'Mun bi matakan da suka dace kafin ɗaura aure da mai HIV a Katsina'

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi, Mukhtari Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rashin nasarar da United ta yi kuskurena ne - Onana

  2. An kama mutum 50 kan yunƙurin zanga-zangar tsadar rayuwa a Ghana

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    An kama masu zanga-zanga fiye da 50 a Ghana kan zargin saɓa umurnin ƴan sanda na haramta zanga-zanga a birnin Accra.

    Wata ƙungiya da ke kiran kanta 'Democracy Hub' ce ta shirya zanga-zangar na kwana uku domin nuna adawa da matsin tattalin arziki a ƙasar.

    Masu zanga-zangar sanye da riguna masu launin ja da baƙi - da suka lulluɓe kansu da tutar ƙasar - sun taru ne a wata tasha da ba ta wuce mil ɗaya ba zuwa fadar shugaban ƙasa, kafin ƴan sanda suka kama su.

    Ƴan jaridar da suka je wurin domin ɗaukar labarai su ma an kama su kafin a sake su daga baya.

    Zanga-zangar da suka yi wa laƙabi da ‘Occupy Jubilee House’ na da zimmar matsa lamba ga gwamnati domin ta yaƙi rashawa da samar da shugabanci nagari sannan kuma a inganta rayuwar al’umma.

    Ƴan sanda sun buƙaci jama’a su ƙaurace wa zanga-zangar saboda ƙarar da aka shigar a kotu domin hana gudanar da ita.

    Sai dai masu shirya zanga-zangar sun ce ba a ba su wata takarda daga kotu ba wadda ta haramta musu fitowa su nuna ƴancin su.

    A yanzu haka an tsaurara matakan tsaro a kusa da fadar shugaban ƙasa a birnin Accra.

    Ghana na fuskantar matsin tattalin arziki inda hauhawar farashin kayan masarufi ta kai kusan kashi 40 cikin 100.

    Kasar - wadda ta ƙarbo bashin dala biliyan uku daga asusun bayar da lamuni na duniya, watau IMF - ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da bashi ya yi wa katutu a Afrika.

  3. Rauni zai hana Messi buga wasannin Inter Miami

  4. Za a fara gwajin riga-kafin cutar HIV a Afirka ta Kudu

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasashen Afirka ta Kudu da Amurka za su fara gwajin riga-kafin cutar HIV, inda suka yi kira ga mutane da su bayar da haɗin kai domin gudanar da gwajin.

    Cibiyar bincike ta Amurka (NIH) ta ce an ƙirƙiri sabon riga-kafin mai suna VIR-1388, domin taimaka wa ƙwayoyin jini masu taimaka wa garkuwar jiki da ake kira 'T-cells', waɗanda ke yaƙar sauran ƙwayoyin cutuka da ke kawo wa jiki hari.

    Riga-kafin zai taimaka wajen sanya garkuwar jiki ya samar da ƙwayoyin 'T-cells', waɗanda za su iya gano ƙwayar cutar HIV domin sanar da garkuwar jiki, don ya ɗauki matakin kare jiki daga mummunar illar da ƙwayar za ta yi wa jiki.

    Cibiyar bincike ta Amurka NIH, da gidauniyar 'Bill and Melinda Gates' da wani kamfanin Amurka mai suna Vir Biotechnology ne suka ɗauki nauyin gwajin riga-kafin.

    Za a gudanar da gwajin ne kan mutum 95 da ba sa ɗauke da cutar a wurare huɗu a Afirka ta Kudu da kuma wuri shida a Amurka.

    Ana sa ran sanar da sakamakon farko na gwajin a ƙarshen shekarar 2024, amma za a ci gaba da gudanar da gwajin kan mutanen har zuwa shekaru uku masu zuwa.

    A shekarar 2020, Cibiyar NIH ta dakatar da gwajin wani riga-kafin HIV a Afirka ta Kudu bayan da aka gano cewa riga-kafin baya hana haɗuwar cutar.

  5. An zargi Google Map da sanadin mutuwar wani mutum

    Google Map

    Asalin hoton, Getty Images

    Iyalan wani Ba'amurke - da ya yi amfani da taswirar google, ya tuƙa motarsa zuwa kan wata gada da ta karye - sun yi zargin cewa ya mutu ne sakamakon gazawar Google wajen sabunta taswirar.

