Za mu ƙara yawan hare-hare a kan Zirin Gaza - Sojin Isra'ila

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Umar Mikail

  1. Sai da safe

    Ƙarshen rahotonnin ke nan a wannan shafi.

    Ku duba ƙasa domin karanta labaran da muka wallafa a yau Asabar, kafin mu kawo wasu sababbi gobe da safe.

    Umar Mikail ke muku fatan alheri.

  2. Za mu ƙara yawan hare-hare a kan Zirin Gaza - Sojin Isra'ila

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    'Yan mintuna da suka wuce, kakakin rundunar sojin Isra'ila, Daniel Hagari, ya ce za su ƙara yawan hare-haren da suke kaiwa kan Zirin Gaza a wannan yammacin.

    "Za mu ƙara yawan hare-harenmu, don mu rage haɗarin da ke gaban dakarunmu a mataki na gaba na wannan yaƙi, kuma za mu ƙara yawansu ne a yau," kamar yadda ya faɗa wa wani taron manema labarai.

    Hagari ya nemi mazauna Birnin Gaza "su ci gaba da guduwa zuwa kudancin birnin don tsira da ransu".

    A yau rundunar ta jejjefa wa mazauna birnin takardu ɗauke da sanarwar cewa lallai su yi hijira zuwa kudanci "idan ba haka ba kuma duk wanda suka gani to yana taimaka wa Hamas ne".

    Tuni Isra'ilar ta kashe sama da mutum 4,000 a hare-haren da take kaiwa tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

    Ta ce harin ramuwar gayya ne bayan Hamas ta kai mata hari tare da kashe mutum 1,400.

  3. Falasɗinawa na cikin irin halin da muka shiga a Afirka ta Kudu - Ramaphosa

    Cyril Ramaphosa

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin taro a birnin Al-Kahira na Masar, Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya kwatanta yanayin da farar hula ke ciki a Gaza da bala'in da baƙar fatar ƙasarsa suka fuskanta lokacin mulkin wariyar launin fata.

    Shugaba Ramaphosa ya ce: "Muna da jajirtattun shugabannin da suka ajiye bambancin da ke tsakaninsu suka zaɓi zaman lafiya, da haka muka kawo ƙarshen wariyar launin fata."

    Ya kuma bayyana kai wa fararen hula hari a Isra'ila da kuma hana shiga da fita a Gaza a matsayin "karya dokokin ƙasashen duniya".

    An shirya taron ne da zimmar lalubo hanyoyin dakatar da kashe rayuka a yaƙin da Isra'ila ke yi a kan Zirin Gza tun bayan da 'yan gwagwarmayar Hamas suka kai hari cikin ƙasar tare da kashe mutum 1,400.

    Isra'ilar ta kashe fiye da mutum 4,300 a lugudne wutar ramuwar gayya.

  4. Haaland ya ci kwallo na tara a Premier League

  5. Me shugabannin duniya suka ce a taron neman zaman lafiya na Masar?

    Alƙahira

    Asalin hoton, Reuters

    Kamar yadda muka bayar da rahoto, wakilan ƙasashen duniya na taro a Masar, inda suka yi kira da murya ɗaya wajen neman a kawo ƙarshen yaƙi tsakanin Isra'ila da Gaza.

    Ga abubuwan da wasu daga cikin shugabannin suka ce:

