Gwamnan Zamfara na zargin Gwamnatin Tarayya da yunƙurin sulhu da ƴan fashi

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Mukhtari Adamu Bawa, Rabiatu Kabir Runka and Zulaiha Abubakar

  1. Gwamnan Zamfara na zargin Gwamnatin Tarraya da ƙoƙarin sasanci da ƴan bindiga

    Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal

    Asalin hoton, FACEBOOK/Dauda Lawal

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal

    Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci gwamnatin tararraya ta gudanar da cikakken bincike game da wata tattaunawar sulhu ta sirri da ake yi da ƴan bindiga a jihar.

    Rahotanni sun bayyana cewar tawagar wasu hukumomi da Gwamnatin Tarayya ta aika sun fara tattaunawa da ƙungiyoyin ƴan bindiga ba tare da sanin gwamnatin jihar ba.

    A ranar Litinin Kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar da wata sanarwa, ta nuna rashin jin dadin yadda wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya suka gana da ƴan bindiga ba tare da tuntuɓar gwamnati da hukumonin tsaron jihar ba.

    Sanarwar ta kuma ƙara da cewar: ''Gwamna Dauda Lawal ya buƙaci gwamnatin tarayya ta fayyace wannan mataki na wasu hukumominta, wanda ya ci karo da ƙudurin gwamnatin jihar na amfani da ƙarfi kan ƴan bindigar.

    Ya ƙara da kira ga gwamnati ta binciki wannan lamari, wanda tamkar zagon ƙasa ne ga yunƙurin gwamnatin jihar na yaƙar ƴan fashin daji.

    Gwamnatin Zamfara ta ce ta samu rahoton yadda jami`an gwamnatin tarayya suka gana da ƙungiyoyin ƴan fashin daji a yankunan Birnin Magaji da Maradun da Mun haye da Bawo da kuma Bagege.

    "Yunƙurin yin sulhun da ƴan fashi da tsohuwar gamnatin jihar ta yi a baya bai yi tasiri ba. Ya kamata mu ɗauki darasi daga kura-kuran baya tare da ɗaukar sabbin hanyoyin dawo da zaman lafiya Zamfara."

    “Kasancewar yaƙi da fashin daji na cikin manyan ƙudurorin gwamnatin jihar Zamfara, ba za mu lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga hakan ba."

    Muna buƙatar Gwamnatin Tarayya ta ɗauki mataki nan take ta hanyar dakatar da duk wata tattaunawa da ake yi da ƴan fashin daji a Zamafra, domin hakan zagon ƙasa ne ga matakan da ake ɗauka." In ji sanarwar.

    • ' Muna fama da karuwar hare-haren 'yan bindiga a yankinmu'
    • Sulhu da 'yan bindiga ne zai kawo ƙarshen matsalar tsaro - Yariman Bakura
    .
  2. Halin da matasa masu son zuwa Turai ke faɗawa a tsibirin Lampedusa

  3. Shugaban Burundi ya yi tir da jita-jitar juyin mulki a ƙasar

    ...

    Asalin hoton, Burundi presidency/X

    Shugaban kasar Burundi Évariste Ndayishimiye ya yi Allah wadai da jita-jitar juyin mulkin da aka yi masa a lokacin da yake jinyar makonni biyu don halartar taro a Cuba da kuma taron Majalisar Dinkin Duniya da ke New York.

    Mako guda bayan da shugaban ya bar kasar a ranar 10 ga watan Satumba, labarin wani makarkashiya da aka yi masa ya fara yawo a shafukan sada zumunta.

    Har yanzu dai ba a bayyana tushen jita-jitan ba.

    A cikin jawabinsa bayan ya koma ƙasar a daren Lahadi, Ndayishimiye ya zarge su a kan "mutanen da a ko da yaushe ke mummunan fata a kan mutum".

    Burundi ya fuskanci juyin mulki sama da 10 cikin nasara da gazawa.

