Aisha Adam Hussaini ce ta lashe gasar Hikayata ta BBC Hausa, 2023

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa, Abdullahi Bello Diginza and Haruna Kakangi

  1. Rufewa

    Masu bin mu a shafin BBC Hausa kai-tsaye, nan muka kawo ƙarshen labaran abubuwan da suka faru musamman kan bikin gasar Hikayata da BBC Hausa ta shirya.

    Muna godiya da bibiyarmu da kuka yi domin ganin yadda wannan gagarumin biki ya gudana, duk kuwa da ba ku samu damar halarta ba.

    Muna fatan wata shekarar ku samu damar halarta, ko ma ku kusance cikin waɗanda za su yi nasara.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke fatan mu kwana lafiya

  2. Hikayata ta ɗaukaka matsayinmu a rayuwa - Tsoffin gwarazan Gasar

    .
    Bayanan hoto, Gwarazan gasar Hikayata ta shekarar 2021

    Tsofaffin gwarazan gasar Hikayata da suka lashe gasar a shekarar 2021, sun shaida wa BBC irin ɗaukakar da suka samu bayan lashe gasar.

    Aisha Dalil - wadda ita ce ta zo da ɗaya a shekarar 2021 - ta ce ta samu tarin alfarmomi bayan nasarar da ta samu ta lashe gasar.

    ''Akwai 'yar uwata ma da aka yi wa alfarma saboda sunanmu ya zo ɗaya, sannan ni ma akwai wani wuri da naje ana bin layi, amma aka yi min alfarma saboda Hikayata''.

    Haka ita ma Zulaihat Al'assan - wadda ke cikin waɗanda suka yi nasara a 2021 - ta shaida wa BBC cewa ta samu damarmaki masu tarin yawa a rayuwarta sakamakon nasarar da ta yi a gasar ta Hikayata.

    ''Haƙiƙa gasar Hikayata ta zame min wani matakin nasara a rayuwata, ta zame mini wani tsani da na taka ta kuma kai ni wani matsayi da ban yi tunanin kai wa ba a rayuwata".

    Ta ƙara da cewa nasarar da ta yi a gasar ta taimaka mata wajen inganta tare da ci gaba da rubuce-rubucenta, lamarin da ya sa har ta kai gamatakin wallafa littafi.

    ''Kuma yanzu haka ma ina dab da wallafa wani sabon littafi da na rubuta mai matuƙar muhimmanci, wannan ba karamar nasara ba ce a rayuwata''.

  3. Yadda Fati Nijar ta cashe a bikin Hikayata 2023 na BBC Hausa

    Bayanan bidiyo, Yadda Fati Nijar ta cashe a bikin Hikayata 2023 na BBC Hausa
  4. Bayani daga bakin gwarzuwar gasar BBC Hausa ta Hikayata 2023

    Bayanan bidiyo, Bayani daga bakin gwarzuwar gasar BBC Hausa ta Hikayata 2023
  5. 'Gasar Hikayata ta haɓaka adabi da al'adun Hausawa'

    Jagoran alƙalan gasar Hikayata, Dakta Jibril shu'aibu Adamu ya ce sun yi amfani da ma'aunai daban-daban wajen tantance labaran da suka yi nasarar lashe gasar Hikayata ta bana.

    ''Akwai ƙa'idoji da ma'aunai da muka yi amfani da su domin tantance waɗannan labari a matakai daban-daban", in ji Dakta ...

    Ya ƙara da cewa wani abin jan hankali shi ne labaran da suka yi zarra a gasar, sun ƙunshi abubuwa na zamani da abubuwan da ke faruwa a rayuwa ta zahiri.

    ''Hikayat ta taimaka wajen haɓaka adabin Hausa da al'adu, domin kuwa za ka ga cewa duka rubuce-rubucen da ake yi a gasar suna mayar da hankali ne wajen haɓaka al'adun Hausawa''.

  6. 'Gasar Hikayata ta sauya salon rubutun zube'

    b

    Fitaccen masanin sadarwa a Najeriya Farfesa Abdallah Uba Adamu., wanda ya kuma ya kasance babban bako mai gabatar da jawabi a taron bikin Hikayata ya ce gasar ta sauya salon rubutun zube.

    Ya ce gasar na mayar da hankali wajen lura da al'amuran zamani, maimakon jigogin da ake amfani da su a rubuce-rubucen zube a shekarun baya.

    ''A yanzu za ka ga cewa matan da ke shiga gasar suna okarin sanya abubuwan fasahar zamani a cikin rubuce-rubucensu''.

    Ya ara da cewa ''Abubuwan da suka shafi kafofin sada zumunta na zamani da fasahohin intanet da na yahoo''.

    Daga arshe ya shawarci masu sha'awar shiga gasar da su ria la'akari da addini da al'ada a wajen rubuce-rubucen nasu.

  7. Na ji farin ciki marar misaltuwa da nasarar da na yi - Gwarzuwar Hikayata

    ...

