Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage
Labarai da dumi-dumi, Ma'aikatar lafiyar Gaza ta ce mutanen da suka mutu a zirin yanzu sun kai 10,569
Ma'aikatar lafiyar Gaza da ke karkashin Hamas ta ce adadin mutanen da aka kashe ya karu zuwa 10,569, a cikinsu mutum 4,324 kananan yara ne, tun lokacin da Isra'ila ta fara kai hare-haren ramuwar gayya bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.
An dai samu karin mutuwar mutum 241 a Gaza tun bayan wallafa adadi na baya-bayan nan a jiya, Talata.
Shugaba Joe Biden na Amurka a baya ya tuhumi sahihancin alkaluman ma'aikatar lafiyar ta Gaza - sai dai Hukumar Lafiyar ta Duniya ta ce ta yi imani abin amincewa ne.
Ƴan Isra'ila na rige-rigen mallakar bindiga bayan harin Hamas
Bayani game da abubuwan da ba ku sani ba kan rikicin Isra’ila da Gaza
'Kusan rabin waɗanda aka kashe jiya a kudancin Gaza suke'
Asalin hoton, Reuters
Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta bayar da rahoton cewa Isra'ila ta kai hare-hare sau 27 a jiya wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 241.
Kusan rabin wadanda aka kashe a kudancin Zirin Gaza suke, duk da iƙirarin da Isra'ila ta yi na cewa waɗannan yankuna sun fi arewacin ƙasar tsaro.
Bugu da kari, ma'aikatar ta bayyana cewa asibitoci 18 da cibiyoyin lafiya 40 a halin yanzu ba sa aiki, kuma jami'an kiwon lafiya 193 ne suka rasa rayukansu a cikin rikicin Hamas da Isra'ila.
Abin da shugaban Hamas ya shaida wa BBC game da rikicin Gaza
Iƙirarin aikata kisan ƙare dangi a Gaza ya janyo suka ga 'yar majalisar Amurka
Ƙarin ƴan fafutuka na zaman dirshen kan takunkumin ECOWAS a Nijar
Wasu ƙarin ƴan fafutuka a Nijar na zaman durshen a Yamai, babban birnin ƙasar kan takunkumin da ƙugiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ta yamma ECOWAS ta kakaɓa wa ƙasar tun bayan juyin mulki.
ƙungiyar Ecowas dai ta sanya wa Nijar takunkumin tattalin arziƙi da kuma rufe harkokin kasuwanci na kan iyaka da Nijar a yunƙurin matsa wa shugabannin juyin mulkin kasar lamba har sai sun mayar da mulkin dimokradiyya.
Shugaban Najeriyar, Bola Tinubu, wanda kuma shi ne jagoran Ecowas, ya bayyana taka-tsantsan wajen mu'amala da Nijar saboda damuwar da ake da ita dangane da hamɓaras da Shugaba Bazoum daga kan mulki.
Gwamnatin mulkin soja a Nijar dai ta ce za ta miƙa mulki bayan shekara uku hannun farar hula.
Takunkumin da Ecowas ta saka wa Nijar ya fara haifar da tsadar rayuwa
Ecowas ba ta yi mana adalci ba – Firaministan Nijar
Masu aikata laifi sun auka wa ƴan Afirka ta Kudu da yaki - minista
Asalin hoton, Getty Images
Ministan ƴan sandan Afirka ta Kudu Bheki Cele, ya ce masu aikata laifuka sun ayyana yaƙi kan 'yan kasar, biyo bayan ƙaruwar laifuka a ƙasar.
Hakan na zuwa ne bayan da aka yi wa ministar sufurin ƙasar fashi da makami a wani mummunan hari da aka kai ranar Litinin.
Sindisiwe Chikunga na tafiya ne daga KwaZulu-Natal zuwa Gauteng lokacin da lamarin ya faru
"Mun kusa rasa wata minista da aka kusan harbe wa," in ji Mista Cele.
Tuni dai aka fara farautar ƴan fashin, inda suka yi awon gaba da wasu kwamfutoci da waya da makaman masu gadin ta.
Ministan ya ce gwamnati za ta magance matsalar karancin ‘yan sanda a kasar, a kokarin da take yi na dakile yawaitar laifuka.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta 'yan sanda da gidajen yari (Popcru) na son a dauki tsauraran matakai kan masu laifi biyo bayan ƙaruwar kashe-kashen 'yan sanda a ƙasar.
