Aisha Adam Hussaini ce ta lashe gasar Hikayata ta BBC Hausa, 2023

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa, Abdullahi Bello Diginza and Haruna Kakangi

  1. Ƴar shekara saba'in ta haifi tagwaye a Uganda - asibiti

    ...

    Asalin hoton, Women's Hospital International and Fertility Centre

    Wata tsohuwa ‘yar kasar Uganda mai shekaru 70 ta haifi tagwaye bayan da ta samu juna biyu ta hanyar ƙyanƙyashe ƙwai a dakin bincike kafin a dasawa mace a mahaifa (IVF) inda ta zama mace mafi tsufa a Afirka da ta haihu, kamar yadda asibitin da ta haifi jariran ya bayyana.

    Cibiyar kula da lafiyar mata ta ƙasashen duniya da cibiyar haihuwa da ke Kampala babban birnin Uganda, ta ce Safina Namukwaya ta haifi namiji da mace.

    "Wannan ba abu ne kaɗai ya yake nuna ci gaba a fanni likitanci amma harda nuna jajircewa na ɗan Adam," in ji asibitin a shafin Facebook, biyo bayan nasarar haihuwa da Namukwaya ta yi ta tiyata a ranar Laraba.

    Namukwaya ta shaida wa gidan talabijin na NTV mai zaman kanta cewa wannan ne karo na biyu da ta haihu cikin shekaru uku, bayan ta haifi yarinya a shekarar 2020.

    Ta kara da cewa ta fuskanci matsaloli da dama a lokacin da take dauke da juna biyu, ciki har da rabuwa da mahaifin yaran.

    "Maza ba sa son jin kina dauke da cikin tagwaye, tun lokacin da aka shigar da ni a nan mijina bai taba zuwa ba."

    Namukwaya ta ce ba ta san yadda za ta yi renon yaran ba, amma ta yi farin ciki da samun su bayan shekaru da dama da suka sha fama na rashin haihuwa.

  2. Hamas ta yi ikirarin hannun mambobinta a harin Birnin Kudus

    Hamas ta yi ikirarin cewa mayakanta ne suka kaddamar da harin Birnin Kudus da safiyar yau, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku, kamar yadda kungiyar ta wallafa a shafinta na Telegram.

    Cikin sanarwar, Hamas ta ce ''ta kai hari ne saboda mayar da martani kan laifukan da ake aikata wa al'umominta ta hanyar mamaya,'' tana mai kafa hujja da ayyukan sojin Isra'ila a Gaza da yadda ta ce ana muzgunawa Falasdinawa a gidajen yarin Isra'ila.

    The statement also called for "an escalation of the resistance," news agency AFP said.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP, ya ambato sanarwar kungiyar na kira ga mambobinta da su ''ci gaba da fadada juriya''.

  3. Ƴan bindiga sun kashe mafarauta 18 a Taraba

    Wasu ‘yan bindiga sun kashe mafarauta 18 a wani harin da suka kai a karamar hukumar Bali da ke jihar Taraba.

    Shugaban kungiyar mafarauta na jihar Taraba, Adamu Dantala ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa an kashe mambobinsa 15 a wata arangama da ‘yan bindiga a wani dutse da ke kusa da garin Maihula a ranar Talata.

    Jaridar Daily Trust ta kuma ruwaito cewa, ‘yan bindigar da yawansu ya haura 200 sun yi yunkurin kai hari a garin Bali, hedikwatar karamar hukumar Bali da wasu kauyukan da ke kewaye amma mafarautan suka yi karo da su.

  4. Ana bincike don gano wadanda suka yi wa gwamnati fashi a jihar Ogun

    Nigeria's police head

    Asalin hoton, Nigeria Police Force/Facebook

    Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta bukaci a gabatar da mata da bidiyon kyamarorin tsaro na wani banki a birnin Abeokuta, yayin da ta fara bincike a kan kisan gillar da aka yi wa wani daraktan kudi a ofishin Gwamna Dapo Abiodun.