    • Babban Sakataren MDD António Guterres ya yi kira da a tsagaita wuta don kai kayan agaji
    • Sarkin Jordan Abdullah ya gargaɗi ƙasashen da ba Larabawa ba su daina aika "saƙo mai haɗari" da ke nuna "rayuwar Falasɗinawa ba ta kai ta 'yan Isra'ila muhimmanci ba"
    • Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce 'yan Afirka ta Kudu sun fahimci irin halin da Falasɗinawa ke ciki "wajen gwagwarmayar neman 'yancinsu"
    • Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya James Cleverly ya ce ya yi magana da gwamnatin Isra'ila kai-tsaye "game da alhakin da ke wuyanta na mutunta dokokin yaƙi da kuma muhimmancin kare rayukan farar hula a Gaza"
    • Ministan Harkokin Waje na Japan Yōko Kamikawa ya ce wajibi ne ƙasashen waje su tabbatar yaƙin "bai daƙile shirin zaman lafiya na Gabas ta Tsakiya ba"
    • Ministan Harkokin Waje na Brazil Mauro Vieira ya yi kira ga duniya da a kiyaye kada yaƙin ya tsallaka wata nahiyar
    • Ministan Harkokin Waje na Jamus Annalena Baerbock ya ce dole ne a kiyaye kada a rura wutar ƙiyayya, "saboda da ma abin da Hamas ke nema ke nan da kuma masu ɗaukar nauyinta"
  6. Isra'ila ta kai hare-hare 250 kan ma'aikatan lafiya, in ji ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila ta kai wa ma'aikata da wuraren kiwon lafiya 250 hari a Zirin Gaza da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu.

    A Zirin Gaza, an kashe ma'aikatan lafiya fiye da 37 bayan hare-hare 69 da aka kai kan cibiyoyin lafiya. Haka nan, an kai wa motocin ɗaukar marasa lafiya 24 hari, inda kuma asibitoci bakwai suka daina aiki.

    A Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, an kai hari 88 kan cibiyoyin lafiya, 26 kan motocin ɗaukar marasa lafiya.

    An samu hare-hare 56 da suka hana waɗanda aka jikkata samun kulawar likitoci.

  7. Mazauna Legas sun yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa

    Gomman masu zanga-zanga ne suka taru a birnin Legas da ke kudancin Najeriya don nuna goyon bayansu ga al'ummar Falasɗinu.

    Mutanen maza da mata sun fito ne a yau Asabar ɗauke da kwalaye iri-iri da ke neman "adalci ga Falasɗinu" da kuma "a bai wa Falasɗinu 'yanci".

    Da yawan waɗanda suka yi magana a wurin taron sun yi kira ga gwamnatin Najeriya ta ƙaurace wa hulɗa da Isra'ila, wadda ta ƙaddamar da hare-hare kan Zirin Gaza bayan mayaƙan Hamas sun kai mata hari.

    Legas

    Asalin hoton, Reuters

    Legas

    Asalin hoton, Reuters

    Legas

    Asalin hoton, Reuters

  8. Dubban mutane na nuna goyon baya ga Falasɗinawa a faɗin duniya

    Ana ci gaba gudanar da zanga-zanga a biranen duniya don nuna goyon baya ga al'ummar Falasɗinawa musamman na Zirin Gaza.

    Yau kwana na 15 ke nan da Isra'ila fara luguden wuta a kan birnin bayan harin da Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba, inda suka kashe mutum 1,400 kuma akasarinsu farar hula.

    Sai dai zuwa yanzu, Isra'ila ta kashe mutum 4,385 a hare-haren ramuwar gayya kan Gaza da kuma sauran garuruwan Falaɗinawa da ta mamaye.

    Warsaw, Poland

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Birnin Warsaw na ƙasar Poland
    Mombasa, Kenya

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Birnin Mombasa na Kenya
    Rome, Italy

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Birnin Rome na Italiya
    Tunis, Tunisiiya

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Birnin Tunis na Tunisiiya
    Duesseldorf, Germany

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Birnin Duesseldorf na Jamus
  9. Sir Bobby Charlton ya mutu yana da shekara 86

  10. 'Mutanen da suka mutu a Gaza sun kai 4,385'

    Hukumomin Falasɗinu sun ce adadin mutanen da suka mutu a yankin Gaza sun kai fiye da 4,000

    Ma'aikatar lafiyar yankin da ke ƙarƙashin ikon Hamas ta ce aƙalla mutum 4,385 ne aka kashe a yankin Zirin Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba.

    Cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce adadin ya haɗar da ƙananan yara 1,756.

  11. Auren zawarawa a Kano da motocin agaji zuwa Gaza cikin hotunan Afirka

  12. Amurka ta buƙaci a bar mashigar Rafah a buɗe

    Mashigar Rafah

    Asalin hoton, EPA

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya yi kira ga duka ɓagarori da su bar mashigar Rafah a buɗe domin bayar da dama a ci gaba da jigilar kayan agaji domin mutanen Gaza, kamar yadda wata sanarwa - da kamfanin dillancin labaran AFP ya gani - ta bayyana.