    Iyalan Philip Paxson sun kai ƙarar kamfanin na Google, bisa zargin kamfanin da rashin sabunta taswirar domin nuna cewa gadar ta karye fiye da shekara tara kafin lokacin.

    Mista Paxson ya mutu cikin watan Satumban 2022 bayan da ya tuƙa motarsa zuwa kan wata gada da ta karye a yankin Hickory da ke jihar North Carolina.

    Mai magana da yawun Google, ya ce kamfanin na nazarain zarge-zargen.

    Mista Paxson, na kan hanyarsa ta komawa gida ne bayan tasowa daga bikin zagayowar ranar haihuwar ƴarsa da aka gudanar a gidan wani abokinsa a lokacin da hatsarin ya afku, kamar yadda iyalan nasa suka bayyana.

    Mazauna unguwar sun yi ta tuntuɓar Google kan ya sabunta taswirarsa bayan da gadar ta karye a shekarar 2013, kamar yadda iyalan suka bayyana a cikin ƙarar da suka shigar.

  6. Shugaban Ghana ya caccaki MDD

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Ghana Nana Akufo-Addo ya caccaki Majalisar Dinkin Duniya lokacin da ya gabatar da jawabi a taron babban zauren majalisar karo na 78.

    Mista Addo ya jaddada buƙatar sake fasalin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniyar.

    Shugaban na Ghana ya kuma zargi Majalisar Dinkin Duniyar da kawar da ido a kan ''rashin adalci, da kama-karya'' da ya ce na faruwa a tsakiyar yankin nahiyar Turai da matsalar masu tayar da ƙayar-baya, da ta`addanci da yawaitar juyin mulki da ke faruwa a nahiyar Afrika.

    "A karon farko da na fara jawabi a zauren Majalisar a shekarar 2017, na yi magana kan batun sake fasalin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, amma shekaru kenan har yanzu babu wani kwakkwaran matakin gyara da aka ɗauka kan haka", in ji Mista Addo.

    Ya ƙara da cewa "Ba za mu iya ci gaba da kiran zaman lafiya da kururuta yin adalci ba, yayin da mammobin MDD ke fuskantar rashin adalci daga gareta, sakamakon rashin fasali da kyakkaywan tsari a Majalisar, inda Manyan ƙasashe ke aikata saɓanin abinda suke wa'azi a kansa, ta hanyar nuna son kai saɓanin abin da ya shafi sauran al'ummar duniya".

    Al'ummar duniya na zargin MDD da rashin yin wani hoɓɓasa tun bayan da mamayar da Rahsa yta yi Ukraine.

    Kan haka shugaban na Ghana ya ce kusan shekara guda da rabi kenan ake gwabza yaƙi a ƙasar Ukraine, amma majalisar ta kasa ɗaukar wani ƙwaƙƙwaran mataki.

    ''Haka kuma ba zan manta da irin tashin hankalin masu tayar da ƙayar baya, da ayyukan ta'addanci ke shafar yankin Sahel, lamarin da ke ci gaba da kawo rashin zaman lafiya a yankin", in ji shi.

    Shugaban na Ghana ya ce waɗannan duka matsaloli ne da Majalisar Dinkin Duniyar za ta iya magancewa.

  7. Zan yi wa al'ummar Kano adalci - Nasiru Gawuna

    Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar APC a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna ya ce nasarar da ya samu a kotu za ta ba shi damar yi wa al’umma adalci.

    A hirarsa da BBC, Gawuna ya ce hukuncin kotun shi ne abin da suka dade suna jira.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  8. An tsinci gawar ɗan jarida cikin ramin bayan gidansa a Zamfara

    NUJ

    Asalin hoton, NUJ

    Kungiyar 'yan Jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Zamfara ta nuna alhininta kan mutuwar Hamisu Danjibga da ya kwashe shekaru yana aikin jarida a ƙasar.

    An tsinci gawar ɗan jaridar - wanda ke aiki da kafar yaɗa labarai ta VON - cikin wani rami da ke bayan gidansa kwana uku bayan ɓacewarsa.

    Wasu ɗaliban makarantar islamiyya ne suka gano gawarsa ranar Laraba da maraice cikin wani rami da ke bayan gidansa, inda suka yi gaggawar ankarar da malamansu.

