An zaɓi Najeriya cikin ƙasashen da za su nemo mafita kan rikicin Gaza

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najieriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Mukhtar Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Kungiyar kwadago ta janye yajin aiki

  2. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Mu kasance gobe da safe idan Allah ya kai mu don samun wasu sababbi.

    Ahmad Tijjani Bawage da Mukhtar Adamu Bawa ke cewa mu kwana lafiya.

  3. Kwamitin Sulhu ya amince da ƙudurin dakatar da yaƙi a Gaza

    Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya zartar da wani ƙuduri da ke kira a dakatar da faɗa a Gaza cikin gaggawa kuma na tsawon lokaci, don ba da damar shigar da kayan agaji.

    An zartar da kudurin a karo na biyar da kwamitin ke yi don cimma yarjejeniya game da yaƙin.

    Amurka babbar abokiyar kawancen Isra'ila - ta kaurace daga amfani da damarta wajen hawa kujerar na-ƙi, ko da yake ta soki lamirin kudurin saboda rashin yin Alla-wadai da hare-haren Hamas a kudancin Isra'ila.

    Kudurin ya kuma yi kira ga Hamas ta sako dukkan mutanen da take garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba.

    Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield, ta bayyana fatan cewa zartar da kudurin zai bai wa Majalisar Dinkin Duniya da abokan kawancenta damar kai karin kayan agaji zuwa Zirin Gaza.

  4. Ina Atiku yake lokacin da PDP ke cewa za ta yi shekara 60 tana mulki? - APC

    APC leader

    Asalin hoton, Abdullahi Umar Ganduje/Facebook

    Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta mayar da martani ga jagoran adawan kasar wanda a ranar Talata ya bayyana damuwar cewa kasar tana kokarin fada wa mulkin kama-karya na jam'iyya daya.

    Dan takarar shugaban kasar a zaben watan Fabrairun 2023 da ya wuce, a ranar Talata ya yi kira ga jam'iyyun adawar Najeriya su hada karfi da karfe wajen ceto kasar daga halin da ta shiga a hannun jam'iyya mai mulki.

    APC dai ta ce tana karfafa tsarin dimokradiyya ne maimakon yi mata kanshin mutuwa.

    Sanarwar da sakataren yada labaran APC na kasa, Felix Morka ya fitar ranar Laraba ta ce kamata ya yi Atiku Abubakar ya mayar da hankali wajen dinke barakar da ke damun PDP.

    A cewarta, tsohon mataimakin shugaban kasar yana fadi-tashi ne, wajen fuskantar zahirin rayuwa bayan faduwa zaben shugaban kasa.

    APC ta ce "abin takaice ne a ce Atiku ya kasa fahimtar gagarumar karbuwar da kasaitacciyyar jam'iyyarmu ta samu a tsakanin al'ummar Najeriya inda yake fargaba maras tushe na mayar da Najeriya mai mulkin kama-karya ta jam'iyya daya".

    Sanarwar ta ce 'yan Najeriya suna da matukar fahimta, kuma suna iya bambancewa tsakanin karkacewar da PDP ta yi, da kuma kudurin APC na zurfafa tafarkin dimokradiyya da inganta kyautatuwar al'amuran rayuwa.

    APC ta zargi Atiku da rufe ido kan abin da ta ce bugun kirjin da PDP ta rika yi kafin mummunar faduwar da ta yi a zaben 2015, game da niyyarta ta mulkar Najeriya tsawon akalla shekara 60.

    A cewar Felix Morka, har yanzu 'yan Najeriya ba su mance da banga da galatsi da almubazzarancin jam'iyyar PDP na tsawon shekara 16 ba.

    Yayin da a dan takaitaccen lokacin da ta shafe a kan karagar mulki, ya ce APC ta aiwatar da manyan gyare-gyare ga dokar zabe ta kuma kawo amfani da fasahohi ciki har da na'urar tantance masu zabe ta BVAS da shafin ganin sakamakon zabe na INEC duka a kokarinta na inganta yin zabuka cikin gaskiya da zurfafa turakun dimokradiyya.

