Sai da safenku
Nan muka zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Mu haɗu da ku gobe Asabar. Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi, Mukhtari Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage
Nan muka zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Mu haɗu da ku gobe Asabar. Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce alkaluman da ke fitowa yanzu game da ɓarkewar cutar amai da gudawa ko kwalara na nuna cewa cutar na ci gaba da ƙaruwa a duniya.
Ta ce ƙasashe 24 ne a yanzu ke ba da rahoton samun ɓarkewar cutar, yayin da wasu ƙasashen ke cikin matsanancin yanayi game da cutar ta kwalara.
Karuwar buƙatun kayayyakin tunkarar cutar amai da gudawa ya kasance wani kalubale ga ƙoƙarin takaita bazuwar kwalarar a faɗin duniya.
Rahoton Hukumar Lafiya ya ce tun a watan Oktoban 2022 wata cibiyar kula da cutuka a duniya — wanda ke kula da harkar samar da alluran riga-kafi— ya dakatar da tsarin yin alluran riga-kafi sau biyu da aka kayyade a ayyukan kai dauki ga barkewar annobar kwalara, maimakon haka an koma yin riga-kafin sau daya.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi wannan jan hankali ne a cikin wani rahoto game da alkaluman annobar kwalara a shekara ta 2022 da ta wallafa ranar Juma'a, inda ya yi karin haske game da karuwa da tsanantar cutar da ake ci gaba da samu.
Rahoton ya ce ko da yake har yanzu babu isassun alkaluman barkewar cutar, amma dai mutanen da aka bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya rahoton sun kamu da kwalara sun ninka na wadanda aka samu a shekara ta 2021.
Kasashen duniya 44 ne suka ba da rahoton barkewar kwalara, karin kashi 25 cikin 100 a kan rahotannin da aka samu a shekara ta 2021.
Kuma ba kawai an samu karin barkewar annobar ba ne, lamarin ya fi girma a wannan karo.
Rahoton ya ce kasashe bakwai da suka hadar da Afghanistan da Kamaru da Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da Malawi da Najeriya da Somaliya da Siriya, duka an samu rahoton fiye da mutum 10,000 da aka tabbatar sun kamu.
A cewar rahoton gwargwadon girman barkewar cutar, gwargwadon wahalar da ake fuskanta wajen shawo kanta.

Asalin hoton, Getty Images
Jamus ta naɗa Julian Nagelsmann a matsayin wanda zai jagoranci tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar a gasar cin kofin nahiyar Turai da Jamus za ta karɓi baƙunci a baɗi.
Tsohon kocin na Bayern Munich, ya sanya hannu kan kwantiragi har zuwa watan Yulin 2024 don haka zai iya barin aikin bayan an kammala gasar.
Kociyan mai shekaru 36, ya gaji Hansi Flick, da aka kora bayan rashin samun sakamako mai kyau a wasannin da ya jagoranta, wanda ya ƙare da Japan ta doke Jamus da ci 4-1 a farkon wannan watan.
Nagelsmann ya kasance bai da aiki tun bayan da Bayern Munich ta sallame shi a watan Maris bayan ya yi ƙasa da shekaru biyu yana jan ragamar ƙungiyar.
Wasansa na farko zai kasance wasan sada zumunci da Amurka a Connecticut cikin wata mai zuwa.

