Isra'ila da Hamas sun tafka laifukan yaƙi - MDD

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu za mu dawo da wasu sababbi.

    Kafin nan, za ku iya duba ƙasa don ci gaba da karanta labaran da muka shafe tsawon yinin yau muna wallafa muku, musamman ma kan rikicin Isra'ila da Falasɗinawa.

    Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Hotuna: Dubban Falasɗinawa na ci gaba da ficewa daga birnin Gaza

    Dubban Falasɗinawa mazauna birnin Gaza na ci gaba da ficewa daga yankin yayin da sojojin Isra'ila da tankunan yaki suka tsaurara matakan tsaro a yankin.

    Sojojin Isra'ila sun fitar da wani bidiyo da ke nuna dogayen layukan mutane suna tafiya a kafa, da dama daga cikinsu suna rike da fararen tutoci.

    Isra'ila ta ce sojojinta na gwagwarmaya a cikin birnin.

    Qatar na ƙoƙarin shiga tsakani a batun sakin mutane goma sha biyu - wasu daga cikinsu Amurkawa tare da tsagaita wuta na kwana uku.

    Ga wasu hotunan yadda al'amura suke a arewacin Gaza a yau Laraba, yayin da mutane ke barin gidajensu domin neman tsira:

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

  3. Ɗiyar tsohon shugaban Amurka Ivanka Trump na ba da shaida a gaban kotu

    Ivanka Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Ɗiyar tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, Ivanka Trump, tana ba da shaida a wata kotu a New York a wata shari'a da ke barazana ga daular kadarorin danginsu.

    Tana bayar da shaida ne kan zargin zamba da ake yi wa kamfanonin Trump -- abu kuma da mahaifinta da manyan ƴaƴansa biyu suka musanta.

    Duk da cewa ba ta cikin waɗanda ake tuhuma a shari'ar, Ms Trump ta taimaka wajen samar da lamuni masu kyau ga kamfanin.

  4. Ten Hag ya dawo da Rashford tawagar United

  5. CBN ya gargaɗi masu ƙin karɓar tsofaffin takardun Naira

    Kuɗi

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gargaɗi masu ƙin karɓar tsofaffin takardun Naira a faɗin ƙasar.

    Wannan na zuwa ne sakamakon fargabar da ake ciki cewa tsofaffin takardun kuɗi za su daina aiki nan da watan Disamba 2023.

    Wata sanarwar da mai magana da yawun bankin CBN, Isah Abdulmunin ya fitar a ranar Laraba, ta ce bankin bai bayar da umarnin janye tsofaffin takardun kuɗi ba daga wajen al'umma.

    Bankin ya ce, “An kuma samu rahotannin damuwa da wasu jama’a ke nunawa kan halacci ko rashinsa na tsoffin takardun kuɗin Naira.

    “Don kauce wa shakku, yayin da muke nanata cewa akwai isassun takardun kudi a faɗin ƙasar nan don gudanar da duk harkokin tattalin arziki na yau da kullun, muna so kuma mu bayyana cewa duk wata takardar kuɗi da Babban Bankin Najeriya, za ta ci gaba da aiki kuma bai kamata a yi watsi da ita ba, kamar yadda yake a sashe na 20(5) na dokar CBN, na 2007.

    Babban bankin ya umarci rassansa a faɗin ƙasa da su ci gaba da bayar da tsofaffin takardun kuɗi da kuma sabbi don ci gaba da rarrabawa ga abokan hulɗar bankuna.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Isra'ila da Hamas sun tafka laifukan yaƙi - MDD

    Rikicin Gaza-Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Babban jami'in hukumar kare hakkin ɗan Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce Isra'ila da Hamas sun aikata laifukan yaƙi.

    Volker Turk ya bayyana a yau Laraba 17 ga watan Nuwamba a mashigar Rafah cewa: "Ta'addancin da ƙungiyoyin mayaka na Falasɗinawa suka aikata a ranar 7 ga watan Oktoba babban laifi ne, kuma laifin yaƙi ne, kamar yadda rashin sakin waɗanda aka yi garkuwa da su laifi ne na yaki."

