Hukumomi sun sanya dokar hana fita a Kano

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Da alheri!

    To a nan muka kawo ƙarshen rahotanni da labaran da muka gabatar muku tsawon wannan rana ta Laraba Ta-bawa, ranar samu.

    Gobe Alhamis za mu dawo don ci gaba da kawo muku sabbin labarai da rahotanni. Kafin nan, Mukhtari Adamu Bawa ke cewa sai da safe

  2. Man City na tsaka mai mai wuya - Guardiola

  3. Real Madrid ta ci Union Berlin da ƙyar da gumin goshi

  4. Ɗalibi ya ratsa ƙasashe shida a kan keke don shiga Jami'ar Al-Azhar, Daga Wedaeli Chibelushi

    Guinean student

    Asalin hoton, NAHLA ELSEIDY/FACEBOOK

    Wani ɗalibi ya yi tafiyar kilomita 4,000 a kan keke inda ya keta ƙasashen Afirka ta Yamma, inda ya jurewa kamu da tsananin zafi don samun gurbi a jami'ar da yake buri.

    Mamadou Safayou Barry ya tashi ne daga ƙasar Guinea don zuwa mashahuriyar jami'ar Al-Azhar ta ƙasar Masar a watan Mayu, da fatan za a ba shi gurbin karatu.

    Matashin ɗan shekara 25 ya yi tafiyar tsawon wata huɗu ne a kan keke inda ya ratsa ta cikin ƙasashen da ke fama da rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi da kuma juyin mulki.

    Ya faɗa wa BBC cewa ya yi farin ciki "matuƙa gaya" da samun tallafin karatu lokacin da ya isa birnin Alƙahira.

    Matashin wanda yana da aure har da ɗa ɗaya ya ce ko da yake ba zai iya ɗaukar nauyin karanta Nazarin Addinin Musulunci a Jami'ar Al-Azhar ba, ko kuma ya hau jirgin zuwa ƙasar Masar, shaharar da jami'ar ta yi, ya yi masa ƙaimin cewa bari ya jarraba sa'arsa don yin wannan tafiya mai cike da tarihi.

    Ya dai ratsa ta ƙasashen Mali da Burkina Faso da Togo da Benin da Nijar da kuma Chadi. Al-Azhar na ɗaya daga cikin cibiyoyin nazarin addinin Musulunci mafi tasiri ga mabiya mazabar Sunni a duniya.

    Kuma tana ɗaya daga cikin jami'o'i mafi tsufa, don kuwa an kafa ta ne a shekara ta AD670. Mamadou Barry ya bar mahaifarsa don zuwa neman ilmin addinin Musulunci, amma dai ya gamu da kallon zargi da kuma ƙiyayya a wasu ƙasashen da ya ratsa ta cikinsu a kan keke.

    A ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar, 'yan ta-da-ƙayar-baya na kai hare-hare a kai a kai kan fararen hula sannan kuma juyin mulkin da aka yi a baya-bayan nan cikin ƙasashen sun janyo rikita-rikitar siyasa.

    "Tafiya ta cikin waɗannan ƙsashe, tana da wahala saboda ba su da tsaro a wannan lokaci," in ji Mamadou Barry.

    "Suna da matsaloli sosai kuma mutane a can suna cikin tsoro - a Mali da Burkina Faso mutane sun riƙa kallo na kamar wani mugun mutum. A ko'ina na ga sojoji ɗauke da manyan bindigogi da motoci," a cewarsa.

    Ya ce an kama shi kuma an tsare shi har sau uku babu wani dalili - sau biyu a Burkina Faso da kuma sau ɗaya a ƙasar Togo. Sai dai Allah ya tarfa wa garin Mamadou Barry nono lokacin da ya isa ƙasar Chadi.

    Wani ɗan jarida ya zanta da shi kuma ya buga labarinsa a intanet, abin da ya hankalin wasu masu kyakkyawar niyya har suka ɗauki nauyin biya masa kuɗin jirgi zuwa Masar.

