An zaɓi Najeriya cikin ƙasashen da za su nemo mafita kan rikicin Gaza

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najieriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Mukhtar Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. 'Yan majalisar dokokin Uganda sun amince a kawo karshen shigar da mai ta Kenya

    ...

    Asalin hoton, ...

    A ranar Talata ne majalisar dokokin Uganda ta amince da wani kudirin doka da ya baiwa kamfanin hakar mai na kasar, Uganda National Oil Company (Unoc), damar sayo da rarraba mai a kasuwannin cikin gida.

    Yayin da ake jiran amincewa daga shugaba Yoweri Museveni, wannan dokar na da nufin kawo karshen dogaro da kamfanonin Kenya da suka dade suna shigar da mai zuwa ƙasar.

    'Yan majalisar da suka goyi bayan kudirin sun ce zai rage farashin mai ta hanyar yanke masu tsaka-tsaki da "kamfanonin mai da ke tasiri ga farashin mai".

    Ministar makamashi ta Uganda Ruth Nankabirwa a kwanan baya ta ce ƙasar na buƙatar dakatar da shigo da mai ta kamfanonin kasar Kenya saboda "hakan na nuna rashin wadatar kayayyaki a Uganda."

    A halin yanzu dai Uganda tana shigo da sama da kashi 90% na man fetur ta tashar ruwa ta Mombasa ta kasar Kenya, tare da shirin kara jigilar mai ta kasar Tanzaniya.

  2. Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kammala sauraron shari'ar zaɓen gwamnan Nasarawa

    Abdullahi Sule

    Asalin hoton, Abdullahi Sule/X

    Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta kammala sauraron shari'ar zaɓen gwamnan jihar Nasarawa.

    Gwamnan jihar Abdullahi Sule na jam'iyyar APC ne ya shigar da ƙarar, yana ƙalubalantar hukuncin kotun ƙorafin zaɓe da ta soke nasarar da ya samu a watan Fabrairu, inda ta ayyana David Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

    Kotun mai alƙali uku ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Uchechukwu Onyemenam, ta shaida wa ɓangarorin da abin ya shafa cewa za ta sanar da su ranar da za ta yanke hukunci.

    A zaman kotun na yau Laraba, lauyan Gwamna Sule, Wole Olanipekun, wanda ya shigar da hujjoji biyar don ƙalubalantar hukuncin kotun zaɓen gwamnan Nasarawa, ya buƙaci kotun daukaka ƙarar ta yi watsi da hukuncin ƙaramar kotu.

    Olanipekun ya ƙara da cewa kotun ta ƙi amincewa da hujjojin shaidunsu a yayin zaman da ta yi, kuma ba ta yi amfani da bayanai daga na'urar tantance masu zaɓe (BVAS) da aka gabatar mata ba.

    Sai dai, lauyan Ombugadu da PDP, Kanu Agabi, ya buƙaci kotun ta yi watsi da ƙarar da Gwamna Abdullahi Sule ya ɗaukaka.

    Agabi wanda ya miƙa wa kotun hukuncin da ƙaramar kotun ta yanke, ya ce a lokacin yanke hukuncin, ƙaramar kotun ta yi cikakken bayani kan yadda ta kai ga yanke hukuncin nata.

    • Kotu ta soke zaɓen Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa
    • 'Kammala ayyukan da na fara ta fi muhimmanci sama da wa'adi na biyu'
  3. Wani likita da aka ritsa da shi a asibitin Al-Shifa ya yi bayani kan halin da suka shiga, Rahoton Orla Guerin daga Birnin Kudus

    Mun yi kokarin samun wani likita da ya makale a cikin Asibitin Al-Shifa, wanda ya zama wata cibiyar bukatun ayyukan jin kan gaggawa, da dakarun sojin Isra'ila suka kutsa, suka shiga cikin dare.

    Dr Ahmed Mokhallalati ya zazzage fushi da bacin rai da kuma damuwar da ke da ita game da halin da marasa lafiyansa suke ciki.

    Ya yi tambaya shin ina kungiyar ba da agaji ta Red Cross take, kuma ina gwamnatocin Birtaniya da na Amurka.

    "Shin kowa jira kawai yake sai mun mutu a nan, sannan a ce 'Allah ya ji kansu, mutanen kirki ne'?"

