An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Nagorno-Karabakh

Asalin hoton, ARTSAKH PUBLIC TV
Kwana guda bayan da sojojin Azerbaijan suka ƙaddamar da farmaki a yankin Nagorno-Karabakh, mayaƙan Armenia sun amince da wasu shawarwarin da Rasha ta bayar na tsagaita wuta.
Ɗaya daga cikin mahimman buƙatun da dakarun Karabakh suka amince da shi, shi ne shawarar kwance ɗamara gaba ɗaya.
Armeniyawa kimanin 120,000 ne ke zaune a yankin Kudancin Caucasus, wanda aka amince da shi a matsayin wani yanki na Azerbaijan.
Shekaru uku da suka gabata, Azerbaijan ta sake kwace wasu yankuna a ciki da kuma kewayen yankin Karabakh, kuma a ranar Talata ta buƙaci miƙa wuya baki ɗaya.
Jami’an Karabakh sun ce aƙalla mutum 27 ne suka mutu, wasu 200 kuma suka samu raunuka tun bayan da sojojin Azerbaijan suka ƙaddamar da wani abin da suka kira yaƙi da ta’addanci.
Fadar shugaban kasar Azerbaijan dai ta ce jami'ai za su gana da wakilan Karabakh na Armenia domin tattaunawa kan "batun sake hadewa" a garin Yevlakh na Azerbaijan a ranar Alhamis.
Garin yana da nisan kilomita 100 daga arewacin Karabakh, babban birnin yankin Khankendi, wanda Armeniyawa suka fi sani da Stepanakert.
Shugabannin yankin sun bayyana a cikin wata sanarwa cewa, ta hanyar shiga tsakani da dakarun wanzar da zaman lafiya na Rasha suka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta daga karfe ɗaya na rana, agogon yankin.
- Amurka ta ce a tsagaita wuta a Sudan bayan kashe kusan mutum 200
- An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria










