Wike ya soke mallakar filayen Peter Obi da su Udo Udoma

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi, Mukhtari Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. An yanke wa tsohon shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ɗaurin rai-da-rai

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Wata kotu a Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta yanke hukuncin ɗaurin rai da rai ga tsohon shugaban ƙasar, Francois Bozize.

    An yanke wa Mista Bozize mai shekaru 76 - wanda a yanzu ke jagorantar ƙawancen 'yan tawaye - hukunci ne a ranar Alhamis bisa tuhume-tuhume da suka haɗa da tawaye da kuma zagon ƙasa ga tsaro.

    An kuma yanke wa fiye da wasu 20, ciki har da ’yan uwan Bozize biyu hukunci.

    A shekarar 2003 ne Bozize ya ƙwace mulki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda shi kuma aka hamɓarar da shi shekara goma bayan da ya fara mulki.

    lamarin da ya haifar da yaƙin basasa da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.

    A yanzu tsohon shugaban na zaune a Guinea-Bissau.

  2. Sojojin Najeriya sun gano maƙerar makamai a Kaduna

    d

    Asalin hoton, X/Nig.Army

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta gano tare da lalata wata masana'antar ƙera makamai a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X ta ce ta gano masana'antar da ke ƙera bindigogi ba bisa ƙa'ida ba, a garin Kafanchan da ke ƙaramar hukumar Jema'a.

    Sojojin sun ce sun shafe mako guda suna tatara bayanan sirri kafin su kai ga gano masana'antar.

    Sanarwar ta ce jami'an sojin sun kuma kama mutum guda tare da makamai 22.

  3. Somaliya ta buƙaci MDD ta jinkirta janye dakarun AU daga ƙasar

    f

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasar somaliya ta buƙaci Majalisar Dinkin Duniya ta jinkirta kwashe dakarun Tarayyar Afirka da ke aikin wanzar da zaman lafiya a ƙasar da wata uku.

    Dakaru 3,000 ne daga cikin 17,000 da ke Somaliya ke shirin barin ƙasar zuwa ƙarshen watan da muke ciki, a mataki na biyu na janye dakarun wanzar da zaman lafiyar Tarayyar Afirka da ke ƙasar.

    To sai gwamnatin Somaliya da har yanzu ke yaƙi da masu tayar-da -ƙayar bayan ƙungiyar al-Shabab ta ce har yanzu tana fama da koma-baya ta fuskar tsaronta.

    Shawarar da Majalisar Dinkin Duniya ta yanke, shi ne janye duka dakarun da ke aikin wanzar da zaman lafiya na ƙasashen waje a ƙasar zuwa ƙarshen shekara mai zuwa.

    A cikin watan Yunin da ya gabata ne aka fara janye dakarun na AU daga ƙasar.

  4. Jamus ta naɗa Nagelsmann a matsayin kocinta

  5. Kotu ta tabbatar da nasarar gwamnan Plateau

    d

    Asalin hoton, Google

    Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Plateau ta tabbatar da nasarar Caleb Mutfwang na jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris.

    Kotun wadda ke zamanta a birnin Jos, ta kuma yi watsi da ƙarar da ɗan takarar jam'iyyar APC ya shigar gabanta domin ƙalubalantar zaɓen.

    Dan takarar jam'iyyar APC, Nentawe Yilwatda, ne ya shigar da ƙorafi a gaban kotun, yana ƙalubalantar nasarar Caleb Mutfwang na PDP da INEC ta ce ya yi a zaɓen.

    Mista Yilwatda na zargin cewa Mutfwang bai cancanci tsayawa takara ba saboda a cewarsa ba jam'iyyar PDP ce ta tsayar da shi ko ta ɗauki nauyin takararsa ba, kasancewar a lokacin jam'iyyar ba ta da cikakken tsarin shugabanci a jihar.

    Sai dai kotun ta ce wanda ke ƙarar ya kasa gamsar gabatar wa kotun ƙwararan hujjoji game da zargin.

    A ranar 20 ga watan Maris ne INEC ta ayyana Caleb Mutfwang a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan da ya samu ƙuri'u mafiya yawa a zaɓen.

    Sakamakon zaɓen ya nuna Mista Mutfwang na PDP ya samu nasara a ƙananan hukumomi 10, yayin da shi kuma Nentawe Yilwatda, na APC ya samu nasara a ƙananan hukumomi bakwai.

  6. Rasha ta rage sayar da mai ga wasu ƙasashe don rage ƙarancinsa a ƙasar

    f

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin Rasha ta ɗauki matakin gaggawar wucin-gadi na dakatar da sayar da man fetur da iskar gas ga wasu ƙasashen waje domin magance matsalar ƙarancin man a kasuwanninta.

    To sai dai ta ce haramcin bai shafi yarjejeniyar sayar da mai da gwamnatin ƙasar ta ƙulla da wasu ƙasashen tsohuwar tarayyar Soviet huɗu ba, da suka haɗar da Belarus da Kazakhstan da, Armenia da kuma Kyrgyzstan.

    "Matakin zai taimaka wajen daidaita kasuwanin man ƙasarmu, don rage farashin man ga 'yan ƙasa ", in ji sanarwar gwamnatin ƙasar.

    Sanarwar ba ta bayyana tsawon lokacin da matakin zai ɗauka ba, sai dai mataimakain ministan makamashin ƙasar, Pavel Sorokin ya ce danganta da yadda kasuwa ta yi hali

    "Muna fatan samun sauyi mai ma'ana cikin gaggawa".

    A 'yan watannin baya-bayan nan Rasha na fama da ƙarancin man fetur da iskar gas.

    Lamarin da ya sa farashinsu suka yi tashin gwauron zabo a ƙasar.

  7. Shugaban mulkin sojin Guinea ya soki ƙasashen yamma a taron MDD

    Kanal Mamady Doumbouya

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Kanal Mamady Doumbouya ya kare matakin juyin mulki a taron MDD

    Shugaban mulkin sojin Guinea Kanal Mamady Doumbouya, ya ce tsarin dimokradiyyar ƙasashen yamma ba ya aiki a nahiyar Afirka, a ƙoƙarinsa na kare juyin mulki a nahiyar.

    Kanal Doumbouya na jawabi ne a gaban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York na Amurka, inda ya ce ƙasashen Afirka na fama ne da wani tsarin mulki da aka ƙaƙaba musu, wanda a cewarsa ke bai wa 'yan nahiyar wahalar gudanar da shi.

    "Lokaci ya yi da za ku daina yi mana jawabai, ku daina ɗaukarmu kamar wasu ƙananan yara", in ji shi.

    A shekarar 2021 ne Kanal Doumbouya ta ƙwace mulki ƙasar bayan kifar da gwamnatin shugaba Alpha Condé na wancan lokaci.

    Ya kuma kare matakinsa na yin juyin mulki a gaban taron na Majalisar Dinkin Duniyar, yana mai cewa ya yi hakan ne "domin kare ƙasarsa daga abin da ya kira "faɗawa cikin tashin hankali".

    Labarin juyin mulkin ƙasar ya yi wa wasu 'yan ƙasar daɗi a lokacin, waɗanda suka riƙa gudanar da gangamin nuna murna fda goyon bayan sojojin a babban birnin kasar Conakry.

    To sai dai ƙungiyar Ecowas ta fitar da ƙasar daga cikinta sakamakon abin da ta kira 'yawaitar juyin mulki a yankin yammacin Afirka'.

    Ƙasar Guinea na daga cikin ƙasashen yankin yammaci da tsakiyar Afirka da ke fuskantar yawaitar juyin mulki a shekarun baya-bayan nan, ciki har da Mali da Burkina Faso da Nijar da Gabon.

    Ƙungiyar Ecowas da ta Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya sun sha yin Allah wadai da yawaitar juyin mulkin da ake samu a yankunan.

  8. Kotun ƙolin Brazil ta bai wa wasu mutane damar mallakar filaye

    s

    Asalin hoton, Reuters

    Al'umomin gargajiya na Brazil na ta murna a wajen kotun kolin ƙasar, bayan hukuncin da kotun ta yi na ba su damar neman haƙƙin mallakar yankunansu na asali.

    Hukuncin da kotun ta yanke kan ƙarar da ƙabilar Xokleng ta shigar, ya yi watsi da haramcin da aka yi musu a baya na mallakar filayensu.

    A baya dai an haramta musu mallakar filaye matuƙar ba su fara rayuwa a yankin ba tun shekarar 1988, lokacin da Brazil ta amince da sabon kundin tsarin mulkin Brazil.

    Kabilar Xokleng dai ta shafe tsawon shekaru tana fuskantar tsangwama a ƙasar.

  9. Zelensky na ziyara a Canada

    Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine, ya isa birnin Ottawa a wata ziyarar farko da yake kai wa Canada tun bayan mamayar Rasha a kasarsa a shekarar da ta gabata.

    Shugaban ya samu tarba daga Firaminista Justin Trudeau.

    Mista Zelensky ya isa birnin Canada ne daga Washington bayan kammala tattaunawa da fadar gwamnatin Amurka ta White House.

    Shugaban Amurka Joe Biden ya amince da bai wa birnin Kyiv taimako na tsaro kan kuɗin da yawansu ya kai dala miliyan 325.

    Wannan ya haɗa da inganta tsaron sararin samaniya,sai dai babu batun makamin linzami mai cin dogon zango da shugaba Zelensky ya nema.

  10. Shugaban Sudan ya gargaɗi MDD kan yaɗuwar yakin ƙasarsa

    e

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban sojojin da ke mulki a Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya gargaɗi Majalisar Dinkin Duniya cewa yaƙin da ake gwabzawa a ƙasarsa zai iya yaɗuwa zuwa sauran ƙasashen Afirka, makwabta.

    Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar jawabi a babban taron Majalisar da aka gudanar a birnin New York na ƙasar Amurka.

    Janar Abdel Fattah ya kuma bukaci ƙasashen duniya sun ayyana abokin hamayyarsa, da ke jagorantar dakarun RSF a matsayin shugaban ƙungiyar 'yan ta'adda.

    Shugaban na Sudan yanzu haka na rangadin diflomasiyya, a ƙoƙarin neman goyon-bayan ƙasashen duniya bayan shafe watanni ana tafka yaƙin basasar da ya yi sanadin dubban rayuka.

    Shi ma shugaban dakarun RSF, Mohamed Hamdan Dagalo ya aike da nasa saƙon bidiyo ga taron Majalisar, yana nuna a shirye yake ya tattauna tsagaita batun wuta.

  11. Marabanku

    Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, Haji babbar rana.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a wannan shafi, domin kawo irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya, musamman Najeriya da makwabtan ƙasashe.

    Kuna iya tofa albarkacin bakinku kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta:facebook;X,Instagram