Gwamnan Zamfara na zargin Gwamnatin Tarayya da yunƙurin sulhu da ƴan fashi

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Mukhtari Adamu Bawa, Rabiatu Kabir Runka and Zulaiha Abubakar

  1. Rufewa

    Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafin na labarai kai-tsaye.

    Muna nan tafe da wasu sabbin rahotannin daga sassan duniya gobe da safe in sha Allah.

    Kafin goben, ku duba ƙasa domin karanta waɗanda muka kawo maku a yau.

    Rabiatu Kabir Runka tare da Mukhtar Adamu Bawa ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Gwamnatin Najeriya ta musanta hawa teburin sulhu da 'yan fashin daji

    .

    Asalin hoton, Presidency

    Gwamnatin Najeriya ta ce babu wani jami'inta da ke gudanar da tattaunawa da wani dan fashin daji ko wata kungiyar 'yan fashin daji.

    Sai dai ta ce gwamnati na nan a kan matsayinta na lalubo duk wata hanya da za ta iya kai wa ga raguwar zaman dar-dar da kuma samun komawar zaman lafiya ga al'ummomin da rikicin 'yan fashin daji ya daidaita.

    Gwamnati, a cikin wata sanarwa da mataimakin darakta a ma'aikatar yada labaran Najeriya, Suleiman Haruna ya fitar, tana mayar da martani ne ga zargin da gwamnatin jihar Zamfara ta yi cewa wasu jami'ai a gwamnatin tarayyar kasar na tattaunawa da 'yan fashi.

    'Yan fashin dai wadanda suka addabi garuruwa da kauyuka da hare-hare da kashe-kashe da kuma satar mutane don neman kudin fansa galibi a jihohin arewa maso yamma musamman ma dai Zamfara.

    Gwamnatin Zamfara dai ta ce ana yin tattaunawa da 'yan fashin ne ba tare da saninta ba.

    Sanarwar ma'aikatar yada labarai dai, ta kuma ce idan wasu garuruwa ko al'ummomi suka yanke shawarar koyi da hanyar da ta taimakawa wasu a wani yanki na kasar ta hanyar tattaunawa a tsakaninsu, gwamnatin tarayya ba za ta yi garajen yin Allah-wadai da irin wannan mataki da al'umma ta bijiro da shi ba.

    Ta ambato ministan yada labaran kasar yana bai wa 'yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatin tarayya da hukumominta na aiki ba dare ba rana, don shawo kan halin da ake ciki da kuma kawo karshen ayyukan 'yan fashin daji da na masu satar mutane don neman kudin fansa da kuma duk wani nau'ion aikata manyan laifuka da ta ce suna raguwa.

    Sanarwar ta ce bai kamata a yi amfani da bambancin siyasa ko rikici tsakanin wadansu mutane cikin wani muhimmin al'amarin tsaron kasa ba, don gudun sanyaya gwiwar dakarun tsaro da kuma durkusar da kokarin gwamnati.

    Ta ambato ministan labaran kasar Alhaji Mohammed Idris yana bayyana kaduwa da takaicinsa a kan sanarwar Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara.

    Ya ce maimakon gwamnan ya jinjinawa jami'an tsaro da hukumomin gwamnatin tarayya saboda kokarinsu cikin gaggawa na kubutar da daliban Jami'ar Tarayya ta Gusau da aka sace, amma sai ta zabi shigar da siyasa cikin muhimmin batun don cimma muradan siyasa cikin sauki.

  3. Dakarun gwamantin Somaliya sun kashe gwamman mayaƙan Al-shabab

    ...

    Asalin hoton, United States Secretary of Defense/X

    Bayanan hoto, ...

    Gwamnatin Somaliya ta bayar da rahoton cewa, dakarunta sun kashe mayakan al-Shabab da dama, bayan wani harin bam da aka kai da babbar mota a birnin Beledweyne, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 10.

    Mataimakin ministan yada labaran ƙasar Abdirahman Al-Adalah ya bayyana cewa sojojin kasar Somaliya da dakarun sa kai sun kai harin ne a wani sansanin 'yan ta'adda a kauyen Caad na jihar Galmudug.

    Ba a tantance ainihin adadin mayaƙan na al-Shabab da ke da hannu ba, kuma kungiyar ba ta mayar da martani ga ikirarin gwamnatin ba.

