Hamas ta saki uwa da ƴarta da ta yi garkuwa da su

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi, Mukhtar Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Daliban Kano sun tafi Indiya a karkashin shirin tallafin karatu na gwamnatin jihar

    Kano post-graduate students on their way to India

    Asalin hoton, Kano state govt

    Kashin farko na ɗaliban da gwamnatin Kano ta ɗauki nauyin karatunsu a kasashen waje sun tashi daga filin jirgin sama na Mallam Aminu zuwa kasar Indiya.

    Ɗalibai 150 ne mata da maza, wadanda gwamnatin Kano ta zaba zuwa karatun digiri na biyu a karkashin shirin gwamnatin na tura hazikan dalibai zuwa kasashen waje don zurfafa ilmi.

    Rukunin na cikin dalibai 1,001 da ke da digiri mai daraja ta ɗaya da aka tantance kuma aka amince da tafiyarsu. Ga karin bayani a cikin rahoton Zahraddeen Lawan:

  2. Bazoum ya musanta zargin tserewa daga Nijar

    Shugaban Nijar Mohamed Bazoum

    Asalin hoton, Bazoum

    Lauyoyin da ke iƙirarin suna wakiltar hamɓararren shugaban Nijar, sun yi watsi da zargin da shugabannin mulkin sojin ƙasar suka yi cewa Bazoum Mohamed da iyalansa sun yi yunƙurin tserewa daga inda ake tsare da su.

    Tun bayan da sojoji suka hamɓarar da Bazoum ne ranar 26 ga watan Yuli, suke ci gaba da yi masa ɗaurin talala a fadar gwamnatin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da lauyoyin suka fitar, sun ce Bazoum bai samu ganawa da lauyoyinsa tun bayan kifar da gwamnatinsa.

    Haka kuma lauyoyin sun yi watsi da zargin da sojojin mulkin ƙasar suka yi kan tserewar Bazoum, suna masu cewa bai yi wani yunƙuri na tserewa daga ƙasar daga inda ake tsare da shi 'ba bisa ƙa'ida ba'.

    Sun ce ya kamata waɗanda ke tsare da shi, su gurfanar da shi a gaban kotu.

    Tawagar lauyoyin sun kuma ce likitansa ne kawai ke samun damar ganawa da shi, tun bayan tsare shi, to amma shi ma a ranar Juma'a an hana shi ganinsa a ƙoƙarinsa na ai masa abinci.

    A cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar ta gidan talbijin a ranar Alhamis, sojojin mulkin ƙasar sun yi iƙirarin cewa an shirya fita da Bazoum zuwa wani wuri a wajen birnin Yamai domin a ɗauke shi - a wasu jirage masu saukar ungulu na wata ƙasa da ba a bayyana ba zuwa -Najeriya.

    Sun ce dakarun sojin ƙasar ne suka daƙile yunƙurin tserewar hamɓararren shugaban, da waɗanda yake tsaren da su, tare da ƙaddamar da bincike game da lamarin.

    Mohamed Bazoum yana kyakkyawar alaƙa da ƙasashen yamma, musamman Faransa, a yaƙin da suke yi da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.

  3. Burkina Faso ta ayyana zazzaɓin Dengue a matsayin annoba

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar lafiya a Burkina Faso ta ayyana cutar zazzaɓin Dengue a matsayin 'annoba', bayan da ɓarkewar cutar a ƙasar ta ti sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 200.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce a wannan shekara kaɗai an samu mutum 50,478 da ake zargi sun kamu da cutar, tare da mutuwar mutum 214, inda kusan kashi 20 na adadin suka mutu a makon da ya gabata.

    Mafiya yawan waɗanda suka mutu a manyan biranen ƙasar suke, Ouagadougou babban birnin ƙasar, da Bobo Dioulasso da ke kudu maso yammacin ƙasar.

    Ma'aikatar lafiyar ƙasar na gudanar da gwajin cutar kyauta, inda take kira ga 'yan ƙasar da su yi riƙa yin gwajin cutar har zuwa lokacin da za a kawar da ita.

    Zazzaɓin Dengue babbar barazana ce ga duniya, wadda lke kashe mutum 20,000 a kowace shekara.

    Tun shekarar 2000, cutar ke ci gaba da ƙaruwa, musamman sakamakon sauyin yanayi, da yawan ƙaurar jama'a daga ƙauyuka zuwa manyan biranen ƙasar.

