Ban kwana
Nan za mu dakata da kawo muku labarai da rahotannin na yau.
Muhammad Buhari Fagge ke fatan mu kwana lafiya daga nan BBC.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
A'isha Babangida and Haruna Kakangi
Nan za mu dakata da kawo muku labarai da rahotannin na yau.
Muhammad Buhari Fagge ke fatan mu kwana lafiya daga nan BBC.

Asalin hoton, AFP
Babbar jam'iyyar adawa a Masar ta ce ba za ta shiga zaɓen shugaban ƙasa da za a yi a ƙasar ba a shekara mai zuwa saboda kama ɗaya daga cikin shugabanninta tare da ɗaure shi a gidan yari na tsawon wata shida.
Gamayyar jam'iyyun da ake kira da Free Current ta ce Hisham Kassem shi ne take sa ran zai zamar mata ɗan takarar shugaban ƙasa.
An same shi da laifin ɓata suna a gidan radiyo da kuma zagin jami'in ɗan sanda.
Magoya bayansa sun bayyana cewa tuhumar da ake yi masa cike take da siyasa.
Ana sa ran shugaba Abdul Fattah al-Sisi zai sanar da shirinsa na sake tsayawa takara karo na uku, amma har yanzu bai yi hakan ba.
Mutum ɗaya ne ya sanar da takararsa ya zuwa yanzu, shi ne Ahmed al-Tantawi, wanda ya ce jami'an tsaro na muzguna masa da shi da tawagarsa.

Asalin hoton, UN
Shugabannin kasashen duniya da ke halartan babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya, sun yi gargadin cewa yunkurin da duniya ke yi na kawo karshen talauci da kuma magance sauyin yanayi na fuskantar koma-baya.
Da yake jawabi a farkon taron na shekara-shekara a birnin New York, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi kira a samar da wani sabon tsari na ceto Shirin cimma maradun ƙarni.
Shirin da ya ƙunshi samar da kudade na biliyoyin daloli da kuma sabbin hanyoyin yafe basuka ga ƙasashe masu tasowa.
Sai dai jami'an diflomasiyya da ƙungiyoyin ba da agaji sun yi gargadin cewa matsalar tsadar rayuwa a duniya da kuma rarrabuwar kawuna dangane da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine na iya kawo cikas ga cimma maradun.

Asalin hoton, Getty Images
Pep Guardiola ya ce ba wani siddabaru yake yi ba a Manchester City da har ya lashe Champions League a karon farko.
City ta dauki Premier League da FA Cup a bara, wadda ta zama ta uku a Ingila da ta lashe kofi uku, wadda ta ci Inter Milan 1-0 a Champions League a wasan karshe.
City za ta fara kare kofin da ta dauka a bara da yin wasan farko a cikin rukuni ranar Talata, inda za ta karbi bakuncin Red Star Belgrade a Champions League.
''Abu ne mai sauki. Da zarar ka dauki kofin farko hanya ta buɗe'' in ji Guardiola.

Asalin hoton, PA Media
Rundunar Sojin Amurka ta nemi taimakon mutane wajen gano jirgin yaƙinta na dala miliyan 100, kirar F-35B bayan matuƙin jirgin ya fice daga cikinsa.
Jirgin ya ɓata ne da yammacin ranar Lahadi, lokacin da matuƙin jirgin ya tashi zuwa kudancin jihar Carolina.
Matuƙin wanda ba a bayyana sunansa ba, ya fice daga jirgin ne ta hanyar amfani da lemar jirgi.
Yanzu dai yana cikin wani yanayi mara daɗi a asibiti.
Ba a dai san takamaimai abin da ya faru ba, amma jami'ai sun ce jirgin na fuskantar matsala ne.
Lokacin da matuƙin ya fice ya bar jirgin cikin tsarin tuƙa kansa.
Jami'ai sun ce sun mayar da hankali wajen neman jirgin kirar F-35B tsakanin wasu tafkuna biyu a arewacin birnin Charleston.
Hukumar lura da jirage ta ƙasar ta ce lokaci na ƙarshe da aka ga sawun jirgin, shi ne tsakanin tafkin Moultrie da na Marion.

