Ma'aikaciyar jinya ce babbar abar zargi kan mutuwar Mohbad - Ƴan sanda

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Tijjani Bawage and A'isha Babangida

  1. Farashin man fetur ba zai daidaita a Najeriya ba sai dala ta sauko - PENGASSAN

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, STATE HOUSE

    Shugaban ƙungiyar ma'aikatan man fetur da gas a Najeriya, Festus Osifo, ya ce har yanzu gwamantin tarayya na biyan kudin tallafin man fetur.

    Shugaban na PENGASSAN ya bayyana haka ne a lokacin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a yau Juma'a.

    "Maganar gaskiya ita ce har yanzu akwai tallafi, saboda lokacin da aka yanke farashin fetur, farashin ɗanyen man fetur na a dala 80 kan kowace ganga. Amma a yau, farashin ganga guda ya kai dala 94. To saboda ya tashi shi ma farashin fetur dole ya tashi," In ji shugaban PENGASSAN.

    Ya ce kafin gwamnati ta iya janye tallafi gaba ɗaya, to dole abu guda biyu su faru.

    "Dalilin da zai sanya farashin fetur ya daina tashi sai dai idan Najeriya ta iya daidaita darajar kudinta da na ƙasashen waje," In ji Osifo.

    "To idan har farashin kudaden ƙasashen waje ya sauko a yau, to ba zamu ci gaba da biyan tallafi ba.

    Amman saboda yanayin farashin danye mai a kasuwar duniya da kuma faduwar darajar Naira ya sanya dole muka gabatar da tallafi."

    Gwamnatin Najeriya ta kwashe gwamman shekaru tana biyan maƙudan kuɗaɗe a matsayin tallafin man fetur, lamarin da ya taimaka wajen sauko da farashin fetur a Najeriya.

  2. Gwamnatin Katsina za ta tura ɗaliban makarantun gwamnati karatu waje

    .

    Asalin hoton, Dr. Dikko Umaru Radda/Facebook

    Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta ware guraben karatu 40 ga ɗalibai ƴan asalin jihar waɗanda za ta tura ƙasar Masar domin karatu a fannin likitanci.

    Gwamnatin ta ɗauki matakin ne a lokacin taron majalisar zartarwar jihar wanda gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya jagoranta.

    Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar, Farfesa Abdulhamid Ahmed ya ce "ƙananan hukumomi 31 za su bayar da sunayen dalibai ɗai-ɗaya, yayin da garuruwan Daura da Funtua kuma za su bayar da sunayen dalibai bibbiyu. Inda za a zaɓi ɗalibai uku a cikin ƙwaryar birnin Katsina.

    Kwamishinan ya ce "ɗaliban da suka kammala makarantun gwamnati ne kaɗai za a ɗauka, kuma shirin tura ɗaliban na da nufin samar da ƙwararrun likitocin da za a ɗauka aiki a cibiyoyin kiwon lafiya na jihar Katsina.

    • Dikko Radda na APC ya lashe zaɓen gwamnan jihar Katsina
    • Ina cikin tashin hankali tun bayan sace ƙawayena a jami'ar Gusau - Ɗaliba
  3. Jami'ar Birtaniya za ta fara digiri na biyu a fannin tsafi

  4. Saka zai iya buga wasan Arsenal da Man city - Arteta

  5. Allassane Outtarra ya rushe gwamnatin Ivory Coast

    .

    Shugaban ƙasar Ivory Coast, Alassane Ouattara ya sauke firaiministan ƙasar da sauran ministoci kamar yadda sakatare janar na shugaban ƙasar Aboudramane Cisse ya sanar a yau Juma'a.

    "Shugaban ƙasa na miƙa godiyarsa ga firaiminista Patrick Achi da sauran ministoci bisa jajircewarsu wajen bautawa ƙasa na tsawon shekaru," In ji Cisse

    Patrick Achi ya zama firaiministan ƙasar a watan Maris ɗin 2021.

    Ƙasar Ivory Coast za ta gudanar da zaben shugaban ƙasa a shekarar.

    An zabi shugaba Alassane Ouattara, a shekarar 2020 a karo na uku, sai dai har yanzu bai bayyana ko zai tsaya takara ba ko a'a.

  6. An yi zanga-zangar ƙin jinin ƴan luwaɗi a Kenya

    .

    Asalin hoton, EPA

    Ƙungiyoyin farar hula da na addini sun gudanar da zanga-zanggar ƙin jinin ƴan luwaɗi a babban birnin ƙasar Kenya, Nairobi, suna masu kiraye-kirayen sauke wasu alƙalan kotun ƙolin ƙasar.

