Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Za mu ƙara yawan hare-hare a kan Zirin Gaza - Sojin Isra'ila

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Matsin rayuwa da ake ciki a yanzu na wucin-gadi ne - Tinubu

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce gwmnatinsa na gudanar da tsare-tsare da manufofi da nufin samar wa 'yan ƙasar ci gaba mai ɗorewa

    Tinubu na wannan jawabi ne a lokacin da wakilan ƙungiyar Musulmi ta kudu maso yammacin ƙasar suka kai masa ziyara ranar Juma'a a fadarsa da ke Villa, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Shugaban ƙasar ya ce ƙasar na buƙatar sadaukarwa domin samun ci gaba.

    “Abu ne da ya shafi makomarmu. dole ne mu samar wa kanmu makoma mai kyau. Allah ba zai ɗora mana abin da ba za mu iya ba. Allah na da dalilinsa na kawo mu wannna matsayi, Abubuwa na ƙara tsananta, amma da yardarsa (Allah), za su yi sauƙi"".

    Tinubu ya kuma kare matakinsa na cire tallafin man fetur da cewa ya yi hakan ne domin tseratar da ƙasar daga durƙushewa.

    "Mun kwashe kimanin shekara 40 muna ta ƙoƙarin kauce wa matakin (cire tallafin mai). Za mu sha wahalar matakin a yanzu, to amma domin tseratar da ƙasarmu daga durƙushewa, ya zama wajibi mu cire tallafin mai".

    “A tarihin ƙasashen da suka ci gaba, babban abin da ya kawo musu ci gaban, shi ne ɗaukar matakai masu tsanani da shugabanninsu suka yi a lokacin da ya dace kan dalilan da suka dace''.

    Shugaban ƙasar ya ce matsalolin da ƙasar ke fuskanta a yanzu na wucin-gadi ne, inda ya tabbatar wa 'yan ƙasar cewa daɗi na zuwa a gaba.

    “Za mu yi bakin ƙoƙarinmu, kuma tattalin arzikinmu zai bunƙasa domin ci gaban 'yan ƙasarmu, ina da tabbaci kan haka, za mu yi aiki don tabbatar da haka", in Tinubu.

  2. WHO ta ce muhimman kayayyaki da magunguna sun nufi Gaza

    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce tana aiki da gwamnatin Masar da ƙungiyar Agaji ta Red Cresent a Falasɗinu, don tabbatar da magunguna sun isa asibitocin Gaza.

    WHO ta ce motocin da ke ɗauke da kayan tallafin na Masar inda suka nufi mashigin Rafah.

    Hukumar ta WHO ta ce motocin na ɗauke da:

    • "Magungunan rage damuwa ga mutum 1,200"
    • "Jakankunan da ke ɗauke da kayan magance raunukan nan-take ga mutum 235.
    • "Magungunan cutuka masu tsanani ga mutum 1,500 da sauran muhimman magungunan ga mutum 300,000 na tsawon wata uku.

    "Waɗannan kayayaki za su tallafa, musamman ga mutane da suka jikkata, da waɗanda ke fama da cutuka masu tsanani, waɗanda suka shafe mako biyu ba tare da samun ingantaccen kulawa sakamakon rashin magunguna da sauran kayayyaki ba," kamar yadda WHO ta bayana.

    Tun da farko, sakataren harkokin wajen Birtaniya ya ce kayan agajin da aka fara kai wa Gaza a safiyar yau, 'bai kamata a ce na ɗan lokaci ba ne'

  3. Republican a majalisar wakilan Amurka ta janye goyon bayanta ga Jim Jordan

    Yan jam'iyyar Republican a majalisar wakilan Amurka sun janye goyon bayansu ga mai ra'ayin riƙau Jim Jordan, bayan da ya sha kaye a zaben shugaban Majalisar Wakilan kasar a karo na uku a jiya Juma'a.

    Republican ce ke da ɗan ƙaramin rinjaye a majalisar, amma goyon bayan da suke bai wa Mista Jordan wanda ke samun goyon bayan Donald Trump ya ragu a makon da ya gabata.

    Ba a dai bayyana wanda za su gabatar a gaba a matsayin shugaban majalisar ba.

    Rashin fitar da kakakin majalisa tsawon makwanni biyu ya sa majalisar ta kasa yin muhawara kan batutuwa da dama, ciki har da buƙatar Shugaba Biden da aka gabatar ranar Juma'a, ta neman sakin tallafin biliyoyin daloli na soji ga Ukraine da Isra'ila.