Kotun sauraren ƙararrakin zaɓe ta Jihar Kano ta bayyana Laraba, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan ƙorafi game da zaɓen gwamnan Kano.
Matakin na zuwa ne bayan ƙarar da jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta shigar gaban kotun ƙorafe-ƙorafen zaɓen jihar, inda take ƙalubalantar nasarar Abba Kabir Yusuf, a matsayin gwamnan Kano a zaɓen 18 ga watan Maris ɗin 2023.
Shari'ar na cikin manyan ƙararrakin zaɓen gwamna da ke matuƙar jan hankali a Najeriya.
APC ta ce Abba Gida-Gida, bai ci zaɓen gwamnan Kano da halastattun ƙuri'u ba.
Ta kuma ce akwai ƙuri'un da aka soke, waɗanda yawansu ya zarce ratar da ke tsakanin ƙuri'un da Abba Kabir Yusuf da ya samu da mai biye masa wato Nasiru Yusuf Gawuna.
Wani ƙarin ƙorafi da APC ta yi shi ne wanda aka ayyana cewa ya ci zaɓen, babu sunansa a cikin rijistar jam'iyyar NNPP.
Kuma Jam'iyyar NNPP ba ta gudanar da zaɓen fitar da gwani ga masu neman takara, kafin zaɓen gwamnan Kano ba.

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon shugaban ƙasar Zambiya Edgar Lungu ya shigar da gwamnatin ƙasar ƙara gaban kotu sakamakon haramta masa halartar taro a Koriya ta Kudu.
Jami`an tsaro sun fidda Mista Lungu daga cikin jirgin sama sakamakon zarginsa da amsa gayyatar babban taron zaman lafiya na duniya ba tare da amincewar gwamnatin Zambiya ba.
Mista Lungu ya buƙaci kotu a Lusaka babban birnin ƙasar ta sake yin duba game da matakin da gwamnati ta ɗauka na dakatar da shi.
Jam`iyyarsa ta (PF) ta bayyana matakin na gwamnati a matsayin karya doka, kakakin Jam`iyyar PF Emmanuel Mwamba ya ce: ''Idan an gayyace shi kuma har an biya kuɗaɗen tafiyarsa tare da ƴan rakiya ko kuma shi ya biya wa kansa, ba ya buƙatar ya sanar da gwamnati.''
Mista Mwamba ya ƙara da cewar a baya gwamnati ta taɓa hana tsohon shugaban zuwa asibiti don duba lafiyarsa a ƙetare duk da cewar ya nemi izini.
Mista Lungu ya sanar da janyewa daga al`amuran siyasa bayan ya sha kaye a hannun shugaban ƙasar Hakainde Hichilema a shekarar 2021, a baya-bayan nan alamu na nuni da cewar ya na burin yin takarar shugabancin ƙasar a zaben shekara ta 2026.

Asalin hoton, AFP
Aƙalla mutum 20 ne suka mutu a Afrika ta Kudu bayan wani mummunan haɗari da ya faru a lardin Limpopo da ke arewacin ƙasar.
Rahotanni sun ce waɗanda haɗarin ya rutsa da su ma'aikatan haƙar ma'adanai ne, lokacin da motarsu ta yi taho mu gama da wata babbar mota.
An kwashe su ne akai su wani babban wajen haƙar gwal a ƙasar- Venetia - wanda mallakin De Beers.
Venetia na kusa da iyakar Bostswana da Zibabwe, wurin da aka ce yana da samar da kashi 40 cikin 100 na gwal ɗin Afrika ta Kudu.