    Likitan fidar ya kuma yi jawabi a kan fargabar da yake da ita game da ma'aikatan lafiya da marasa lafiyan da suka ritsa da su a cikin Al-Shifa yayin da dakarun Isra'ila suka kutsa kai.

    Ya ce sojojin Isra'ila sun harbi mutanen da suka yi yunkurin barin asibitin a 'yan kwanakin nan, kuma har wasu daga ciki sun riga mu gidan gaskiya. Isra'ila ta ce tana kai hari ne a kan Hamas sannan tana kokarin ganin ta rage cutar da fararen hula.

    Ta zargi Hamas da gudanar da cibiyar tafiyar da ayyukan soji a karkashin asibitin. Likitan ya fada mana cewa bai taba ganin ko bindiga daya ba ko kuma kasancewar Hamas a asibitin, duk da yake ya ce ba shakka akwai hanyoyin karkashin kasa a kasan duk wani gini da ke Gaza ciki har da asibitin Al-Shifa.

    Dr Mokhallalati ya dage a kan cewa fararen hula ne kawai a asibitin kuma ya kalubalanci sojojin Isra'ila su kawo shaida da ke nuna kasancewar Hamas a wurin.

  4. Lamarin tsaro na ƙara taɓarɓarewa a Najeriya - Rahoto

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani rahoton da kamfanin Beacon Consulting, mai nazari kan tsaro a shiyyar Afirka ta yamma ya fitar ya nuna cewa fiye da mutum dubu aka kashe a Najeriya a watan Oktoban 2023 sanadiyyar hare-haren `yan bindiga da mayakan Boko Haram.

    Kazalika rahoton ya ce fiye da mutum 500 ne aka sace don karbar kudin fansa.

    Rahoton da bayyana cewa lamarin tsaro ya kara tabarbarewar a Najeriya, daga watan Satumban wannan shekarar zuwa watan Oktoban da ya wuce.

    Kamfanin Beacon Consulting, a rahoton nasa na watan Oktoban da ya wuce ya bayyana cewa Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubale ta fannin tsaro a sassan kasar da dama.

    Ya ce ana fama da matsalar harin `yan bindiga da wasu kungiyoyi, ciki hár da kungiyar Boko Haram da ta IPOB, wato masu fafutukar ballewa da nufin kafa kasar Biafra.

    Kuma alkaluman da kamfanin ya fitar sun nuna an rasa rayukan jama`a, an kuma sace mutane a hare-haren da aka kai kan al`umma a kananan hukumomi 266 da ke fadin Najeriya.

    Alƙaluman sun nuna lamarin ya fi kamari ne a arewacin Najeriya, inda aka kashe mutum 326 a jihar Borno, jihar Zamfara kuma an kashe mutum 262, Yobe kuma mutum 60, sai kuma Binuwai 38. Yayin da mutum 39 suka rasu a jihar Rivers, Anambara 27, Lagos kuma 19.

    • Yadda ƙungiyar Ansaru ke jan matasa a Birnin Gwari
    • 'Rashin tsaro ya nakasa mu, dusa muke ci domin rayuwa a yanzu'
  5. An zaɓi Najeriya cikin waɗanda za su nemo mafita kan rikicin Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ƙasashen musulmi ta duniya ta OIC da ta ƙasashen larabawa sun zaɓi Najeirya cikin jerin ƙasashen da aka ɗora wa alhakin sasantawa tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa don kawo ƙarshen yaƙin da ke tsakanin ƙasashen.

    Wanda hakan ya sa Najeriya ta zama ƙasar baƙar fata daga yankin kudu da sahara a Afrika da aka zaɓa don yin wannan sulhu.

    Sauran ƙasashen da aka zaɓa domin shiga tsakani kan rikicin na Isra’ila da Falasɗinawa sun haɗa da Saudiya, da Jordan, da Masar, da Qatar, da Turkiya, da kuma Indonisiya.

    Ministan harkokin waje na Najeriya, Yusuf tuggar, wanda ya tabbatar wa BBC da batun, ya ce wanna ya ƙara ɗaukaka darajar Najeriya.

    Ya kuma ce matakin zai taimaka wajen matsa wa ɓangarorin biyu lamba wajen kawo dawwamammen zaman lafiya a tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa.