    Ya kara da cewa: "Hare-haren Isra'ila kan Falasɗinawa shi ma laifi ne na yaƙi, kamar yadda kuma tilastawa 'yan ƙasar gudun hijira ba bisa ka'ida ba, shi ma ya zama laifin yaƙi.

    "An katse rayuwar mutanen Gaza, hakan rashin adalci ne da zalunci," in ji Mista Turk.

    Ya yi kira da a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta cikin gaggawa.

    yana mai cewa lamari ne na kare hakkin bil'adama, "isar da isassun agaji ga Gaza, da kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma kawo karshen mamayar."

  7. Hezbollah ta yi gargaɗin cewa yaƙi zai ɓarke idan ba a daina ruwan ban kan Gaza ba

    Mutum na biyu mafi mukami a ƙungiyar Hizbullah - waɗanda ke samun goyon bayan Iran a Lebanon - ya ce kisan da Isra'ila ke yi wa fararen hula a Gaza na barazanar yaɗuwa zuwa babban yaƙi a Gabas ta Tsakiya.

    Sheikh Naim Qassem ya shaida wa BBC cewa "abubuwa masu matukar muni da haɗari na iya faruwa a yankin, kuma babu wanda zai iya dakatar da abin da zai biyo baya".

    Mataimakin shugaban ƙungiyar Hezbollah ɗin na magana ne a wata hira da aka yi da shi a birnin Beirut, yayin da ma'aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce an kashe fiye da mutane 10,000 a can.

    Hare-haren Isra'ila sun biyo bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba wanda ya kashe mutane 1,400 - 1,000 daga cikinsu fararen hula ne.

    "Haɗarin gaske ne," in ji shi, "saboda Isra'ila tana ƙara kai hare-hare kan fararen hula tare da kashe mata da yara da yawa. Shin zai yiwu hakan ya ci gaba da karuwa, ba tare da kawo haɗarin gaske a yankin ba? Ina tsammanin ba haka ba."

  8. Sojan rundunar Isra'ila ta musamman na cikin mutum 32 da aka kashe a Gaza

    Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da mutuwar wani jami'in sojinta na musamman a yaƙin Gaza.

    Ya zuwa yanzu Isra'ila ta tabbatar da cewa mambobin mambobin dakarun tsaron ƙasar 32 ne suka mutu a Gaza tun lokacin da aka fara kai farmakin ƙasa a ranar 27 ga watan Oktoba.

    An kashe Sgt Jonathan Chazor, ɗan shekara 22, mamba na sashin Shaldag na sojojin saman Isra'ila a wani fafatawa a arewacin Gaza, in ji IDF.

    Dakarun tsaron Isra'ilar ta wallafa sunayen sojoji 350 da suka mutu tun bayan fara yaƙin, waɗanda akasarinsu an kashe su a hare-haren Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.

  9. Tinubu ya saka hannu kan ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi na 2023

    Tinubu da muƙarraban gwamnatinsa

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saka hannu kan ƙwarya-ƙwaryan ƙasafin kuɗi na shekara ta 2023 wanda ya kai naira tiriliyan 2.176.

    Shugaban Najeriyar ya saka hannun ne a yau Laraba a fadarsa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

    Wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya fitar, ta ambato Tinubu na cewa kasafin kuɗin zai karfafa tsarin tsaron Najeriya da kuma magance matsalar giɓin ababen more rayuwa da Najeriya ke fuskanta, da sauransu.

    Shugaba Tinubu ya yaba wa majalisar dokoki ta ƙasa bisa gagarumin nazari da amincewa da ta yi da kasafin kuɗin, inda ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ɓangaren zartarwa zai tabbatar da ganin an yi amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata.

    Cikin waɗanda suka halarci saka hannu kan kasafin kuɗin sun haɗa da shugaban majalisar dattawa, Sen Godswill Akpabio, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, da shugaban kwamitin kuɗi na majalisar dattijai, da Sen Olamilakan Adeola.