  4. 'Isra'ila ta ce 'yan ƙasarta su fice daga Masar da Jordan'

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito gwamnatin Isra'ila na kira ga 'yan ƙasarta da ke zaune a ƙasashen Masar da Jordan su yi bakin ƙoƙarinsu domin barin ƙasashen biyu.

    Wata sanarwar da AFP ya samu daga majalisar tsaron Isra'ila, ta ce "muna gargaɗi ga mai ƙarfi ga masu yin tafiye-tafiye zuwa Masar (ciki har da Sinai) da kuma Jordan. Muna kira ga mutane kada su je waɗanan ƙasashe, kuma waɗanda ke cikin ƙasashen a halin yanzu, su yi ƙoƙarin fita daga cikinsu".

    A farkon wannan makon ma, Isra'ila ta yi wa 'yan ƙasarta da ke zaune a Turkiyya makamancin wannan gargaɗi.

  5. Kayan agajin mashigin Rafah sun yi kaɗan - MDD

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce kayan agajin da aka soma shiga da su Gaza, ba su kai abin da ake buƙata ga dubban fararen hular da ke buƙatar agajin ba.

    Jami'ar MDD mai kula da 'yan gudun hijirar Falasɗinu, Juliette Touma, ta ce akwai buƙatar ci gaba da shigar da kayan agajin.

    "Abin da fararen hula ke buƙata a Gaza shi ne ci gaba da ba su damar samun tallafin, ciki har da musamman man fetur ga cibiyoyin bayar da ruwan sha'', kamar yadda ta shaida wa BBC.

    Isra'ila ta amince da shigar da manyan motoci 20 ɗauke da kayan agaji zuwa Gaza ta mashigin Rafah, sai dai ba ta amince a shigar da man fetur ba.

    To amma Misis Touma ta ce man fetur na da matuƙar muhimmanci ga tasosahin samar da ruwan sha, "ruwan sha na dab da ƙarewa a Gaza, a wasu wuraren ma tuni ya ƙare", in ji jami'ar.

  6. Labarai da dumi-dumi, Kayan agaji sun soma shiga Gaza

    Kayan agaji sun soma shiga Gaza bayan amincewa da buɗe kan iyakar Rafah, Kali wasu hotunan yadda kayayakin agaji suka soma shiga Gaza daga kan iyakar Masar da Gaza.

  7. Labarai da dumi-dumi, An buɗe mashigin Rafah don kai agaji ga fararen hula a Gaza

    An buɗe mashigin kan iyakar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar domin kai kayan agaji ga dubban fararen hula.

    An ga manyan motoci ɗauke da kayan agaji na shiga ta kan iyakar daga Masar zuwa Gaza.

    Kawo yanzu ba a san tsawon wane lokaci mashigin zai ɗauka a buɗe ba.

    Isra'ila ta amince da barin manyan motocin 20 shiga zuwa Gaza.

    Majalisar Dinkin Duniya ce ta yi kiran buɗe kan iyakar domin isar da kayan agaji ga fararen hular da ke cikin tsananin buƙatar tallafin.

  8. Isra'ila ta umarci Red Crescent ta kwashe mutane daga asibinti a Gaza

    Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasɗinu ta ce sojojin Isra'ila sun ba ta umarnin gaggauta kwashe mutane daga asibitin Al-Quds da ke arewacin Gaza nan take, saboda shirin kai harin Bom da za ta yi.

    Ƙungiyar Likitocin ta ce yanzu haka akwai marasa lafiya 4,000 a asibitin, sannan dubban fararen hula na neman mafaka a cikinsa.

    Ta yi kira ga ƙasashen duniya su ɗauki matakin gaggawa don daƙile wani bala'i da ka iya faruwa.

    A halin da ake ciki kuma, jami'an kiwon lafiya a Gaza sun ce ci gaba da kai hare-hare ta sama da Isra'ila ke yi, ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 4,100 a Gaza.

    Fararen hula miliyan ɗaya ne ke gudun hijira kuma yawancinsu ba su da abinci ko tsaftataccen ruwan sha.

  9. Assalamu Alaikum

    Masu bin mu a shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiya.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassa daban-daban na duniya.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta da muhawara.