    Bugu da kari, gwamnatin ta bayyana cewa dakarunta sun kwato ƙauyuka daga hannun mayaƙan jihadi a yankin na Hiiraan.

    Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya gana da sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin a kasar Djibouti, inda suka tattauna kan yaki da kungiyar Al-Qaeda da ta shafe sama da shekaru 15 tana yi a Somaliya.

    Somaliya na samun tallafi iri-iri daga Amurka, da suka haɗa da taimakon soji da horo, inda sojojin Amurka ke kai hare-hare ta sama kan al-Shabab.

  4. An gano magen da ta ɓata bayan shekara 11

    UK Cat

    Asalin hoton, Sian Sexton

    An mayar da wata mage da aka ba da rahoton ta bata tsawon shekara 11 da ta wuce ga mai ita.

    Magen mai suna Daisy ta gaza komawa gidansu bayan ta fita zuwa yankin Caerphilly daga yankin Dorset da mai ita, Sian Sexton, a shekara ta 2012.

    Sai dai a makon jiya, Sian Sexton ta samu wani rahoto mai ban mamaki, inda aka yi kiran ta daga wani asibitin dabbobi na Caerphilly, ana sanar da ita cewa an kawo wata mage da aka makalawa wani maballi zuwa asibitin.

    "Har yanzu ina cike da mamaki," matar mai shekara 43 ta ce.

    Misis Sexton, wadda tuni ta canza unguwa ta ce ta gano cewa magenta Daisy ta yi ta rayuwar gararamba a unguwar Caerphilly da ta bata tsawon sama da shekara 10.

    Mutanen yankin ne suka dauke ta zuwa asibiti bayan sun damu game da batun lafiyar magen.

    Gaba daya gashin Daisy ya "cukurkude" kuma ta kamu da mura, in ji Misis Sexton.

    UK Cat

    Asalin hoton, Sian Sexton

    "Tana ta atishawa, kuma da kyar take numfashi saboda toshewar hanci, su [mutanen da suka kai ta] ba su taba tunanin za ta kai wani hunturun a waje ba," ta kara da cewa.

  5. Gwamna Abba Kabir ya aika wa majalisa kasafin kudin naira biliyan 58

    .

    Asalin hoton, FACEBOOK/ABBA KABIR YUSUF

    Bayanan hoto, Gwamna Abba Kabir Yusuf

    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya gabatar wa majalisar jihar kasafin kuɗi na cike giɓi a yau Litinin na sama da naira biliyon 58.

    Daftarin kasafin kuɗin ya isa majalisa a dai-dai lokacin da majalisar ke zama ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar, Isma’il Falgore.

    Shugaban majalisar ya karanto ƙudirin inda ya ce gwamnan na neman amincewar majalisar kamar yadda sashe na 121 ƙaramin sashe na A da B na tsarin mulkin 1999 ya tanada.

    Gwamnatin ta yi bayanin cewa kasafin kuɗin na cike giɓi ya zama dole saboda ta samu damar ƙarasa wasu ayyuka masu mahimmanci da ta fara.

    Majalisar ta ɗage zaman ta zuwa gobe domin ci gaba da tafka muhawara kan amincewa ko ƙin amincewa da kasafin kuɗin cike giɓin.

  6. Najeriya na fama da yawan shari'o'in da ake ɗaukakawa

    Court room

    Asalin hoton, Court of Appeal

    Shugabar kotun ɗaukaka kara a Najeriya, Mai shari'a Monica Dongban-Mensem, ta ce akwai kararraki guda 39,526 da ke gaban kotun ɗaukaka karar kasar.

    Mai shari'a Dongben-Mensem ce ta sanar da haka yayin wani biki don shiga sabuwar shekara shari'a ta 2023/2024 ranar Litinin a Abuja.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito babbar mai shari'ar tana cewa kotun daukaka kara ta karbi jimillar kara 7,295 da aka daukaka da kuma kudurorin shari'a 3,665 a shekarar shari'ar da ta wuce.

    ”Kotun ta yanke hukunci a kan kara 3,765 sannan ta cimma matsaya a kan kudurorin shari'a 5,617; ta kori kara 1,030, sannan ta ba da umarnin a ci gaba da sauraron kara 10,381. “Har yanzu kotun na da jimillar kara 39,526 da aka daukaka ya zuwa ranar 31 ga watan Agustan 2023.

