Dillalan man fetur na barazanar dakatar da ayyuka a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Haruna Kakangi

  1. Kwalara ta kashe mutum 9 a Habasha

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin lafiya a Habasha sun ce mutum 9 sun mutu sakamakon ɓarkewar cutar amai da gudawa a yankin Benishangul-Gumuz da ke arewa maso yammacin ƙasar kamar yadda tashar talabijin na ETV ya ruwaito a ranar Lahadin da ta gabata,

    Wani jami'in kiwon lafiya na yankin, Abdulmunhem Al-Beshir, ya ce "wasu mutum 131 ne suka kamu da cutar yayin da kuma wasu 9 suka mutu," in ji ETV.

    An samu bullar cutar a gundumomi uku, a cewar hukumar lafiya ta Benishangul-Gumuz.

    A halin da ake ciki kuma, barkewar cutar kwalaran ta kuma kashe 'yan gudun hijirar Sudan 9 a yankin Amhara da ke arewa maso yammacin Habasha.

    Kafofin yaɗa labaran cikin gida sun ce annobar kwalara ta bazu a yankuna 11 na kasar a cikin shekarar da ta gabata, inda ta kashe mutum 320.

    Yaƙin basasa na shekaru biyu da fari ya haifar da mummunan rikicin jin kai a yankin

  2. Kotu za ta yanke hukunci kan karar zaben gwamnan Zamfara

    ...

    Asalin hoton, twitter

    Yau ake sa ran kotu sauraron karar zaben gwamnan jihar Zamfara za ta yanke hukunci a wani zama da za ta yi a garin Sokoto.

    Tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya kalubalanci nasarar Dauda Lawal a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar a zaɓen 2023.

    Hukumar zaben Najeriya, INEC ta sanar da Dauda Lawal na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a cikin watan Maris na bana.

    A cewar Inec Dauda Lawal ya samu kuri'u 377,726 inda ya doke Bello Matawalle wanda ya samu kuri'u 311,976.

    Akwai kananan hukumomi 14 a jihar Zamfara wadanda daga ciki ta ce Dauda Lawal ya samu nasara a kananan hukumomi 10, yayin da Matawalle na APC ya lashe zabe a kananan hukumomi hudu.

    Sai dai bayan kafa gwamnati, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Bello Matawalle a matsayin ƙaramin ministan tsaro na ƙasar.

    • Dauda ya lashe zaben gwamnan jihar Zamfara
  3. Tinubu ya isa Amurka don halartar taron babban zauren MDD

    ...

    Asalin hoton, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Facebook

    Bayanan hoto, ...

    Shugaba Bola Tinubu ya isa birnin New York domin halartar taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 78.

    Shugaban ya samu tarba daga ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar da Wakilin dindindin na Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Farfesa Tijjani Muhammad-Bande da sauran jami'an gwamnati.

    Taken babban taron na bana shi ne: 'Sake gina amintaka da karfafa haɗin kai tsakanin ƙasashen duniya da kuma haɓaka yunƙurin tabbatar da muradin ƙarni.'

    Tinubu zai kuma gabatar da jawabinsa na farko a ranar 19 ga watan Satumba.

    Shugaban zai kuma shiga tattaunawa daban-daban kan batutuwan da suka hada da ci gaba mai dorewa da rigakafin annoba da ayyukan sauyin yanayi, da sake fasalin kudi na duniya a lokacin ziyarar tasa.

    • Ko kun san me ake tattaunawa a taron Majalisar Dinkin Duniya?
  4. ...Daga Bakin Mai Ita tare da Raba-gardama na shirin Labarina

  5. SERAP ta maka Tinubu a kotu kan alawus ɗin wasu ministoci

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Ƙungiyar kare hakkin ƴan ƙasa da tabbatar da shugabanci na gari a Najeriya 'SERAP’ ta kai ƙarar shugaba Bola Tinubu kotu kan gazawar sa wajen hana tsofaffin gwamnonin da suke rike da mukamin minista karbar kudaden fansho na jihohi.

    Kungiyar SERAP dai na neman kotu ta tilasta wa Tinubu ya umarci wadannan tsofaffin gwamnonin da su daina karbar irin wadannan kudade.

    A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Lahadi, mataimakin shugaban ƙungiyar a Najeriya, Kolawole Oluwadare, ya ce ministocin da abin ya shafa su ne Nyesom Wike da Bello Matawalle da Adegboyega Oyetola.

    Sauran tsofaffin gwamnonin sun hada da Badaru Abubakar da David Umahi da Simon Lalong da Atiku Bagudu da kuma Ibrahim Geidam.

    Sanarwar ta ce "“Nadin waɗanda ke karbar fansho na rayuwa a matsayin ministoci wani aiki ne na son rai da kuma saɓa wa ƙa'ida".