    Ana zargin wasu 'yan fashi ne suka harbe Mista Taiwo Oyekanmi ranar Laraba, lokacin da yake komawa ofis daga banki, inda ya dauko motar banki mai sulke bayan ya karbo wasu kudade don amfanin jihar.

    Kwamishinan 'yan sandan Ogun Abiodun Alamutu, ya ce an kashe daraktan kudin ne a gadar NNPC da ke kusa da Kuto a birnin Abeokuta.

    A cewarsa, likitoci ne a asibitin gwamnatin jihar suka tabbatar da mutuwar jami'in bayan an garzaya da shi jim kadan da harbin da aka yi masa.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa 'yan fashin sun tare motar bankinsu Taiwo Oyekanmi a kan gada, inda mutum biyar suka dirgo daga ciki rike da bindiga da guduma, kuma a take suka harbi daraktan, sannan suka yi amfani da guduma suka balle akwatun kudin.

  5. DR Congo ta bayyana takaici kan janye jami'an sa ido a zabe na Tarayyar Turai

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ta bayyana damuwa kan matakin da Tarayyar Turai ta dauka na janye jami'an sa-ido a zaben kasar.

    A ranar 20 ga watan Disamba ne ake sa ran gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a kasar Kongo, inda 'yan takara 23 za su fafata a zaben shugaban kasa.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da zaman ɗar-ɗar na siyasa ke karuwa.

    Soke zuwan jami'an sa-idon shi ma ya faru ne daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan batun tura jami'an na Tarayyar Turai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ACP ya bayyana.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Kongo ta ce ta kuduri aniyar samun nasarar gudanar da zaben cikin gaskiya da amana da kuma 'yanci, sannan za ta yi maraba da duk wasu jami'an sa-ido da ke son yin aiki "bisa doka da kuma ka'idojin Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo".

    Kungiyar Tarayyar Turai ta ce ta janye masu sa-idon nata ne a zaben, bayan ta gaza samun izinin tura muhimman na’urorin sadarwa kamar tarho mai aiki da tauraron dan'adam da kuma wasu kayayyakin intanet.

    Masu sa-ido tsakanin 80 zuwa 100 na Tarayyar Turai ne aka sa ran turawa don ganin yadda babban zaɓen da za a yi ranar 20 ga watan Disamba zai gudana.

    • Joseph Kabila: Yadda aka aike da miliyoyin kudin al'umma ga iyalai da abokan tsohon shugaban Kongo
    • Adadin wadanda suka rasu sakamakon arangama a sansanonin MDD a Dimokraɗiyar Congo ya kai 19
  6. Cutar kwalara ta kashe mutum 23 a ƙasar Habasha

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Akalla mutum 23 ne suka mutu sakamakon barkewar kwalara da ta addabi al’ummomin da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a gabashin Habasha, in ji kungiyar ba da agaji ta Save the Children.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Alhamis, kungiyar ba da agajin ta Birtaniya ta ce mutane fiye da 770 ne aka tabbatar suka kamu da cutar kwalara a cikin mako biyu kacal a wani yanki na kasar Somaliya, wanda ambaliyar ruwa ta fi tsanani a baya-bayan nan.

    Ambaliyar ruwan ta shafi mutum miliyan 1.5 a fadin ƙasar, inda adadin da aka tilastawa barin gidajensu ya kai 600,000, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

    Sai dai kashi 10 cikin 100 na wadanda abin ya shafa ne a halin yanzu ke samun agaji yayin da Habasha ke ci gaba da kokawa da gibin kudade, in ji ta.

    Sama da gundumomi 90 a fadin kasar Habasha sun ba da rahoton bullar cutar kwalara, inda kungiyar agaji ta Save the Children ta yi gargadin cewa lamarin na iya tabarbarewa, yayin da ake sa ran samun ruwan sama a aƙalla yankuna uku.

    • Abubuwan da ke janyo cutar amai da gudawa da hanyoyin magance ta
    • Cutar kwalara na kara kamari a wasu jihohin Najeriya
  7. Ƙasar China ta bai wa Afrika ta Kudu gudummawar janareta 450

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasar Afrika ta Kudu ta sami gudummawar Jenaretar samar da wutar lantarki guda 450 daga Ƙasar China domin magance matsalar ƙarancin wutar lantarki a ƙasar.