Asalin hoton, Dauda Lawal/Facebook
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya kira taron gaggawa na Majalisar Tsaron Jiha, biyo bayan sace ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau.
Wannan taron gaggawan an kira shi ne saboda ɗaliban da aka sace a muhallinsu dake wajen jami’a, a Ƙauyen Sabon Gida na ƙaramar Hukumar Bungudu.
A wata sanarwar manema labarai, wacce mai magana da yawun gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya fitar yau Juma’a, ta ce an kira taron gaggawan ne domin tabbatar da ganin an ceto dukkanin waɗanda aka sace, tare kuma da bin hanyoyin kawo ƙarshen matsalar tsaron da ke addabar Zamfara.
Ya ƙara da cewa, Gwamna Dauda Lawal ya bai wa mataimakinsa Mani Mallam Mummuni umarnin jagorantar taron na majalisar tsaro.
Ya ce: “A yayin wannan taro, shugabannin ɓangarorin tsaron na Zamfara sun tabbatarwa da mataimakin gwamnan ƙudurinsu na wanzar da zaman lafiya. Sun kuma shaidawa mataimakin gwamnan cewa sun samu nasarar ceto mutum Shida cikin waɗanda aka sace. “Sun ƙara ƙara da cewa, jami’an tsaro sun samu nasarar kashe ‘yan bindiga da dama cikin waɗanda suka saci ɗaliban, inda kuma suke ci gaba da bin sahun ragowar.
Ya ja hankalin shugabannin tsaron da su ƙara tsananta sintirin jami’an su a wuraren da aka san suna da hatsari.
Mataimakin gwamnan ya kuma jaddada wa al’umman Zamfara cewa gwamnati da jami’an tsaro ba za su yi ƙasa a gwiwa ba, har sai an shawo kan wannan matsala.

Asalin hoton, SOUTHERN DISTRICT OF NEW YORK
An tuhumi dan majalisar dattijai daga New Jersey Robert Menendez bisa zargin karbar dubun dubatar daloli a matsayin cin hanci, cewar ma'aikatar shari'ar Amurka.
Masu shigar da kara sun ce Sanata Robert Menendez da matarsa sun karbi sanda-sanda na zinare da kunshin kudi a ambulan-ambulan daga 'yan kasuwar New Jersey.
Sanatan da matarsa sun karbi kudade cikin sirri a matsayin agaji ga gwamnatin Masar, kamar yadda masu shigar da kara suka yi zargi.
Robert Menendez da matarsa gaba daya sun musanta tuhume-tuhumen da aka yi musu.
Duk mutanen biyu suna fuskantar tuhuma uku kamar hada baki wajen karbar cin hanci da hada baki wajen tafka almundahana kan ayyukan rashin gaskiya da hada baki don tatsar kudade da sunan damar ayyukan hukuma.
Tuhumar na zuwa ne bayan wani dogon bincike da ma'aikatar shari'a ta gudanar tsawon shekaru. Masu shigar da kara sun zargi Robert Menendez da matarsa Nadine ta karbi cin hanci na kudi da zinare sannan an biya mata kudin tallafi bashin gidaje da wata motar alfarma daga wasu mutane guda uku daga New Jersey: Wael Hana, Jose Uribe and Fred Daibes.
Baya ga taimaka wa gwamnatin Masar, sun kuma karbi kudade a matsayin cin hanci don amfani da ikon Robert Menendez a kujerarsa ta sanata don kare 'yan kasuwa guda uku a cewar takardar tuhumar.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, IRNA
Hukumomi a lardunan Balochistan da Sistan na ƙasar Pakistan sun ce ruwan sama mai karfin gaske da kuma zubar kankara, ya hallaka mutum uku, yayin da aka kwantar da 1, 346 a asibiti.
Babban darektan ofishin tunƙarar bala'o'i na ƙasar, Majid Mohebi, ya ce an kuma samu afkuwar guguwa mai karfi a biranen Zabul, Zahak, Hamon, Hirmand da kuma Nimroz, inda ta kwantar da mutum sama da 90.
Kamfanin dillancin labarai na ISNA ya ruwaito Majid na cewa guguwar ta janyo wa mutane matsaloli na rashin numfashi da ciwon zuciya da kuma matsala a idanu a tsawon lokacin da ta afku.
Sashen kula da yanayi a lardunan Sistan da Balochistan ya sanar da cewa za a ci gaba da fuskantar mamakon ruwan sama haɗe da guguwa a yankin arewaci har zuwa ranar Litinin.

Asalin hoton, Channels TV
Matasa a Abuja, babban birnin Najeriya sun bi sahun takwarorinsu na Legas, wajen gudanar da taron tunawa da fitaccen mawakin Afro MohBad.
Dandazon matasan sanye da fararen riguna da kuma ke riƙe da kyandira, sun taru ne a dandalin Unity Fountain inda suke rera wakokinsa.
Ana ta aika sakonnin alhini kan mutuwar mawakin da kuma neman a bayyana takamaimai abin da ya haddasa mutuwarsa ga jama'a.
Suna kuma yin kira da a yi wa marigayin adalci.