Asalin hoton, ISNA
Kungiyar Al-Nasr da Ronaldo yake buga wasa ta shaida wa Hukumar Kwallon Kafa ta Iran cewa ba za ta yi atisaye na ƙarshe ba a filin wasa na Azadi gabanin wasansu da Persepolis.
Kamfanin dillancin labarai na Iran ISNA ya ce dalilin wannan mataki shi ne tarbar da aka yi wa Ronaldo da sauran abokan wasansa, kuma Ƙungiyar ba ta son shiga haɗarin fita daga otel zuwa filin wasa na Azadi ba.
A gefe guda kuma, Kocin Espinas da ke zaune a otel ɗaya da Al-Nasr ya ce an fasa wani ɓangare na otel ɗin saboda yawan magoya bayan Ronaldo.
Ali Asghar Amiri ya ce, "Cunkoson magoya bayan ya janyo an lalata wani ɗan karamin lambu da ke otel ɗin da kofofi da wani ɓangare na shiga ciki."
A gobe ne Persepolis za ta karɓi baƙuncinAl-Nasr ta Saudiyya a wasan farko na rukuni na kofin zakarun Asia a filin wasa na Azadi, ba tare da 'yan kallo ba.

Asalin hoton, Reuters
Wani kamafani da ke hada kayan sha a Poland ya naɗa butun-butumi a matsayin shugabansa karon farko a tarihin duniya.
Kamfanin ya ce ya naɗa butun-butumin da aka sanya masa fasahar AI a matsayin gwaji, domin ganin tasirinsa a matsayin shugaba.
Daraktan kamfanin ya ce har butun-butumin da aka raɗa wa suna Mika na matakin gwaji ne, kuma za ta jagoranci kamfanin kan yadda za a tsara harkokin sadarwarsa da ci gabansa.
Mai ba da umarnin kamfanin ya ce fasahar mai suna Mika ta na ci gaba da gwaji domin ita ce za ta fito da kamfani a gaban sada zance.
Mika ta ce za ta ɓullo da wani sabon tsari da ɗan adam ba zai iya ɓullo da shi ba.
"Zan riƙa ɗaukar mataki kan dogaro da bayanai da muka tattara domin cimma abubuwan da kamfanin ya sa a gaba. Babu son zuciya, aiki za a yi wanda babu son rai cikinsa da zai cimma muraden kamfaninmu,"in ji Mika.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, REUTERS / FREE THE NAMAZIS / @NEDASHARGHI / X.
Amurkawa biyar da aka ayyana a matsayin waɗanda Iran ta yi garkuwa da su, sun kama hanyarsu ta zuwa gida, sanadin musayar fursunoni tsakanin ƙasashen biyu.
An cika sharaɗin ƙarshe na musayar fursunonin, wadda Qatar ke jagoranta bayan kuɗaɗen Iran da yawansu ya kai dala biliyan shida waɗanda aka tsare a Koriya ta Kudu sun shiga asusun bankinta a Doha.
Al`amarin da ya sa shirin musayar fursunonin ya kai mataki na gaba, inda Iran ta sallami mutanen da take tsare da su: maza 4 da mace 1 daga gidan kurkuku, kuma tuni suka kama hanyarsu ta zuwa Qatar, inda za su haɗu da manyan jami`an Amurka kafin su isa Washington.

Asalin hoton, other
Tun farko Amurka ta ce an tsare 'yan ƙsar nata ne bisa zarge-zarge marasa tushe saboda wani al'amari mai alaka da siyasa.
Yayin tattaunawar neman mafitar dambarwa, ƙasashen biyu sun cimma wata matsaya da ta bayar da damar canzawa fursunonin wuri daga kurkukun Evin zuwa wani gida a birnin Tehran.
A nata ɓangaren,Amurka ta yafe wa mutum biyar ƴan asalin Iran da take tsare da su a kurkuku, bayan samun su da laifukan karya takunkuman da ƙasar ta ƙaƙabawa Iran, ko da yake ba dukkansu ne za su koma Iran ba.
Yan Iran da Amurka ta yafe wa sun haɗar da Reza Sarhangpour da Kambiz Attar Kashani da Kaveh Lotfolah Afrasiabi da Mehrdad Moein Ansari da kuma Amin Hasanzadeh.