    Sanarwar ta ambato Mista Blinken na cewa "An gaya mana cewa: Kada Hamas ta yi katsalandan a wannan tallafi da ake kaiwa, domin ceton rayuka"

    "Fararen hular Falasɗinu ba su da hannu a harin da Hamas ta kai, don haka bai kamata a bari su wahala sakamakon ayyukan ƙungiyar ba"

    Tun da farko Majalisar Dinkin Duniya ta yi ƙorafin cewa motocin agaji 20 da Isra'ila ta amince da shigarsu zuwa Gaza ta mashigar Rafah, ba za su wadaci mutanen da ke cikin buƙatar tallafin a yankin ba.

  13. Yadda aka ɓarke da murna bayan shigar da kayan agaji ta mashigar Rafah

    A yau ne aka bayar da damar buɗe mashigar Rafah domin shigar da kayan agaji daga Masar zuwa Gaza.

    An bayar da dama ga manyan motoci 20 maƙare da kayan tallafi domin shiga cikin Gaza don raba wa fararen hular da ke buƙatar tallafin.

    Manyan motocin ɗauke da abinci da ruwan sha da magunguna, to sai dai babu man fetur.

    Mazauna duka ɓangarorin kan iyakar sun ɓarke da murna da sowa yayin da motocin suka fara shiga, saboda yadda ake tsananin buƙatar tallafin a yankin na Gaza.

    Bayanan bidiyo, Kalli yadda aka ɓarke da murna bayan shigar motocin da ke dauke da kayan agaji
  14. Dubban magoya bayan Falasɗinawa sun yi zanga-zanga a birnin Landan

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban masu zanga-zanga a Birtaniya sun taru a tsakiyar birnin Landan domin nuna goyon bayansu ga Falasɗinawan.

    Masu shirya zanga-zangar - da aka yi wa laƙabi da "Nuna goyon baya ga Falasɗinawa' - sun yi kiran gaggauta dakatar da wuta a Gaza, tare da bayar da damar aikewa da cikakken agaji ga masu buƙata

    Masu zanga-zangar riƙe da tutar Falasɗinawa sun yi ta rera waƙoƙin "A bai wa Falasɗinawan 'yanci".

    Dubban mutanen sun cika wasu titunan birnin ciki har da titin da ke kai wa fadar firaministan ƙasar.

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    A ranar Juma'a ma an gudanar da irin wannan zanga-zanga a wasu ƙasashen duniya irin su Thailand da Australiya da Netherlands da Afirka ta Kudu da wasu ƙasashen Larabawa masu yawa.

  15. Gane Mini Hanya tare da Gwamnan Katsina Dikko Radda

    Kimanin makwanni biyu da suka gabata ne gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya kaddamar da rundunar yan sintiri ta jihar wadda ta yi wa lakabi da 'Community Watch Corp'.

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin

    Hakan na zuwa ne yayin da jihar, kamar sauran jihohin arewa maso yammacin Najeriya ke fama da matsalar tsaro.

    A wata tattaunawa da manema labaru, gwamnan ya ce babu ranar da za ta zo ta wuce ba tare da matsalar tsaron ta haddasa mutuwar wani daga cikin al’ummar jihar ba.

    A tattaunawarsa da Rabiatu Kabir Runka lokacin ziyarar da ya kawo ofishinmu da ke Abuja, Gwamna Dikko Radda ya yi bayani kan yadda aka samar da rundunar da kuma fayyace wasu abubuwa na siyasa da suka faru tun bayan karɓar mulkinsa a jihar.

  16. MDD ce za ta raba kayan agaji a Gaza

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dinkin Duniya ce za ta raba kayan agaji da suka isa Gaza yau ta mashigar Rafah , kamar yadda wakilin BBC da ke wurin, Rushdi Abu Alouf, ya bayana.