    Masu zangar-zangar na gudanar da hakan ne sakamakon hukuncin da kotun ta yanke a watan Satumba da kotun ƙoli ƙasar ta yanke na ba masu nemna jinsi izinin yin rijistar ƙungiyarsu.

    Ɗaruruwan masu zanga-zangar sun riƙa rera kalmomin addini tare da ɗaga alamomin addini a gaban ginin kotun ƙolin ƙasar da ginin majalisar ƙasar. Wannan zanga-zanga ita ce mafi girma ta biyu da aka yi a ƙasar tun bayan yanke hukuncin.

    An gudanar da irin wannan zang-zangar a birnin Mombasa, , inda duka masu zanga-zangar ke kira da kotun ƙolin ta soke hukuncin da ta yi.

    Sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun ce zanga-zangar wani gagarumin gangamin nuna ƙiyayya, aun kuma yi kira da hukumomi su kare haƙƙin masu ƴan luwaɗi.

  7. Bayani kan iyalan da ke riƙe da rigar Annabi Muhammad a Turkiyya

  8. Uwargidan Alex Ferguson ta mutu

  9. Ma'aikaciyar jinya ce babbar abar zargi kan mutuwar Mohbad - Ƴan sanda

    ..

    Asalin hoton, X/@iammohbad_

    Rundunar ƴan sanda a jihar Legos ta yi karin haske a kan binciken da take yi a kan mutuwar mawakin Najeriyar nan, Ilerioluwa Aloba wanda aka fi sani da suna Mohbad.

    Yayin wani taron manema labarai da ta gabatar a hedikwatarta da ke Ikeja a birnin Lagos, kwamishinan 'yan sanda a jihar, CP Idowu Owohunwa ya ce marigayin ya fara barkewa da amai sannan sai tsigar jikinsa ta rika tashi bayan wata ma'aikaciyar jinya ta yi masa allura har sau uku.

    Ya ce ma'aikaciyar jinyar Feyisayo Ogedemgbe ta yi wa Mohbad allurorin ne ranar 12 ga watan Satumban 2023.

    Taron dai a cewar Kwamishinan 'Yan sanda Idowu Owohunwa, kokari ne na bayar da bayanai a kan rahotannin farko-farko a kan binciken da 'yan sanda suke yi don bankado abubuwan da suka kai ga mutuwar Mohbad.

    Ya kara da cewa ya zuwa yau Juma'a, 'yan sanda sun yi wa jimillar shaidu guda 26 tambayoyi.

    Kwamishinan 'yan sandan Lagos ya ce a cikin wadanda 'yan sanda suka yi wa tambayoyi har da mahaifin Mohbad da mahaifiyarsa da kanwarsa da dan'uwansa da matarsa da manajansa.

    Ya ce an kai Mohbad asibiti be bayan ya rasu, kuma likitocin da ke aiki suka ba da tabbacin mutuwarsa ranar 12 ga watan Satumba.

    Ma'aikaciyar jinyar Feyisayo Ogedemgbe, in ji Idowu Owohunwa, wadda abokin Mohbad, Ayobami Sodiq da aka fi sani da Spending, ya sanya, ta yi wa mawakin allurori a gidansa, wadanda aka yi imani sun haddasa sanadin da ya kai ga mutuwar mawakin.

    • Ƴan sanda na neman amaryar da ta yi harbi da bindiga lokacin bikinta
    • A dakatar da jana'izar sirri ga masu zanga-zangar Najeriya da aka kashe - Amnesty
  10. Gwamnatin Kano ta haramta amfani da wasu littattafai kan zargin koyar da batsa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin jihar Kano ta ce a wani mataki na kokarin kare tarbiyar yara ɗalibai, ta haramta amfani da wasu litattafan koyarwa a makarantun nazari da firamare da kuma sakandare a faɗin jihar.

    Matakin ya zo ne a matsayin martani game da damuwar da aka nuna kan cewa an saƙala wasu abubuwa na "batsa wadanda ke yin illa ga tarbiyyar yara ƴan makaranta."

    Sanarwar haramcin na ƙunshe ne cikin wani bayani da ya fito daga ofishin mai bai wa gwamna shawara kan makarantu masu zaman kansu a ranar Juma'a.

