekara biyar ne a nahiyar suka takure sakamakon rashin samun ingantaccen abinci.

  15. Mutum 81 ne suka mutu a harin Kaduna – Hedikwatar tsaron Najeriya

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, NIGERIAN AIR FORCE HQ/FACEBOOK

    Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta ba da tabbacin mutuwar mutum 81 sakamakon harin kuskure da wani jirgin sojin Najeriya ya kai kan farar hula a Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya.

    Manjo Janar Edward Buba, Daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron ne ya bayyana haka inda ya ce mutum 70 ne suka jikkata sakamakon harin.

    A baya dai, hukumar ba da agajin gaggawa ta ba da rahoton cewa sama da mutum 85 ne suka mutu sakamakon harin da aka kai, yayin da wasu ƙungiyoyi ke cewa adadin mutanen da suka mutu ya zarce haka.

    Hedikwatar tsaron ta kuma ce daga yanzu, za ta tabbatar da inda za ta kai hari ɗari-ɗari kafin jefa bom.

    "Za mu ci gaba da aiwatar da ayyukanmu bisa ƙa'idojin aiki wanda hakan muke yi,"

    "Game da abin da ya faru a Kaduna, sojoji sun ɗauki darasi kuma za su ci gaba da aiki da shi. Za mu tabbatar ba a sake ganin irin haka ba a gaba."

    Janar Buba ya kuma mayar da martani game da zarge-zargen da wata ƙungiyar arewa ta yi cewa an kai harin ne domin rage yawan al'ummar arewa inda ya ce "rundunar sojin Najeriya ta ƙunshi ma'aikata daga kowace ƙabila a Najeriya. Ko ma me ƙungiyar ta ce, harin ya faru ne a kan kuskure."

    • 'Gwamnati za ta biya diyya ga al’ummar Tudun Biri'
    • Hare-haren jiragen yaƙin Najeriya bisa kuskure takwas a kan fararen hula
  16. Sojojin Najeriya sun kama jirgin ruwa ɗauke da gangar mai fiye da 3,000 na sata

    .

    Asalin hoton, AFP

    Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta kama wani jirgin ruwa ɗauke da gangar mai 3,665 da take zargi na sata ne a yankin Igbokoda na jihar Ondo.

    Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce ta kama ma'aikatan jirgin 17, da take zargi da satar man daga rijiyar mai ta Ebesan a ƙaramar hukumar Ilaje da ke jihar.

    Daraktan yaɗa labaran rundunar, Commodore Ayo-Vaughan, ya ce an kama jirgin ne a ranar Alhamis.

    Ya ce rundunar ta samu bayanan sirri kan ayyukan mutanen da take zargi da sace man, inda nan take ta tura jami'anta waɗanda suka yi nasarar kama mutanen.

    Sanarwar ta ce sojojin sun gano cewa an daɗe ana amfani da jirgin wajen satar man daga kowane ɓangare na rijiyar.

    Jirgin na da girman da zai iya ɗaukar nauyin metric ton 15,000, kuma a lokacin da aka kama shi yana ɗauke da man da nauyinsa ya kai metric ton 500.

    Satar mai a kudancin Najeriya dai wata matsala ce da ta daɗe tana ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya, inda ɓata-gari ke sace ɗimbin mai ta hanyar fasa bututan man ko amfani da rijiyoyin mai ba bisa ƙa'ida ba, lamarin da ke ƙara haifar da koma-baya kan tattalin arzikin ƙasar.

  17. Amurka ta soki yadda Isra'ila ke yaƙi a Gaza

    Anthony Blinken

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Anthony Blinken, Sakataren harkokin wajen Amurka

    Amurka ta soki yadda Isra'ila ke yaƙi a zirin Gaza, a daidai lokacin da aka shiga watanni biyu da ɓarkewar yaƙin tsakaninta da Hamas.

    Sakataren harkokin wajen Amurka ya ce Isra'ila ba ta cika alƙawarin da ta ɗauka na kare farar hula a yaƙin da ta ke ƙara zafafawa a Gaza ba, idan aka kwatanta da halinda ake ciki a yanzu.

    Anthony Blinken ya shaidawa manema labarai a Washington cewa, akwai matakai da dama da Isra'ila ya kamata ta ɗauka domin tabbatar da cewa Falasdinawa Farar hula sun isa tudun mun tsira cikin nutsuwa.

    Mr Blinken ya ce ba wai kawai su isa wurare masu aminci kaɗai ba, har da yi musu bayanin inda ya kamata su nufa, da lokacin da za su tafi, suna buƙatar abubuwa kamar ruwan sha da abinci da magani.

    Babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya, Martin Griffiths ya ce yana fatan buɗe iyakar Isra'ila da Kerem Shalom ka iya sauƙaƙa kai kayan agaji cikin sauri ga Falasdinawa.

  18. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, da Hausawa ke yi wa kirari da ''Haji babbar rana''.

    Nabeela Muktar Uba ke muku sallama a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafa a shafukanmu na sada zumunta.

    Ku biyo mu...