  5. Gwamnatin Birtaniya ta sha kaye a kotun ƙoli kan batun tura ƴan ci-rani Rwanda

    Manufofin gwamnatin Birtaniya na neman tura ƴan ci-rani Rwanda na dab da rugujewa bayan da kotun ƙolin ƙasar ta ce hakan ba ya bisa ka'ida.

    Ministoci sun ce shirin mayar da masu neman mafaka da kuma hana su dawowa yana buƙatar a fara magance tsallakawar ƙananan jiragen ruwa.

    Sai dai kotun ƙolin ta amince da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke a baya wanda ya ce manufar ta sa mutanen da aka aika zuwa Rwanda fuskantar cin zarafi.

    Firaminista Rishi Sunak ya mayar da martani da cewa "wannan ba shi ne sakamakon da muka yi tsammani ba".

    Manufar mai cike da ce-ce-ku-ce ta kasance ƙarƙashin ƙalubalen doka tun lokacin da Boris Johnson ya fara sanar da ita a cikin watan Afrilun, 2022.

    Tuni dai gwamnati ta kashe fam miliyan 140 kan shirin amma hukuncin da babbar kotun Birtaniya ta yanke a ranar Laraba ya kawo karshen yiwuwar samun nasarar manufofin a yadda take a halin yanzu.

    An hana tashin jirage a watan Yunin bara bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta ce matakin ya saɓa wa doka saboda rashin kare hakkin ɗan Adam.

  6. Takarar shugaban ƙasa da ta yi zafi tsakanin Weah da Boakai a Laberiya

    Zaɓen Laberiya

    Asalin hoton, Reuters

    Sakamakon farko na zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu a Laberiya na nuna cewa an yi fafatawa mai zafi.

    Yayin da aka samu kusan kashi huɗu na sakamakon zaɓen, ɗan takarar adawa Joseph Boakai na gaban Shugaba George Weah.

    Ya zuwa yanzu Mista Boakai yana da kashi 50.7 na kuri'un da aka kaɗa, yayin da Weah ke da kashi 49.3, in ji hukumar zaɓen ƙasar.

    A zagayen farko, dukkan mutanen biyu sun yi kankankan da juna, yayin da ɗan takarar da ya zo na uku ya samu kashi 2 na kuri'un da aka kaɗa.

  7. Gobara ta tashi a wani sansanin ƴan gudun hijira a Borno

    Gobara

    Asalin hoton, Nema

    Akalla yara biyu ne suka mutu bayan da wata gobara ta tashi a wani sansanin ƴan gudun hijira a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Jami’in Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Nema, Mannir Gidado, ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin tashin gobarar, sai dai ana zargin mutanen da suke dafa abinci a cikin tantunansu kusa da tufafinsu da kuma gadajensu da haddasa gobarar.

    Nema ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, amma ba ta bayyana ko yara ne ba.

    Gobarar ta kuma lalata fiye da tantuna 1,000 a sansanin Muna Alamdari da ke kusa da Maiduguri babban birnin jihar, kamar yadda Gidado ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Dubban mutane ne ke zaune a sansanin bayan da aka tilasta musu tserewa gidajensu saboda rikicin da aka shafe kusan shekaru 15 ana yi da masu iƙirarin jihadi.

  8. Za a binciki Chelsea kan wasu kudi da ta biya lokacin Abromovich

  9. Mawaƙin Najeriya Oladips ya mutu yana da shekara 28

    Oladips

    Asalin hoton, OLADIPS/YOUTUBE

    Ana ci gaba da ta'aziyyar shahararren mawakin nan na Najeriya Oladips, wanda ya rasu yana da shekaru 28 a duniya.

    "Har yanzu muna cikin kauwa yayin da muke magana," in ji jami'an gudanarwar kamfaninsa a wani sako da suka wallafa a shafin Instagram. Ba a san musabbabin mutuwarsa ba kawo yanzu.

    Oladips ƙwararren mawaƙi ne wanda ya rera wata waka kan batutuwan siyasa kamar zanga-zangar ENDSars na nuna rashin amincewa da cin zalin 'yan sanda.