    Littattafan da aka dakatar sun hada da 'The Queen Primer' da 'Basic Science for Junior Secondary School" published by Razat Publishers, 2018 editon' da "Active Basic Science 2014 edition by Tora Ajorin and others'

    Sauran sun hada da; "Basic Science and Technology for Junior Secondary School 1, 2, da 3" na W.K Hamza da Bakare' da kuma "New Concept English for Senior Secondary Schools for JSS 2" a cikin edition na 2018 wanda J. Eyisi da A. Adekunle suka rubuta'.

    • Kotu ta ayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano
    • Alƙalan da suka yi shari'ata sun yi kuskure - Abba Kabir Yusuf
  11. Kenya ta tura ƴan sanda na musamman bayan ƙazamin fadan kabilanci

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Kasar Kenya ta tura dakaru na musamman na ‘yan sanda domin shawo kan rikicin kabilanci da ya ɓarke a garin Sondu da ke yammacin kasar da ke kan iyakar kananan hukumomin Kericho da Kisumu.

    Mutum bakwai ne suka mutu, wasu da dama kuma suka rasa matsugunansu a sabon rikicin da ya barke a ranar Laraba.

    Ministan cikin gida, Kithure Kindiki ya ce za a sauya shugabannin tsaron yankin na Kisumu da Kericho bayan rikicin.

    "An yi asarar rayuka, an lalata dukiya, an kuma dagula lamurran jama'a a cikin kwana biyun da suka gabata," in ji Mista Kindiki.

    Shugabannin yankin sun yi kira da a gaggauta warware rikicin kan iyaka tsakanin al'ummomin da ke rikici da juna.

    An kashe mutum uku a irin wadannan rikice-rikice a watan Yuli.

    Garin Sondu na da tarihin tashe-tashen hankula na kabilanci da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane a lokutan zaɓuka.

  12. Yaƙin Siriya: Harin jirage marasa matuƙa ya kashe mutane da dama

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar lafiya ta ƙasar Siriya ta ce wani hari da aka kai da jiragen sama marasa matuka a birnin Homs na kasar Syria a lokacin bikin yaye daliban makarantar soji ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 89.

    Ma'aikatar ta ƙara da cewa waɗanda suka mutu sun hada da mata da kananan yara.

    Wata kungiya mai nazari kan harkokin Syria wadda ke da mazauni Birtaniya ta bayyana cewa an samu asarar rayuka 116.

    Rundunar sojin Syria na alaƙanta harin da “kungiyoyin ta’addanci da ke samun goyon bayan dakarun kasa da kasa,” amma babu wata ƙungiya ta musamman da ta dauki alhakin kai harin.

    Ana kyautata zaton cewa an turo jiragen ne daga yankunan da dakarun 'yan adawa ke iko da su a arewa maso yammacin Homs.

    Baya ga haka, an samu rahoton asarar rayukan fararen hula sakamakon wani luguden wuta da gwamnati ta yi a yankunan Idlib da Aleppo.

    • Syria: Asibitoci na fama da rashin wurin kwantar da marasa lafiya
    • Yadda fadan kabilanci ya fi shafar Musulmai a India
  13. Kudi ne ke kai 'yan wasa Saudiyya-Ibrahimovic

  14. Kenya za ta nemi ƙarin rancen dala biliyan 1 daga China

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban kasar Kenya William Ruto na shirin tafiya kasar China a wannan watan domin samun lamuni na dala biliyan 1 na gudanar da ayyukan tituna da suka tsaya cik, a cewar mataimakinsa Rigathi Gachagua.

    Gachagua ya bayyana cewa da yawa daga cikin ‘yan kwangila sun dakatar da ayyukansu saboda rashin biyansu hakkokinsu.

    Duk da dimbin bashin da Kenya ke bin China, shugaba Ruto na da niyyar neman karin lamuni na dala biliyan 1, tare da tsawaita lokacin biyan bashin da ake bi.

    A halin yanzu Kenya na bin China bashin sama da dala biliyan 8 daga rancen da aka samu musamman don ayyukan more rayuwa a zamanin gwamnatin shugaba Uhuru Kenyatta.

    Da yake jawabi game da almubazzarancin jami'un gwamnati, Gachagua ya ambata cewa shugaban ya sanya takunkumi kan tafiye-tafiyen da ba su da mahimmanci ga jami'an gwamnati.

    Gwamnatin ta kuma umarci ma’aikatu da su rage kasafin kudin shekara mai zuwa da kashi 10%.

    Wadannan matakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jama'a ke nuna rashin jin dadinsu kan tsadar rayuwa da ƙarin haraji da gwamnati ta yi.