    Hakan na nufin ya kauce wa shiga Sudan a kan keke, wadda sassanta a yanzu suka koma fagen yaƙi. A ranar 5 ga watan Satumba, ya sauka a birnin Alƙahira.

    Himmarsa ta sanya har shugabar tsangayar nazarin addinin Musulunci, Dr Nahla Elseidy ta gana da shi. Bayan tattaunawa ne kuma, sai ta bai wa Mamadou Barry gurbin karanta fannin addinin Musulunci da cikakken tallafin karatu.

    • Jami'ar Al-Azhar ta yi fatawa kan Boko Haram
    • Limamin Al-Azhar da ElBaradei sun koka
  5. Labarai da dumi-dumi, An sanya dokar hana fita a Kano

    Police

    Asalin hoton, Nigeria Police/Facebook

    Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta sanya dokar hana fita ta tsawon sa'a 24, bayan yanke hukuncin kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamnan jihar.

    Wata sanarwa da rundunar ta fitar, ɗauke da sa hannun kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, ta ce dokar ta fara aiki ne daga ƙarfe shida na yammacin ranar Laraba zuwa shida na maraice ranar Alhamis.

    'Yan sanda sun ce an sanar da gwamnatin jihar game da wannan mataki a cikin wata wasiƙa da aka aika mata.

    CP Mohammed Usaini Gumel, ya ce jami'ansa da haɗin gwiwar sauran jam'ian tsaro, za su yi sintiri a lungu da saƙo na Kano, domin tabbatar da bin doka da oda.

    Sanarwar ‘yan sandan ta yi kira ga al’ummar Kano su bai wa wannan mataki hadin kai.

    Haka kuma rundunar ta gargaɗi mutane game da karya dokar, tana mai cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

  6. Magoya bayan APC sun yi zagayen murna da hukuncin kotu

    Jami'iyar APC ta gudanar da zagaye domin nuna murna da hukuncin kotun sauraron ƙorafe-korafen zaɓen jihar, da ya tabbatar wa jam'iyyar da nasara a shari'ar ƙarar da ta shigar tana ƙalubalantar nasarar NNPP.

    Shugaban Jam'iyyar na jihar Abdullahi Abbas ne ya ya jagoranci ɗauruwan matasan jam'iyyar waɗanda zuka yi jerin-gwano a kan wasu titunan birnin Kano domin nuna murnarsu da hukuncin kotun.

    Ɗaruruwan matasan sun yi ta kiɗa-kiɗe da bushe-bushe tare da rera waƙoƙin jam'iyyar musamman ta ɗan takarar jam'iyyar Dakta Nasiru Yusuf Gawuna.

    Rahotonni daga Kano sun ce shugaban jam'iyyar ya hau saman mota tare da ɗaga wa ɗaruruwan magoya bayan jam'iyyar hannu a lokacin zagayen murnar.

    Tun da farko rundunar 'yan sandan jihar ta gargaɗi mutanen jihar kan gudanar da duk wani nau'in gangami ko jerin gwano ko zanga-zanga da murnar da za ta iya haddasa rikici bayan hukuncin kotun.

    A ɗazu da rana ne kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamnan jihar ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP tare da ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris.

  7. Matan Iran na fuskantar ɗaurin shekara 10 kan shigar 'da ba ta dace ba'

    Women

    Asalin hoton, EPA

    Majalisar Iran ta zartar da wata doka mai cike da taƙaddama, da za ta ƙara tsananin hukunci da tara a kan mata da 'yan matan da suka karya tsauraran dokokin sanya tufafi.

    Waɗanda suka yi shigar tufafin "da bai dace ba" na iya fuskantar sama da shekara 10 a gidan yari a ƙarƙashin ƙudurin dokar.

    Duk da haka, ƙudurin na buƙatar amincewar Majalisar Shura kafin ya tabbata zama doka.

    Matakin na zuwa ne shekara ɗaya bayan jerin zanga-zangar da ta ɓarke a kan mutuwar Mahsa Amini lokacin da take tsare a hannun jami'an hizba bisa zargin sanya hijabin da bai dace ba.

