An kama gwamman masu kokarin ballewa daga Ghana

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Ghana sun cafke 'yan awaren kasar 30, bayan wata arangama da suka yi da' yan sanda.
Kungiyar 'yan awaren ta shafe kusan shekaru goma tana kokarin ballewa daga kasar domin kafa wata kasa mai suna ''Yammacin Togo'' da suke fatan za ta hade da lardin Volta dake gabashin Ghana.
Yankin bai fada cikin iyakokin kasar da a baya aka sani da Gold Coast ba.
A shekarar 1956 mutanen suka zabi hadewa da kasar Gana wadda a lokacin ke kokarin samun 'yancin kai.
'Yan tawayen sun yi nasarar satar makamai daga rumbun ajiye kayayyakin 'yan sanda, kuma suna tare hanyoyin da ke kusa da yankunansu.

Ranar jumma'a ne wasu da ake zargin mambobin kungiyar 'yan awaren ne suka afkawa ofisoshin' yan sanda biyu tare da tsare jami'ai uku, in ji wani babban jami'i.
Ministan yankin Archibald Letsa ya ce an kai harin ne da hantsi a garuruwan Aveyime da Mepe a yankin Volta.
"Muna aiki don ganin an saki' yan sandan, mun tsinci kanmu cikin damuwa saboda wannan al'amari'' In ji shi.
Ya ce 'yan awaren - wadanda ke son kafa sabuwar kasa sun kafa shingaye a wurare daban-daban na shiga yankin, mai nisan kilomita 150 daga arewa maso gabashin Accra babban birnin kasar.