    • Abin da ya kamata ku sani kan asusun bayar da lamuni na duniya (IMF)
    • Abin da ya sa sabon shugaban Kenya William Ruto ya dauki matakin zaftare tallafi kan fetur
  15. An dakatar da 'yan wasan PSG kan rera wakar batanci

  16. Matar da ta riƙa cin ciyawa a hannun ƴan fashi ta samu goma ta arziƙi a wajen gwamna

    Gov Dauda

    Asalin hoton, Dauda Lawal/Facebook

    Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, ya karɓi wata dattijuwa wadda ƴan bindiga suka sace da kuma bidiyonta ya karaɗe shafukan sada zumunta.

    Bidiyon dai ya nuna wata uwa da ‘ya’yanta a hannun ƴan bindiga, waɗanda har suka koma cin ciyawa. Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, na cewa ganin halin da matar ta shiga, ya zama tilas a tashi haikan wajen shawo kan matsalar ta ƴan fashin daji da kuma tabbatar da cewa iyalai sun samu ababen more rayuwa.

    Sanarwar ta ce gwamnan ya karɓi matar ne domin hakan na cikin zimmarsa ta ganin an kare rayuka da ma dukiyoyin al’ummar Zamfara.

    “Gwamna Lawal ya karɓi Hauwa’u Salisu, matar da ta rasa komai saboda rikicin ƴan fashin daji.

    Ya nuna zimmarsa ta ganin an kawo karshen matsalar tsaro a Zamfara, sannan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan da ayyukan ƴan bindiga ya daidaita,” in ji sanarwar.

    Gwamnan ya bai wa matar wani sabon gida da za ta zauna da ‘ya’yanta. Ya kuma tabbatar wa matar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ciyar da 'ya'yanta da kuma samar musu abubuwan da suke buƙata.

    Har ila yau, gwamnan ya bayar da umarnin cewa a gaggauta sanya yaran matar a makaranta da kuma ba su cikakken tallafin karatu.

    Ya kuma buƙaci dukkan hukumomi su yi ƙoƙari wajen binciko iyalai marasa galihu da ke fuskantar irin waɗannan matsaloli, don ganin cewa an ba su taimakon da ya kamata.

    • 'Babu mu babu Sulhu da 'yan fashi a Zamfara'
    • An ceto mutane 30 da aka yi garkuwa da su a jihar Bauchi
  17. Kamfanin NNPC na Najeriya ya ce ba shi da niyyar kara kudin litar mai

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin samar da man fetur na Najeriya ya bai wa masu sayen mai a gidajen man fetur dinsa cewa ba shi da niyyar kara kudin litar mai.

    A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X tsohon shafin Tuwita, NNPC ya ce sabanin rade-radin da ake yi na karin farashin litar mai a kasar, masu sayen man fetur na iya ci gaba da shan mai a gidan man fetur dinsa da ke fadin kasar a cikin farashin mafi rahusa.

    Sanarwar NNPC na zuwa daidai lokacin da wasu kafofin yada labaran Najeriya ke cewa farashin litar mai a tashoshin sauke man fetur na kasar, ya kai naira 720 duk lita daya, abin da ya sa ake jin farashin zai iya kai wa naira 729 a gidajen mai matukar gwamnatin kasar ba ta ci gaba da biyan kudin tallafi ba.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa harkoki sun tsaya a tashoshin sauke man fetur, yayin da a wasu wurare, wasu gidajen man fetur suka rufe.

    Wasu direbobin mota a birane kamar Abuja da Kano sun ba da rahotannin cewa sun sha mai a farashin da ya haura abin da aka saba sayarwa a baya.

    • Farashin man fetur ya faɗi a defo-defon Najeriya - IPMAN
    • Ko sauya mota daga mai amfani da man fetur zuwa gas na da illa?
  18. Muryar dan'adam ta fi razana namun daji a kan gurnanin zaki - Bincike

    Lion

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani bincike a Afirka ta Kudu ya gano cewa muryoyin dan'adam sun fi cusa matukar tsoro a zukatan manyan namun daji a kan gurnanin zakuna.

    Masu ilmin kimiyya sun rika sanya muryoyin maganganun mutane da suka yi ta hanyar amfani da lasifikokin da aka boye a wasu kafofi da ke cikin ruwa a gandun daji na kasa da ke Kruger.

    Namun daji kimanin kashi 95 cikin 100 ciki har da mariri da mugun dawa da rakuman dawa da damisa suna matukar shiga firgici sannan cikin hanzari su sheka da gudu.

