Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo karshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu,za mu sake dawowa domin ci gaba da kawu muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Aisha Babangida ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Gwamnan Katsina ya ba da umarnin dakatar da malami kan zargin neman ɗaliba

    Gwamnan Katsina jihar Katsina, Dikko Radda

    Asalin hoton, Katsina State Government House

    Bayanan hoto, Gwamnan Katsina jihar Katsina, Dikko Radda

    Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya bayar da umarnin dakatar da wani malamin makarantar sakandare bisa zargin sa da laifin neman ɗaliba da niyyar lalata.

    Hakan na ƙunshe ne a wata takarda da gwamnan ya rubuta wa kwamishinar ilimi a matakin farko ta jihar, Hadiza Yar'adua.

    Umarnin gwamnan na zuwa ne bayan samun rahoton cewar malamin, wanda shi ne shugaban makarantar da ke a ƙaramar hukumar Dandume, na neman ɗalibai mata.

    Sanarwar wadda ta samu sa hannun daraktan yaɗa labaru na ofishin sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Faskari, ta kuma buƙaci da a yi bincike kan zargin da ake yi wa malamin tare da ɗaukan matakan da suka dace.

  3. Abokan hulɗar BBC Hausa

  4. Su wane ne ke da kuri'a a majalisar tsaro na MDD?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a gudanar da kuri'ar tsagaita bude wuta da yammacin yau a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ke da wakilai biyar na dindindin - Amurka da Birtaniya da Faransa da Rasha da kuma China.

    Ƙididdiga na nuna ƙasashen biyar masu nasara a yakin duniya na biyu, waɗanda suka taimaka wajen kafa Majalisar Dinkin Duniya.

    Akwai wasu mambobin majalisar guda 10 da ke karba-karba, a halin yanzu sun hada da: Albaniya da Brazil da Ecuador da Gabon da Ghana da Japan da Malta da Mozambique da Switzerland da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.

    Sai dai iko ya rataya ne kan mambobi biyar na cikakken lokaci, wadanda ke da ikon yin watsi da duk wani kuduri da ya zo gabansa.

    Tuni dai Amurka ta sha alwashin daƙile yunkurin tsagaita buɗe uta a Gaza

  5. An kama ƴan sandan da suka roƙi baturiya kuɗi

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Police Force

    Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar Juma’a ta ce ta kama wasu ‘yan sandan sa-kai wadanda aka gani a wani faifan bidiyo suna roƙon kudi daga hannun wata mata ‘yar ƙasar Holland mai tuka babur a unguwar Ojongbodu da ke kan titin Iseyin/Ogbomosho a jihar Oyo.

    Bayanin kama su ya fito ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Muyiwa Adejobi, ya fitar, inda ya ce an kama su ne saboda rashin ɗa’a, wanda ba za a amince da shi ba, da kuma hukunta su.

    Adejobi ya kuma bayyana cewa "Kwamishanan 'yan sanda na jihar Oyo, CP Adebola Ayinde Hamzat, ya ƙaddamar da binciken ladabtarwa kan lamarin nan take."

    “Hukumar ‘yan sanda ta yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da bayar da umarnin hukunta ‘yan sandan sa-kan da jami’in ‘yan sanda da ke sa ido a kan su.”

    Ya bayyana lamarin a matsayin wanda ya ci karo da ɗabi'ar ‘yan sanda ba kuma ba za a taba amincewa da shi ta kowace hanya ba.

  6. BBC ta ga bidiyon yadda aka yi wa Falasɗinawa tsirara a Gaza

  7. ‘Yan sanda sun yi wa tsohon shugaban ƙasar Saliyo Koroma tambayoyi

    ...

    Asalin hoton, AFP

    An yi wa tsohon shugaban kasar Saliyo, Ernest Bai Koroma tambayoyi a hedkwatar 'yan sanda da ke Freetown, babban birnin kasar, kan yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

    Koroma, wanda ya mulki ƙasar na tsawon shekaru 10 kacal, ya isa ne da misalin karfe 10:00 na agogon kasar a sashin binciken manyan laifuka karkashin wani babban rakiyar 'yan sanda da sojoji.

    Ba a dai bayyana tsawon lokacin da aka kwashe ana tambayar sa ba amma daga baya tsohon shugaban ya wallafa wata sanarwa a shafukan sada zumunta cewa za a ci gaba da yin tambayoyin a ranar Asabar.

    ‘Yan sanda sun gayyaci Koroma a ranar Alhamis inda suka buƙaci ya bayyana cikin sa’o’i 24 domin amsa tambayoyi a wani bangare na binciken da suka yi kan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar 26 ga watan Nuwamba.

    Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a barikin soji da gidan yari da wasu wurare a ƙasar Saliyo a watan da ya gabata, inda suka sako fursunoni kusan 2,000 tare da kashe sama da mutum 20 a wani mataki da mahukuntan kasar suka ɗauka na yunkurin kifar da gwamnatin ƙasar.

    Ya zuwa yanzu dai an kama mutum 71 da suka haɗa da jami’an soji 45 da ‘yan sanda bakwai da kuma fararen hula 13.

  8. Mitocin da muke watsa shirye-shiryenmu

  9. 'Wani ɗan jaridan Gaza da ake tsare da shi yana sansanin sojin Isra'ila'

    Wani ɗan jarida daga Gaza wanda aka gani a hoto an dauke shi zuwa sansanin sojin Isra'ila, kamar yadda wani abokin aikinsa ya shaida wa BBC Radio 4 PM.

    Isra'ila ta saki da dama daga cikin fursunonin amma Diaa Kahlot, ɗan jaridan Gaza bai cikin wanda aka saka a cewar abokin aikinsa Lamis Andoni.

    A cewar Andoni, fursunonin da aka saki sun shaida wa iyalan Diaa cewa an kai shi sansanin soji na Zikim da ke Isra’ila.

    “Ba mu da masaniya game da makomarsa.

    Hotuna da bidiyon wadannan mutane suna da ban tsoro, kuma abin mamaki," in ji shi.

  10. Ku yi hankali da jabun takardun naira a hannun jama'a - CBN

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban Bankin Najeriya, CBN, ya sanar da bankuna da ‘yan Najeriya cewa su yi hattara da jabun takardun naira musamman kudaden da ake kashewa a wuraren sayar da abinci da sauran cibiyoyin kasuwanci a kasar.

    A cewar Babban Bankin, laifi ne da za a iya yanke wa mutum hukuncin dauri a gidan yari idan aka kama shi da jabun takardun kuɗin.

    Babban Bankin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a.

    CBN ya ci gaba da cewa, “An jawo hankalin CBN kan yadda wasu mutane ke yawo da jabun takardun kudi, a kasuwannin sayar da kayan abinci da cibiyoyin kasuwanci a manyan biranen kasar nan.“

    Don kauce wa shakku, sashe na 20 (4) na dokar Babban Bankin (2007) da aka yi wa kwaskwarima, ya bayyana karara cewa amfani da jabun takardun kuɗi a hannun jama'a ko kasuwanni a Najeriya laifi ne da za a yanke hukuncin dauri mafi karanci na shekaru biyar.

    “CBN na ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro domin kwace irin waɗannan jabun takardun kudin Naira da kuma gurfanar da masu su a kotu.“

    Haka kuma ana kira ga jama’a da su kai rahoton duk wanda ake zargi yana da jabun takardun naira zuwa ga hukumomi.

    • CBN ya ce a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi
    • 'Yan Najeriya na kumfar baki a kan 'ɓacewar sabbin takardun naira'
  11. Sojojin wanzar da zaman lafiya a DR Kongo na ci gaba da ficewa daga ƙasar

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Kusan sojojin Sudan 250 ne suka fice daga gabashin Dr Kongo, kwanaki bayan sojojin Kenya sun fara ficewa daga yankin, bayan ƙarewar yarjejeniyar.

    Sojojin na daga cikin dakarun gabashin Afirka da aka kai ƙasar shekarar da ta gabata domin aikin wanzar da zaman lafiya a rikici tsakanin dakarun sojin DR Kongo da 'yan tawayen ƙungiyar M23.

    Rahotonni da dama na cewa ƙungiyar 'yan tawayen na samun goyon bayan ƙasar Rwanda, zargin da ƙasar ta sha musantawa.

    Akwai fargabar ci gaba da rikicin a gabashin ƙasar, ka iya shafar zaɓen ƙasar da za a yi cikin wannan wata.

    Suma sojojin Sudan ta Kudu sun fice daga birnin goma a jirgin sama a ranar da yarjejeniyar wanzar da zaman lafiyar soji a gabashin ƙasar ke ƙarewa.

    Shugaban ƙasar DR Kongo Felix Tshisekedi ba ya son zaman dakarun a ƙasar, don haka ya ƙi amincewa da tsawaita wa'adin zaman nasu.

    An dai kai sojojin ne da nufin kawo ƙarshen rikici da ƙungiyar 'yan tawayen M23.

