Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Gaza na rura wutar tunzuri a manyan makarantun Amurka
Muhawara kan yaƙin da ake tafkawa tsakanin Isra'ila da Hamas na ƙaruwa a manyan makarantun Amurka. A irin wannan lokaci na shafukan zumunta da ke buƙatar kowa ya ɗauki ɓangare, anya akwai wani wuri daban da matasan Amurka za su tattauna da juna?
Ɗaruruwan ɗalibai ne suka taru a farfajiyar Jami'ar Columbia da ke Birnin New York makon da ya gabata don gudanar da zanga-zangar goyon baya ga Falasɗinawa da kuma Isra'ila - da kuma yin tir da kashe-kashe.
Masu goyon bayan Isra'ila akasarinsu Yahudawa, sun yi shigar fari da shuɗi na tutar Isra'ila. Kusan duk tsawon taron ba su ce komai ba, suna nuna hotunan mutanen da Hamas ta kashe a harin da ta kai Isra'ila.
Ɗaliban da ke goyon bayan Falasɗinawa kuwa, sun yi ta ɗaga alamomin da ke cewa "A Ba wa Falasɗinawa 'Yanci" kuma "A Kawo Ƙarshen Mamaya". Wata ɗaliba daga Gaza ta yi magana game da mahaifiyarta da ta maƙale sakamakon kullen da Isra'ila ta yi wa yankin.
Duk da cewa suna nesa da juna, bambancin tunaninsu ya fi haka nisa sosai kuma ratar na ƙaruwa yayin da agogo ke ci gaba da juyawa.
Ɗaya daga cikin shugabannin zanga-zangar ya karanto wata wasiƙa da ƙungiyar ɗalibai biyu suka rubuta kwana ɗaya bayan harin Hamas da ya kashe mutum aƙalla 1,400.
Harin "na abin tarihi ne ga Falasɗinawa, waɗanda suka karya katangar da take kashe su a wurin da ya fi ko'ina cunkoso a duniya".
"Duk da ƙalubalaen da ke gabansu," mai maganar ya ci gaba da bayani, "Falasɗinawa sun kai harin ramuwar gayya kan 'ya mulkin mallaka azzalumai."
A wajen waɗannan ɗaliban, harin da aka kai wa Isra'ila na da muhimmanci a rikicin da aka shafe shekaru ana yi don neman 'yancin Falasɗinawa. Kuma luguden wutar da Isra'ilar ke yi bayan haka alama ce ta rashin imani a kan Falasɗinawan.
Mutum kusan 3,000 ne suka mutu a Gaza sakamakon hare-haren ramuwa da Isra'ilar ke kaiwa, yayin da aka tarfa mutum fiye da miliyan biyu bayan garƙame yankin ta hanyar kashe lantarki da katse ruwan sha.
Jagororin Isra'ila na amfani da kaausasan kalamai, ,inda Ministan Tsaro Galant ya siffanta 'yan gwagwarmayar Hamas da "dabbobi". Kazalika, adadin mutanen da za su mutu zai ƙaru idan Isra'ila ta fara kai hari ta ƙasa.
Masu magana a wajen macin sun yi tir da kashe-kashen farar hula kuma suka yi shuru na mintuna. Amma ba su ambaci sunan waɗanda Hamas ta kashe ba.
Masu shirya zanga-zangar sun faɗa wa BBC cikin wata sanarwa cewa ba su ƙaunar ganin an kashe farar hula kuma "suna goyon bayan kiyaye rayuka da kuma adalci".
Sun ce "me ya sa ake gallaza wa ƙasa guda - ta Falasɗinawa - saboda ayyukan Hamas".
Sai dai masu goyon bayan Isra'ila ba su ji shi yana ambaton kashe-kashen da Hamas ta yi ba a kan 'yan ƙabilarsu da mabiya addininsu.
"Idan kuna goyon bayan kisan fararen hula, ba ku san 'yancin ɗan'adam," a cewar ɗaya daga cikin takardun da suke riƙe da su.