    Mata sun riƙa ƙona hijabai da ɗan kwalayensu, wasu kuma suna kaɗa shi a sama yayin zanga-zangar ƙasa gaba ɗaya don nuna adawa da hukumomi, wadda aka ba da rahoton cewa an kashe ɗaruruwan mutane, lokacin da jami'an tsaro suka yi musu dirar mikiya.

    Ƙarin wani adadi na mata da 'yan mata sun daina lulluɓe kansu a bainar jama'a kwata-kwata hatta bayan lafawar yamutsin, duk da komawar 'yan hizba kan tituna da kuma kafa kyamarorin bibiyar kai komon jama'a.

    A ƙarƙashin dokar ƙasar Iran, wadda ta dogara da fashin baƙin Shari'ar Musulunci, mata da 'yan matan da suka balaga dole ne su sanya hijabi kuma su sanya dogayen riguna waɗanda ba su ɗame jikinsu ba.

  8. Solskjaer ya caccaki halayyar 'yan wasan Man United

  9. Majalisar dokokin Burkina Faso ta amince da tura sojoji Nijar

    Majalisar dokokin wucin-gadi a Burkina Faso ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da aika dakarun ƙasar zuwa Nijar mai makwabtaka, inda sojoji suka ƙwace mulki ranar 26 ga watan Yuli.

    Kafar talbijin ta ƙasar ta ambato ministan tsaron ƙasar Kanal Manjo Kassoum Coulibaly na cewa za su ƙwashe wata uku a Nijar da zaɓin tsawaita zaman nasu, domin gudanar da abin da ya kira "yaƙi da ta'addanci tare da taimaka wa wajen maido da zaman lafiyar ƙasashen yankin Sahel".

    A ranar 30 ga watan Agusta ne gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta amince da aika dakarunta zuwa Nijar a wani martani ga kungiyar Ecowas da ke shirin aika dakarunta zuwa ƙasar.

    Ƙasashen Burkina Faso da Mali na daga cikin ƙasashe ƙalilan da ke goyon bayan sojojin da suka ƙwace mulki a Nijar, waɗanda ke fuskantar matsin lamba daga ƙungiyar Ecowas na mayar da ƙasar cikin tafarkin dimokraɗiyya ko ta fuskanci matakin soji daga ƙungiyar.

    A ƙarshen makon da ya gabata ne ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar suka amince da kafa wata kungiyar ƙawancen sojijn ƙasashen yankin Sahel, da nufin magance matsalolin bai ɗaya da ƙasashen ke fuskanta, ciki har da batun masu iƙirarin jihadi.

  10. Wakilin Tarayyar Turai ya gana da firaministan Nijar

    Firaministan Nijar

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan da sojojin Nijar suka naɗa, Ali Lamine Zeine ya tattauna da jakadan Tarayyar Turai a Nijar, Salvador Franca Da Silva.

    Hakan na zuwa ne bayan Burkina Faso ta amince da tura sojoji zuwa ƙasar Nijar, mai maƙwaftaka.

    Ba a dai bayyana cikakken bayani kan abin da tattaunawar ta ƙunsa ba, amma hakan ya zo ne, mako biyu bayan Da Silva ya nuna rashin amincewarsa kan hana shi shiga ofishin jakadancin Faransa a Nijar.

    Hakazalika, ministan tsaro na Burkin Faso, Manjo Janar Kassoum Coulibaly ya ce ƙasarsa za ta tura sojoji zuwa ƙasar ta Nijar.

  11. Arsenal za ta buga Champions League karon farko bayan 2016/17

  12. Tarayyar Turai ta dakatar da ba da kuɗi ga hukumar zaɓen Zimbabwe

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Tarayyar Turai ta sanar da dakatar da bayar da tallafin kudi ga hukumar zaɓen ƙasar Zimbabwe saboda nuna damuwa kan yadda ta gudanar da zaɓen watan Agusta.