    A ranar Lahadi kafin isowarsa, ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta sanar a kan dandalin sada zumunta na X (tsohon Twitter) cewa "babu wani abu kamar haka da ya faru", yana mai kira ga mutane da kada su damu da "wadannan jita-jita da ke dauke da tashin hankali".

    • Burundi: An gano manyan kaburbura fiye da 4,000
    • Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza ya rasu sakamakon bugun zuciya
  4. An shawarci ƙasashe masu arziƙin man fetur game da sauyin yanayi

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon firaiministan Burtaniya Gordon Brown ya bukaci ƙasashen da suke samar da man fetur su fara biyan haraji na musamman wanda kasashe marassa ƙarfi za su yi amfani da shi wajen magance matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa.

    Ya ƙara da cewar Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Norway sun samu riba mai yawa a bara biyo bayan tashin gwauron zafin da farashin mai ya yi.

    Mista Brown ya ce harajin dala biliyan ashirin da biyar zai taka muhimmaiyar rawa cikin kuɗaɗen sauyin yanayi don ƙasashe matalauta.

    A makon da ya gabata lokacin taron Majalisar Dinkin Duniya a New York, shugaban majalisar Antonio Guterres ya bayyana takaicinsa game da rashin kulawa da batun tallafawa masu tasowa.

    • Wutar daji ta tilasta kwashe mutanen wani gari a Kanada
    • Abin da ya sa Sarki Charles ba zai halarci taron COP27 na bana ba
  5. Ƴan bindiga sun sace Kwamishina a jihar Benue

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin jihar Benue ta tabbatar da sace kwamishinan yaɗa labarai da al’adu da yawon shaƙatawa, Matthew Abo da kuma tsohon shugaban karamar hukumar Ukum, Iorwashima Erukaa.

    Babban Sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar, Tersoo Kula, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce wasu ‘yan bindiga ne suka yi garkuwa da Abo a gidansa da ke Sankara da misalin karfe takwas ranar Lahadi da daddare, yayin da aka yi garkuwa da Erukaa a ranar Asabar.

    “Ƴan bingidan da suka yi garkuwa da mutanen biyun da har yanzu ba a san inda suke ba, sun tuntubi iyalan Erukaa amma har yanzu ba su tuntubi dangin Abo ba,” in ji sanarwar.

    "Gwamnan wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin Allah-wadai kuma abin da ba za a amince da shi ba, tuni ya umarci hukumomin tsaro da su fara aiki nan take domin ganin an sako mutanen biyu cikin koshin lafiya."

    Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, domin gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin jihar ta kasance mai aminci ga kowa.

    • An kama wadanda ake zargi da kona Fulani a Benue
    • Hatsarin kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a Benue da Lagos
  6. Sabon rikici ya ɓalle a Habasha

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Ana cigaba da gwabza faɗa a yankin Amhara na kasar Habasha tsakanin dakarun gwamnati da ƴan tawayen Fano waɗanda suka afka birnin Gondar a ranar Lahadi.

    Rundunar sojin ƙasar (ENDF) ta wallafa a shafinta na facebook cewar ta samu nasarar kashe sama da ƴan tawaye 50 yayin da suke tsaka da kai hari.

    Rahotannin sun bayyana yadda kafafen yaɗa labarai mallakar ƴan tawayen suka sanar da karbe ikon yankuna da dama tare da kame gomman sojojin kasar.

    Rahotannin da BBC ba ta gama tantancewa ba.

    An sanar da ɗage taron zaman lafiya na shekara-shekara da aka shirya gudanarwa a birnin Bahir Dar a watan Oktoba sakamakon wasu dalilai da ba a bayyana ba.

    • Ethiopia: Hotunan karya da ake yadawa kan yunwa a Amhara
    • Yaƙin Tigray: Ana zargin sojojin Eritrea da yi wa mata fyaɗe duk da yarjejeniyar zaman lafiya
  7. Wani ɓangare na kotun ƙolin Najeriya ya kama da wuta

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani ɓangare na harabar kotun ƙolin Najeriya da ke birnin Abuja ya kama da wuta a safiyar ranar Litinin.