    Tauraruwar gasar Hikayata ta 2023, Aisha Adam Hussaini ta bayyana farin ciki da murna da ta shiga a lokacin da aka ayyana sunanta a matsayin wadda ta zo ta ɗaya a gasar.

    'Har muka iso zauren Hikayata ba mu san mataki na nawa muka zo ba, sai a lokacin bikin aka bayyana'', kamar yadda ta shaida wa BBC.

    ''Bakina ba zai iya misalta irin farin ciki da murnanr da na shiga a lokacin da na ji sunana a matsayin wadda ta zo ta aya a gasar''.

    Labarin nata mai taken Rina A Kaba ya yi tsokaci ne a kan irin yadda mata ke amfani da magungunan mata, ba tare da la'akari da irin illar da ire-iren waanan magunguna ke haifarwa ba.

  8. Hotunan yadda aka gudanar da bikin gasar Hikayata ta 2023

    .
    Bayanan hoto, Shugaban sashen Hausa na BBC da mai ɗakin gwamnan jihar Katsina da uwar gidan shugaban jam'iyyar APC na ƙasa a lokacin da suke miƙa kyauta ga wadda ta zo ta ɗaya a gasar, Aisha Adam Hussaini daga jihar Kano
    .
    Bayanan hoto, BBC ta bai wa gwarzuwar kyautar naira miliyan ɗaya, yayin da ta samu ƙarin kyaututtuka daban-daban daga maharta taron
    .
    Bayanan hoto, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, da Sanata Lawal Usman da aka fi sani da 'mista La' tare da sarkin Katagum a lokacin da suke mika kyautar naira 750,000 ga wadda ta zo ta biyu a gasar, Aisha Abdullahi Yabo
    .
    Bayanan hoto, Baki da dama ne suka samu halarci taron karrama gwarazan gasar
  9. Gwarazan gasar Hikayata ta BBC Hausa, 2023

    ...

    Ta daya: Aisha Adam Usaini

    Ta biyu: Aisha Abdullahi Yabo

    Ta uku: A'isha Sani Abdullahi

  10. Labarai da dumi-dumi, Gwarazan Gasar Hikayata ta 2023 sun samu ruwan kyautuka

    Gwarazan Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta 2023 sun samu kyautuka daga manyan baki da suka halarci bikin karramawar a Abuja.

    Ga bayanin wasu daga cikin manyan bakin da suka bai wa gwarazan gasar bana kyautar kudi kamar haka:

    1. Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, uwargidan shugaban jam'iyyar APC na kasa ta bai wa:

    a. Aisha Adam Usaini - $1,500

    b. Aisha Abdullahi Yabo - $1,000

    c. A'isha Sani Abdullahi - $500

    2. Gwamna Kebbi Nasir Idris N3,000,000

    3. Sanata Tanko Al-Makura N1,000,000

    4. Uwargidan Gwamnan jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Umar Radda N1,000,000

    5. Sanata Abdul'aziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, kuma Sanatan Zamfara ta Yamma N5,000,000

    6. Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila N500,000

  11. Labarai da dumi-dumi, A'isha Adam Usaini ce gwarzuwar Hikayata ta 2023

    Aisha Usaini

    Sunan labarin gwarzuwar gasar Hikayata ta 2023 shi ne Rina a Kaba

  12. Labarai da dumi-dumi, A'isha Abdullahi Yabo ce ta zo ta biyu a bana

    Aisha Yabo

    A'isha Abdullahi Yabo ce ta zo ta biyu da labarinta mai suna Bakin Kishi.

    Ta samu kyautar naira 750,000 da lambar yabo

  13. A'isha Sani Abullahi ce ta zo ta uku a gasar Hikayata ta 2023

    A'isha Sani Abdullahi

    A'isha Sani Abdullahi daga birnin Jos a jihar Filato ce ta zo ta uku a Gasar rubuta gajerun labarai ta mata zalla a 2023.

    Ita ce ta rubuta labarin Tuwon Kasa don wannan gasa ta BBC Hausa.

    Kuma ta samu lambar yabo da kyautar kudi naira 500,000.

  14. 'Harshen Hausa ya fi kowane harshe yaduwa a Afirka'

    ,,

    Babban mai gabatar da jawabi a dakin taron, Farfesa Abdallah Uba Adamu na jami'ar Bayero ya ce BBC ta kasance hantsi leka gidan kowa ta fannin sadarwar zamani.

    Yayin da yake gabatar da jawabi a wajen dakin taron karrama gwarazan gasar, Farfesa Abdallah ya ce BBC ba ta nuna son zuciya ta fuskar watsa labaranta.

    Ya kara da cewa BBC ba ta nuna son zuciya a lokacin da take watsa labaranta.

    Ya kuma ce kaf nahihar Afirka babu wani harshe da ya fi harshen Hausa yaduwa.