    Ya kuma taɓo batun lafiyar kwakwalwa da shiga damuwa a cikin wakokinsa.

    "Kwararren mawaki ne da ya iya rera baituka masu daɗi, " kamar yadda wani masoyinsa ya wallafa a shafin Twitter.

    Mawakin yana shirin sake sabon kundin wakokinsa mai suna 'SUPERHERO ÀDÚGBÒ' a ranar Alhamis kafin mutuwarsa. Wakarsa ta karshe da ya rera ita ce ake kira 'Die Young'.

    Oladips ya yi suna a lokacin da ya lashe gasar rap mai suna 'King is Here' wanda mawaki Dbanj ya ɗauki nauyi a shekarar 2015.

    Mutuwar Oladips na zuwa ne ‘yan watanni bayan da wani fitaccen mawaki, Mohbad, ya mutu a watan Satumba, abin da ya janyo zanga-zanga a sassan ƙasar domin buƙatar yin bincike da nufin kama waɗanda ke da hannu a mutuwarsa.

  10. Rundunar sojojin Isra'ila ta ce ta gano makamai da kayan aikin Hamas a Al-Shifa

    Israeli soldiers

    Asalin hoton, Israel Defense Forces

    Wani sabon bayani daga rundunar sojojin Isra'ila ya yi karin haske kan sakamakon samamen da dakarunsu suka kaddamar cikin asibitin Al-Shifa na Gaza.

    A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, sojojin Isra'ila sun ce sun gano "wata cibiyar gudanar da aikace-aikace da makamai da kuma kayayyakin fasaha" mallakar kungiyar Hamas a cikin sashen daukar hoton maras lafiya na MRI da ke asibitin.

    Ta ce ta gano "kayayyakin ayyukan fasaha tare da kayan aikin sojoji da na fadace-fadace" a daya daga cikin sassan asibitin.

    Ta ce an aika "kayayyakin ayyukan fasaha da na tattara bayanan sirri" don gudanar da "cikakken nazari daga hukumomin da ke da alaka".

    Sun ce yayin da suka dakarunsu suka shiga asibitin, sun yi artabu da adadin mayakan Hamas kuma sun kashe su, ba tare da fadada bayani ba.

    Rundunar ta ce tana "ci gaba da gudanar da aiki a ginin asibitin, yayin da take tatsar bayanan sirri da kuma hana cutar da jami'an lafiya da fararen hulan da ke samun mafaka."

    Ta kuma fitar da hotuna da dama na abin da ta ce makaman da ta samu ne a lokacin aikin da ta gudanar a asibitin.

    Israel soldiers

    Asalin hoton, Israel Defense Forces

  11. Mugun mafarkin da ya ingiza matashi buga wa mahaifinsa taɓarya a Kaduna

    Nigerian police head

    Asalin hoton, Nigerian Police/Facewbook

    'Yan sanda a jihar Kaduna sun ce sun kama wani matashi mai shekara 20, bisa zargin kashe mahaifinsa ta hanyar buga masa tabarya bayan ya zuciyarsa ta kaddara masa cewa uban na yunkurin halaka shi.

    "Ya shaida mana cewa yana yin mafarke-mafarke, inda yake ganin siffar mahaifin nasa, mai kimanin shekara 50, yana zuwar masa a cikin sigar jemage," in ji mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar.

    ASP Mansur Hassan ya shaida wa manema labarai cewa suna ci gaba da gudanar da bincike kan matashin da suke zargi wanda ya fito daga yankin karamar hukumar Zangon Kataf.

    Ya ce zuwa yanzu ba su samu wata shaida da ke nuna cewa matashin na da wata matsalar kwakwalwa, ko kuma yana shan kayan maye.

    Jami'in 'yan sandan ya ambato matashin na cewa babu kyakkyawar alaka tsakaninsa da mahaifin, wanda ya riga mu gidan gaskiya.

    'Yan sandan sun ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da matashin mai suna David Phillips a gaban kotu.

