Ma'aikaciyar jinya ce babbar abar zargi kan mutuwar Mohbad - Ƴan sanda

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage and A'isha Babangida

  1. Narges Mohammadi ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a bana

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwamitin zaman lafiya mai kula da kyautar Nobel ya ba da shelar cewa wata ƴar kasar Iran, mai fafutukar kare haƙƙin mata, Narges Mohammadi ce ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a bana.

    Kwamitin ya ce ta samu kyautar ne saboda fafutukar da take yi a kan cin zarafin mata a Iran da kuma kokarinta na inganta 'yancin ɗan'adam da 'yancin kowa da kowa.

    Narges Mohammadi ƴar kasar Iran ce mai fafutuka kuma mataimakiyar shugaban cibiyar kare hakkin bil adama, wadda wani da ya taɓa lashe kyautar Nobel a kan zaman lafiya, Shirin Ebadi ya kafa.

    Narges Mohammadi ta fuskanci hukuncin dauri da dama tun daga shekara ta 2011 kuma a halin yanzu tana tsare a gidan yarin Evin da ya yi kaurin suna a Tehran a kan tuhumar "yaɗa farfaganda".

    A bana kuma, an saka ta a cikin shirin mata 100 na BBC- shirin da ya kunshi jerin manyan mata 100 masu kokarin zaburar da mutane da kuma karfin faɗa-a-ji daga ko'ina a fadin duniya.

    A yayin da ake sanar da lashe kyautar, kwamitin Nobel ya ce "jajircewarta da gwagwarmayarta ne suka sanya ta cancancin lashe kyautar".

    • Tauraruwar da mahaifinta ya yi wa 'kisan kare mutuncin dangi'
    • Matakai biyar da suka tauye 'yancin matan Afghanistan
  2. Amurka za ta mayar da jiragen saman Venezuela gida

    Amurka ta sanar da cewa za ta ci gaba da mayar da jiragen saman Venezuela gida bayan cimma yarjejeniya da gwamnatin ƙasar.

    Wani babban jami'i ya ce jirgin farko zai tashi nan da kwanaki masu zuwa ɗauke da 'yan Venezuela waɗanda suka shiga Amurkan ba bisa ka'ida ba.

    Gwamnatin Venezuela ta ki amincewa ta karɓi jirage daga Amurka tun bayan da ƙasashen biyu suka samu matsala a 2019.

    A lokacin gwamnatin Trump ne ya ce ba ya ɗaukar Nicolas Maduro a matsayin halastaccen shugaban ƙasar.

    To amma dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta fara farfaɗowa a cikin shekaru biyu da suka wuce.

  3. Zimbabwe ta sanya wasu takunkumai saboda cutar kwalara

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin kasar Zimbabwe ta bullo da wasu takunkumai da nufin shawo kan barkewar cutar kwalara da ake zargin ta kashe fiye da mutum 100.

    Matakan sun hada da dakatar da wadansu tarukan jama'a da kuma taƙaita adadin mutanen da aka bari su halarci jana'iza a yankunan da annobar ta shafa, wadanda suka hada da gundumomi da dama a faɗin ƙasar da kuma wasu sassan babban birnin kasar, Harare.

    An kuma hana yin musabaha da raba abinci a wajen jana'iza.

    A ranar Laraba ne ma’aikatar lafiya ta sanar da mutuwar mutum 100 da ake zargi sun kamu da cutar kwalara, inda 30 daga cikinsu, aka tabbatar da cutar kwalara ce.

    Ma'aikatar ta kuma tabbatar mutum 905 sun kamu da cutar kwalara a cikin mutane sama da 4,600 da ake zargin sun kamu.

    Kasar Zimbabwe dai na yawan samun bullar cutar kwalara.

    Daya daga cikin bullar cutar mafi muni tsakanin 2008 zuwa 2009, mutane sama da 4,200 ne suka mutu, yayin da kusan mutum 100,000 suka kamu.

    A cikin watan Agusta, Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (Unicef) y​ta danganta bullar cutar da rashin tsaftataccen ruwan sha da fashewar magudanar ruwa a kai a kai da rashin kula da tsaftar muhalli a daidai lokacin da ake samun karuwar jama'a a biranen kasar.

    • Lafiya Zinariya: Rawar da mata za su taka wajen yaki da cutar kwalara
    • Cutar Kwalara ta barke a Jamhuriyar Nijar
  4. Rasha ta ce ta lalata jirage marasa matuka na Ukraine

    Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Rasha ta ce ta lalata jirage marasa matukan Ukraine da dama waɗanda suka yi ƙoƙarin kai mata hari a yammacin ƙasarta.

    Sanarwar Rashan ta zo ne kwana guda bayan ta kai harin makamai masu linzamin a kan wani ƙauyen Ukraine da ya yi sanadin rasa rayukan mutum fiye da 50.

    Ƙasashen duniya dai na ta Alla-wadai da wannan hari da Rashan ta kai.

    Yawancin waɗanda suka mutu sakamakon harin a ƙauyen na halartar jana'iza ne.

    Fadar gwamnatin Amurka ta bayyana harin a matsayin mai tada hankali.

    Shi ma Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak, ya ce wannan ya nuna irin rashin imanin Rasha.

    Hroza dai na cikin yankin Kharkiv da ke gabashin Ukraine.

    • Me yasa jirage marasa matuƙa ke da muhimmanci a yakin Ukraine?
    • Harin ramuwar gayyar da Ukraine ke kai wa na tafiyar wahainiya
  5. Sauyin yanayi ya raba yara miliyan 43 da muhallansu a duniya - Unicef

    Yara

    Asalin hoton, Reuters

    Wani rahoton Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ya ce fiye da yara miliyan 43 ne suka rasa muhallansu a tsakanin shekarun 2016 da kuma 2021 saboda abubuwan da suka shafi tsananin sauyin yanayi da aka fuskanta.

    Irin wannan yanayin ya haɗar da iska da ruwa da ambaliyar ruwa da fari da kuma gobarar daji.

    Yawancin Rabin waɗanda abin ya shafa a Philippines da India da kuma China suke.

    To amma kuma rahoton ya gano cewa yaran da suke zaune a ƙasashen kusurwar gabashin Afirka da kananan tsibirai sune suka fi rauni.

    Rahoton ya kuma yi gargaɗin cewa yayin da duniya ke ci gaba da ɗumama, akwai yiwuwar wasu yaran miliyan 100 ma za su iya rasa muhallansu zuwa nan da shekaru 30 masu zuwa.

    Laura Healy, na daga cikin waɗanda suka rubuta rahoton, ta bayyana cewa yara za su iya rabuwa da iyayensu ko masu kula da su.

    Ta kuma ce za su iya fuskantar cin zarafi na zahiri ko kuma abin da zai shafi tunaninsu, musamman idan suna ganin yadda muhallansu ke lalacewa.

    • Ƙasar da yara suka fi shan uƙuba a duniya
    • Najeriya ce kasar da yara suka fi tsunburewa a Afirka — UNICEF
  6. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Juma'a - Hajj Babbar Rana.

    Ahmad Tijjani Bawage da Aisha Babangida ne za su kasance da ku a wannan lokaci.

    Ku kasance da mu tsawon yinin yau, domin sanin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.