  6. Qatar na son Hamas ta saki 'yan Isra'ila 50 don tsagaita wuta tsawon kwana uku

    Yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan yaƙi a Gaza, rahotanni sun ce masu shiga tsakani na Qatar na tattaunawa kan yarjejeniya tsakanin Hamas da Isra'ila game da sakin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a harin na ranar 7 ga watan Oktoba da kuma Isra'ila ta tsagaita buɗe wuta.

    Yarjejeniyar, wadda ake tattaunawa tare da hadin gwiwar Amurka, za ta kunshi sakin fararen hula kusan 50 da aka yi garkuwa da su daga Gaza, domin musanya yarjejeniyar tsagaita bude wuta na kwanaki uku,

    Yarjejeniyar da aka tsara, tare da hadin gwiwar Amurka, ta ƙunshi sakin 'yan Isra'il 50 da Hamas ke garkuwa da su don a tsagaita wuta na kwana uku kamar yadda wani jami’in da ya yi bayani kan tattaunawar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Bugu da kari, za a saki wasu mata da kananan yara Falasdinawa da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila, kuma Isra'ila za ta kara yawan taimakon jin kai a Gaza.

    Sun kara da cewa, Hamas ta amince da yarjejeniyar, amma Isra'ila ba ta yi ba, kuma tana ci gaba da tattaunawa kan batun.

  7. Farashin kayan masarufi ya ƙara tashi a Najeriya

    ...

    Farashin kayan masarufi a Najeriya ya haura zuwa kashi 27.33 cikin 100 a watan Oktoban 2023, sanadin hauhawar farashin kayan abinci bayan cire tallafin man fetur na gwamnatin Bola Tinubu.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar na Oktoban 2023 a ranar Laraba.

    Rahoton ya nuna tashin farashin kayan masarufi daga kashi 26.72 cikin 100 na watan Satumba 2023 zuwa 27.33 cikin 100 inda yake nuna ƙaruwar 0.61 cikin 100.

    Bugu da ƙari, rahoton ya kuma yi nuni da cewa, hauhawar farashin kaya a duk shekara ya kai 6.24 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Oktoba na shekarar 2022 wanda ya kasance a kashi 21.09 cikin 100.

    • Hanyoyi tara da za su taimaka muku rage kashe kuɗi sakamakon tashin farashin kayayyaki
    • ‘Matsin rayuwa ya tursasa mini sakin uwargidata don samun saukin dawainiya’
  8. Mene ne ke faruwa?

    Gaza war

    Asalin hoton, Getty Images

    Da misalin karfe 2:30 na rana agogon Gaza da Isra'ila, ga yadda abubuwa suka kasance:

    • Wani dan jarida a cikin asibitin Al-Shifa a Birnin Gaza ya ce dakarun Isra'ila na cikin ginin asibitin, inda suke bi daki-daki suna gudanar da tambayoyi ga marasa lafiya da ma'aikatan lafiya, sannan sun tara maza a haraba
    • Rundunar sojojin Isra'ila ta ce aikin da ta sa gaba a asibitin Al-Shifa yana ci gaba kuma dakarunta na bincike don neman "kayan aikata ta'addanci da makaman" kungiyar Hamas
    • Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai kayayyakin asibiti, ciki har da kwalaben sanya jarirai bakwaini zuwa asibitin amma wata kungiyar ba da agaji a fannin lafiya ta ce ba kwalaben sanya bakwaini ake bukata ba - man fetur din da za a kunna su, su yi aiki
    • Babban jami'in ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya da kuma babban daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya sun bayyana damuwa game da tsaron lafiyar ma'aikatan asibiti da marasa lafiya, bayan aikin da dakarun Isra'ila a cikin asibitin Al-Shifa
    • An man fetur lita 25,000 zuwa kudancin Gaza ta hanyar mashigar Rafah - karon farko kenan da Isra'ila ta bari aka shigar da irin wannan kayan amfani tun da aka fara yaki
    • Shigar da man fetur din na nufin manyan motocin daukar kaya na Majalisar Dinkin Duniya za su iya samun mai, amma har yanzu Isra'ila tana hana kai man fetur din zuwa asibitoci da cibiyoyin samar da ruwan sha da na tsaftar muhalli
    • Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya fara sauka a Gaza, abin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce zai sanya "mawuyacin halin" da ya tilasta wa al'ummar Gaza ficewa daga gidajensu ya "kara muni"
  9. MDD za ta koma kai kayan agaji ta sama zuwa Nijar

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Majalisar Dinkin Duniya (MDD) za ta ci gaba da kai kayan agaji da kwashe ma'aikatanta a Nijar yayin da gwamnatin sojin ƙasar ta janye takunkumin hana zirga-zirgar jiragen sama a cikin gida.