  12. El-Ghazi ya shigar da ƙara kan sallamarsa daga Mainz

  13. Netanyahu ya ce 'babu inda ba za mu shiga ba a Gaza'

    Netanyahu and some Israeli soldiers

    Asalin hoton, EVN

    Da yake jawabi yayin wata ziyara da ya kai wani sansanin sojojin a kusa da Gaza, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce "babu wata maboya" ga 'yan ta-da-kayar-bayan Hamas da suka kai hare-haren 7 ga watan Oktoba, kuma "babu wani wuri a Gaza" da sojojin Isra'ila ba za su kai ba.

    Netanyahu ya ce: "Ko kun tuna lokacin da aka ce ba za mu kutsa, mu shiga Gaza ba? To, mun shiga.

    "Sun ce ba za mu iya kai wa tsakiyar Birnin Gaza ba - mun isa. Sun ce ba za mu shiga asibitin Al-Shifa ba - mun shiga.

    "Babu wani wuri a cikin Gaza da ba za mu iya shiga ba. Babu wurin buya, babu wata mafaka, babu wurin labewa ga Hamas masu aikata kisan gilla.

    "Za mu je kuma mu kakkabe Hamas sannan mu kubutar da mutanen da ake garkuwa da su - wadannan ayyuka ne da babu makawa a kansu."

  14. Hotuna: An sheka ruwan sama a sansanonin Falasɗinawa 'yan gudun hijira

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce ruwan saman da aka yi a yau Laraba, zai kara dagula al'amura ga dubban mutanen da rikici ya raba da gidajensu da ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira a Gaza.

    Da yawan wadannan mutanen suna samun mafaka ne a tantunan da aka kakkafa.

    Ga wasu cikin hotunan da suka fito daga Khan Younis inda Falasdinawa da yawa suka koma bayan sun tsere daga arewacin Gaza.

    Gaza rain

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Mutane na tarar ruwan da ya kwanta cikin bokiti daga saman rufin tanti
    Gaza rain

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ruwan sama ya janyo kwantawar ruwan tabo, da kuma cabalbali a daukacin sansanin
    Gaza rain

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka zabga ya taru a saman rufin tantuna
    Gaza rain

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wannan karamin yaro yana taimakawa wajen sharce ruwan saman da ya taru a kasa
  15. Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da nasarar Gwamna Sanwo-Olu na Legas

    Sanwo Olu

    Asalin hoton, Babajide Sanwo-Olu/Facebook

    Kotun ɗaukaka ƙara da ke jihar Legas ta tabbatar da nasarar gwamna Babajide Sanwo-Olu, a matsayin zaɓabɓen gwamnan jihar.

    Alkalan kotun ɗaukaka ƙaran a wani mataki na bai ɗaya, sun yi watsi da karar da jam’iyyar PDP ta shigar saboda rashin gamsassun hujjoji.

    Mai shari’a Yargata Nimpa, da mai shari’a Samuel Bola da kuma mai shari’a Paul Bassey ne suka yanke hukuncin.

    Ita ce shari'ar gwamna ta farko da kotun daukaka kara a Najeriya ta yanke, tun bayan zabukan watan Fabrairu na 2023.

    Babajide Sanwo-Olu ya lashe zaɓen gwamnan Lagos ne a matakin wa'adi na biyu.

    Babban jami'in tattara sakamakon zaɓe na jihar, Professor Adenike Temidayo Oladiji ya ce Sanwo-Olu ya yi nasara da adadin ƙuri'a 762,134.

    Yayin da jam'iyyar LP ta zo ta biyu inda ɗan takararta, Gbadébo Rhode-Vivour ya samu ƙuri'a 312,329, sai kuma ɗan takarar PDP Abdulazeez Olajide Adeniran da ya zo na uku da ƙuri'a 62,449.

    Sai dai, har yanzu duk bangaren da bai amince ba, yana da dama ta karshe a shari'ance, ya daukaka kara zuwa Kotun Koli.