    Ya ce jerin gwanon manyan motocin maƙare da kayan tallafin sun taso daga kan iyakar Rafah, inda suka bi ta Khan Younis na kudancin Gaza.

    Motocin jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun yi musu rakiya zuwa gidajen ajiye tallafin a kudancin birnin.

    Daga nan ne jami'an na MDD za su yanke hukunci kan yadda za su rabar da tallafin, da yiwuwar a aike da shi zuwa makarantun MDD, inda dubban fararen hula ke zaune, da kuma asibitocin yankin, kamar yadda ya bayyana.

  17. Ba za mu fice daga ƙasarmu ba - Shugaban Falasɗinawa

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabannin ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya da na Turai sun gudanar da wani taro a birnin Alƙahira na ƙasar Masar, domin tattauna batun rikicin Isra'ila da Gaza.

    Yayin da yake jawabi a wajen taron, shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas, ya ce babu wanda zai tilasta wa Falasɗinawa barin ƙasarsu.

    "Ba za mu amince da ficewa daga ƙasarmu ba, za mu ci gaba da zama a ƙasarmu, a kowane hali kuwa", in ji shi.

    Mahmoud Abbas shi ne shugaban gwamnatin Falsɗinawa, da ke da iko da yankunan Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, to amma ba ya iko da yankin Zirin Gaza.

    A baya ƙasar Masar da sauran ƙasashen Larabawa sun ce ba za a amince da kwararar Falasɗinawa domin zama 'yan gudun hijira ba, saboda a cewarsu hakan zai tilasta fitar da su daga ƙasarsu.

    Taron wanda aka yi wa laƙabi da 'Taron Zaman Lafiya' ya ƙunshi wakilai daga ƙasashen Jordan da Qatar da Italiya da Sifaniya da Tarayar Turai da Birtaniya.

    Sai dai ba a ga wakilan ƙasashen Amurka da Isra'ila da Iran a wajen taron ba.

  18. Hotunan yadda aka shigar da kayyakin agaji ta mashigar Rafah

    kayan agaji

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Da safiyar ranar Asabar ne aka buɗe mashigar kan iyakar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar domin kai kayan agaji ga dubban fararen hula.
    kayan agaji

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An ga manyan motoci ɗauke da kayan agaji na shiga ta kan iyakar daga Masar zuwa Gaza.
    kayan agaji

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Kawo yanzu ba a san tsawon wane lokaci mashar za ta ɗauka a buɗe ba.
    e

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Isra'ila ta amince da barin manyan motocin 20 shiga zuwa Gaza.
    kayan agaji

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Majalisar Dinkin Duniya ce ta yi kiran buɗe kan iyakar domin isar da kayan agaji ga fararen hular da ke cikin tsananin buƙatar tallafin.
  19. Babbar mota cike da akwatunan gawa na cikin motocin agaji da suka shiga Gaza

    Wakilin BBC da ke mashigar Rafah, Rushdi Abu Alouf, na kallon manyan motocin da ke ɗauke da kayan agaji na shiga Gaza daga masar ta mashigar Rafah.

    Ya ƙirga motoci 20 da suka shiga Gaza ya zuwa yanzu, kamar yadda ya ce.

    Wannan shi ne adadin motocin da Isra'ila ta amince su shiga Gaza a halin yanzu.

    Daya daga cikin motocin na maƙare da akwatunan gawa, yayin da sauran ke ɗauke da magunguna.

    Jami'an Falasɗinawa sun ce mutum 4,137 ne suka mutu a Gaza, tun bayan da Hamas ta ƙaddamar da hari kan Isra'ila makonni biyu da suka gabata.

    Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar kai hare-haren boma-bomai zuwa Gaza.

  20. 'Yan Isra'ila 210 ake garkuwa da su a Gaza

    Mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila ya ce sun sanar da iyalan 'yan ƙasarta 210 cewa ana garkuwa da su a Zirin Gaza.

    Wannan adadi bai haɗar da Amurkawan na biyu, uwa da 'yarta ba (Judith da Natalie Raanan) da Hamas ta sanar da sakinsu ranar Juma'a da daddare.