    Hukumar kula da ayyukan jin kai ta sama ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHAS) ta samu sanarwar cewa an dage takunkumin zirga-zirgar jiragen sama na ayyukan cikin gida, wanda ke ba da damar dawo da ayyukan.

    Ta ce wannan yunƙurin zai sauƙaƙa isar da kusan tan 2.4 na kayayyakin jinya da taimako a kowane wata, tare da "kwashe ma'aikata da kayan agaji masu mahimmanci ga lafiya da tsaro".

    Duk da cigaban da aka samu, MDD na hasashen kalubalen da za a fuskanta wajen zuba wa jiragenta man fetur.

    MDD a watan Agusta ta ce za ta ci gaba da kai kayan agaji kasar da ke yammacin Afirka bayan da aka hamɓarar da shugabanta Mohamed Bazoum a wani juyin mulki a watan Yuli.

    Sai dai kasashen Yammacin duniya da suka hada da Faransa da Amurka da kuma Tarayyar Turai sun janye tallafin da suke bai wa kasar sakamakon juyin mulkin.

    A cewar MDD, kusan 'yan Nijar miliyan 4.3 ne suka dogara da taimakon jin-kai.

  10. Babban jami'in Man United Arnold zai bar ƙungiyar

  11. Man fetur ya shiga Gaza, amma ga manyan motocin MDD kawai

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Tun bayan munanan hare-haren da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, Isra'ila ta kakaba wa Gaza kawanya, tare da hana shigar da man fetur zuwa Gaza..

    An takaita tallafin jin kai daga Masar, kuma a cikin wannan mako, sauran man da Majalisar Dinkin Duniya ke da shi a Gaza ya kare.

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa an daina rarraba kayan agaji a Gaza.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce isar lita 25,000 a yau na man fetur zuwa Gaza kaɗan ne kawai na adadin da ake bukata na ayyukan jin kai.

    Ta ce har yanzu an hana shigar da man fetur don sarrafa janareta a asibitoci da wuraren ruwa da tsaftar muhalli.

    Kamfanonin sadarwa sun ce suna sa ran kashe hanyar sadarwa ta wayar tarho da katse intanet a cikin yini guda saboda ƙarancin mai.

  12. Asibitin Al-Shifa ya zama alama da ke nuna yaƙi

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Babban asibitin birnin Gaza, Al-Shifa, ya zama wata alama da ke nuna yaƙi.

    Yayin da mamayar Isra'ila ke haddasa hasarar rayuka da barna, asibitin na fuskantar matsalar bukatar agajin gaggawa

    Sai dai matsalar ta ta'allaka ne kan rashin man fetur, yayin da Isra'ila ta takaita shigarta, tana mai cewa Hamas na iya yin amfani da shi ta hanyar da ba ta dace ba.

    Halin da ake ciki a asibitin Al-Shifa yana nuna irin sarkakiyar rikice-rikicen.

    Isra'ila dai ta yi iƙirarin kawo man fetur da ƙwalaben saka jarirai.

    • WHO ta ce ayyuka sun tsaya cak a babban asibitin Gaza
    • Tsagaita wuta zai ba Hamas damar sake shiri don kai hare-hare - Anthony Blinken
  13. Ƙasar Zimbabwe na gudanar da bincike kan mutuwar ɓauna 16

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Hukumomin ƙasar Zimbabwe na gudanar da bincike kan mutuwar bauna 16 a kusa da dajin Hwange na kasar.

    Tinashe Farawo, mai magana da yawun hukumar kula da wuraren shakatawa na kasar Zimparks, ya fada a shafin sada zumunta na X cewa, an dauki samfura don gwaji bayan an gano gawarwakin dabbobin a sansanin namun daji na Matetsi ranar Talata.

    Sansanin yana arewa maso yamma tsakanin Hwange National Park da Victoria Falls.

    Shafin intanet mai suna ConserveZim ya ambato wani jami'in ZimParks yana cewa ana zargin sun mutu ne sakamakon kamuwa da cutar anthrax.