Ba Jami'ar Colombia ce kaɗai ke fuskantar wannan ba.
Ƙungiyoyin ɗalibai a Jami'ar Harvard sun fitar da sanarwa da ke ɗora wa Isra'ila alhakin kashe fararen hularta, abin da ya jawo cecekuce daga ƙungiyar tsofaffin ɗalibanta.
A sauran makarantun ƙasar, ana sukar makarantun da kuma ɗalibai kan ko dai suna goyon bayan tsattsauran ra'ayi ko kuma sun yi shuru game da hakan.
"Yankin Golf [na ƙasashen Laraba] na haɓaka, amma ina ganin abin da ke faruwa yana nuna halin da ake ciki ne a Isra'ila da Falasɗinu," a cewar Zachary Lockman, farfesa a Jami'ar New York.
A cewarsa, lamarin ya rarraba kan ɗalibai, yana mai cewa a kwalejoji da kuma shafukan zumunta mutane na ganin abin a matsayin: 'Ko dai suna tare da mu ko kuma suna goyon bayan maƙiyanmu'.
Farfesan ya bayyana wasu abubuwa da suka faru a baya don gane abin da ke rura wutar muhawarar a yanzu.
Na farko, gwagwarmayar Falasɗinawa ta zama abin da masu sassauƙan ra'ayi ke sha'awa a Amurka. Da yawa na siffanta abin da ƙarancin adalcin da ke faruwa a ɓangaren ƙabilanci a Amurka da irin katange Gaza da Isra'ila ke yi.
A Amurka, masu sukar gwamnatin Isra'ila na kallon ta ne a matsayin 'yar mulkin mallaka.
Har wa yau, ra'ayin Amurkawa kan Isra'ila na sauyawa tsawon shekaru. Akwai yiwuwar matasa za su fi ƙin goyon bayan Isra'ila, a cewar wani bincike na cibiyar Pew Research Center a watan Yulin 2022.
Haka nan, rabuwar kai ta ƙaru. A karon farko, mai yiwuwa ne 'yan jam'iyyar Democrat su fi tausaya wa Falasɗinawa, a cewar ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da Gallup ta gudanar, su kuma 'yan Republican za su fi tausaya wa Isra'ila.
Ɗaliban da ke goyon bayan Falasɗiwana na ganin cewa yayin da suke samun ƙarin goyon baya, har yanzu 'yan siyasa da kafofin yaɗa labaran Amurka da malaman jami'a sun fi goyon bayan Isra'ila.
A macin na ranar Alhamis, ƙungiyar Students for Justice in Palestine ta yi tir da shugabancin Jami'ar Columbia saboda ƙin goyon bayan Falasɗinawa.
"Na yi wa mahaifiyata ƙarya," in ji wata ɗaliba daga Gaza cikin masu macin, "na ce mata ba ni da wata matsala a jami'a."
Matasan Yahudawan da ke goyon bayan Isra'ila kuma, kan ce suna jin rashin ƙwarin gwiwa wani zubin idan ana muhawara a makaranta.
"Hatta a wannan jami'ar mai sassaucin ra'ayi, mutane ba su girmama junansu," a cewa Lihi Tal mai shekara 24, wadda ke karatu a COlumbia bayan ta kammala hidimar ƙasa a Isra'ila.
"Muna jin kamar mu kaɗai ne a jami'ar nan. Akwai waɗanda ke goya mana baya, amma dai ina jin tsoron na ce ni Bayahudiya ce."
Wasu ɗaliban kuma na da tsattsauran ra'ayi game da rikicin.
Masu goyon bayan Isra'ila sun nuna hotunan mutanen da Hamas ta kashe a harinta, amma ba su nuna waɗanda aka raunata a Gaza ba sakamakon hare-haren Isra'ila.
Kamar sauran 'yan uwansu, su ma sun ce ba su goyon bayan ƙuntata wa fararen hula a kwaone ɓangare, amma dai sun fi mayar da hankali kan waɗanda Hamas ta kashe.