Asalin hoton, Reuters
Amurkawan da Iran ta tsare bisa tuhume-tuhume daban daban sun haɗa da: Morad Tahbaz wanda aka kama a 2018 da Siamak Namazi,ɗan kasuwa da aka kama a 2015 da ɗan`uwansa Baquer da Emad Shargi waɗanda aka kama a 2018 bisa tuhume-tuhumen leƙen asiri da kuma ƙarin mutum biyu da ba a bayyana sunayensu ba.
A Najeriya, ‘yan kasuwa masu sayar da man fetur sun bayyana yiwuwar dakatar da ayyukansu, saboda ƙarin kuɗaɗen haraji da suka yi zargin gwamnatin ƙasar ta yi.
Sun kuma bayyana ci gaba da biyan hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ruwa ta NIMASA da dalar Amurka maimakon kuɗin ƙasar naira, da ƙara dagula al’amura.
Tashin farashin man fetur da na kayan abinci da sufuri na daga cikin dalilan da hukumomi suka ce na janyo hauhawar farashi, lamarin da ke jefa miliyoyin ‘yan ƙasar cikin ƙangin rayuwa da matsin tattalin arziƙi.
Ga ƙarin bayanin da wani jami'i a cikin dillalan man fetur ɗin ƙasar, Bashir Ahmed DanMallam ya yi wa Habiba Adamu ta wayar tarho.

Asalin hoton, AFP
Ƴan tawayen Azbinawa daga arewacin Mali sun ce sun kwace iko da sansanonin sojoji biyu da ke yankin tsakiyar ƙasar, a daidai lokacin da rikici ke karra ƙazancewa tsakaninsu da gwamnatin sojin ƙasar.
Wani jami'in Mali ya shaida wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa, an samu wasu mutane da suka mutu a hare-haren na ranar Lahadi a garin Léré da ke yankin Timbuktu, sai dai bai tabbatar da adadinsu ba.
Yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan awaren Abzinawa suka yi a shekarar 2015 ta yi rauni tun bayan hamɓarar da gwamnatin farar hula a shekarar 2020, kuma korar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a watan jiya ya kara ruruta wutar rikicin.
Kakakin kungiyar 'yan tawayen wanda aka fi sani da Coordination of Azawad Movements (CMA) ya shaida wa AFP cewa: "Mun kai hari tare da kwace iko da sansanonin sojoji biyu a garin Léré a wannan Lahadin."
A karshen mako ne shugabannin sojojin Nijar da Burkina Faso da Mali suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro ta hadin gwiwa a birnin Bamako, inda suka yi alkawarin bayar da taimako ga juna idan sojojin kasashen waje ko kuma masu tayar da kayar baya na cikin gida suka kai musu hari.

Asalin hoton, AP
Minista mai kula da kamun kifi a Somaliya ya tabattar wa BBC cewa sojojin ƙasar sun amshe kammala karɓe iko da garin Amara, wanda a baya yake ƙarƙashin ikon mayaƙan ƙungiyar Al-Shabaaba.
Gwamnatin Somaliya ta ce yanzu haka akwai gagarumin shirin soji da za ta ƙaddamar kan mayaƙan na Al-Shabaab, a ƙoƙarinta na kakkaɓe ayyukan ƙungiyar.