    A cikin 2020, aƙalla giwaye 30 ne suka mutu a kusa da yanki ɗaya daga abin da ake zargi da ƙwayar cuta ce.

    • Zimbabwe na tsaka-mai-wuya kan hare-haren da giwaye ke kai wa jama'a
    • An nemi ɗauki bayan ƙudajen zuma miliyan biyar sun faɗo daga mota
  14. Tinubu zai tafi bikin 'yancin kai na Guinea-Bissau

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu na shirin ganawa da shugabannin ƙasashen duniya a birnin Bissau na ƙasar Guinea domin halartar bikin cikar kasar shekara 50 da samun 'yancin kai. .

    Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar ta ce a ranar Alhamis ne Shugaba Tinubu zai isa Bissau domin halartar bikin da Shugaban Ƙasa Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo ya shirya.

    Kodayake Guinea-Bissau a hukumance ta cika shekaru 50 da samun 'yancin kai a ranar 24 ga watan Satumban 2023, an shirya gudanar da bikin a ranar 16 ga watan Nuwamba.

    Sanarwar ta ƙara da cewa Tinubu zai koma Najeriya kwana ɗaya bayan gama bikin.

    • Ina Tinubu ya shiga ?
    • Kwana 100 na mulkin Bola Tinubu
  15. Shugaban Sudan ta Kudu ya kori shugaban 'yan sanda bayan jita-jitar juyin mulki

    Shugaban Sudan ta Kudu

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya kori babban hafsan 'yan sandan kasar Laftanar Janar Majak Akec Malok daga mukaminsa, a wani mataki na hukunta jami'an tsaron bayan samun rahotannin yuƙurin yi masa juyin mulki

    Shugaban ya sanar da maye gurbinsa a gidan talabijin na kasar, inda ya nada Laftanar Janar Atem Marol Biar a matsayin sabon shugaban 'yan sanda.

    A ranar 11 ga watan Nuwamba ne aka fara yada jita-jitar juyin mulkin, yayin da Shugaba Kiir ke birnin Riyadh don halartar taron Saudiyya da Afirka.

    Washegari, rahotonni sun ce an kama jami’an soji da na leken asiri 27.

    Ƙasar ta gabashin Afirka da ke shirin gudanar da zabenta na farko tun bayan samun 'yancin kai a shekara ta 2011, na fuskantar sauye-sauyen tsaro da aka dade ana jira.

    A halin da ake ciki kuma, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya kara wa'adin dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin Abyei da ake takaddama a kai na tsawon shekara guda.

    • Me ya sa juyin mulki ke sake dawowa a Afirka?
    • Su wane ne janar-janar da ke yaƙi da juna a Sudan
  16. Jami’in kan iyaka ya ce lita 25,000 na man fetur ta isa Gaza

    Kimanin lita 25,000 na man fetur ya shiga Gaza a safiyar yau daga mashigar Rafah a Masar, kamar yadda wani jami'in kan iyakar yankin ya shaida wa BBC.

    Isar da kayayyakin na zuwa ne bayan Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar agaji ta Médecins Sans Frontières sun yi gargadin cewa man fetur zai kare a Gaza ranar Laraba.

    Isra'ila ta shafe makonni tana hana jigilar man da ake kaiwa Gaza, tana mai cewa kungiyar Hamas za ta iya sacewa tare da yin amfani da shi don ayyukan soji.

    Tun da farko dai rundunar sojin Isra'ila ta ce za a sake man fetur a wasu manyan motocin Majalisar Dinkin Duniya da ke jigilar kayan agaji zuwa Gaza ranar Laraba.

    • Me ke faruwa a Asibitin Al-Shifa na Zirin Gaza?
    • Me ya sa Isra'ila ta raba Gaza zuwa ɓangare biyu?
  17. Majalisar wakilan Amurka ta amince da ƙudirin ci gaba da samar wa gwamnati kuɗi

    Majalisar wakilan Amurka ta amince da wani ƙudiri na wucin-gadi da zai hana tsayar da ayyukan gwamnati a kasar.

    'Yan Democrats da dama sun amince da matakin, bayan sabon kakakin majalisa daga jam'iyyar Republican, Mike Johnson ya gabatar da kudirin.