    Wannan gudummawar wani bangare ne na shirin ba da taimako na fasaha da kasashen China da Afirka ta Kudu suka rattabawa hannu a yayin taron BRICS na watan Agusta a birnin Johannesburg.

    A cikin yarjejeniyar, China ta yi alƙawarin ba da gudummawar kayan aikin gaggawa na rand miliyan 167 (dala miliyan 8.9) da tallafin raya kasa na rand miliyan 500.

    Afirka ta Kudu dai na fama da matsalar katsewar wutar lantarki lamarin da ya haifar da takaici matuka.

    Miliyoyin mutane suna kasancewa cikin duhu a kowace rana - wani lokaci har na tsawon sa'o'i 10 - a birane da garuruwa a fadin Afirka ta Kudu.

    • Najeriya: Yadda rashin lantarki ke kassara harkokin kasuwanci a fadin ƙasar
    • Dalilin da ya sa jam’iyyun siyasa 7 suka ƙulla ƙawance a Afrika ta Kudu domin ƙalubalantar ANC
  8. Hotunan zauren taron Hikayata ta 2023

    ...

    Zauren da za a gabatar da bikin karrama gwarazan gasar gajerun kagaggun labarai ta Hikayata da BBC Hausa ta shiya.

    ...

    A yau Alhamis ne da misalin karfe 4:00 na yamma za a gabatar da bikin a Abuja babban birnin Najeriya.

    ...
    Bayanan hoto, Wannan ne karo na takwas da ake gabatar da gasar, wadda BBC Hausa ke shiryawa.
    ...
    Bayanan hoto, Za a rabar kyaututtukan kudi da kambi da takardar shaidar shiga gasar ga gwarazan gasar ta bana
    ...

    Ku sha kallo lafiya, kuma za mu ci gaba da kawo muku bayanai a wannan shafi kafin da kuma a lokacin wannan biki.

  9. Shugaban COP28 ya musanta amfani da taron don ƙulla yarjejeniyar man fetur

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya a kan sauyin yanayi na COP28, kuma babban jami'in kamfanin man fetur na Hadaddiyar Daular Larabawa, (Adnoc) Sultan al-Jaber ya musanta zargin yin amfani da taron wajen kulla cinikin man fetur da iskar gas.

    Ya musanta bayanan wasu takardu da aka fallasa.

    Gidan rediyon BBC ya ruwaito a ranar Litinin cewa wasu takardu da aka fallasa, sun bayyana shirin da Hadaddiyar Daular Larabawa ke yi, na tattaunawa da kasashen duniya 15 a kan batun man fetur.

    Al-Jaber ya bayyanawa wani taron manema labarai cewa, irin wadannan zarge-zargen na da nufin zagon kasa ne ga shugabancinsa na COP28, yayin da BBC ta tsaya tsayin daka a kan rahoton da ta bayar na bincike.

    A yau ne aka bude babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na Cop28, inda shugabannin ƙasashen duniya suka fara hallara a Hadaddiyar Daular Larabawa.

    • Waiwaye: Ɗage haramcin bizar Dubai da yaƙi da yunwa
    • Ko kun san me ake tattaunawa a taron Majalisar Dinkin Duniya?
  10. Blinken na ziyara karo na uku a Isra'ila tun bayan harin 7 ga watan Oktoba

    Blinken and Israeli President

    Asalin hoton, EPA

    Sakataren wajen Amurka Antony Blinken ya gana da shugaban Isra'ila Isaac Herzog a birnin Tel Aviv yau.

    Blinken na wannan ziyara ce a yankin na Gabas ta Tsakiya karo na uku, tun bayan fara yakin Isra'ila da Hamas, ranar 7 ga watan Oktoba.

    "Mun gani a makon jiya, kyakkyawan sakamakon da aka samu na komawar mutanen da aka yi garkuwa da su zuwa gida, cikin danginsu," Blinken ya ce a lokacin ganawar.