    Shugabannin ƙasashen yankin gabashin Afirka na buƙatar tattaunawa don kawo ƙarshen rikicin, yayin da shugaba Tshisekedi ke son amfani da ƙarfin soji.

    A nan gaba kaɗan ne cikin wannan wata za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasar, Mista Tshisekedi na buƙatar ƙuri'un yankin gabashin ƙasar, wannan dalili ne watakila ya sa yake son murƙushe gomman ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

    Kusan shekara 20 da aka shafe ana yaƙarsu, bai samar da wani ingantaccen sakamako ba.

  12. Amurka ta ƙi amincewa da buƙatar MDD na tsagaita wuta a Gaza

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Wakilin Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Robert Wood, ya ce ba za su goyi bayan tsagaita buɗe wuta a Gaza nan take ba.

    "Yayin da Amurka ke matuƙar goyon bayan zaman lafiya mai dorewa, wanda Isra'ilawa da Falasdinawa za su iya rayuwa cikin lumana da tsaro, ba ma goyon bayan kiran tsagaita buɗe wuta a Gaza cikin gaggawa."

    "Wannan zai yi shuka gabar da za ta haifar da yaƙi na gaba saboda Hamas ba ta da sha'awar ganin dorewar zaman lafiya," kamar yadda ya shaida wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

    Amurka tana ɗaya daga cikin membobin dindindin waɗanda ke da haƙƙin yin watsi da ƙudurin.

    • Tsagaita wuta zai ba Hamas damar sake shiri don kai hare-hare - Anthony Blinken
    • Abin da ya kamata ku sani kan yarjejeniyar Isra'ila da Hamas
  13. Isra'ila ta yi watsi da kiran tsagaita wuta a taron Majalisar Dinkin Duniya

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya Gilad Erdan, ya yi watsi da kakkausan kiraye kirayen tsagaita wuta a Gaza.

    Ya shaida wa Majalisar Dinkin Duniya cewa "tsagaita bude wuta ya tabbatar da ikon Hamas a Gaza" kuma haka zai aike da sakon cewa "An gafartawa Hamas duk da zaluncin da ta yi da gangan".

    Erdan ya kuma ce "Al'ummar duniya sun bai wai Hamas dama har taka gazallaza wa Falasɗinawa

    Ya Ƙara da cewa, "Idan ba tare da matsin lambar soji kan Hamas ba, babu wata diplomasiyya da za ta iya tabbatar da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su."

    • Yadda Hamas ta haɗa dakarun da suka kai wa Isra'ila harin 7 ga Oktoba
    • Wakilin BBC a Gaza: ‘Na sare, rayuwa ta tarwatse a kan idona’
  14. El-Rufa'i da Muhammadu Sanusi II sun kai ziyara Tudun Biri

    ...

    Asalin hoton, Majeeda Emirate Photography

    Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i da Khalifar Tijjaniyya a Najeriya, Muhammadu Sanusi II sun kai ziyara garin Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

    Mutanen biyu sun kai ziyarar ce a ranar Juma'a, kwanaki bayan harin da sojojin Najeriya suka kai a ƙauyen 'bisa kuskure.'

    ..

    Asalin hoton, Majeeda Emirate Photography

    A ranar Lahadin da ta gabata ne wani jirgi maras matuƙi mallakin sojojin Najeriya ya harba bam sau biyu a kan masu bikin Maulidi a ƙauyen.

    ..

    Asalin hoton, Majeeda Emirate Photography

    Tun farko hukumomi sun bayyana cewa mutum 85 ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar harin.

    Amma daga baya rundunar sojojin ƙasa ta Najeriyar ta ce mutum 81 ne harin ya hallaka.

    ..

    Asalin hoton, Majeeda Emirate Photography

    Sai dai al'ummar ƙauyen da kuma wasu ƙungiyoyi sun bayyana cewa yawan waɗanda suka mutu sanadiyyar harin sun zarce alƙaluman da hukumomi suka bayar.

    ...

    Asalin hoton, Majeeda Emirate Photography

    Tuni dai rundunar sojojin Najeriya ta nemi afuwa game da harin, kuma hukumomi sun ce za su biya diyya.

    • Harin sojoji a Kaduna: 'An ƙona mana yara an ƙona mana mazaje'
    • 'Gwamnati za ta biya diyya ga al’ummar Tudun Biri'
  15. Ƙasar Afrika ta Kudu ta kama mutum 133 da ake shirin yin safararsu

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Ƴan sanda a Lardin Limpopo a Afirka ta Kudu sun Kuɓutar da mutum 133 da ake zargin an yi safararsu.

