Amurka za ta dawo da kai agajin abinci a Habasha

Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta ce za ta ci gaba da kai kayan agajin abinci a faɗin ƙasar Habasha a watan Disamba, watanni shida bayan dakatar da su bisa zargin cin hanci da rashawa.
Hukumar ci gaban ƙasashen duniya ta Amurka (USAid) ta ce gagarumin garambawul zai tabbatar da cewa kayan abinci sun kai ga waɗanda suka fi buƙata.
Sake dawo da tallafin zai kasance a kan gwaji na shekara guda, in ji hukumar.
Miliyoyin mutanen Habasha na fuskantar ƙarancin abinci saboda illar tashe-tashen hankula da tsananin yanayi.
Amurka ta dakatar da bayar da agaji a watan Yuni, inda ta yi ƙorafin yadda ake karkatar da kayayyakin tare da hadin gwiwa.
- Anya tallafi na kaiwa ga 'yan Ethiopia kuwa?
- Yakin Ethiopia da Tigray: Labarin birnin Mekelle da aka raba da sauran duniya