    Tun daga shekarar 2022, Tarayyar Turai ta kasance daya daga cikin masu ba da gudummawa ga wani aiki na inganta karfin hukumar zaɓen Zimbabwe (ZEC).

    Aikin zaɓen wanda hukumar raya ƙasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ke gudanar da shi, za a kammala shi ne a watan Disamban 2024.

    Tarayyar Turai ta ba da gudummawar dala miliyan 4.7 ga aikin zaɓen wanda an kashe wasu daga cikin.

    Duk da haka, Tarayyar Turai ta ce za ta janye daga aikin zaɓen, wanda "a halin yanzu ana bincike saboda damuwa da wasu masu sa ido kan zaɓuka na ƙasa da ƙasa suka nuna game da 'yancin kai da kuma bayyana gaskiya na ZEC a lokacin zaben 2023".

    Kungiyar ta kuma ce janye tallafin zai sa ƙaimi ga gudanar da kuɗaɗen raya ƙasashe na Tarayyar Turai.

    Kungiyar ta fara shirin dakatar da tallafin kuma ta sanar da shirin ga hukumar zaɓen Zimbabwe da ma'aikatar kuɗi ta ƙasar.

    Sai dai ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a Zimbabwe kuma za ta iya dawo da tallafin.

  13. Wanne zaɓi ya rage wa Abba Kabir Yusuf a Kano?

  14. Ƙudurin dokar hana luwaɗi a Kenya ya ba da shawarar ɗaurin shekara 50

    ....

    Asalin hoton, James Wakibia/SOPA Images/LightRocket via Getty Images

    Wani ƙudurin dokar haramta luwaɗi a Kenya, wanda aka fi sani da Dokar Kariyar Iyali 2023, ya bayar da shawarar ɗaurin shekaru 50 ga waɗanda aka kama da laifi, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.

    Ɗan majalisar dokokin garin Homa Bay, Peter Kaluma ne ya gabatar da ƙudurin, yana ba da shawarar haramta luwadi da auren jinsi daya da kuma duk wani ayyuka da kyamfen na ƴan luwadin.

    Tana ƙara neman haramta faretin 'yan luwadi da majalisunsu da tattaki kan tituna, da kuma daudanci.

    Masu gidajen da ake amfani da su wajen yin luwaɗi ma za su biya tarar dala 14,000 ko kuma za su fuskanci hukuncin dauri na shekaru bakwai idan kudirin ya tabbata.

    A makon da ya gabata, malaman addini da wasu kungiyoyin fararen hula sun gudanar da zanga-zangar hana luwaɗi a birnin Mombasa da ke gabar teku.

    Wannan ya biyo bayan sake aiwatar da hukuncin da Kotun Koli ta Kenya ta yanke a tsakiyar watan Satumba na ba da damar yin rajista na kungiyoyi masu zaman kansu na ƴan luwadi da maɗigo.

    • An kama mutum 57 a Lagos bisa zargin luwadi
  15. Kotu ta ayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano

  16. Kotun Amurka ta amince da buƙatar Atiku kan sakin bayanan karatun Tinubu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata Kotun Lardi a Arewacin Jihar Illinois ta Amurka, ta amince da buƙatar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gabatar na neman a saki bayanan karatun Shugaba Bola Tinubu na jami’ar Jihar Chicago.

    Alkalin kotun, Jeffrey Gilbert, mai shari’a a Amurka, ya yanke hukuncin ne a ranar Talata, inda ya umarci jami'ar Chicago da ta gabatar da “dukkan takardun da suka dace da kuma waɗanda ba na sirri ba” ga Abubakar Atiku cikin kwanaki biyu.

    Atiku dai ya garzaya kotu ne domin neman umarnin da zai tilasta wa jami’ar sakin bayanan Tinubu.

    Duk da cewa takardun shaidar Tinubu sun nuna cewa ya kammala karatunsa a shekarar 1979 tare da digiri na farko a fannin akanta, akwai zargin da cewa akwai naƙasu a bayanan da ke cikin takardar.