    A farkon wannan watan ne, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta yi gargaɗin cewa cutar ka iya zama babbar barazana ga yankunan Afirka.

    Wannan ko ba ya rasa nasaba da ƙaruwar dumamar yanayi, wanda ke taimaka wa sauro -wanda shi ne ke yaɗa cutar - rayuwa.

    An ɗaukar cutar ta hanyar cizon sauron da ke dauke da ƙwayar cutar.

    WHO ta ce rabin al'ummar duniya a yanzu na cikin hatsarin kamuwa da zazzaɓin Dengue, inda aka yi kiyasin cewar mutum miliyan 100 zuwa 400 na kamuwa da cutar a kowace shekara.

    Mafiya yawan masu ɗauke da cutar ba sa nuna wata alama, amma waɗanda ke nuna alamun, babbar alamar cutar da suke nuna wa ita ce zazzaɓi mai tsanani, da ciwon kai da ƙaiƙayin jiki, da tashin zuciya da ƙananan ƙuraje.

  4. Wanne irin taimako mutanen Gaza ke buƙata?

  5. Ana shirye-shiryen buɗe iyakar Rafah

    Wannan wani hoto ne daga daren jiya na cire shingaye daga kan iyakar Rafah a shirye-shiryen shigar da motocin agaji na farko zuwa Gaza.

    An wallafa hotunan ne a shafin sada zumunta ta Telegram kuma BBC ta tabbatar, rubutun da ke kan ginin ya nuna "Rafah Land Port".

    ...

    Asalin hoton, TELEGRAM

    ...

    Asalin hoton, TELEGRAM

    ...

    Asalin hoton, TELEGRAM

  6. Ramaphosa zai halarci taro Masar kan rikicin Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa na shirin halartar taron zaman lafiya a birnin Alkhariya ranar Asabar, domin tattauna yadda za a kawo ƙarshen rikicin Isra'ila da Gaza.

    Shugaban ƙasar Masar ya gayyace shi ne don shiga tattaunawar, wadda za ta shafi "rikicin Isra'ila da Zirin Gaza, da buƙatar taimakon gaggawa da kuma yin kira a dawo da shirin zaman lafiya", in ji fadar shugaban Afirka ta Kudu a cikin wata sanarwa.

    Ya ce Ramaphosa ya damu matuƙa game da hare-haren da ake kai wa fararen hula, da matsugunan mutane da kuma buƙatar jin ƙai a Zirin Gaza.

    A baya shugaban na Afirka ta Kudu ya ce a shirye yake ya shiga tsakani a rikicin Isra'ila da Falasɗinu.

    Ya ce al'ummarsa za su iya yin amfani da ƙwarewar da suke da ita na magance rikice-rikice a Afirka da ma sauran su.

  7. Kotu ta ɗaure mutumin da ya yi wa surukarsa ƙaryar aura mata Buhari

    Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Buhari Sallau/Facebook

    Wata kotun majistare a Minna da ke jihar Neja a arewa ta tsakiyar Najeriya ta yanke wa wani mutum mai suna Gambo Adamu hukuncin ɗauri na shekara guda bisa zargin damfarar surukarsa.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Malam Gambo ya riƙa shaida wa surukarsa cewar yana shirya aure tsakaninta da tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

    Surukar tasa, wadda bazawara ce ta garzaya kotu ne tare da koken cewa surukin nata ya yi mata wala-wala bayan karɓar kuɗin da suka kai naira miliyan biyar daga hannunta da sunan zai haɗa aure tsakaninta da tsohon shugan ƙasar.

    Ta shaida wa kotu cewa wata rana Gambo ya kai mata naira 100,000 a matsayin sadakinta, da huhun goro ɗaya da kuma soyayyiyar kaza da nufin cewa kyauta ce daga tsohon shugaban ƙasar, bayan ya yi mata ƙaryar ɗaura auren.

    Ta ce a matsayinta na Amariya, ta yi ta dakon sabon angon nata ya zo ya ɗauketa.

    Yayin da ba ta ganshi ba ne ya yanke shawarar kai surukin nata gaban kotun domin ta shiga tsakaninsu.