    Kudirin ya bayar da damar a cigaba da bai wa gwamnati kuɗaɗen gudanarwa har zuwa tsakiyar watan Janairu.

    Sama da 'yan Republican casa'in ne suka jefa kuri'ar nuna adawa da kudirin, inda suke ƙorafin cewa babu batun ƙayyade kuɗaɗen kashewar da suke so.

    A yanzu za a kai wannan ƙudiri gaban majalisar dattijai, domin ta amince da shi kafin cikar wa'adi a ranar Juma'a.

    • McCarthy ya zama sabon shugaban majalisar Amurka
    • Shugaba Biden na fuskantar barazanar tsigewa
  18. Shugaban Ghana na son ƙasashen Turai su biya diyyar cinikin bayi

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban ƙasar Ghana Nana Akufo-Addo ya yi kira ga shugabannin kasashen Afirka da na yakin Caribbean da su hada kai wajen neman ƙasashen Turai su biya su diyyar cinikin bayi da kuma abubuwan da suka faru lokacin mulkin mallaka.

    Ya bayyana hakan a matsayin wani "hakki bisa adalci."

    Akufo-Addo ya jaddada cewa, kasashen Afirka na bin bashin diyya daga kasashen da suka yi cinikin bayi, yana mai cewa hakan na kawo cikas ga ci gaban Afirka.

    Da yake jawabi a wajen wani taro na neman biyan diyyar da aka yi a birnin Accra, wanda ya samu halartar shugabanni daga kasashen Afirka da Caribbean, ya jaddada muhimmancin magance wannan batu a duniya.

    Taron dai na da nufin samar da hadin kai tare da tsara wani shiri ga kasashen Afirka da na kasashen waje domin biyan diyyar.

    Shugaban ya kuma jaddada a taron Majalisar Dinkin Duniya a watan Satumba cewa babu wani adadin kuɗi da zai iya biyan irin wahalar da zaluncin da bayi suka fuskanta a lokacin mulkin mallaka.

    • Yadda tasirin cinikin bayi ke ci gaba da shafar nahiyar Afrika
    • Wane ne sabon shugaban kasar Ghana?
  19. Isra'ila ta ce ta kai kwalaben saka jarirai da abincinsu zuwa asibitin Al-Shifa

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Sojojin Isra'ila sun ce sun samar da kwalaben saka jarirai da abinci jarirai da kuma magunguna ga babban asibitin Gaza, Al-Shifa.

    Akwai jarirai da dama a asibitin, waɗanda a karshen mako aka fitar da su daga kwalaben da aka saka su sakamakon ƙarancin wutar lantarki a asibitin.

    Jiya, bayan da dakarun sojin Isra'ila ta sanar da cewa za ta samar da kayayyakin, babban jami'in kula da agajin jinya ga Falasɗinawa ya ce ba kwalaben saka jarirai ne kaɗai ake bukata ba harda man da za a iya sarrafa janareta da zai samar da wutar lantarki.

    Isra'ila dai ta haramta shigar da mai zuwa Gaza tun bayan barkewar fada da Hamas a watan jiya, tana mai cewa Hamas za ta yi amfani da shi ta hanyar soji.

    • Sojojin Isra’ila sun amince su kwashe jarirai daga babban asibitin Gaza
    • Mutumin da ya rasa duka ƴaƴansa huɗu a hari ɗaya da Isra'ila ta kai
  20. An gargaɗi ƴan Brazil kan tsananin zafin da suke fama da shi

    ...

    Asalin hoton, SEBASTIAO MOREIRA/EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK

    An fitar da gargaɗi a yankuna dubu uku da birane da ke faɗin Brazil, sakamakon yanayi na tsananin zafi da ake fuskanta.

    A birnin Rio de Janeiro, yanayin ya kai maki 42 a ma'aunin salshiyos -- mataki mafi girma da aka taɓa gani a cikin watan Nuwamba.

    Sannan har yanzu akwai sama da wata guda kafin a shiga yanayin ko lokacin da ake gani na zafi ne a ƙasar a bisa al'ada.

    Mahukuta dai na bayyana wannan sauyin yanayi da ake gani da tasirin El Nino da sauran matsalolin sauyin yanayi.

    • Sauyin Yanayi: Ranakun da ake samun tsananin zafi sun ninka a duniya
    • An yi rana mafi tsananin zafi a tsawon shekara 60 a China