    Hakan ya nuna karuwar shari'o'in da aka daukaka daga 34,037 da ke gaban kotun tun daga shekarar shari'a ta 2021/2022,” in ji Mai shari'a Monica.

    Ta ce jimillar rukunin alkalai guda 98 aka kafa don sauraron shari'o'in zabe a fadin kasar, wadanda za su saurari jimillar korafe-korafen zabe 1,209 da aka shigar.

    A cikin korafe-korafen a cewar Mai shari'a Monica, an shigar da kara biyar a gaban kotun zaben shugaban kasa kuma tuni kuton ta kammala aiki, yayin da alkalai suka yi hukunci a kan kararrakin zaben 'yan majalisar dattijai guda 147 da kuma kararrakin da ake ci gaba da yankewa har 417 na zaben 'yan majalisar wakilai.

    Haka zalika, akwai jimillar korafe-korafe 557 masu alaka da zabukan 'yan majalisun dokokin jihohi da kara 83 a kan zabukan gwamnoni su ma da ake yankewa, a cewarta jiha 28 ne aka gudanar da zaben gwamna, kuma an shigar da korafi kan zaben a jiha 24.

  7. Kafofin yaɗa labaran Rasha na yaɗa farfaganda da kalaman yaƙi- MDD

    .

    Asalin hoton, EPA

    Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun ce wasu kalaman yaƙi da farfagandar kafofin yada labaran Rasha ka iya zama wata hanyar aikata kisan ƙare dangi

    Erik Mose wanda ke jagorantar tawagar ya shaidawa hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya cewa har yanzu suna kan ci gaba da gudanar da bincikensu.

    Wakiliyar BBc ta ce "tawagar ta tattara bayanan hare-haren da aka kai kan asibiti, shaguna da gidan cin abinci da kuma tashar jirgin ƙasa.Duk kayayyakin more rayuwa na farar hula wanda a ƙarƙashin dokar ƙasa da ƙasa bai kamata a kai su masu hari ba an kai musu."

    Dangane da tsarin Moscow na mayar da yaran Ukraine zuwa Rasha da kuma yankunan da ta mamaye, Mista Mose ya yi nadama cewa ba a yi karin haske dangane da yanayin lamarin da kuma rukunnan yaran da ake mayar wa ba.

  8. Cutar mashaƙo na ci gaba da yaɗuwa kamar wutar daji a Najeriya

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar yaki da cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane sama da 400 sanadin cutar mashako ko Diptheria a kasar.

    Cutar dai na ci gaba da yaɗuwa kamar wutar daji inda yanzu haka ta bazu a cikin ƙananan hukumomi 105.

    Mashako dai ta yi sanadin mutuwar yara akalla 453 kamar yadda alƙaluman da hukumomi suka fitar ranar Lahadi 24 ga watan Satumban 2023 suka nuna.

    Hukumar ta ce matsalar ta fi ƙamari a jihar Kano inda aka tabbatar da cewa mutane fiye da dubu shida sun kamu da cutar.

    Hukumomi a ƙasar sun ce suna ɗaukar matakan riga-kafi domin daƙile bazuwar mashako.

    Latsa hoton da ke ƙasa domin sauraren cikakken bayani a rahoton Habiba Adamu.

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraren rahoton Habiba Adamu
  9. An shiga damuwa bayan sojoji sun ɗage zaben shugaban ƙasa a Mali

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahukunta a Mali sun ɗage zaɓen shugaban ƙasar da aka tsara tun farko za a yi a watan Fabrairun 2024.

    Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar, Abdoulaye Maiga ne ya bayyana wasu gyare-gyare da za a yi wa tsarin mulkin ƙasar da kuma dokokin zaɓe a matsayin dalilan da suka janyo ɗage zaben.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar, Abdoulaye Maiga ya ce "An ɗage zaɓukan da a baya aka tsara gudanarwa a ranar 4 da kuma 18 ga watan Fabrairun 2024 saboda dalilan yin gyare-gyare.

    Ya ce dalilan sun haɗa da batun amincewa da sabon kundin mulkin ƙasar da kuma gyaran fuska ga dokokin zaɓe.

    Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula da jam’iyyun adawa sun bayyana rashin jin daɗinsu a kan wannan sanarwa.

    Tun da farko, shugaba Assimi Goita ya nemi a gudanar da zaɓen ne a shekara ta 2026, daga baya kuma ya janyo shi zuwa 2025 bayan fuskantar matsin lamba daga ƙungiyar Ecowas.