    Alƙalin kotun, mai shari'a Ibrahim Musa Zago, ya ɗaure surukin nata wata 12 a gidan yarin, da zaɓin tarar naira 100,000, saboda samunsa da laifin cuta, laifin da ya saɓa da sashe na 322 na kundin final cod.

    Haka kuma kotun ta umarci Malam Gambo ya biya surukar tasa naira miliyan biyu a matsayin diyya.

  8. An kashe kaji 45,000 a Mozambique bayan ɓullar murar tsuntsaye

    Kaji

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'ai a Mozambique sun ce fiye da kaji 45,000 aka kashe, aka kuma ƙona tare da binne su a kudancin kasar domin daƙile yaɗuwar cutar murar tsuntsaye a ƙasar.

    An shigar da kajin ne daga makwabciyarta Afrika ta Kudu, inda cutur murar tsuntsaye ta ɓarke.

    Cutar ta yaɗu zuwa gundumar Morrumbene da ke kudancin lardin Inhambane na Mozambique.

    Hukumomi na ƙoƙarin daƙile cutar, yayin da fargaba ke ci gaba da bazuwar cutar zuwa wasu sasan ƙasar.

    Murar tsuntsaye, cuta ce da ke kama kaji da sauran tsuntsayen daji.

    Cutar kan yaɗu ta hanyar cuɗanya da tsuntsayen gida cikin kwanaki, ta hanyar kashi da yawun tsuntsayen da suka kamu, ko ta hanyar cin abinci ko shan ruan da suka gurɓace.

  9. Magajin Garin Zazzau ya rasu

    Zazau

    Asalin hoton, Zazzau Emirate Council/Facebook

    Magajin Garin Zazzau, Alhaji Mansur Nuhu Bamalli, ya rasu.

    Kafin rasuwarsa shi ne Jakadan Najeriya a Moroko, kuma ƙani ga sarkin Zazzau, Dakta Ahmed Nuhu Bamalli.

    Cikin wata sanarwa da masarautar Zazzau ta fitar mai ɗauke da sannun jami'inta na hulɗa da jama'a, ta ce Ambasada Mansur Nuhu Bamalli ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke Legas yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Moroko.

    Marigayin, mai shekara 42, ya bar mata ɗaya da ƴaƴa biyu.

    A shekarar da ta gabata ne tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya naɗa shi jakadan Najeriya a Moroko.

  10. Hare-haren Isra'ila na kawo cikas wajen fara shiga da kaya zuwa Gaza

    Kan iyakar Rafah

    Asalin hoton, Getty Images

    Masar ta ce hare-haren Isra'ila sun faɗa kusa da kan iyakar Rafah har sau huɗu, tun bayan ƙaddamar da hare-hare a kan Gaza.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an rufe kan iyakar ne tun bayan da hare-haren Isra'ila uku suka faɗa kusa da kan iyakar a ranar 9 da 10 ga watan Oktoba, waɗanda ta ce sun raunata mutanen Masar da na Falasɗinu a kan iyakar.

    A ranar Litinin wakilin BBC da ke kudancin Gaza ya tabbatar da cewa hare-haren da Isra'ila ke kai wa ta sama sun faɗa kusa da kan iyakar, inda suka lalata gine-ginen ɓangaren Falasɗinawa da wani titi.

    Wani Bidiyo da BBC ta tantance ya nuna yadda aka kai hare-haren kan iyakar a wannan ranar.

    Masar ta ce a yanzu ta buɗe kan iyakar domin bayar da damar shiga Gaza daga ɓangarenta, toi sai dai ba a san yaushe za ta buɗe ɓangaren Gaza ba domin bayar da damar ficewa ga fararen hula.

  11. 'Lokacin kai agaji ga al'ummar Gaza na ƙara ƙurewa'

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ƴan gudun hijirar Falasɗinawa, UNRWA, Juliette Touma, ta ce Gaza ta kasance wani 'sansanin azabtuwa' ga fararen hula' cikin ƴan makonnin nan.

    Yayin da take magana da BBC, ta yi kira da a dakatar da hare-haren da ake kai wa Gaza saboda kai kayyakin buƙatar agaji cikin gaggawa.

    “Lokaci na ƙurewa. Abin ya kusa kai wa mako biyu. Tsawon mako biyu UNRWA ba ta samu damar kai tallafi zuwa Gaza ba", in ji jami'ar.