Aƙalla jami'an ƴan sanda 67 ne aka kashe a hare-haren masu aikata laifi tun watan Janairu, in ji Popcru.
'Abin da ya sa muka tsani baƙi a ƙasarmu'
Kenya : Matar da ta zamewa masu aikata laifi a Kenya ƙadangaren bakin tulu
Fiye da sunaye 600 ne a cikin jerin waɗanda za su fice daga Gaza a yau
Asalin hoton, EPA
Hukumomin Falasɗinawa sun fitar da wani jerin sunayen wasu ‘yan ƙasashen waje sama da 600 da aka ba su izinin ficewa daga Gaza ta hanyar Rafah zuwa Masar.
Jerin sunayen ya haɗa da mutane daga ƙasashe daban-daban da suka haɗa da Philippines da Ukraine da kuma Kanada.
Babu ƴan ƙasar Burtaniya a cikin jerin sunayen na yau.
Mashigar Rafah, wacce a halin yanzu ita kadai ce hanyar shiga da fita zuwa Gaza, an sake buɗe ta ne a ranar 1 ga watan Nuwamba.
Me ya sa mashigar Rafah a Gaza ke da muhimmanci
Me ya sa ba za a buɗe mashigar Rafah ga kowa ba?
Adadin waɗanda suka mutu a ambaliyar ruwa a Somaliya ya kai 29
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, ...
Hukumar kula da bala'o'i ta kasar Somaliya ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a ƙasar ya kai 29.
Ambaliyar ruwan ta yi sanadiyar raunata kimanin mutane 850,000 kamar yadda shugaban hukumar Mahamuud Moallim ya bayyana a ranar Talata.
Mutane 14 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon ambaliyar ruwan a ranar Asabar da ta gabata daga hukumar kula da jin ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya.
A farkon makon nan ne Somaliya ta ayyana dokar ta-baci a jihohin da lamarin ya fi shafa da suka haɗa da Jubbaland da Hirshabeelle Kudu maso Yamma da kuma Galmudug.
Ambaliyar dai ta fara ne a watan da ya gabata bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya haifar da ambaliyar daga kogin Juba da Shabelle.
An yi ruwan sama misalin na shekara 20 cikin kwana ɗaya a Libya
Ambaliyar Ghana: ‘Ruwa ya cinye gida da gonata'
'Yaya za mu tsagaita wuta bayan Hamas na garkuwa da mutanenmu?'
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, ...
Blinken ya ce Amurka da Isra'ila sun amince cewa "babu yiwuwar komawa zuwa ranar 6 ga Oktoba munanan hare-haren da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Octoba.
Kasashen biyu dai na da nufin kawo karshen rikicin cikin sauri da kuma rage radadin da fararen hula ke fuskanta.
"Dole ne masu kiran gaggauta tsagaita wuta su yi bayanin yadda sakamakon da ba za mu amince da shi zai kasance yayin da Hamas- ke gargukwa da fiye da mutum 200 - waɗanda ke da niyyar maimaita harin 7 ga watan Octoba." in ji Blinken
Blinken ya kammala da cewa, hanya daya tilo da za a iya daƙile irin wadannan rikice-rikicen a nan gaba ita ce a samar da dauwamammen zaman lafiya da tsaro.
Tsagaita wuta zai ba Hamas damar sake shiri don kai hare-hare - Anthony Blinken
Burin China a yaƙin Isra'ila da Hamas
Najeriya ta soke ziyarar da firaministan Czech ya shirya kai wa Abuja
Asalin hoton, Government of the Czech Republic
Kafofin labaran Czech sun bayyana cewa Najeriya ta soke ziyarar da firaministanta Petr Fiala ya shirya kai wa Abuja, babban birnin ƙasar ta Afirka ta Yamma.
Kakakin gwamnatin Jamhuriyar Czech Václav Smolka ya shaida wa jaridar Blesk ta Czech cewa, "Najeriya ta sanar da mu cewa ba ta iya samar da isashen shirin tarba da tsare-tsaren ziyarar firaminstan ba, don haka mun amince da soke ziyarar."