    A watan Afrilun 2021 ne dai, gwamnatin mulkin sojan Mali ta ba da tabbacin gudanar da zaɓe cikin watan Fabrairun 2024.

    Cibiyar tsara dabarun mulki ta Afrika ta ce yanayin tsaro na ƙara taɓarɓarewa a Mali tun bayan da gwamnatin mulkin sojin ta fara yanke hulɗa da ƙasashen duniya, da kuma dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Juyin mulki biyu da Mali ta yi fama da su, suna da alaƙa da gazawar hukumomi wajen magance rikicin ƴan ta-da-ƙayar-baya da masu iƙirarin jihadi da ya yaɗu a Afirka ta Yamma cikin shekara 10 da ta wuce.

    Yanayin tsaro ya ƙara ƙazancewa a Mali saboda rikici tsakanin ƙungiyoyi biyu masu ɗauke da bindiga.

    Ba a san martanin da kungiyar Ecowas za ta mayar ba, game da wannan sanarwa ta shugabannin mulkin sojan na Mali.

  10. An hana tsohon shugaban ƙasar Zambiya fita motsa jiki

    Edgar Lungu

    Asalin hoton, ANDY LUKI JR

    An gargaɗi tsohon shugaban ƙasar Zambiya, Edgar Lungu da ke zuwa motsa jiki a bainar jama'a, bayan ƴan sanda sun bayyana motsa jikin nasa da cewa siyasa ce.

    Motsa jikin da yake yi duk ranar Asabar tare da mutanen gari da kuma magoya bayan jam'iyyarsa ta PF na ɗaukar hankali a ƙasar.

    An buƙaci Mista Lungu ya nemi izinin ƴan sanda kafin ya sake fita motsa jikin.

    Umarnin na ƴan sanda na zuwa ne bayan fara yaɗa jita-jitar cewa tsohon shugaban kasar zai sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a 2026.

    Sanarwar da ƴan sandar suka fitar ta ce , "Rashin snaar da jami'anta kafin yin gangamin na jami'iyyar PF ya saɓa doka."

    "Ya kamata a ce duk wani abin da tsohon shugaban ƙasar zai yi, ya yi aiki tare da sauran jami'an tsaronsa kuma ya nesanta kansa da duk wasu ayyuka na siyasa."

    Sai dai lauyan tsohon shugaban ƙasar, Makebu Zulu, ya shaida wa BBC cewa wanda yake karewar zai ci gaba da fita motsa jikinsa ba tare da ya sanar da jami'an tsaro ba.

    Mista Zulu ya yi barazanar ɗaukar matakin shari'a a kan gwamnati matukar har aka hana tsohon shugaban ƙasar mai shekara 66 fita motsa jikin da yake duk ranar Asabar.

  11. Hukumomi sun rufe shagunan sayar da magunguna sama da 100 a jihar Kogi

    .

    Asalin hoton, PA

    Kwamitin duba ingancin magunguna a jihar Kogi ta Najeriya ya ba da sanarwar rufe shagunan sayar da magani sama da 100 wadanda ya ce suna aiki ba bisa ƙa'ida ba, a tsakanin watan Janairu zuwa Satumban 2023.

    Mataimakin shugaban kwamitin, Dr Lawal Muhammed Omuya ne ya bayyana haka a ranar Litinin a wata sanarwa da ya fitar don tunawa da ranar masu haɗa magani ta duniya a bana.

    Ya ce "kwamitin ya kai samame ne a shagunan sayar da magungunan daga watan Janairu zuwa Satumban 2023, domin kawo ƙarshen ayyukan masu sayar da jabun magunguna a jihar Kogi".

    "Gurɓacewar aikin kwararrun masu magunguna za a iya kallonsa ta ɓangarori da dama da suka haɗar da mutanen da suke da ilimi da kuma marasa ilimi da ke gabatar da kansu a cikin al'umma a matsayin masana kuma suke gabatar da ayyukan da ya kamata a ce ƙwararren masanin magani ne kawai zai yi."

    "A ɗaya ɓangaren kuma, muna la'akari da shagunan sayar da magani da ba a gina su bisa ƙa'idojin aikin ba, saboda mutane da dama na sayen magunguna wajen su bisa tunanin amintattun shagunan sayar da magunguna ne da za su samu inganttun magunguna.