    Kungiyar NUJ reshen jihar cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana takaicinta kan halin da ɗan jaridar ya mutu.

    Ta kuma yi kira ga jami'an tsaro su gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin tare da hukunta su.

  9. Ba ma fargabar zuwa kotun ɗaukaka ƙara - Ganduje

    Ganduje

    Asalin hoton, Facebook/Abdullahi Ganduje

    Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya yaba da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano da ta tabbatar da ɗan takarar jam'iyyar APC, Hon. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris.

    Tsohon gwamnan jihar Kanon ya ce hukuncin bai zo masa da mamaki ba, "saboda abubuwa guda biyu, na farko shi ne sanin abubuwan da suka faru a lokacin zaɓe, na biyu kuma al'umma sun riƙa gudanar da addu'o'i tare da roƙon Allah ya tabbatar mana da wanna nasara".

    Ganduje ya ce jam'iyyar APC ba ta da wata fargaba game da ɗaukaka ƙarar da jam'iyyar NNPP mai mulki za ta ɗaukaka.

    Shugaban APCn ya gode wa al'ummar jihar bisa addu'o'in fatan alkairi da suke yi wa jam'iyyarsa a tsawon lokacin da aka ɗauka ana shari'ar.

    A ranar Laraba ne kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamna ta sanar da soke nasarar Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP tare da tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna na APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

  10. Binciken BBC ya gano TikTok na gurɓata ɗabi'u

    t

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani binciken BBC ya gano cewa shafin TikTok na sa mutane yin wasu abubuwan na taɓara waɗanda suka saɓawa al'ada da gurɓata ɗabi'u.

    Binciken ya gano yadda shafin ke karfafa yaɗawa da bayyana ra'ayi a kan wasu batutuwa, wanda ke iya sauyawa ko ɓata tarbiyya a rayuwar yau-da-kullum.

    Shafin na Tiktok na nuna wa mutane wasu irin nau'ikan bidiyo da ba don son rai ko zaɓinsu ba ne kallon bidiyon.

    Sai dai shafin na Tiktok na cewa ya tsara ayyukansa ne ta yadda zai tabbatar da tsaro da kuma tafiya kan abin da ke jan hankali mutane ko suke tattaunawa ko faruwa.

  11. Saudiyya ta ce a shirye take ta daidaita alaƙarta da Isra'ila

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Yariman Saudiyya Mohammed Bin Salman, ya ce ƙasarsa na kan gaɓar daidaita alaƙar diflomasiyya da Isra'ila.

    A wata tattaunawa da kafar Talabijin Fox News ta Amurka, Yariman ya ce batun Falasɗinu na da mutuƙar muhimmanci wajen daidaitawarsu.

    Sannan ya ce a yanzu dai fatansu shi ne ganin an sassautawa rayuwar Falasdinawa a cikin 'yanci.

    Ya kuma yi gargaɗin cewa idan har Iran - abokiyar gabar Saudiyya da Isra'ila - ta mallaki makamin nukilliya, to ita ma ƙasarsa za ta bi sahunta.

  12. Ba za mu ci gaba da bai wa Ukraine makamai ba - Poland

    Andrzej Duda

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Shugaban ƙasar Poland Andrzej Duda

    Ƙasar Poland ta ce ba za ta iya ci-gaba da bai wa Ukraine makamai ba, a maimakon hakan za ta mayar da hankali ne sake wajen inganta tsaronta.

    Ƙasar na bijiro da wannan batu ne a daidai lokacin da dangataka ke ƙara yin tsami tsakanin ƙasahen biyu, bayan da Poland ta yanke hukunci haramta shigar mata da tsaba daga Ukraine domin kare manomanta.

    Wannan tsamin dangataka ya yi tsanani ne tun lokacin da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi zargin cewa gwamnatin Poland na taimaka wa Rasha.

    Gwamnatin Poland ta yi takaicin kalaman shugaba Zelensky da ke cewa wasu ƙasashen na ƙaryar nuna musu goyon-baya.

  13. Marabanku

    Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Abdullahi Bello diginza ke fatan kasancewa da ku a wannan shafi, domin kawo irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya, musamman Najeriya da makwabtan ƙasashe.

    Kuna iya tofa albarkacin bakinku kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta: facebook; X, Instagram