Me ya sa alaƙar Iran da Hamas ke da ƙarfi?

ईरान और हमास

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jagoran addini na Iran Ayatollah ali khamenei
    • Marubuci, बीबीसी मॉनिटरिंग
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, .
  • An wallafa

Tun bayan da ƙungiyar Hamas ta ƙaddamar da harin da 'ba a taɓa ganin irinsa ba' kan sojoji da fararen hular Isra'ila a kusa da Zirin Gaza, jita-jitar suka yi ta yaduwa kan rawar da Iran ta taka a wannan hari da irin alaƙarta da kungiyoyin Falasɗinawa.

Rikicin na baya-bayan nan ya ɓarke ranar 7 ga watan Oktoba lokacin da ƙungiyar Hamas ta ƙaddamar da hari da asubar fari kan sojoji da fararen hular Isara'ila.

Fiye da 'yan Isra'ila dubu guda ne suka mutu a harin, sannan kuma Hamas ta kama kusan mutum 200 ta yi garkuwa da su.

A martanin da ta mayar, Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare ta sama a kan Zirin Gaza mai dimbin jama'a. Lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 3000 kawo yanzu.

Isra'ila ta rufe ilahirin iyakokin Gaza. A yanzu babu batun shigar da abinci da magunguna ba kuma wutar lantarki.

Yiwuwar yaɗuwar wannan rikicin zuwa wasu sassan na ci gaba da ƙaruwa. Dakarun Isra'ila na fuskantar wuta ta ɓangaren tuddan Golan.

Yayin da ƙungiyar Hezbollah ta zame musu matsala a kudancin Labanon.

A lokaci guda kuma, ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran a iraƙi na yin barazana ga sansanonin sojin Amurka, haka kuma ƙungiyar mayaƙan Houthi ta Yamen na bayar da tallafin soji ga ƙungiyoyin Falasɗinawa. To sai dai Iran ce kadai ke amfana da ayyukan wadannan kungiyoyi.

Yayin da jami'an Iran ke murna kan harin da Hamas ta kai wa Isra'ila a matsayin nasara ga Falasdinawa, sun fito ƙarara sun musanta hannun Tehran a kitsa harin.

A ɗaya ɓangaren kuma, Amurka da Isra'ila sun yi zargin haka, ba tare da ƙwaƙƙwarar hujjar da za ta tabbatar da hannun Iran a harin ba. Iran na da kyakkyawar alaƙa da ƙungiyoyin Falasɗinawa.

Tallafin kuɗi da kayan aiki da Iran ke bai wa ƙungiyoyin da ke Gaza na taimaka musu wajen mayar da martani kan hare-haren da Isra'ila ke kai musu ta sama da ta ƙasa.

yayinda da ake tsaka da wanna rikici, ya zama wajibi a aza ayar tambaya kan yadda Iran ta zama babbar ƙasar da ke tallafa wa ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi a Falasdinu da yadda wanna tallafi ke tasiri a ɗabi'unta.

Tarihin goyon bayan

इस्लाइल हानिया

Asalin hoton, Reuters

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun bayan juyin-juya halin Iran a shekarar 1979, jamhuriyar musuluncin ke alfahari da tallafa wa Falasdinawa.

Kafin juyin-juya-halin, Iran ce - ƙasar musulmi ta biyu a duniya da ta amince da wanzuwar ƙasar Isra'ila, - a Lokacin tana ƙarƙashin jagorancin Mohammad Reza Pahlavi.

Amma yanzu a cikin ƙasashen yankin gabas ta tsakiya, Iran ce ƙasar da ta ƙi amincewa da Isra'ila a matsayin ƙasa, a daidai lokacin da sauran ƙasashen musulmin yankin suka fara gyara alaƙarsu da Isra'ila.

Ayatollah Ruhollah Khomeini - wanda ya kafa jamhuriyar musuluncin - ya mutu ne sakamkon cutar Kansa.