  12. Koken 'yan Kasuwar Maigatari game da rufe iyakar Najeriya da Nijar

  13. Wani bangare na masallacin Ghana mai dumbin tarihi ya rufta

    Ghanaian Mosque

    Asalin hoton, William Haun

    Bayanan hoto, An ga yadda gara ta lalata sassan masallacin lokacin da aka dauki hotunansa a 2018

    Wani bangare na masallaci mai dumbin tarihi a garin Bole na arewa maso yammacin Ghana, ya ruguje bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya.

    Rufin kasa na Masallacin Bole ya rufta bayan halin ko-in-kula tsawon shekaru da kuma gara da ta addabe shi.

    Jami'an kula da gine-ginen tarihi a Ghana sun ce gara ta raunana tsaikon katako da ke rike da rufin ginin, abin da ya janyo ruftawarsa bayan wani mamakon ruwan sama.

    Masallacin wanda akasari na kasa ne, an gina shi ne a tsakanin karshen Karni na 19 da kuma a farkon karni na 20.

    Jami'ai sun ce za a iya gyara masallacin da ya lalace, da taimakon mutanen garin wadanda suna da masaniya a kan fasaha da tsarin ginin.

    Hukumomin kula da gine-ginen tarihi a Ghana sun shawarci mutanen garin kada su ce za su rushe sauran ginin masallacin don gina wani sabo.

    • An yi jana'izar mutum takwas da rufin masallacin Zazzau ya ruftawa
    • Yunƙurin rushe masallaci mai shekara 700 a China ya jawo zanga-zanga
  14. Kotu ta tabbatar da zaben Gwamnan Sanwo-Olu na jihar Lagos

    Sanwo-Olu

    Asalin hoton, Governor Sanwo-Olu/Facebook

    Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Lagos ta tabbatar da nasarar Gwamna Babajide Sanwo-Olu a matsayin halastaccen gwamna.

    A wani hukunci da illahirin alkalan suka amince da shi, kuma Mai shari'a Mikail Abdullahi ya karanta a madadin alkalan uku ranar Litinin, kotun ta yanke hukuncin cewa korafin jam'iyyar PDP da dan takarar Olajide Adediran ba shi da tushe, don haka kuma sun yi watsi da karar.

    A kokarin tabbatar da hukuncin da ta yanke, kotun da farko nanata kin amincewar farko-farko da bangarorin da ke cikin shari'ar suka nuna kafin ta yi nazari game da batutuwan da ta bijiro da su don yin shari'a.

    Kotun ta saurari bahasi a kan tambayar ko tana da hurumin sauraron karar, Mai shari'a Mika'il Abdullahi ya ce tabbas kotun tana da hurumi.

    Sai kuma batu na biyu da ke neman hukunci a kan ko jam'iyyar APC ta ba da sunan Sanwo-Olu da mataimakinsa Obafemi Hamzat bisa hanyar da ta dace su tsaya mata takara a zaben 18 ga watan Maris.

    Kotun ta kafa hujjoji da tanade-tanaden tsarin mulki da kuma na kundin zabe da dumbin shari'o'in da aka yanke hukunci dangane da batun, inda ta jaddada cewa korafin batu ne da ya kamata a ce tuni an kammala da shi kafin gudanar da zabe kuma ba shi da alaka da zabukan da aka kalubalanta.

    Kotun ta kuma ce masu korafin ba 'ya'yan jam'iyyar APC ba ne wadda ake kara ta hudu don haka ba su da hurumin kalubalantar zaben fid-da-gwanin da ya fito da 'yan takarar biyu.

  15. An gano ƴan'uwan matar da aka ga gangar jikinta a bakin kada

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani shaida ya bayyana wa kafofin labarai yadda ya ga rabin gangar jikin mutum a bakin wani kada.

    Magajin garin Pinellas ya ce an kashe dabbar bayan an tabbatar da samun ragowar gaɓobin jikin Sabrina Peckham mai shekaru 41 a kusa da wani ruwa.

    Bincike ne kawai zai iya tabbatar da dalilin mutuwar matar.

    Da tsakar rana aka kira ƴan sanda da mataimakansu bayan ganin gangar jikin mutum a hanyar da ruwa ya ke wucewa.

    The alligator was captured and killed by police

    Asalin hoton, CBS

    Jamarcus Bullard ya ƙara da cewar yana kan hanyarsa ta zuwa neman aiki ne ya hango kada da wani abu mai kama da mutum-mutumi a bakinsa.