    “Yayin da da yawa daga cikin ‘yan waɗanda suka ajiye aiki ba a biyan su kuɗaɗen fansho ba, tsofaffin gwamnonin da ke rike da mukamin minista na samun makudan kuɗaɗen alawus-alawus idan sun bar ofis."

    "Gwamnatin Tinubu tana da nauyin hana tsofaffin gwamnonin karbar duk wani hakki na ritaya yayin da suke aiki a matsayin ministoci."

    SERAP dai ta ce wannan dabi’a ba ta dace ba, musamman idan aka yi la’akari da kalubalen tattalin arzikin da ƙasar ke fuskanta.

    Amma kuma har yanzu ba a sanya ranar sauraron karar ba.

    • Najeriya: 'Yan fansho na barazanar yin zanga zanga
    • Mun zaɓo ministoci ne bisa cancanta - Tinubu
  6. Kongo ta musanta ikirarin yunkurin juyin mulki a ƙasar

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Congo-Brazzaville ta musanta rahotannin da ke nuna yunƙurin juyin mulki a kan shugaba Denis Nguesso, wanda ya shafe shekaru 39 a kan karagar mulki.

    Hakan dai ya biyo bayan wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba a kafafen sada zumunta ke cewa sojoji na ƙoƙarin hamɓarar da shugaban mai shekaru 79, wanda a halin yanzu yake birnin New York domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78.

    "Gwamnati ta musanta wannan labarin na karya," in ji Ministan Yada Labarai Thierry Moungalla a kan X (tsohon Twitter) ranar Lahadi.

    "Muna tabbatar da ra'ayin jama'a game da kwanciyar hankali da ke mulki tare da kiran mutane sun ci gaba gudanar da ayyukansu cikin natsuwa da kwanciyar hankali."

    Gwamnatin ƙasar ta kuma buga sanarwar musanta rahotannin da ke nuna yunkurin juyin mulkin a shafin ta na intanet.

    A ‘yan watannin nan dai an yi ta samun juyin mulki a nahiyar Afirka, inda aka yi juyin mulki na baya-bayan nan a makwabciyarta Gabon a watan Janairu.

    Shugaba Nguesso dai ya hau karagar mulki a ƙasar a wani juyin mulkin soja a shekarar 1979.

    • Me ya sa juyin mulki ke sake dawowa a Afirka?
    • Wace illa juyin mulkin Nijar zai yi wa duniya?
  7. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 17 a arewacin DR Congo

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Aƙalla mutum 17 sun mutu sakamakon zaftarewar kasa a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

    Bala'in ya afku ne da daddare ranar Lahadi a kusa da gabar kogin Kongo, a arewacin birnin Lisala, babban birnin lardin Mongala.

    Mata bakwai da maza bakwai da yara uku ‘yan kasa da shekara biyar ne suka mutu.

    An yi jana’izar su a ranar da abin ya faru saboda rashin wurin ajiye su a dakin ajiyar gawarwaki na yankin kamar yadda jami’in Lisala, Désiré Koyo ya shaida wa BBC.

    Mutuwar ta biyo bayan mamakon ruwan sama da aka kwashe kwanaki ana yi.

    Shaidu sun ce gidaje da dama da ke kusa da kogin sun nutse kuma mazauna yankin na ƙoƙarin aikin ceton mutane daga baraguzan ginin.

    Gwamnan Mongala, César Limbaya, ya aika da ta'aziyya ga dukkan iyalan waɗanda suka mutu.

    Ya kuma ayyana kwanaki uku na zaman makoki tun daga ranar Litinin

  8. Ma'aikatan agaji sun mutu wajen kai dauki a Libiya

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Jami'ai sun ce akalla ma'aikatan agaji uku 'yan Girka sun mutu a wani mummunan hatsarin mota lokacin da suke kan hanyar zuwa Bengazi na Libiya domin isa Birnin Derna da ambaliyar ruwa ta daidaita.

    Rahotanni sun ce wasu karin mutum 7 na cikin muwuyacin hali a asibiti, jami'an ƙasar Girka sun ce su na bincike kan musabbabin hatsarin.

    A bangare guda wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman Abdoullaye Bathily ya kai ziyara Derna inda ya ce lamarin mai tayar da hankali ne ganin birnin ya daidaice baki dayan.

    Ya ƙara da cewa gine-gine sun ruguje kuma ko ina aka juya gawarwaki ne yashe a kasa.

    Ana ci gaba da aikin ceto amma lamarin ba mai sauki ba ne in ji shi.

    Ya ce yanzu da kayan agajin kasashen waje suka fara isa, za a mayar da hankali kan taimaka wa wadanda suka tsira, yayin da wasu za su yi kokarin ci gaba da kwashe gawarwakin da suka fara ruɓewa.

    • 'Tamkar ambaliyar tsunami ce ta auka wa birnin Libya'
  9. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkan mu da safiyar Litinin.

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a fadin duniya.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.