    Sautukan da aka nada na gurnani da gunjin zakuna na haddasa fargaba kadan; wasu giwaye sun mayar da martani ta hanyar yin barazana ga kafar da sautin zakunan take fitowa.

    Ana jin cewa namun dajin sun fahimci cewa mu'amala da mutum, abu ne mai matukar hatsari, saboda farauta da amfani da bindiga da kuma cuna karnuka, su kama su.

    • Zuri'ar gwaggon birin da ya kusa ƙarewa a duniya 'na ta hayayyafa' a Uganda
    • Ya za ku yi idan kuka ga damisar Google a dakinku?
  19. Senegal za ta ci gaba da hana amfani da manhajar TikTok

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Senegal ta ce za ta ci gaba da aiki da matakin hana amfani da manhajar sada zumunta ta TikTok da ta sanya a watan Agusta.

    Hukumomi sun dakatar da manhajar ne bisa zargin cewa mutane na amfani da ita wajen yaɗa sakonnin nuna kiyayya da zagon kasa da ke barazana ga zaman lafiyar kasar”.

    Ministan sadarwa na Senegal Moussa Bocar Thiam a ranar Alhamis ya ce ƙasar za ta ci gaba da amfani da TikTok ne kawai idan kamfanin ya sanya hannu a kan yarjejeniya don ba da damar cire saƙonnin da ke tallata abin da ya bayyana a matsayin masu tayar da hankali.

    "A halin yanzu, ana ci gaba da hana amfani da manhajar TikTok har sai kamfanin ya amince da sa hannu a yarjejeniyar da muke so a rubuce" in ji Mista Thiam, bayan tattaunawa da wakilan kamfanin.

    Haramta amfani da TikTok a Senegal dai ya zo bayan kama jagoran 'yan adawan kasar, Ousmane Sonko.

    Hukumomin kasar sun yi ikirarin cewa, ana amfani da manhajar ne wajen yaɗa “saƙonnin nuna kyama da tada zaune tsaye” wadanda ke yin barazana ga zaman lafiyar Senegal yayin da zanga-zanga ta barke bayan kama Sonko.

    • Abin da ya sa Amurka ke barazanar haramta TikTok a faɗin ƙasar
    • Ko kun san wanene shugaban kamfanin TikTok?
  20. Farashin man fetur a Najeriya ya haura zuwa naira 720 kan lita

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Dillalan man fetur a Najeriya sun ce farashin man fetur ya ƙaru zuwa naira 720 a kan lita ɗaya daga naira 651, a wani lamari da ya sanya tashoshin sauke mai suka kasance tamkar babu kowa

    Wannan a cewar dillalan man ya samo asali ne daga yawan sauyin da ake samu na darajar kuɗaɗen waje.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa dillalan man fetur su ma sun bayyana cewa gidajen mai da dama na rufewa a kullum yayin da kasuwar sayar da mai ke ƙara tabarbarewa.

    Sun ce hakan na iya haifar da matsalar karancin man fetur a cikin watanni masu zuwa.

    Da yake jawabi a wurin taron shugabannin kungiyar masu samar da man fetur da iskar gas ta Najeriya, a Abuja ranar Alhamis, shugaban ƙungiyar, Benneth Korie, ya ce a halin yanzu harkoki sun tsaya a tashoshin sauke man fetur masu yawa.

    Shi ma shugaban kamfanin PETROCAM Trading, Patrick Ilo da yake zantawa da jaridar, ya bayyana cewa kudin man fetur da suka shigo da shi metrik tan 52,000 a ranar Talata, ya kai naira 720 duk lita daya ba tare da tallafin hukuma.

    A cewarsa, matukar farashin man fetur ya kai naira 720 duk lita daya a tashoshin sauke man fetur, to mai yiwuwa ne kudin lita daya zai iya kai wa naira 729 a gidajen mai na jihar Lagos, idan gwamnatin Najeriya tabbas ta dakatar da biyan tallafin man.

    A wasu sassan Najeriya ma, an fara ba da rahotannin samun karin kudin man fetur din a gidajen mai, ko da yake, har yanzu ba a ji wani bayani daga hukumomin Najeriya a kan wannan batu.

    Shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur a cikin jawabinsa na kama mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023, lamarin da ya haddasa hauhawar farashi da matsin rayuwa.

    • Kalaman 'yan Najeriya bayan sake ƙara kuɗin man fetur
    • Mece ce gaskiyar mayar da tallafin man fetur a Najeriya?