    Sauran sun haɗa da Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, kwamitin majalisar wakilai, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ministan kasafin kuɗi, Atiku Bagudu, da kuma shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta ƙasa, Zachs Adedeji.

  10. Kotu ta bayar da belin tsohon shugaban CBN, Godwin Emefiele

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Mai sharia'a Olukayode Adeniyi na babbar kotun tarayya da ke Abuja a Najeriya ta bayar da belin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

    Alƙalin ya bayar da umarnin sakin Emefiele nan take ga lauyoyinsa, waɗanda aka ɗora wa alhakin kai shi kotu a zaman da za a yi a makon gobe da kuma duk lokacin da ake buƙata.

    Alƙalin ya kuma ce wajibi ne ga tsohon shugaban bankin na CBN ya ajiye dukkanin takardun tafiye-tafiyensa a hannun magatakardar kotun kafin shari'ar ta kankama.

    Haka nan ta kuma ce dole ne a daina tsare shi ba tare da shari'a ba.

    Kotun ta ce ba za ta kawar da idonta daga batun cewa ya shafe kwana 151 a tsare ba, kuma kotun ta ce dole ne gwamnatin tarayya da ministan shari'a su martaba umarnin kotu.

    • Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele
    • Yadda za ku gane jabun sabon kudin Najeriya
  11. Birtaniya da Amurka sun fitar da sabuwar sanarwar tsaro kan Uganda

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Babbar hukumar Biritaniya da ofishin jakadancin Amurka da ke Uganda sun ba da gargadi game da ƙaruwar barazanar ta'addanci a Uganda, musamman ga baƙi 'yan kasashen waje.

    Suna ba da shawarar hana halartar manyan tarukan da suka haɗa da ayyukan addini da bukukuwan kade-kade, yayin da shahararren bikin Nyege Nyege ke gabatowa.

    Bugu da kari, gwamnatin Burtaniya ta shawarci 'yan kasarta da su guji ziyartar wuraren shaƙatawa biyo bayan harin baya-bayan nan da kungiyar 'yan ta'adda ta Allied Democratic Forces (ADF) ta kai wanda ya yi sanadin mutuwar wasu ma'auratan Birtaniya da Afirka ta Kudu tare da jagoransu ɗan Uganda.

    Uganda ta fuskanci ƙaruwar rashin tsaro, inda a baya-bayan nan aka daƙile hare-haren da kungiyar ADF ta kai kan majami'u da kuma wani mummunan harin da ta kai a wata makaranta a watan Yuni.

  12. Pepe ya kafa tarihi a gasar Champions League

  13. An kashe wani mutum lokacin gwajin maganin bindiga a Bauchi

    ...

    Asalin hoton, MERSEYSIDE POLICE

    An harbe wani mutum a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya wajen gwajin maganin bindiga, kamar yadda kakakin ƴan sanda, Ahmed Wakil ya bayyana.

    Ya ƙara da cewa an kama bokan wanda ake zargin shi ne ya bai wa mutumin maganin bindigar sannan kuma ya harbe shi, tare da wasu mutane biyu yayin da sauran waɗanda ake zargi suka gudu.

    Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa sunan wanda aka harba shi ne Muhammadu Ali, mai shekara 43.

    Kakakin ya kara da cewa, ‘yan sanda sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kai Ali asibiti, sai dai an tabbatar da mutuwar sa a lokacin da suka isa.

    Ya kuma gargadi jama’a da su guje wa irin waɗannan abubuwa.

    Za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike, in ji Wakil.

    Ƴan Najeriya da dama sun yi amanna da amfani da asiri wanda suke ganin zai ba su kariya, inda mutane da dama ke tuntubar bokaye kan irin waɗannan batutuwa.

    Sai dai an samu rahotannin kashe mutane da dama wajen irin wannan gwaji na maganin bindiga.