Yayin da Najeriya ba ta ce uffan kan lamarin ba, wasu majiyoyin yaɗa labarai na kasar Czech sun nuna cewa wataƙila sokewar na da nasaba da goyon bayan da Czech ke baiwa Isra'ila a rikicin da ake fama da shi da kungiyar Hamas.
Czech dai tana cikin ƙasashen da suka kaɗa ƙuri'ar ƙin amincewa da ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya na tsagaita buɗe wuta a rikicin Isra'ila da Hamas, yayin da kuma Najeriya ta amince da tsagaita buɗe wuta.
Fiala ya kai ziyara a yankin kudu da hamadar sahara daga makon da ya gabata don neman damar kasuwanci ga kamfanonin Czech.
Ya zagaya ƙasashen Habasha da Kenya, inda ya tattauna da shugabannin kasashen.
Ana sa ran zai gana da shugaban Ghana Nana Akufo-Addo a Accra a ranar Alhamis, kafin ya kammala ziyarar tasa a Ivory Coast a ranar Asabar.
Me ya sa Najeriya ta rufe wasu ofisoshin jakadancinta?
Dan Najeriyar da zai raka biloniyan Japan yawon shakatawa duniyar wata
Falasɗinawa na makokin waɗanda suka mutu a wajen asibiti
Falasɗinawa na makokin waɗanda suka mutu sakamakon harin bama-bamai da Isra'ila da kai a daren jiya a kan gidaje a arewacin Gaza a wajen asibiti.
Kamfanin dillancin labaran Wafa ya bayar da rahoton mutuwar mutane sakamakon harin .
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Labarai da dumi-dumi, Ƙasashen 'G7 na goyon bayan dakatar da yaƙi don ayyukan jin ƙai a Gaza'
Gungun ƙasashe mafi ƙarfin tattalin arziƙi a duniya G7 ciki har da Birtaniya da Amurka ta fitar da wata sanarwa, tana mai cewa tana goyon bayan dakatar da yaƙi don ayyukan jin ƙai a Gaza.
Sanarwar da ministocin harkokin waje suka fitar waɗanda suka yi taro a birnin Tokyo - sun kuma amince da 'yancin da Isra'ila ke da shi na kare kanta "bisa la'akari da dokokin ƙasashen duniya".
Dalilai huɗu da suka hana Falasɗinawa samun ƙasarsu ta kansu
Takaddamar Isra'ila da shugaban MDD saboda kalamansa kan harin Hamas
Hukumomin Hamas sun ce an kai harin bama-bamai a gidaje a birnin Gaza
Asalin hoton, ...
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Falasɗinawa ta Hamas a Gaza ta sanar da cewa, a daren jiya Isra'ila ta kai hare-haren bama-bamai ta sama kan gidaje a birnin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa Wafa ya bayyana cewa, an kashe fararen hula da dama sakamakon hare-haren a birnin Gaza.
Dakarun sojojin Isra'ila ba su bayar da takamaiman bayani kan waɗannan hare-hare ta sama ba.
Idan dai ba a manta ba a baya Isra'ila ta kwashe makonni tana gargadin mutane da su fice daga birnin Gaza da arewacin yankin, amma dubbai sun rage.
Ya zuwa ranar Talata, hukumomin yankin sun bayyana cewa har yanzu mutane kusan 600,000 ne ke zaune a Gaza da yankin arewa."
Sabon harin Isra'ila ya kashe fararen hula fiye da 30 a Gaza
Sabbin bayanan gaskiya guda 5 bayan mako huɗu na yaƙin Gaza
An kaɗa ƙuri'ar amincewa da damar zub da ciki a jihar Ohio
Asalin hoton, Getty Images
Masu kaɗa ƙuri'a a jihar Ohio da ke Amurka sun amince a yiwa tsarin mulkin jihar kwaskwarima domin amincewa da damar zub da ciki a jihar.
Wannan ya sa a yanzu jihar ta kasance ta bakwai a Amurka da ke goyon-bayan zub da ciki, wanda ke biyo bayan hukuncin kotun koli na bara da ke cire wannan doka a matakin tarayya.
Wakilin BBC ya ce wannna batu na da muhimmanci matuƙa musamman ga babban zaɓen shugaban kasa da ke tafe a baɗi.