    "Na fahimci jikin mutum ne, daga nan sai na garzaya hukumar kashe gobara don sanar da su,'' kamar yadda ya shaida wa kafar labarai ta Fox 13.

    Iyalan Misis Peckham sun kaddamar wata gidauniyar neman tallafi a shafin sada zumunta bayan sun tabbatar da cewar tana rayuwa ne a matsugunin marasa muhalli kafin mutuwarta.

    • Kada ya ciji wani yaro sanadiyyar ambaliyar ruwa
    • Yadda mutane ke zaƙulo gawarwakin ‘yan uwansu don gudun kada a yi titi a kansu
    The waterway in Largo where the alligator was caught

    Asalin hoton, Google

  16. Cutar mashaƙo ta kashe mutum 453 a Najeriya - NCDC

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar dakile cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa aƙalla mutum 453 ne suka rasu sanadin cutar mashaƙo nau'in diphtheria a ƙasar bayan sake ɓullarta a Najeriya.

    Da dama daga cikin waɗanda cutar ta kashe yara ne ƙanana.

    NCDC ta ƙara da cewar kashi 80 na waɗanda suka kamu da cutar, mutane ne da ba su yi riga-kafinta ba.

    Cutar mashaƙon ta diphtheria tana haifar da wahalar numfashi da matsala a zuciya, musamman tsakanin yaran da ke fama wata lalura mai hatsari.

    Hukumomin Lafiya a Najeriya sun tabbatar da kamuwar mutum 7,202 daga cikin 11,587 da aka yi zargin sun kamu da cutar daga watan Satumban bara.

    Cutar dai ta fi yaɗuwa ne a Arewacin Najeriya, musamman jihar Kano.

    Hukumar NCDC ta ja hankalin iyaye su tabbatar an yi wa ƴaƴansu riga-kafi, kuma a kai duk wanda ake zargin ya kamu da cutar asibiti cikin gaggawa.

    • Cutar mashaƙo ta kashe mutum 80 a Najeriya
    • Abubuwan da ya kamata ku sani game da cutar mashaƙo da ta ɓulla a Kano
  17. 'An ceto ɗalibai 14 na Jami'ar Tarayya ta Gusau da ƴan bindiga suka sace'

    ...

    Asalin hoton, X/Federal University Gusau

    Jami'ar Tarayya ta Gusau da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya ta ce ya zuwa yanzu an ceto ɗalibai 14 da leburori biyu waɗanda ƴan bindiga suka sace a daren Juma'ar da ta gabata.

    Wata sanarwa da hukumar jami'ar ta fitar, na cewa a jimilla, an ceto mutum 16, 14 dalibai, 2 kuma ma'aikata tun bayan faruwar lamarin.

    Sanarwar ta ce ɗaliban, waɗanda suka shiga firgici a hannun ƴan bindigar, tuni aka haɗa su da iyalansu.

    Haka nan sanarwar ta buƙaci ɗalibai da malaman jami'ar su ci gaba da tafiyar da lamurransu kamar yadda suka saba.

    Ta kuma yaba wa dakarun Najeriya bisa ƙoƙarin da suka yi na ƙwato waɗanda aka sace.

    • Sace ɗaliban Zamfara abin kunya ne - Amnesty
    • An ceto wasu daga cikin ɗaliban da aka sace a Jami'ar Tarayya ta Gusau
  18. Jagoran ƴan Mafiya a Italiya ya mutu

    .

    Asalin hoton, reuters

    Wani sanannen jagoran ƙungiyoyin masu aikata laifi a Italiya, Matteo Messina Denaro, wanda sunan sa ya jima a jadawalin mutanen da jami'an tsaro suke nema ruwa a jallo ya mutu.

    An ayyana Mista Denaro mai shekaru 61 a matsayin shugaban ƙungiyar masu aikata miyagun laifuka ta Cosa Nostra Mafia, ya kwashe shekaru talatin yana tsere wa jami'an tsaro kafin su kama shi a watan Janairu

    Lokacin da aka kama shi ya na fama da lalurar sankara, al'amarin da ya sa jami'ai suka dinga kai-komo da shi tsakanin gidan yari da asibiti a watan da ya gabata.

    An ɗora alhakin kisan mutane da dama a kan Mista Denaro.

    .