    • Kotu ta tabbatar da nasarar zaɓen Shugaba Tinubu
    • Dalili biyar na korar ƙararrakin Atiku da Obi
  17. An ɗaure ƴar TikTok a kan yin Bismillah kafin cin naman alade

    ...
    Bayanan hoto, ...

    Wata kotu a Indonesiya ta yanke wa wata mata mai suna Lina Lutfiawati hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari bisa samun ta da laifin yaɗa wani faifan bidiyo na TikTok, inda a ciki ta faɗi kalamar 'Bismillah' kafin ta ci naman alade.

    An samu Lutfiawati mai shekaru 33 da laifin "tunzura kalaman ƙiyaya" ga ɗaidaikun mutane da ƙungiyoyin addini.

    Kotun ta kuma ce matar za ta biya tarar sama da dalar Amurka 16, za a iya tsawaita zaman ta na gidan yari da watanni uku idan ba ta biya ba.

    A watan Maris ne ta saka bidiyon inda ta furta "Bismillah" - wata jimlar Larabci da ke nufin "da sunan Allah" - kafin ta ci naman alade, wanda haramun ne cin sa a addinin musulunci.

    Miliyoyin mutane ne suka kalli bidiyon inda kuma ya sha suka, lamarin da ya sa wata 'yar Indonesiya ta kai ƙarar ta ga 'yan sanda saboda "tana cin naman alade da saninta a matsayinta ta musulma kuma har da furta kalmar Bismillah.

    ‘Yan sanda sun tuhumi Lutfiawati a watan Mayu da laifin yaɗa labaran ƙiyayya, suna mai cewa hakan wani aiki ne na nuna ƙiyayya kan ƙabilanci da addini.

    Kungiyoyin masu ra'ayin mazan jiya da suka hada da Majalisar Malamai da babbar ƙungiyar malaman addinin Musulunci ta Indonesia su ma sun fitar da hukunce-hukuncen da suka kira faifan bidiyon da cin mutuncin addinin musulunci.

    • An ɗaure marubucin da ya yi ɓatanci ga addinin Musulunci a Algeria
    • Pakistan: Kisan dan Sri Lankan da ake zargi da batanci ga Annabi ya janyo zanga-zanga
  18. Kotu ta tabbatar da zaɓen gwamnan Bauchi, Bala Mohammed

    ...

    Asalin hoton, Senator Bala Abdulkadir Mohammed/Facebook

    Kotun sauraron ƙorafin zaben gwamna a jihar Bauchi ta tabbatar da nasarar Bala Mohammed na jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, 2023.

    A game da haka, kotun ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar APC da dan takararta na gwamna, tsohon babban hafsan sojin sama, Sadique Abubakar suka shigar.

    Ta ce babu wani kwaƙƙwaran dalili na soke zaɓen saboda an gudanar da shi ne bisa ƙa'ida.

    A watan Maris ne INEC ta bayyana cewa Bala Mohammed ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Sadique Abubakar.

    • Zaɓen Najeriya 2023: Sakamakon zaɓen gwamnan jihar Bauchi
  19. Tarayyar Turai ta dakatar da tallafin abinci ga Somaliya kan zargin sata

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Tarayyar Turai ta tabattar da cewa a yanzu haka ta dakatar da kuɗin da take tura wa Shirin Samar da Abinci na Duniya (WFP), waɗanda ake amfani da su wajen kai ɗauki a ƙasar Somaliya.

    Mai magana da yawun kungiyar, Balazs Ujvari ya ce an ɗauki matakin ne domin kare kuɗaɗen ƙungiyar.

    Wani bincike na Majalisan Dinkin Duniya ya gano yawaitar sace-sace na taimakon da aka tura domin bai wa mutanen Somaliya da ke cikin mawuyacin hali, kuma ana zargin jami'an gwamnati da na tsaro da kuma ma'aikatan agaji da hannu cikin wannan ta'asa.