  15. Ko Isra'ila za ta ci gaba da yaki, dole ne a kare fararen hula - Amurka

    Blinken in Israel

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Blinken ya kuma gana da Shugaban Isra'ila Isaac Herzog a lokacin wannan ziyara tasa

    Yanzu kuma, bari mu dan waiwayi Gabas ta Tsakiya, inda sakataren wajen Amurka yake ziyara karo na uku kenan tun bayan fara yakin Isra'ila da Hamas ranar 7 ga watan Oktoba.

    Wata sanarwa da aka fitar a kan ganawar Anthony Blinken da Firaminista Benjamin Netanyahu, ta ce sakataren harkokin wajen Amurka, ya jaddada goyon bayan Amurka ga ''yancin Isra'ila na kare kanta daga tarzomar 'yan ta'adda' a daidai lokacin da take aiki da dokokin kasashen duniya.

    Amma ta kara da cewa: "Sakataren ya jaddada muhimmancin la'akari da bukatun kare ayyukan jin kai da fararen hula a kudancin Gaza, kafin daukar duk wani matakin sojoji a can."

    Tun bayan fara yakin, ma'aikatar lafiyar Gaza wadda Hamas ke tafiyarwa ta ce mutane sama da 14,800 aka kashe yayin hare-haren Isra'ila a ciki har da kananan yara kimanin 6,000.

    Kuma kamar yadda wakilinmu na diflomasiyya ya nunar tun da farko, wannan bayani na sakatare Blinken ya nuna cewa sakon Amurka ga Isra'ila ga alama karara - na nuna cewa jazaman ne sai an canza salo da dabarun aiki

  16. Ma'aikatan BBC Hausa a wurin bikin karrama gwarazan Hikayata 2023

    Shugaban sashen Hausa na BBC da Usman Minjibir
    Bayanan hoto, Shugaban sashen Hausa na BBC da Usman Minjibir
    Badariyya Kalarawi
    Bayanan hoto, Badariyya Kalarawi
    ...
    Bayanan hoto, Shugaban sashen Hausa, Aliyu Tanko da Haruna Kakangi
    ...
    Bayanan hoto, Aliyu Tanko da Abdulrazak Bello
    Badariyya da Usman da Rabia'atu
    Bayanan hoto, Badariyya da Usman da Rabia'atu
    Umaymah Sani
    Bayanan hoto, Umaymah Sani
    ...
    Bayanan hoto, Aminu Kutama da Madina Maishanu da Fauziyya Hassan
    ..
    Bayanan hoto, Abdullahi Bello da Fatima Othman
    ..
    Bayanan hoto, Mustapha Shaba
    ...
    Bayanan hoto, Awwal Janyau
    ...
    Bayanan hoto, Mukhtar Bawa da Umar Mika'il
    ...
    Bayanan hoto, Lawal Nuhu Sualaiman
    ..
    Bayanan hoto, Umar Mika'il da Abba Awwal
    ...
    Bayanan hoto, Khalifa Dokaji
  17. Shugaban sashen Hausa na BBC na gabatar da jawabin maraba

    .

    Shugaban sashen Hausa na BBC Aliyu Abdullahi Tanko na gabatar da jawabin maraba ga dimbin bakin da suka halarci taron.

    Shugaban sahen ya yi wa manyan bakin da suka halarci taron fatan komawa gidajensu lafiya

  18. Bikin Hikayata: Dakin taro ya dauki harama

    b
    Bayanan hoto, Badariya Tijjani Kalarawi

    Tuni dakin taron taron da ake gabatar da bikin karrama gwarazan Hikataya ya cika makil gabanin fara gagarumin bikin.

    Badariyya Tijjani Kalarawi tare da Rabi'atu Kabir Runka ne za su jagoranci gabatar da bikin.

    ..
    Bayanan hoto, Rabi'atu Kabir Runka da Badariyya Tijjani Kalarawi

    Tuni manyan baki suka hallara a dakin taron, ciki har da sarakunan gargajiya da manyan 'yan siyasa

  19. Bikin Hikayata: Baki na ci gaba da isa dakin taro

    ,

    Tuni baki ke ta kwarara babban dakin taron da ake gabatar bikin karrama gwarazan gasar Hikayata.

    ,

    Baki maza da mata, manya da matasa ne ke ta turuwa domin zuwa wajen taron.

    Wannan ne dai karo na takwas da BBC Hausa ke shirya wannan gasa, da nufin karfafa wa mata gwiwa a fagen rubuce-rubuce

  20. Shirye-shiryen bikin fara bikin gasar Hikayata

    ..

    Shirye-shirye sun kankanma domin fara gabatar da bikin gasar Hikayata ta BBC Hausa.

    Da maraicen nan ne za a gabatar da gagarumin bikin domin karrama mutanen da suka yi fice a gasar.

    Matan da suka yi nasara a gasar za su samu kyaututtukan kudi da lambobin yabo da kuma takardun shaidar shiga gasar.