Asalin hoton, ELLA WILLIAMS
Gwamnatin Moroko ta ce ƙauyuka kusan dubu uku da ke da yawan al'umma miliyan biyu da dubu ɗari takwas girgizar ƙasa ta faɗawa a farkon watan nan.
Ministan da ke kula da kasafin kuɗin ƙasar Faouzi Lekja, ya ce kusan gidaje dubu sittin ne girgizar ƙasar ta shafa, kuma kashi ɗaya cikin uku na gidajen sun ruguje gaba ɗaya.
Ministan ya ce aikin sake gina yankunan da lamarin ya shafa dole ya girmama tsarin fasahar gine-ginen gargajiyar yankin.
Girgizar ƙasar ta yi sanadin mutuwar mutane kusan dubu uku.

Asalin hoton, ICRC
Wani alƙalin kotun soja a Guantanamo Bay ya yanke hukuncin cewa ɗaya daga cikin mutum biyar da ake tuhuma kan hare-haren 9 ga watan Satumba, ba shi da lafiyar da zai iya tsayawa gaban shari'a a wata ƙara mai ɗauke da hukuncin kisa.
Likitoci sun gano mutumin da ake ƙarar Ramzi bin al-Shibh yana fama da larurar gigitar rayuwa mai alaka da taɓin hankali, kuma abubuwa suna yi masa gizo.
Lauyansa tun tuni ya yi iƙirarin cewa mutumin da yake karewa ya yi fama da "azabtarwa daga jami'an CIA".
A Juma'ar nan, aka tsara Al-Shibh zai fuskanci zaman sauraron al'amura, kafin fara shari'a gadan-gadan.
Kanal Matthew McCall a sansanin sojojin Amurka da ke gefen gabashin Cuba ya amince da sakamakon binciken lafiya na likitoci, wanda a watan Agusta ya ce matsalar da ke damun tunanin Al-Shibh ta yi munin da ba zai iya kare kansa a gaban shari'a ba.
Jami'an kwamitin likitoci sun cimma matsayar cewa mutumin ya zama mai juyayyen tunani kuma hankalinsa ya tabu, kamar yadda jaridar The New York Times ta ruwaito.
Wannan ta sa, bai cancanci ko dai ya tsaya gaban shari'a ba, ko kuma ya amsa laifin da ake tuhumar sa, a cewar wani rahoto da aka gabatar ranar 25 ga watan Agusta ga alkalin da ke shari'ar.
A cewar rahoton, likitocin lafiyar ƙwaƙwalwa na soja sun ce larurar da yake fama da ita, ta sanya "ba zai iya fahimtar sigar zaman shari'ar da ake yi masa, ko kuma cikin hankalinsa ya ba da hadin kai ba".
Ya kamata a gurfanar da shi gaban shari'a ranar Juma'a ne tare da sauran mutum huɗu, a cikinsu har da Khalid Sheikh Mohammed, wanda aka yi imani shi ne ya shirya hare-haren ranar 9 ga watan Satumba.
Kafin shari'ar, Kanal Mathew McCall ya yanke shawarar cire Al-Shibh daga mutanen da ake ƙarar da ake yi.
Ana sa ran, za a ci gaba da zaman shari'ar ga sauran mutanen huɗu kamar yadda aka tsara tun da farko.

Ukraine ta ce ita ta kai hari yau Juma'a a Tekun Bahar Aswad da ke yankin Crimea.
Sojojin Ukraine ɗin sun ce harin na makami mai linzami ya lalata sansanin soji a birnin Sevastopol.
Wata majiya a rundunar sojin saman Ukraine ta shaida wa BBC cewa Ukraine ta yi amfani da makamai masu linzami da ƙasashen yamma suka ba ta wajen kai harin a Crimea.
A makon da ya gabata ma sun kai wani hari a sansanin soji da ke Crimea wanda ya lalata wani jirgin ruwa na Rasha.