  14. Amurka ta gargaɗi Isra'ila kada ta sake mamaye Gaza bayan yaƙi

    Israel soldiers

    Asalin hoton, ISRAEL DEFENSE FORCES

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi gargadin cewa kada Isra'ila ta sake mamaye Gaza bayan kammala yaki da kungiyar Hamas.

    Blinken ya kuma dage a kan cewa Hamas ba za ta ci gaba da mulki a can ba, don kuwa hakan zai iya sanyawa a sake maimaita hare-haren da suka faru ranar 7 ga watan Oktoba.

    Ya ce ba za a tilasta wa mutane barin yankin ba, ko kuma yi musu kofar rago ko cin iyakar zirin, sannan Hukumar Falasdinawa mai sansani a Gabar Yamma ce ya kamata ta karbi ragamar mulki.

    Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce Isra'ila "za ta karbi alhakin dukkan harkokin tsaro" na Gaza har illa masha Allahu.

    Bai dai yi karin haske ba a kan yadda abin zai kasance lokacin da yake jawabi yayin wata hira ta talbijin ranar Litinin, sai dai wani wakili a majalisar ministocin yaki, ya fada wa BBC cewa Netanyahu ba ya nufin sake mamaya ba.

  15. Emiefele ya sake bayyana a gaban kotu

    Emefiele

    Asalin hoton, CHANNELS TV

    Hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta Najeriya ta gurfanar da Godwin Emefiele, tsohon gwamnan babban bankin ƙsar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a yau Laraba.

    Wannan matakin dai ya zo ne bayan umarnin da kotu ta bayar na gurfanar da Emefiele ranar Litinin da ta gabata, ko kuma a sake shi ba tare da wani sharaɗi ba.

    Dangane da rashin biyayyar da hukumar ta yi, kotun ta sake nanata umarninta tare da ɗage ci gaba da shari'ar har zuwa ranar Laraba.

    Mai shari’a, Olukayode Adeniyi na babbar kotun birnin tarayya ya ba da umarnin a sake Emefiele, wanda ya kwashe sama da kwanaki 149 a hannun jami’an tsaro ba tare da wani sharaɗi ba ko kuma a kai shi kotu domin neman beli.

    Ya bayyana a gaban kotu da misalin karfe 12:30 tare da rakiyar jami’an hukumar EFCC.

    • Abin da ya kamata ku sani game da kama gwamnan CBN Emefiele
    • Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele
  16. Isra'ila ta kara wa'adin ficewar fararen hula da sa'a daya saboda 'yawan mutane'

    Sojojin Isra'ila sun kara tsawon lokacin da suka bayar ga fararen hula don su fice daga arewacin Gaza, da sa'a daya a yau, saboda abin da ta kira "gagarumin amsa kira da mutane suka yi".

    Da farko, sojojin Isra'ila sun bude hanyar ne tsawon sa'a hudu don bai wa fararen hula damar ficewa zuwa kudancin Zirin Gaza.

    Sai dai a wani sako da ya wallafa a shafin X, Cogat, wanda wani sashen Ma'aikatar Tsaron Isra'ila ne, ya ce rundunar sojin kasar "ta kara lokacin ficewar ne da sa'a daya, wato ya zuwa karfe 3:00 na rana, don bai wa 'yan Gaza damar komawa kudu saboda tsaron rayuwarsu".

    Babu masaniya a kan ko mutane nawa ne suka yi amfani da hanyar da aka tanada don ficewa a yau, sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce wadanda suka fice din sun kai 15,000.

    Duk da haka, ana jin cewa akwai dubun dubatar mutanen da suka rage a yankin arewa na Zirin Gaza.

  17. 'Yan kwadago sun shiga yajin aiki a jihar Imo bayan 'kai wa shugabanninsu farmaki'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Manyan ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya biyu na NLC da TUC, sun sanar da shiga yajin aiki a fadin kasar daga ranar 14 ga watan Nuwamba, saboda harin da suka ce an kai wa ɗaya daga cikin shugabanninsu cikin makon jiya a jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar.