    A bara, Tarayyar Turai ta kashe sama da dallar Amurka miliyan bakwai kan shirin samar da abinci na WFP Somaliya.

    A nata ɓangaren Kungiyar tallafa wa ƙasashen duniya ta Amurka ta ce ba ta da shirin dakatar da tura agajin abinci zuwa Somaliya.

    • Shin talauci na raguwa a duniya?
    • Al`ummar jihar Nasarawa na korafi game da tallafin kayan abinci
  20. Muhimman abubuwan da Tinubu ya faɗa a taron MDD

    Bola Ahmed Tinubu

    Asalin hoton, Bola Ahmed Tinubu/X

    Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabinsa na farko a taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, inda ya bayyana wasu abubuwa masu muhimmanci ga ci gaban Afirka da hadin gwiwar duniya.

    A jawabinsa, shugaban ya jaddada buƙatar mayar da hankali na musamman kan nahiyar Afirka, inda ya lissafo kalubalen baya, waɗanda Afirka ke fama da su har yanzu.

    Ƙalubalen da ya bayyana sun haɗa da karya alkawuran da aka yi a baya.

    Ya kwatanta lamarin da lokacin da aka kawo ƙarshen yaƙin duniya na biyu lokacin da kasashe suka taru suka haɗa kai domin sake gina al'ummomin da yaƙi ya ɗaiɗaita.

    Ya kuma jaddada muhimmancin hukumomin duniya da hadin kan ƙasashe wajen kawo ci gaba a nahiyar Afirka.

    Tinubu ya yi kira ga hukumomin duniya da ɓangarori masu zaman kansu kan su bayar da fifiko ga ci gaban Afirka tare da bayyana bukatar yin gyare-gyare don samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arziki, da yin adalci wajen rabon arziƙi tsakanin al'ummar duniya.

    Ya ce: "Matuƙar dai da gaske ake yi kan taken taron wannan shekara, dole ne sai hukumomi da ƙasashen duniya da ɓangaren masu zaman kansu su fifita batun ci gaban Afirka, don hakan zai amfane su ba Afirka kawai ba."

    Ya ƙara da cewa "sanadiyyar wasu matsaloli daga ciki da waje, tsare-tsaren tattalin arziƙin Najeriya da Afirka sun zamo tarnaƙi ga ci gabansu, da bunƙasar masana'antu, da samar da aikin yi da kuma rabon arziƙi."

    "Idan har Najeriya na son ta sauke nauyin da ke kanta ga al'ummarta da sauran nahiyar Afirka, dole ne ta samar da aiki da tsarin bunƙasa makomar al'umma."

    Jawabin na Tinubu ya kuma mayar da hankali ga mahimmancin mulkin dimokuradiyya a matsayin jigon kiyaye muradun jama'a da jin dadinsu, tare da yin Allah-wadai da juyin mulkin soja da tsare-tsaren siyasa na rashin adalci.

    Ya ambaci batun tattaunawar da ake yi da shugabannin sojoji a Nijar, ta neman mayar da mulkin dimokuradiyya a ƙasar, da yin tsokaci kan yaƙin da ake yi da masu iƙirarin jihadi a yankuna da dama, musamman a yankin Sahel.

    Shugaban ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakin dakatar da kwararar makamai da masu tayar da ƙayar baya ke yi zuwa kasashen yammacin Afirka domin yaƙar wannan mummunar bulaguro.

    A karshe ya jaddada tasirin sauyin yanayi a Najeriya da Afirka, inda ya bayyana bukatar samar da hanyoyi na musamman ga nahiyar da suka dace da manufofin tattalin arziki, kamar shirye-shiryen yaƙi da fataucin hamada da sare dazuka, tare da yin kira da a ƙara saka hannun jari daga kasashe masu karfin tattalin arziki don tallafa wa kasashen Afirka.

    • Ko kun san me ake tattaunawa a taron Majalisar Dinkin Duniya?
    • Sukar da Tinubu ke sha kan yunƙurin tura sojoji Nijar