Al-Shabab ta kwace yankuna daga hannun sojojin Somalia

Asalin hoton, Getty Images
Mayakan kungiyar al-Shabab sun sake kwato akalla wurare biyu da sojojin Somaliya suka kwace a wani sabon farmaki da suka kai.
Akwai rahotannin da ke cewa bangarorin biyu sun samu gagarumar asara a lokacin da ake gwabza kazamin fadan neman iko da Cowsweyne.
Majiyoyi a wani asibitin sojoji sun ce an kai akalla sojoji 50 da suka jikkata domin samun kulawa.
Shugaba Hassan Sheikh Mohamud dai ya yi alkawarin kawo ƙarshen al-Shabab cikin watanni.
A ranar Juma'ar da ta gabata sojoji da mayakan sa-kai sun yi shagulgulan murnar karbe wani sansanin mayakan al-Shabab da ke El Bur.
- Masu mayafi da ke yaƙar mayaƙan al-Qaeda da al-Shabab a Somaliya
- Al-Shabab ta ce ta kame wani otal a Somalia