Masu zanga-zanga sun sake hawa kan tituna a ranar Juma'a a Ghana, kwana guda bayan kama wasu daga cikinsu da ƴan sanda suka yi a jiya Alhamis.
An yi wa zanga-zangar laƙabi da kawo karshen rashin kyakkyawar jagoranci da cin hanci da rashin tsaro da kuma tawayar tattalin arziki.
Wasu gungun kungiyoyi ne suka zo suka haɗu da matsawa gwamnati lamba don kyautata yanayin rayuwar ƴan ƙasar.
Sun ce sun shirya zamna dirshe na tsawon kwanaki uku.
Ƴan sanda riƙe da makamai sun kama mutane akalla 50 a ranar Alhamis, inda suka tsare su na tsawon yinin jiya.
AN ruwaito cewa ƴan sandan sun ci zarafin wasu daga cikin masu zanga-zangar ciki har da ƴan jarida guda uku, inda ɗaya daga cikinsu ta kasance mai gabatar da labarai a gidan talabijin.

Asalin hoton, BBC/ADEKOLA OLAWALE
An buga wa magoya baya da ke makokin mutuwar fitaccen mawakin Afro MohBad a birnin Lagos, yayin da 'yan sanda ke cewa masu taron suna tare hanya ga ababen hawa.
Sun taru ne a mashigin Lekki da ke tsakiyar birnin bayan wani bikin raye-rayen tunawa mutuwar mawakin mai shekara 27, wanda ya rasu makon jiya a wani asibitin Lagos.
Ana ta aika sakonnin alhini kan mutuwar mawakin da kuma neman a bayyana takamaimai abin da ya haddasa mutuwarsa ga jama'a.
Hukumomin Lagos a yanzu sun tono gawarsa a wani bangare na binciken da ake gudanarwa.
Raye-rayen an shirya su ne ranar Alhamis don juyayin MohBad, wanda ainihin sunansa shi ne Ilerioluwa Aloba, a wani dandali cikin Victoria Island.
Masu makokin sun sanya fararen riguna kuma sun rirrike kyandira ko kuma sun kunna fitilun wayoyinsu a lokacin da suke rawa ga wakokin marigayin, wanda ake nuna masa kauna saboda wayewar kansa da kuma wasu lokuta amfani da batsa a kade-kadensa da kuma fitacciyar barkekiyar muryarsa.
Taurarin mawaka kamar Davido da Falz da kuma Zlatan na cikin jerin mashahuran 'yan fim din Nollywood, inda suka hadu don nuna jimamin mutuwar mawakin da 'yan kallo.

Asalin hoton, BBC/ADEKOLA OLAWALE

Asalin hoton, BBC/ADEKOLA OLAWALE

Ministan Abuja Nyesom Wike ya soke ikon mallakar filayen ɗan takarar shugaban Najeriya a jam'iyyar LP, Mista Peter Obi da na tsohon gwamnan Cross River Liyel Imoke da ke birnin tarayyar.
Cikin wata sanarwa da babban sakatare a ma'aikatar Abuja, Olusade Adesola ya fitar, ta nuna cewa filayen Peter Obi da na Imoke na daga cikin fuloti 165 da hukumomin babban birnin suka ƙwace.
Sanarwar ta ce Wike ya soke ikon mallakar filayen ne saboda rashin gina su da aka yi.
Sauran manyan mutanen da matakin soke mallakar filayen ya shafa, akwai tsohon ministan tsare-tsare na ƙasa, Udo Udoma da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Ufot Ekaett, da tsohon sanatan Edo ta Arewa, Sanata Victor Oyofo.
Jami'an tsaron Najeriya sun ce sun kashe aƙalla ‘yan bindiga 23 a ƙaramar hukumar Danko-Wasuguta jihar Kebbi cikin makon nan, tare da kuɓutar da wasu mutanen da 'yan bindigar suka yi garkuwa da su.
Bayanai dai na nuna cewa hukumomin tsaro tare da hadin gwiwar 'yan ƙungiyoyin sintiri sun fara yin aiki tare wajen ganin sun kakkabe ‘yan bindiga da ke tsallakawa daga jihohi masu makwabtaka domin addabar yankunan jihar ta Kebbi.
Hon Hussaini Bena shi ne shugaban ƙaramar hukumar Danko-Wasugu. Ga kuma ƙarin hasken da ya yi wa Usman Minjibir dangane da wannan nasara.