    "Matakin kuma zai ba da damar kara kai tallafin jin kai ga fararen hulan da ba su ji ba, ba su gani ba a Gaza, wadanda ke bukatar hakan ido rufe. Don haka wannan al'amari ya haifar da sakamako mai kyau. Wannan muhimmin abu ne kuma muna fatan za a ci gaba."

    Blinken a yanzu yana tattaunawa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, kuma zai gana da Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas nan gaba a Ramallah.

    • Burin China a yaƙin Isra'ila da Hamas
    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
  11. Tinubu ya gana da sarki Charles

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya gana da Sarki Charles na Ingila gabanin babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP28 a Hadaddiyar Daular Larabawa.

    ...

    Asalin hoton, Ajuri Ngelale/Twitter

    ...

    Asalin hoton, Ajuri Ngelale/Twitter

  12. Ƴan ci-rani huɗu sun mutu a tekun Sifaniya

    ...

    Asalin hoton, SALVAMENTO MARITIMO/FACEBOOK

    Ƴan ci-ranin Moroko hudu sun mutu a gaɓar tekun kudancin Sifaniya, kusa da birnin Cadiz, inda aka kai wasu huɗu zuwa asibiti saboda tsananin sanyi.

    An gano gawawwakin mutanen huɗu waɗanda suka nutse a ranar Laraba a cikin kwale-kwalen da ya ɗauki ƴan ci-rani 32.

    An ruwaito cewa ma’aikatan jirgin sun tilastawa 27 daga cikin mutanen tsalle zuwa cikin tekun, kuma an ceto 23 da rai.

    Ƴan sandan Sifaniya sun fara bincike kan lamarin.

    Mataimakiyar Firaiministar Sifaniya kuma ministar kwadago, Yolanda Diaz, ta ce "ta firgita" da labarin.

    "Abu ne mara daɗi yayin da waɗanda suka zo neman rayuwa mai inganci suka gamu da ajalinsu,” in ji ta, yayin da take kira ga Turai ta ɗauki mataki.

    Ƙasar Sifaniya dai na ɗaya daga cikin manyan wuraren da ƴan ci-rani ke tashi daga Arewacin Afirka zuwa Turai, inda a cikin shekarar da ta gabata kaɗai, dubbunai suka tsallaka cikin Turai.

    • Yadda ƴan ci-rani ke jefa rayuwarsu cikin hatsari wajen tsallaka teku
    • Ƙaura mai hatsari da ba a cika dawo ba
  13. Ma'aikatan Thai sun koma Bangkok ga iyalansu

    ...

    Asalin hoton, Thai Ministry of Foreign Affairs

    Wasu ‘yan kasar Thailand 17 da aka sako sun koma Bangkok bayan da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su.

    Wasu daga cikin danginsu sun isa filin jirgin Suvarnabhumi da sanyin safiyar Alhamis, suna jiran dawowar ’yan uwansu.

    Sakin ‘yan kasar ya banbanta da yarjejeniyar da ya zuwa yanzu Hamas ta saki mata da kananan yara 70 na Isra’ila.

    Akwai sauran mutanen Thailand tara da ake garkuwa da su.

  14. Shugaban Isra'ila zai gabatar da jawabi kan rikicin Gaza a taron COP 28

    Ana sa ran shugaban Isra'ila Isaac Herzog zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi COP28 a Dubai, inda zai tattauna da jami'an diflomasiyya kan sako mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.

    Taron zai kuma samu halartar shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas.

    Shugaban na Isra'ila ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa "yana da niyyar shigar da shugabannin kasashen duniya a wani babban yunkuri na jin kai don mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su."

    • Yadda Hamas ta haɗa dakarun da suka kai wa Isra'ila harin 7 ga Oktoba
    • WHO ta ce ayyuka sun tsaya cak a babban asibitin Gaza
  15. Rashin adalci a shari'ar zaɓen Kano na iya haddasa tashin hankali - NNPP

    NNPP

    Asalin hoton, NNPP/Facebook

    Jam’iyyar adawa ta NNPP a Najeriya ta ce hana ta kwace mata zaben da ta ci a jihar Kano, zai iya janyo tashin hankalin da zai yaɗu zuwa sauran ƙasahen Afirka.