    • Sanwo-Olu ya yi tazarce a Legas
    • Da gaske ambaliya ta kusa shafe gadar Third Mainland ta Lagos?
  16. Matasan Brazil sun ci 9-0 sun kai hari sau 81 a gasar kofin duniya

  17. Manchester City ta sanar da cin ribar kasuwanci

  18. Ba mu ne muka ce Isra'ila ta kai samame Asibitin Al-Shifa ba - Gwamnatin Amurka

    Kirby

    Asalin hoton, EPA

    Mai magana da yawun fadar White House ka harkokin tsaron kasa John Kirby ya ce Amurka ba ta ce ta amince Isra'ila ta gudanar da samamen sojanta a zagayen asibitin Al-Shifa ba.

    Da yake jawabi yayin wani taron manema labarai, Kirby ya ce wannan ma kamar sauran aikace-aikacen sojojin Isra'ila, ba Amurka ce ke amincewa da gudanar da su ba.

    Ya ce wadannan tsare-tsare ne na Isra'ila da take aiwatarwa bisa ka'idojin da ta kafa, sannan Amurka ba ta sa ran sai Isra'ila ta sanar da ita kafin ta aiwatar da wani takamaiman aikin soja.

    Ya ki amincewa ya yi cikakken bayani game da tattaunawar da aka yi tsakanin Shugaba Joe Biden da Firaminista Benjamin Netanyahu, amma ya ce shugabannin biyu ba su mayar da hankali kan aikin da Isra'ila ke yi a asibitin Al-Shifa ba.

    • Asibitocin da yakin Isra'ila da Hamas ya ritsa da su a Gaza
    • Abin da shugaban Hamas ya shaida wa BBC game da rikicin Gaza
  19. 'Yar Najeriyar da ta kafa tarihin ado da karin gashi mafi tsawo a duniya

    Nigerian wig record

    Asalin hoton, WORLD GUINNESS RECORD

    Wata 'yar Najeriya ta kafa tarihin shiga kundin bajinta na Guinness saboda sanya ƙarin gashi mafi tsawo da aka saka da hannu.

    Helen Williams ta saka karin gashi da ya kai tsawon mita 351.28.

    Helen ta shafe tsawon kwana 11 tare da kashe naira miliyan biyu wajen saka karin gashin.

    Ta kuma yi amfani da gashi har ɗauri 1,000 da gwangwanin man feshi 12 da dankon jona gashi 35 da kuma karfen rike gashi 6,250.

    "Wannan bajinta, na ɗaya daga cikin abubuwa mafi fice da na taɓa yi a rayuwa. Har yanzu na kasa yarda da cewa ni ce na yi," in ji ta.

    Duk da kasancewarta mai saka karin gashi tsawon shekara takwas, ta ce ba abu ne mai sauki ba saka karin gashi mafi tsawo a duniya, inda ta ce ta rika "jin matukar gajiya" a lokacin da ta kwashe tana yi.

    "Kawaye da dangina ne suka karfafa min gwiwa. Kuma ba na so na ba su kunya, don haka na mayar da hankali sosai. Ga shi yanzu, sakamakon haka, na saka karin gashi mafi tsawo da aka taɓa yi da hannu a duniya," Helen ta ce.

    Nigerian wig record

    Asalin hoton, WORLD GUINNESS RECORD

  20. An kama waɗanda suka yi wa shugaban ƙungiyar ƙwadago duka

    A ranar Laraba ne mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mal Nuhu Ribadu, ya nemi afuwar gamayyar ƙungiyar ƙwadago kan harin da aka kai wa shugabanta a Najeriya, Joe Ajaero, a Owerri, babban birnin jihar Imo, a ranar 1 ga watan Nuwamba.

    Ajaero, wanda ya je garin Owerri domin jagorantar zanga-zanga, ya sha duka tare da tsare shi na sa’o’i da dama.

    Sakamakon haka, ƴan ƙwadagon suka bai wa gwamnati wa’adin biya musu wasu buƙatu da suka haɗa da kama waɗanda suka kai hari kan Ajaero, tare da yin barazanar shiga yajin aikin a faɗin ƙasar idan ba a biya musu bukatun ba.

    “Sakamakon afkuwar lamarin, an umarci hukumomin da suka dace da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da gurfanar da waɗanda suka aikata laifin," in ji Ribadu.

    Sai dai wasu rahotanni na cewa tuni an riga an kama wasu da ake zargi da hannunsu a lamarin.