    Shugaban Hukumar agajin gaggawa a Yanklin Birnin Tarayya, Abbas Idris ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin, inda ya ce tuni jami'an kai ɗauki suka isa harabar kotun, sai dai ya tabbatar da cewa lamarin ya shafi wani ɓangare ne kawai na kotun.

    A cewarsa: "ofisoshi biyu ne lamarin ya shafa kuma babu wanda ya rasa ransa."

    Abbas ya ƙara da cewa yanzu haka jami'an kai ɗauki sun samu nasarar shawo kan wutar.

    Bayanan farko-farko da ke fitowa na cewa wutar lantarki ce ta haddasa gobarar.

    • Me yake jawo gobara a kasuwannin Najeriya kuma yaya za a magance ta?
    • Gobara ta ƙona kimanin shaguna 50 a kasuwar Singa
  8. Ƴan fim ɗin Amurka za su janye yajin aiki

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Marubutan fina-finai a masana'antar shirya fina-finai ta Amurka Holly Wood na shirin kawo karshen yajin aikin da suka kwashe kusan watanni biyar suna yi bayan da kungiyar tasu ta cimma matsaya da masu daukar nauyin fina-finan.

    Mambobin kungiyar dai sun kafa sharadin cewa dole ne a rattaba hannu kan wata yarjejeniyar shekara uku da masu daukar nauyin fina-finan kafin su amince su koma bakin aiki.

    Yarjejeniyar ta zo ne bayan tattaunawar kwanaki biyar da zimmar kawo karshen yajin aikin mafi tsawo da ya shafi Hollywood cikin shekaru da dama.

    Fiye da marubuta dubu goma sha ɗaya ne suka shiga yajin aikin, lamarin da ya shafi wasu manyan fina-finan talabijin masu dogon zango da ake haskawa a Amurka.

    Bukatun da suke nema a biya musu sun hada da karin kudi, da kuma taka birki ga fasahar nan ta kwaikwayon dabi'un ɗan'adam ta AI da suke fargabar za ta iya raba su da hanyar neman abincinsu.

    • Yajin aikin jaruman Hollywood ya zamo tarnaƙi ga fina-finai
    • Masana na ganin Ƙirƙirarriyar basira ta AI ka iya kawo ƙarshen ɗan Adam
  9. Armeniya ta bayyana ra'ayinta game da kwararar ƴan gudun

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Armeniya ta ce 'yan gudun hijira sama da dubu ɗaya daga Nagorno Karabakh sun tsallaka kan iyakarta, tawaga ta farko da ta tsere tun bayan da Azabaijan ta kwace yankin a ranar Talatar da ta gabata.

    Rahotanni sun ce 'yan kabilar Armeniyawa na barin birnin Stepanakert a motoci da dama. Wasu 'yan gudun hijira sun ce da kyar suka tsira yayin da sojojin Azabaijan suka yi musu ruwan bama-bamai a kauyukansu. A halin yanzu Azerbaijan ta maido da wutar lantarki a Stepanakert yayin da take karfafa ikonta.

    Jakadan Armeniya a London Vrzhan Nerse-syan, ya ce kasarsa na yin duba a kan yarjejeniyar tsaronta.

    • 'Rufe sansanoni ƴan gudun hijira a Borno ya tagayyara su'
    • Yadda ƴan Armeniya ke kone gidajensu a Nogorno-Karabakh da Azerbaijan ta kwace
  10. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar BBC Hausa barkan mu da safiyar Litinin

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye tare da ni Aisha Babangida da Zulaiha Abubakar

    Ku kasance da mu domin sanin wainar da ake toyawa a faɗin duniya, musamman ma a Najeriya da makwabtanta