    Wata sanarwa da mukaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abba Kawu Ali, ya fitar, kuma babban jami'i mai binciken kuɗi na jam'iyyar, Ladipo Johnson ya karanta a gaban ofisoshin jakadancin Kasashen Yamma ranar Laraba, NNPP ta yi ikirarin cewa akwai alamun da ke nuna cewa ana yunkurin yi wa zaben mafi rinjayen al'ummar Kano zagon kasa.

    'Ya'yan jam'iyyar suna ci gaba da zanga-zanga a Kano tun bayan hukuncin kotun daukaka kara da ya sake tabbatar da soke nasarar gwamnan NNPP, Abba Kabir Yusuf.

    A ranar Laraba kuma, magoya bayan jam'iyyar sun yi zanga-zanga zuwa ofisoshin Tarayyar Turai da ofishin jakadancin Amurka da na Birtaniya da kuma Hukumar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas).

    Suna dai nuna ɓacin-rai ne kan hukuncin zaɓen gwamnan Kano da kotun korafin zaɓe da kuma ta ɗaukaka ƙara suka yanke a kan zaben gwamnan jihar Kano, da ya bai wa Nasir Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, gaskiya.

    Ladipo Johnson ya ce jam'iyyar ba ta kallon takardar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da wasa, "kuma za mu yi duk abin da ya kamata bisa tsarin doka domin ƙwato abin da duniya ta sani cewa namu ne."

    "Yayin da NNPP ta garzaya zuwa Kotun Koli don bin kadi, mun damu da batun zaman lafiya, musamman na jihar Kano da kuma arewacin Najeriya baki-ɗaya. Don haka, muna son Kotun Koli ta yi adalci wajen dawowa al'ummar jihar Kano da gwamna Abba Kabir Yusuf, nasararsu.

    "Yayin da muka je kotun karshe, hankula sun tashi a Kano. Kowane lungu-lungu da sako na jihar na cike da ɓacin rai, inda batun hukuncin kotun ya zama batun da ake tattaunawa a ko'ina, musamman a tituna, ofisohi, da gidaje," in ji NNPP.

    Ta kuma ce tana son faɗa wa shugabannin duniya cewa abin da ake shirin yi, ba abu ne mai kyau ga Najeriya kaɗai ba, har ma da Afirka da kuma duniya baki-ɗaya.

    "Yunkurin kwace wa al'umma nasara a Kano, zai haifar da sakamako a kan al'amuran siyasa da tattalin arziki da kuma rayuwar mutanen jihar," in ji jam'iyyar.

    NNPP ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki ciki har da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, su janyo hankalin shugaban ƙasa da Kotun Koli wajen tabbatar da cewa an yi wa jam'iyyar da kuma al'ummar Kano, adalci.

    • Takardun hukuncin shari'ar Kano sun tada jijiyoyin wuya
    • Me ya sa shari'ar zaɓen gwamna ta hana 'yan siyasar Kano barci?
  16. An kashe mutum uku a Birnin Ƙudus bayan dakatar da faɗa a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Israel Police

    Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ce an kashe mutum uku sakamakon wani harin harbe-harbe da aka kai birnin Kudus kuma akwai wasu shida da suka jikkata.

    Rundunar ‘yan sandan Israila da farko ta ce wasu mahara biyu ne suka bude wuta a wata tashar mota da ke wajen birnin Kudus a safiya yau Alhamis.

    'Yan sandan dai sun ce daga baya jami'an tsaro sun kashe maharan biyu da ake zargi.

    Ministan tsaron kasar Isra'ila Itamar Ben Gvir ya ce maharan ƴan ƙungiyar Hamas ne kuma mazauna gabashin birnin Kudus ne.

    "Waɗannan da alama 'yan Hamas ne, waɗanda ke magana da muryoyi biyu, murya ɗaya na abin da ake kira tsagaita buɗe wuta da kuma muryar ta'addanci ta biyu," in ji Gvir, wanda ke magana da manema labarai a wurin da aka kai harin.

    Ya ƙara da cewa harin ya nuna muhimmancin raba makamai ga fararen hula a Isra'ila.

