Abin da Isra'ila take lissafawa kafin ta auka wa Gaza

An wallafa

A tsawon kwanaki, Isra'ila ta bayyana cewa dakarunta na shirin shiga cikin Gaza tare da niyyar kawo karshen ƙungiyar Hamas, bayan kaddamar da samame zuwa kudancin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

Sama da sojojin wucin gadin 300,000 ne aka kira domin taimaka wa dakarun tsaron Isra'ila.

An girke tankokin yaƙin Merkava a gonaki da filaye na yankin Isra'ila da ke kusa da iyakar Gaza, da makaman atilari da kuma dubban sojoji waɗanda suke shirye domin gwabza faɗa.

Sojojin sama da kuma na ruwa a Isra'ila na ci gaba da far wa mayaƙan Hamas da na ƙungiyar Islamic Jihad ta Falasɗinawa da kuma wuraren ajiye makamansu a Gaza, inda suka kashe tare da jikkata fararen hula da dama a lokacin, da kuma wasu kaɗan daga cikin kwamandojin Hamas.

Ɓangarorin biyu da ke faɗa da juna sun musanta tare da ɗora wa juna laifi kan wani harin ranar Talata da aka kai kan wani asibiti a Gaza, wanda ya janyo mutuwar mutane da dama, inda mutane ke cewa hakan zai ƙara sanya fargaba ta ƙaru a yankin.

Don haka, me ya sa har yanzu Isra'ila ba ta mamaye Gaza ba kamar yanda ta yi alkawari?

Akwai abubuwa da dama da suka sa hakan ba ta faru.

Ziyarar shugaba Biden

Ziyarar gaggawa da shugaban Amurka Joe Biden ya yi zuwa Isra'ila a wannan mako, na ƙara nuna yadda Fadar White House ta damu matuka kan taɓarɓarewar al'amura a yankin.

Washington na nuna damuwa kan manyan abubuwa guda biyu: buƙatar agajin gaggawa da ke ƙaruwa da kuma barazanar cewa rikicin zai iya yaɗuwa a faɗin Gabas Ta Tsakiya.

Shugaban na Amurka ya riga da ya nuna adawarsa kan komawar Isra'ila a Gaza don yin mamaya, bayan janyewa a shekara ta 2005. A cewarsa, hakan zai zama "babban kuskure".

A hukumance, Biden na ziyara Isra'ila ne domin nuna goyon baya da Amurka ke da shi ga babbar ƙawartata ta da ke yankin Gabas Ta Tsakiya, da kuma jin shirin da ƙasar ke yi a kan Gaza.

A ɗaya ɓangaren kuwa, ana ganin cewa zai iya kiran gwamnatin Benjamin Netanyahu da ta sassauto kan irin tsauraran mataki da ta ɗauka kan Gaza. Amurkar za ta so jin yadda Isra'ilan za ta iya ficewa daga Gaza da kuma lokaci, in har ta kaddamar da mamaya.

Duk wani yunƙurin Isra'ila na kaddamar da mamaya kan Gaza yayin da ta kuma girke dakarun sojin sama a Tel Aviv, lamarin ba zai yi wa ƙasar ko kuma Amurka kyau ba.

A wata ziyararsa gab da lokacin da aka kai hari kan asibitin Al-Ahli Arab da ke Gaza, shugaba Biden ya fito fili ya goyi bayan irin abubuwan da Isra'ila ta yi, cewa makamin roka na Falasɗinawa ne ya haddasa fashewar.

Jami'an Falasɗinu sun ce harin da Isra'ila ta kai ta sama ya faɗa kan asibitin.

BBC na ƙoƙarin tabbatar da adadin waɗanda suka mutu, wanda ake fargabar sun kai ɗaruruwa, da kuma gano musabbabin fashewar.

Gargaɗin Iran

A ƴan kwanaki da suka wuce, Iran ta fitar da gargaɗin cewa ba za a bar Isra'ila ta ci gaba da kai wa Gaza hari ba. Me hakan ke nufi?

Iran ce ke samar da kuɗaɗe da horarwa da kuma ke iko da yawancin mayaƙa ƴan Shi'a a Gabas Ta Tsakiya. Ɗaya cikinsu ita ce Hezbollah a Lebanon, wadda ke zaune kusa da iyakar Isra'ila a arewaci.

Ƙasashen biyu sun gwabza yaƙi a 2006 da ya lalata wurare da dama da kuma ya ƙasa karewa, inda nakiyoyi da aka binne a kasa suka janyo lalacewar tankokin yaƙin Isra'ila na zamani da kuma yi musu kwantan-ɓauna.