    Ƙungiyoyin na neman a ladabtar da wasu jami’an 'yan sanda da suke da hannu wajen kamawa da cin zarafin jagoransu, Joe Ajaero a Imo.

    Harin dai ya faru ne a yayin wata zanga-zangar da shugabannin kwadago suka jagoranta, ta neman biyan albashin ma’aikata da aiwatar da mafi ƙarancin albashi na kasa, da sauran haƙƙoƙin ma’aikata.

    Gwamnan jihar ya musanta hannu a lamarin, yayin kuma da aka sauya wa kwamishinan ‘yan sanda wurin aiki .

    Yajin aikin dai ya haɗar da umarnin katse wutar lantarki da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin sama na Imo, lamarin da ke kara tada jijiyoyin wuya a jihar wadda tuni take fama da matsalolin ƴan a-ware.

    A baya dai, ƙungiyoyin sun yi barazanar shiga yajin aiki saboda tabarbarewar tattalin arziki, amma suka janye bayan tattaunawa da shugaban ƙasar, Bola Tinubu.

    Ƙungiyoyin ƙwadagon sun sanya ranar Talata mai zuwa don fara yajin aiki a fadin kasar, matukar ba a biya musu bukatunsu ba.

    • Kotu ta dakatar da ƙungiyoyin ƙwadago daga shiga yajin aiki a Najeriya
    • NLC: Kungiyar ƙwadago a Najeriya ta yi zanga-zanga kan ƙarin albashi
  18. Makiyayi ya gartsa wa kada cizo don kubutar da kansa

    Croc

    Asalin hoton, PA Media

    Bayanan hoto, Kadoji suna da kariya a idon doka a yankin Northern Territory da Australia

    Wani makiyayi dan kasar Australia ya tsallake rijiya da baya, bayan ya yi artabu da wani kada da ya far masa, inda shi ma ya gatsa wa kadan cizo.

    Mai kiwon shanun Colin Deveraux ya shafe tsawon wata daya yana jinya a asibiti, bayan zabgegen kadan mai tsawon kafa goma ya raunata shi a yankin Northern Territory.

    Ya fada wa tashar labarai ta ABC News cewa ya gartsa wa kadan cizo ne a kan fatar idonsa lokacin da yake fafutukar tsira da rai.

    Mista Colin Deveraux ya ce ya shiga garari ne bayan ya tsaya a wani tafki lokacin da yake tafiya a kusa da Kogin Finniss cikin watan jiya.

    Ya ce ya dan tsaya a gefe, bayan ya lura da kifayen da ke ninkaya a ruwa. Amma lokacin da ya dan ja da baya, sai ya ji kawai kada ya cafkar masa kafar dama, inda ya jijjiga shi kamar tsumma sannan ya fizge shi cikin ruwa.

    Makiyayin ya fada wa tashar ABC cewa da farko ya sa daya kafarsa ya shuri kadan - kafin ya sa baki ya gartsa masa cizo.

    "Ina cikin wani yanayi na rudewa… sai kwatsam na ji hakorana sun kama fatar idonsa. Tana da matukar kauri, kamar wata jakar fata, amma kawai sai na ja da karfi, ai kuwa sai ya sake ni.

    "Na yi tsalle na fito, na nufi wurin da motata take. Amma ya sake biyo ni kamar tafiyar mita hudu, kafin kuma sai ya tsaya."

    Mista Colin Deveraux ya ce ya yi amfani da tawul da igiya wajen daure kafarsa da ke zubar da jini, sannan dan'uwansa ya tuko shi a mota, tafiyar kilomita 130 zuwa Asibitin Royal Darwin.

    • Abin da ya sa aka sauya wa kadoji 1,000 wurin zama a India
    • Mutumin da ke rayuwa da macizai da kadoji 400 a gidansa
  19. Al-Ittihad ta sallami tsohon kocin Tottenham Nuno Espirito Santo

  20. An dakatar da magoyin bayan Crystal Palace kan ci zarafin Son