Asalin hoton, Philip Shaibu/Facebook
An hana mataimakin gwamnan jihar Edo Philip Shaibu shiga ofishinsa da ke gidan gwamnati a Benin babban birnin jihar.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa, Shaibu ya isa gidan gwamnatin ne da safiyar yau Litinin, inda ya iske kofar shiga ofishin nasa a kulle.
Ya ce bai samu wata takarda daga ofishin gwamnan ba, da ke umurtar sa da sauya wurin aiki, wanda kuma ita ce ya kamata ta zama hanyar ba shi umarnin barin ofishinsa da ke gidan gwamnati.
“Har yanzu ban samu wata sanarwa ba a hukumance da aka umarce ni na canza ofis.
"Ma'aikatan ofis dina ne kawai suka samu saƙon, ba ni ba."
"A yanzu haka da nake magana da ku, ina tsaye a bakin kofa,” in ji shi yayin da yake tattaunawa da wani wanda ba a san ko wane ne ba.
A makon da ya gabata, an aika da wata wasiƙa daga ofishin shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin jihar, wadda ke ɗauke da saƙon umurni ga mataimakin gwamna, Philip Shu'aibu kan cewa an mayar da ofishinsa zuwa gini mai lamba 7, Dennis Osadebey Avenue, GRA, Benin City.

Asalin hoton, AFP
Hukumomin samar da ruwa a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, sun bukaci mazauna birnin da kewayen da su taƙaita yawan ruwan da suke amfani da shi sakamakon karancin ruwa da ake fama da shi wanda zai iya haifar da durƙushewar al'amura.
Kamfanonin samar da ruwa na 'Rand' da 'Johannesburg' a ranar Lahadin da ta gabata sun ce yawan ruwan da mazauna yankin ke amfani da shi "yana kawo cikas ga tsarin samar da ruwa" kuma ya haifar da ƙarancinsa a rumbun adana ruwan.
Kamfanonin sun buƙaci mazauna yankin da su taƙaita wanka zuwa mintuna biyu bayan haka, kada su yi amfani da ruwa sai idan sun yi ba-haya, kuma su kiyayi wanke motoci har sai karshen mako-mako, su guji amfani da ruwa mai tsafta ga lambuna, da kuma bayar da rahoton duk inda ruwa ke tsiyaya.
A halin yanzu Johannesburg na ƙarƙashin takunkumin ruwa na shekara-shekara, yawanci daga Satumba zuwa Maris.
Rashin ruwa na baya-bayan nan ya haifar da rashin gamsuwa a tsakanin mazauna da cibiyoyi, kamar asibitoci.

Asalin hoton, FACEBOOK/Dauda Lawal
Kotun sauraron ƙorafin zaɓen gwamnan jihar Zamfara ta tabbar wa Dauda Lawal Dare da nasara a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a watan Maris na shekara ta 2023.
A zaman yanke hukunci da kotun ta yi yau a birnin Sokoto, ta ce Dauda shi ne ya samu ƙuri'u mafi yawa a zaɓen.
Tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ne ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar nasarar Dauda a kotun wadda ke zaman ta a birnin Sokoto.

Asalin hoton, AFP
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa mutane a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a Libiya na cikin haɗarin kamuwa da cutuka saboda gurɓacewar ruwa da kuma rashin tsaftar muhalli.
Majalisar ta ce tawaga daga hukumominta guda tara na gudanar da ayyukan agaji, ciki har da bayar da magunguna da za su taimaka wa mutune 15,000 a tsawon wata uku.
Dubban mutane ne suka halaka lokacin da wasu madatsun ruwa biyu a yankin Derna suka ɓalle a makon da ya gabata.
Majalisan Ɗinkin Duniyar ta ce har zuwa yanzu, mutum 11,300 ne suka mutu kuma har yanzu ba a san inda mutum 10,000 suke ba.
A cikin wata sanarwa, MDD ta ce ''Majalisar ɗinkin duniya a Libiya na ci gaba da haɗa hannu da hukumomin ƙasar da kuma abokan aiki daga ƙasashen waje domin tabbatar da ganin an isar da taimakon da ya dace ga mutanen da suke buƙata a kan lokaci."