Tun bayan nan, Hezbollah ta sake samun karfi da kuma makamai tare da taimakon Iran, inda yanzu ake tunanin cewa ƙungiyar na da rokoki da makamai masu linzami kusan 150,000 , wanda yawanci suka kasance masu cin dogon zango.

Akwai fargabar cewa idan Isra'ila ta mamaye Gaza, to Hezbollah za ta iya sake buɗe sabon sansani a iyaka da Isra'ila, abin da zai tilasta ƙasar ta shiga yaƙi a wurare biyu.

Sai dai babu tabbacin cewa Hezbollah na son shiga yaƙi a daidai wannan lokaci, musamman ma ganin cewa jiragen ruwan yaƙi na Amurka na shawagi a kusa da tekun Mediterranean, a shirye kuma domin taimakawa Isra'ila.

Hakan zai bai wa Isra'ila wani tabbaci cewa kowane irin hari daga Hezbollah, zai janyo martani mafi muni daga sojojin ruwan na Amurka.

Za a iya tunawa cewa, duk da cewa a farkon yaƙi na karshe da Isra'ila tayi da Hezbollah a 2006, mayakan sun samu nasarar lalata wani jirgin ruwa na yaƙi mallakin Isra'ila, ta hanyar amfani da makamai masu linzami.

Matsalar jin-kai

Tunanin gwamnatin Isra'ila na matsalar jin-kai na jan kafa, idan aka kwatanta shi da na sauran ƙasashen duniya, idan aka zo ga batun kawar da Hamas daga Gaza.

Yayin da adadin mutanen da suka mutu a ɓangaren Falasɗinawa ke karuwa sakamakon hare-hare babu kakkautawa da Isra'ila ke kai wa, an maye gurbin alhini da ake yi wa Isra'ila a faɗin duniya bayan kaddamar da hari da Hamas tayi a ranar 7 ga watan Oktoba, da kiran na ganin an dakatar da kai hare-hare ta sama a Gaza tare da buƙatar kare fararen hula.

Idan sojojin ƙasa na Isra'ila suka shiga cikin Gaza da karfi, to adadin waɗanda suka mutu zai iya ƙaruwa.

Sojojin Isra'ila ma za su mutu, daga hare-haren kwantan-ɓauna, da gwanayen harbin laɓe - yawancin faɗan na iya faruwa ne a ƙasa.

Sai dai akwai yiyuwar cewa fararen hula ne abin zai sake shafa.

Gagarumar gazawar jami'an leƙen asirin Isra'ila

Jami'an leƙen asirin Isra'ila sun gamu da ɓacin rana a wannan watan.

Shin Bet, hukumar leƙen asirin cikin gida, ta ɗauki alhakin gazawar saboda gaza gano cewa Hamas za ta kawo hari.

Ya kamata a ce tana da masu ba ta bayanai da kuma na leƙen asiri a cikin Gaza, tare da bin diddigin kwamandojin Hamas da ƴan Islamic Jihadi ta Falasɗinawa.

Sai dai duk da haka abin da ya faru a safiyar ranar Asabar a kudancin Isra'ila ya zama gazawar sirri mafi muni a tarihin ƙasar tun bayan yakin Yom Kippur a 1973.

Jami’an leƙen asirin Isra’ila na can suna ƙoƙarin ganin cewa sun gyara kuskuren da aka samu a cikin kwanaki 10 da suka wuce, tare da taimaka wa jami'an tsaron ƙasar gano sunaye da wuraren da aka yi garkuwa da su ƴan ƙasar da kuma inda kwamandojin Hamas ke ɓuya.

Mai yiwuwa sun nemi a ba su ƙarin lokaci domin tattara ƙarin bayanai ta yadda idan sojojin ƙasa suka shiga Gaza, to za su iya zuwa kai tsaye wurin da ake ajiye da mutanen, maimakon yawo cikin ɓaraguzan gine-gine a arewacin Gaza suna fuskantar hare-hare akai-akai, yayin da ake ta samun masu yin Allah-wadai daga yawancin ƙasashen duniya.

Ɓangarorin Hamas da na Islamic Jihadin na Falasɗinawa da ke aiki bayan hare-haren bama-bamai da Isra'ila ke ci gaba da kai wa, za su shirya kai hare-hare da yin kwantan-ɓauna ga duk wani sojin Isra'ila da suka gamu da shi.

Wannan zai kasance abu mai haɗari musamman a cikin wuraren ɓuya na karkashin ƙasa, sannan jami'an leƙen asirin Isra'ila za su yi sha'awar gano wuraren da mayaƙan suke.