    • Wane ne Yahya Sinwar shugaban Hamas na Gaza?
    • Isra'ila-Gaza: Me ya sa wannan yaƙi ya zama daban da sauran
  17. Me masana ke cewa game da kasafin kuɗin Tinubu na 2024

    Masana tattalin arziki a Najeriya na cigaba da tofa albarkacin bakinsu a kan kudurin kasafin kuin ƙasar na badi, wanda shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa majalisar dokoki.

    Wasu masana na ganin cewa gwamnati na da kyakkyawar aniya ta inganta rayuwar al`umma, amma kuma suna sukar kasafin, saboda, a cewar su, ba a gina shi a kan asashin da kwalliya za ta biya kudin sabulu ba.

    Ga rahoton Ibrahim Isa.

    Bayanan sautiLatsa hoton sama domin sauraron rahoto
  18. Mutum 13 sun mutu a wata gobara a Kazakhstan

    ...

    Asalin hoton, ...

    Hukumomi a Kazakhstan sun ce an samu tashin gobara a wani otel a daya daga cikin manyan biranen kasar Almaty, inda mutane 13 suka mutu.

    Jami'ai sun ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Alhamis agogon ƙasar, an kuma yi nasarar kwashe baƙi da ke zaune a otal din su 59 zuwa wani wurin na daban.

    Mutanen sun mutu ne sakamakon shakar hayaki, kuma kawo yanzu ba a san komai dangane da musabbabin tashin gobarar ba.

    Jami'an kashe gobara sun ce sun yi amfani da injinan feshin kashe gobara 13 kafin su shawo kan wutar kar ta yadu gine-ginen da ke kusa da Otal din.

    • Gobara ta ƙona kimanin shaguna 50 a kasuwar Singa
    • Me yake jawo gobara a kasuwannin Najeriya kuma yaya za a magance ta?
  19. COP28: Shugabannin duniya sun fara hallara a UAE don taron sauyin yanayi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabannin ƙasashen duniya sun fara hallara a Hadaddiyar Daular Larabawa, a babban taron majalisar dinkin duniya kan sauyin yanayi na Cop28.

    Taron na zuwa ne bayan duniya ta fuskanci matsanancin yanayin da aka jima ba a gani ba.

    Matakin yin taron na bana a birnin Abu Dhabi ya janyo ce-ce-ku-ce, wadda ɗaya ce daga cikin manyan kasashen da ke fitar da man fetur da iskar gas a kasuwar duniya.

    A farkon makon nan wasu bayanai da aka kwarmatawa da BBC ta gani sun nuna yadda daular Larabawan ke ƙokarin amfani da damar taron sauyin yanayin wajen kulla huldar kasuwannin iskar gas da man Fetur.

    Sai dai shugaban taron, Dr Sultan al-Jaber, ya musanta hakan.

    • Ko kun san me ake tattaunawa a taron Majalisar Dinkin Duniya?
    • Wace ƙungiya ce G20 kuma me ya sa take da muhimmanci?
  20. Fitaccen tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Henry Kissinger ya rasu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Henry Kissinger, da ke sahun gaba wajen sauya manufofin hulda da kasashen wajen kasarsa, ya rasu, yana da shekara 100 a duniya.

    Ya yi aiki tare da shugabannin Amurka Nixon da Ford, lamarin da ya sanya shi yin fice a duniya.

    Henry Kissinger ya tsere daga ƙasarsa ta haihuwa wato Jamus a lokacin da yake shekara 15 a duniya.

    Bayan zuwa Amurka, ya fara ne da shiga aikin soja daga baya ya zama ɗalibin Jami'ar Harvard.

    Ya jagoranci Amurka kan batutuwa da dama da suka hadar da na China da tsohuwar Tarayyar Sobiyet da Gabas ta Tsakiya.

    Sai dai, ba za a manta da harin bam da Amurka ta kai kan kasar Cambodia ba, da dubun dubatar mutanen da suka mutu a lokacin mulkinsa, don haka wasu ne ma wasu ke zarginsa da aikata laifin yaki.