    Misis Touma ta ce ba ta san yaushe za a buɗe kan iyakar Rafah ba domin bai wa fararen hula damar ficewa daga Gaza.

    Yayin da aka tambaye ta kan matakin da UNRWA za ta ɗauka don ganin kayan agajin bai faɗa hannun ƙungiyar Hamas ba, sai jami'ar ta ce hukumarta na iya bambance tsakanin fararen hula da ƴan Hamas.

    Don haka tana lura sosai kan abubuwan da ke faruwa, kuma ma'aikatanta kimanin 13,000 na bayar da agaji ga mutanen da ke buƙatarsa, "mun shafe gomman shekaru muna wannan aiki".

  12. Dala na ci gaba da hauhawa a kasuwannin bayan fage a Najeriya

    Kuɗaɗe

    Asalin hoton, Getty Images

    A Najeriya farashin dala - a kasuwannin bayan fage a Abuja da Legas - ya kai tsakanin naira 1,150 zuwa 1,155 a ranar Alhamis.

    Rahotonin na cewa a ranar Alhamis an sayar da dalar a hukumance kan naira 986, sai dai daga bisani farashin ya sauka zuwa naira 782.68

    Masana da 'yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki na ci gaba da kokawa tare da nuna fargaba kan yadda farashin dala ke ci gaba da tashi musamman a kasuwannin bayan fage.

    Lamarin da suke cewa ka iya kawo koma-baya ga kamfanoni masu zaman kansu da ke ƙasar, sakamakon ƙaruwar tsadar shigo da kayyaki da kamfanonin ke buƙata daga ƙetare.

    Wani abu da masana ke cewa zai rage yawan ribar da kamfanonin ke samu, da ƙara hauhawar farashin kaya a kasar, tare da rage sarrafa kayyaki masu yawa.

    Tun bayan rantsar da shugaba Bola Tinubu, ya ɓullo da wasu tsare-tsare kan kuɗaɗen ƙasashen waje, da nufin farfaɗo da darajar naira, a wani yunƙuri na rage tashin farashin kayan masarufi a ƙasar.

  13. An gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan Falasɗinawa a Faransa

    Masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a birnin Paris

    Asalin hoton, Getty Imagese

    Daruruwan mutane ne suka gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa a birnin Paris, bayan da wata kotu ta ba da izinin gudanar da zanga-zangar.

    An dai fara gudanar da taron ne cikin lumana, daga baya kuma aka samu arangama da 'yan sanda, bisa fargabar cewa za a iya samun tashin hankali.

    A baya ministan cikin gida na Faransa ya yi kira da a daile zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa bayan harin da Hamas ta kai kan Isra'ila.

    Sai dai wata kotu a birnin Paris ta yanke hukuncin cewa haramcin ya keta 'yancin yin zanga-zanga.

    Faransa - wadda ke da al'ummar Musulmi da Yahudawa da dama - ta kasance cikin shirin ko ta kwana tun bayan fara rikicin Isra'ila da Hamas.

  14. Amurka za ta gabatar da kasafin kuɗi don tallafa wa Isra'ila da Ukraine

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce zai gabatar da wani kwarya-kwaryar kasafin kudi na gaggawa ga Majalisar Dokoki don bayar da tallafin soji ga Isra'ila da Ukraine.

    A wani jawabi da ba kasafai ake yaɗawa a gidan talbijin ba daga ofishinsa na Oval, ya ce tabbatar da nasarar ƙasashen biyu na da matuƙar muhimmanci ga tsaron Amurka da shugabancinta a duniya.

    Ya kuma gargadi Rasha cewa duk wani hari da za ta kai wa ƙawancen tsaro ta NATO zai sa Amurkar ta ɗauki matakin kare ƙawayenta.

    Mista Biden ya ce idan muka tsame hannunmu, muka kyale Putin ya shafe 'yancin kan Ukraine, sauran masu mulkin kama karya na duniya za su samu ƙwarin gwiwar aikata hakan.

    "Daga nan kuma za a samu bazuwar rikice-rikice da tashe tashen hankula a duniya', in ji shugaban na Amurka.

  15. Assalamu Alaikum

    Masu bin mu a shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar ranar Juma'a 'Haji babbar rana' kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassa daban-daban na duniya.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta da muhawara.