    Kafar yaɗa labarai ta SABC ta ruwaito cewa mutanen da suka haɗar da yara da manya an same sune cikin wasu ƙananan bas-bas guda 10.

    Wannan ne karo na uku da irin haka ke faruwa tun ƙarshen makon da ya gabata.

    A Ranar Lahadi ne hukumomi a Limpopo suka kama fiye da ƙananan yara 400 da aka shigar da su Zimbabwe ba tare da wani babba a tare da su ba.

    Hukumomin Zimbabwe sun musanta rahoton inda suka ce yara 124 ne kaɗai.

    Ƙungiyar Save the Children ita ma ta ƙaryata iƙirarin Afirka ta Kudu cewa an sato yaran ne inda ta ce ba wai an kasi su Afirka ta Kudu bane domin yin aikatau.

    • 'Yadda masu safarar mutane suka ja hankalina da daɗin baki'
    • An yi safarar sa don cire masa ƙoda yanzu kuma ya shiga ɓuya
  16. Ba zan daina murna ba idan mun ci kwallo duk da an dakatar da ni - Arteta

  17. Matatar man Dangote ta karɓi ɗanyen man fetur a karon farko

  18. Gwamnatin Kano ta mayar da martani kan umarnin kotu na rufe asusun jihar

    Bayanan sautiLatsa lasifikan sama don sauraron rahoton

    Gwamnatin jihar Kano ta ce ta umarci lauyoyinta su bibiyi wata takarda da suka ce tana yawo a shafukanta sanda zumunta da ke cewa kotu ta bayar da umarnin rufe asusun gwamnati.

    A cikin makon nan ne takarda ta ɓulla a shafukanta intanet wadda ake cewa, ta fito ne sakamakon wata buƙata da bangaren waɗanda aka yiwa rusau a masallacin idi suka shigar.

    Sai dai ma’aikatar shari’ar jihar Kano ta ce har yanzu ba a basu kwafin takardar umarnin kotun ba.

    Ga rahoton Zahraddeen Lawan daga Kano

    • Yadda rusau ke ƙara jefa mutane cikin fargaba a Kano
    • Za mu kama gurbatattu - Tubabbun 'yan daban da suka koma 'yan sandan sa-kai
  19. Muna da ƴancin karɓar baƙuncin kofin duniya - Saudiyya

  20. A biya mutanen Tudun Biri diyya, kuma a buɗe iyakar Najeriya da Nijar - Sheikh Bala Lau

    ...

    Asalin hoton, Abdullahi Bala Lau/Facebook

    Shugaban ƙungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iƙamatul Sunnah (Jibwis) a Najeriya ya faɗa wa shugaban Najeriya cewa akwai buƙatar a hukunta wanda ke da hannu a jefa wa masu taron Maulidi bam a jihar Kaduna.

    Sheikh Bala Lau ya nemi Shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamitin da zai yi bincike kan lamarin yayin da shugaban ya je yin sallar Jama'a a hedikwatar kungiyar da ke Abuja.

    “Shugaban kasa mun san irin ƙoƙarin da kake yi amma akwai buƙatar a kafa kwamitin bincike don hukunta duk wanda yake da hannu a lamarin, kuma a biya su diyya,” kamar yadda limamin ya fada a huɗubarsa ta Jama'a.

    Ya ƙara da cewa “yin hakan zai saukaka wa mutanen yankin da kuma tabbatar da zaman lafiya”.

    Kazalika, limamin wanda ya yi huduba cikin Larabci, da Hausa, da Ingilishi, ya nemi Shugaba Tinubu ya buɗe iyakar Najeriya da Nijar, wadda aka rufe a matsayin takunkumi kan sojojin da suka kifar da gwamnatin Bazoum Mohamed ta farar hula a makwabciyar ta Najeriya.

    “Shugaban ƙasa, mutane da dama suna kawo mana kuka cewa har yanzu iyakar Najeriya na rufe, suna da kayayyakin da za su iya lalacewa."

    Muna kira a buɗe iyakar saboda ‘yan arewacin Najeriya da Nijar su ci gaba da hulɗar kasuwanci da kuma zamantakewa a matsayin ‘yan uwa.”

    Hukumar agajin gaggawa ta NEMA ta ce mutum 85 ne suka mutu ranar Lahadi da ta gabata lokacin da jirgi maras matuki na rundunar sojin Najeriya ya jefa wa mazauna garin Tudun Biri bam sau biyu bisa kuskure.

    • Jirgi ya yi ruwan bam a kan masu taron Mauludi a Kaduna
    • Hare-haren jiragen yaƙin Najeriya bisa kuskure takwas a kan fararen hula