A zamaninsa ya yi ta yin amfani da batun Falasdinawa wajen ƙara wa gwamnatinsa kima a idanun musulman duniya, tare da ƙoƙarin haɗa kan musulmai ba tare da la'akari da bambancin da ke tsakanin 'yan Shi'a da 'yan Sunni ba.

Khomeini ya kuma ɓullo da bikin 'Ranar Kudus' da ake yi a ranar ƙashe ta watan azumin Ramadan a kowace shekara domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa.

Haka kuma Iran na daya daga cikin ƙasashen da ke sha'awar kafa ƙungiyar ci gaban Falasdinawa ta 'Palestine Liberation Organization'(PLO). To sai dai alaƙarta ta PLO ta yi tsami a lokacin da shugaban PLO Yasser Arafat ya goyi bayan Iraƙi a lokacin yakin Iran da Iraƙin.

A shekarar 1988 Ayatollah Ali Khomeini ya bayyana Arafat a matsayin 'butulu kuma shashasha'. A lokacin, Yasser Arafat ya so cimma yarjejeniyar siyasa da Isra'ila, to amma shugabannin Iran sun nuka adawa da duk wata tataunawar zaman lafiya da Isra'ila.

Ali Khomeini na matsayin jagoran Iran, a yayin da ƙungiyoyin Falasdinawa suka fara amun saɓani kan amincewa da isra'ila. Daga nan ne kuma Iran ta daina daga goyon bayan kungiyar PLO mai ƙungiyar Fatah zuwa ƙungiyar Hamas mai tsattsauran ra'ayi da ƙungiyar Jihadin Falasdinawa ta PIJ.

Bayan zaɓukan 2007, Hamas ta karɓe ikon Gaza, yayin da da Fatah ta ƙarbi iko da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan. Sakamkon wannan bambancin siyasa tsakanin ƙungiyoyin Falasɗinawa da ke adawa da juna, sai Iran ta karkatar da tallafin da take bai wa Falasɗinawa zuwa yankin Zirin Gaza da Hamas da PIJ ke iko da shi.

Waɗannan ƙungiyoyi masu kaifin kishin musulunci sun shiga ƙawancen aikin soji da ƙawayen Iran da ke yankin, irin su Hezbollah da kungiyoyin Syria, inda suka haɗa kai wajen adawa da Isra'ila da Amurka.

To sai dai an samu saɓani a ƙawancen nasu.

A lokacin yaƙin basasar Syria da ka fara a shekarar 2011, inda Iran ta goyi bayan shugaba Bashar al-Assad, yayin da Hamas ta ayyana goyon bayanta ga ɓangaren da ke adawa da Assad.

Shugabannin Hamas da suka kwashe shekaru masu yawa suna zama a syrai sun rufe ofishinsu a Damascus.

Sakamakon sukar da shugaban Syria Bashar al-Assad ke sha kan hare-haren da yake kai wa ƙungiyoyin adawa, ya sa Hamas ta fice daga ƙasar tare da kafa sansaninta a Qatar a shekarar 2012.

Tallafi bayan daidaituwar alaƙa

ईरान-हमास

Asalin hoton, Getty Images

Alaƙar Iran da ƙungiyoyin Falasɗinawa, musamman Hamas ta ƙara ƙarfi, ganin cewa a yanzu da ƙungiyar ta zama saniyar-ware a idanun duniya.

Rashin yin galaba a kan shugaba Assad a Syria, da kuma matakin ga gwamnatin Masar ta ɗauka na rufe kan iyakar Sinai da Gaza, ya sanya Hamas fara samun rauni ta fuskar kuɗi.

Wannan shi ne dalilin da ya sa Hamas ta fara neman mafaka a Iran.

Har yanzu ba a sanya Hamas cikin manyan ƙawayen Iran, sai dai ana jiran ganin ko ƙungiyar za ta kyautata alaƙarta da babbar ƙawar Iran, wato Syria za ta kyautata ko akasin haka.

