Sojojin Isra'ila sun ce za a ci gaba da tsagaita buɗe wuta a Gaza

Asalin hoton, Getty Images
Sojin Isra'ila sun sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Gaza da ƙarin kwana guda, daidai lokacin da masu shiga tsakani ke kokarin ganin an sako karin wadanda bangarorin biyu ke tsare da su.
Isra'ilawa 12 da 'yan Thailand 4 da mayaƙan Hamas ke tsare da su a Zirin Gaza, da kuma suka samu 'yanci a jiya Laraba sun isa Isra'ila.
Ita ma Isra'ila ta saki Falasdinawa mata da kananan yara 30 da ta ke tsare da su agidajen kasonta.
Majiyar FalasƊinawa na cewa za a Ƙara tsawaita tsagaita wutar da kwanaki 4, yayin da majiyar Isra'ila ke cewa da kwanaki 2.
Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken na Tel Aviv domin bukatar kara wa'adin.
- Yadda Hamas ta haɗa dakarun da suka kai wa Isra'ila harin 7 ga Oktoba
- Abin da ya kamata ku sani kan yarjejeniyar Isra'ila da Hamas