    Asalin hoton, Reuters

    A shekara ta 2002 kotu ta yanke masa hukuncin laifukan da suka haɗa da kashe wasu masu yaƙi da ƙungiyoyin mafiya, wato Giovanni Falcone da Paolo Borsellino.

    Ya taɓa ikirarin zai cika maƙabarta da gawarwakin waɗanda ya kashe.

    Duk da tsere wa jami'an tsaron da ya ke yi tun 1993, Messina Denaro ya na bayar da umarni daga maɓoyarsa.

    Kafafen yaɗa labarai sun bayyana cewar ya yi dogon suma a ranar Juma'a a asibitin birnin L'Aquila inda ya bayyana buƙatar kar a yi amfani da hanya mai sauƙi wajen mutuwarsa saboda tsananin ciwo.

    • An kama 'yan Mafia 90 a Italy
    • Black Axe mafia: Ƴan sanda sun cafke ƴan Najeriya 30 da ke ayyukan asiri a Italiya
  19. Kasar Benin ta dauki mataki bayan yawaitar gobara a ma'ajiyar man fetur

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Gwamnatin ƙasar Benin ta dauki mataki bayan wata mummunar gobara ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 34 a wata ma'ajiyar man fetur a kudancin ƙasar.

    Gwamnatin ƙasar ta bayar da umarnin tantance dukkan wuraren ajiyar man don hana faruwar irin wannan lamari a wasu wurare.

    Ma’aikatar da ke kula da harkokin gwamnati ta fitar da wata sanarwa inda ta jaddada bukatar magance matsalar ajiyar man fetur ta hanoyoyin da ba su dace ba, duk da kokarin da gwamnati ke yi na dakile ayyukan fasa-kwauri da suka shafi ajiyar man fetur da sayar da mai a fadin kasar.

    Gobarar ta faru ne a wata kasuwa mai cike da jama'a a garin Seme Podji da ke kusa da kan iyaka da Najeriya a ranar Asabar.

    Ministan cikin gidan kasar Benin, Alassane Seidou ya shaida wa manema labarai cewa jarirai biyu na cikin wadanda suka mutu a lamarin kuma aƙalla wasu karin mutum 20 suka jikkata kuma ana jinya a asibiti.

    • Kimanin mutum 70 sun jikkata a gobarar da ta tashi a Kano
    • Gobara ta ƙona kimanin shaguna 50 a kasuwar Singa
  20. Ƴan sanda sun kama wani mutum bisa laifin dukan ƴaƴansa har suka mutu

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan sanda a Thailand sun kama wani magidanci bisa zargin shi da lakaɗa wa ƴarsa tare da wasu ƙananan ƴaƴansa dukan da ya yi sanadin mutuwar su.

    Haka nan kuma mutumin, mai suna Songsak Songsaeng ya kashe wasu ƴaƴansa maza ƙanana guda biyu a lokacin da yake auren tsohuwar matarsa.

    Waɗannan tuhume-tuhume sun biyo bayan gano gawar ƴarsa mai shekara biyu binne cikin ɗakin girki.

    Sai dai binciken da ƴan sandan suka gudanar ya gano cewar mutumin yana da lalular ƙwaƙwalwa, ya kuma kashe yaran ne saboda ba ya son koke-kokensu.

    An tuhumi matarsa da laifin mutuwar ƴarsu mai shekaru biyu, yayin da tsohuwar matarsa ke fuskantar tuhumar mutuwar ƴaƴanta maza biyu. Dukkan iyayen uku na tsare a hannun jami`an tsaro.

    A farkon wannan wata maƙwaftan Mista Songsak suka sanar da jami`an tsaro a yankin Bang Ken cewar ya na dukan ƴaƴansa mata, rahoton da ya sa ƴan sada suka ceto yaran daga gidan.

    Gwajin ƙwayoyin halitta da jami`an tsaro suka gudanar ya tabbatar da Mista Songsak ya kashe wasu ƴaƴansa maza biyu da ya haifa da matarsa ta uku waɗanda aka tono gawarsu shekaru goma da suka wuce, bayan mahaifiyarsu ta shaida wa ƴan sanda yadda ya kashe jarirai hudu.

    Ƴan sandan sun tabbatar da ya binne sauran gwawarwakin ne a harabar wani tsohon gidan mai.

    • Bunkasar kasuwar beraye a Thailand
    • Thailand ta mayar da Musulmi 1300 Burma