Yayin da take ƙoƙarin faɗaɗa ayyukanta a yankin gabas ta tsakiya, ƙungiyar ba ta da ƙawaye masu yawa. Saboda Larabawa da ƙasashen Musulmai kamar UAE da Moroko da Bahrain da Sudan sun ƙara inganta alaƙarsu da Isra'ila tsakanin shekarun 2020 zuwa 2021.

Waɗannan ƙasashe na da alaƙa ta ƙut-da-ƙut da Saudiyya. Haka kuma akwai rahotonnin da ke cewa Saudiyya na tattauna wata yarjejeniya domin kyautata alaƙa da Isra'ila.

To sai dai da alama harin baya-bayan na da Hamas ta kai wa Isra'ila da kuma hare-haren da Isra'ilar ke kai wa yankin Zirin Gaza na nuna alamar kawo ƙarshen wannan tattaunawa.

To sai dai kafofin yaɗa labaran Saudiyya sun zargi Hamas da yunƙurin cika muradin Iran na kawo cikas ga yunƙurin Saudiyya na samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

A yanzu ana ganin Hamas na faɗan ita kaɗai, to amma idan faɗan ya ci gaba zai iya shafar ƙungiyoyin Falasɗinawa da Iran, waɗanda ke adawa da ƙulla alaƙa da ƙasar Isra'ila.

Ta ya Iran ke tallafa wa ƙungiyoyin Falasɗinawa?

ईरान और हमास

Asalin hoton, Getty Images

Ƙungiyoyin Falasɗinawa a Gaza da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan na samun tallafin soji daga dakarun Ƙurɗawa, wani ɓangare na dakarun juyin juya hali na (IRGC)

Mayaƙan Ƙurɗawa ne ke tafiyar da ayyukan sojin Iran a ƙasashen duniya. Babu shakka wannan tallafi na kuɗi ne. Baya ga haka dakarun na safarar ƙananna makamai da wasu kayayyakin hada makaman zuwa Iran.

Bayan harin na 7 ga watan Oktoba, tsohon kwamandan IRGC Hussein Kanani Moghaddam ya yi cikakken bayani kan taimakon da Iran ke bai wa Hamas.

Wannan ya hada da taimaka wa Hamas wajen ƙera manyan makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da za su iya shallake na'urar kakkaɓo makamai da Isra'ila ke da ita, kamar yadda kafar yada labaran Al-Monitor ta wallafa a 2021.

A cikin rahoton, an bayyana wasu hanyoyin da Iran ta bi wajen safarar makamai zuwa Gaza. Rahoton ya ƙara da cewa Iran ta aike da makamai daga Masar ta ƙasa da ta ruwa, waɗanda suka isa inda ake so su isa.

A baya-bayan nan mayaƙan Ƙurɗawa kan yi amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai makamai Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da wasu wuraren. Sai dai ba a bayyana cikakkun alƙaluman tallafin da Iran ta bai wa Falaɗinawa ba.

Sai dai a cikin watan Aprilun 2023, Gallant ya yi kiyasin cewa Iran na aike wa da tallafin dala biliyan 10 ga ƙungiyar Hamas a kowace shekara. Baya ga haka ƙungiyar PIJ na samun maƙudan rupees daga Iran ɗin.

Kafin harin baya-bayan nan da Hamas ta kai, babban kwamandan dakarun juyin-juya-hali na IRGC, Manjo Janar Hussein Salami, ya bayyana cewa a shekarar 2022, makamai masu linzami ba za su zama abu mai muhimmanci a rikicin Isra'ila da Falasɗinawa ba, yana mai cewa abu mafi muhimmanci a yaƙin zai kasance a ƙasa.

Ya ƙara da cewa. "A yau Falasdinawa na da ƙarfin da za su yi yaƙi a ƙasa. Domin Isra'ila tana da babban rauni ta ƙasa".

Hare-hare ta sama ba za su fayyace ƙarfin yaƙin ba. Makamai masu linzami na da muhimmanci ga yaƙin nesa, amma ba za su yi tasiri a yaƙin ƙasa ba."