A zaɓen da kuma aka gudanar a Kentucky, gwamnan Democrats, Andy Beshear, ya yi nasara a wani sabon wa'adi na biyu, bayan fafatawa a zaɓen da ya yi zafi.
A can Mississippi kuma an tsawaita lokacin kada kuri'a, inda gwamnan Republican ke fuskantar ƙalubale wajen riƙe kujerarsa.
Roe v Wade: Kotun Ƙolin Amurka ta soke ƴancin da mata suke da shi na zubar da ciki
Wasu mata sun shigar da ƙara saboda rashin basu damar zubar da ciki
Isra'ila ta ce Falasɗinawa za su cigaba da iko da Gaza bayan kammala yaƙi
Asalin hoton, Rex Features
Bayanan hoto, ...
Ministan tsare-tsare a Isra'ila ya ce Falasɗinawa za su cigaba da iko da yankin Gaza idan suka kammala yaƙin da suke yi da Hamas.
Ron Dermer ya yi watsi da batun da ake yi cewa Isra'ila na ƙoƙarin mamaye yankin na dindindin.
A wata tattaunawa da BBC, ya yi ƙarin haske da jaddada abubuwan da Firaministan Benjamin Netanyahu ke nufi da kalamansa na ranar Talata cewa Isra'ila za ta ƙwace ikon bada tsaro a Gaza domin hana yaɗuwar ta'addanci.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar agaji ta Red Cross ke roƙon Isra'ila ta mutunta dokokin ƙasashen duniya da tabbatar da cewa kayan agaji sun isa cibiyoyin kula da waɗanda aka jikkata, bayan harin da aka kai wa ayarain motocin agaji a jiya talata a Gaza.
Wani jami'in agaji ya bayyana yadda ake yanke kafar marasa lafiya da yara ba tare da alurar kashe radadi ba, saboda yanayi na tsanani da ake ciki a asibitocin Gaza.
Ana damuwa kan yawaitar kisan ƴan jarida a rikicin Isra'ila da Falasɗinawa
Halin da aka shiga a Gaza ranar da aka katse hanyoyin sadarwa
Ana zargin sojojin Habasha da kai hare-hare a Amhara
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, ...
Mazauna yankin arewa maso yammacin ƙasar Habasha mai fama da tashin hankali na Amhara sun ce suna zargin dakarun gwamnati da kai hare-hare da jiragen sama marasa matuka, yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin sojoji da mayakan sa-kai.
Mazauna yankin Gabas da Yammacin Gojjam da kuma tsakiyar birnin Gonder na yankin sun shaida wa sashen Amharic na BBC cewa sun ga faɗan da aka kwashe kwanaki ana gwabzawa.
Rikicin dai a cewar mazauna yankin ya haɗa da amfani da manyan makamai da jirage marasa matuka, lamarin da ke haifar da damuwa ga lafiyar fararen hula.
A wata gunduma kuma, mazauna garin sun ce an kai hari ta sama a wata makaranta.
A birnin Lalibela mai tarihi, limamai da wani fitaccen dan adawa sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "rashin kulawa da harba manyan makamai na iya jefa majami'u cikin hatsari, waɗanda Kungiyar Ilimi da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNECSCO ta amince da su a matsayin wuraren tarihi na duniya.
Tashe tashen hankula sun ɓarke a cikin watan Agusta bayan kwashe watanni ana takun saka dangane da umarnin da gwamnati ta bayar na rusa wata ƙungiyar sa kai ta yankin.
Mayakan sa kai na yankin da aka fi sani da Fano sun mamaye manyan garuruwan yankin inda suka mamaye filin tashi da saukar jiragen sama na takaitaccen lokaci a farkon rikicin amma tun daga lokacin sojojin gwamnati suka fatattake su.
Sojojin dai sun ci gaba da gudanar da ayyukansu a ƙananan garuruwa da kauyuka.
Yunkurin da BBC ta yi don jin ta bakin jami'an Amhara bai yi nasara ba kuma babu wani bayani a hukumance game da fadan da aka sake gwabzawa.
Yadda aka kassara rundunar sojin Habasha
Habasha: Mahara sun hallaka mutun 32 a jihar Oromo
Assalamu alaikum
Masu bin mu a wanna shafi muna muku maraba da shigowa shafin kai-tsaye na BBC Hausa.
Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da duniya ke ciki.
Sai ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.