Aljeriya ta gabatar da tsarin sasanta rikicin siyasar Nijar

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Umar Mikail

  1. Babu wanda ya isa ya kori Kwankwaso daga NNPP - Buba Galadima

  2. Mu zama lafiya

    Masu bibiyarmu a wannan shafi, ƙarshen rahotannin ke nan.

    Za mu kawo wasu sababbi a wani shafin gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Umar Mikail ne ke cewa sai da safenku.

  3. Aljeriya ta gabatar da tsarin sasanta rikicin siyasar Nijar

    Nijar

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan Harkokin Waje na Aljeriya Ahmed Attaf ya ba da shawarar sabuwar hanyar da za a bi wajen sasanta rikicin siyasar maƙwabciyarta Nijar.

    Cikin shawarwarin har da tsari na wata shida da zai miƙa mulki ga farar hula.

    Ministan wanda ya fara ziyarar aiki a ƙasashen Afirka ta Yamma zuwa ƙasashen Benin da Ghana da Najeriya, ya kuma jaddada goyon bayan ƙasarsa ga matakin sasanta rikicin cikin laluma, maimakon ƙarfin soja.

    Aljeriya na shirin shirya taron Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) don mayar da Nijar ɗin kan tsarin mulkinta, sannan ta nemi a sassauta wa masu juyin mulkin da kuma gudanar da taron neman inganta yankin na Sahel.

    A makon da ya gabata ne hafsoshin tsaro na ƙungiyar Ecowas ta ƙasashen na Afirka ta Yamma suka taru a birnin Accra na Ghana, inda suka ce sun saka ranar afka wa sojojin mulkin Nijar ɗin, amma ba su faɗi ranar ba.

    Janar Abdourahmane Tchiani, wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban Nijar, ya ce nan da shekara uku sojojin za su mayar da mulki ga farar hula, matakin da Ecowas ɗin ta yi fatali da shi.

  4. An yi jana'izar shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin

    Prigozhin

    Asalin hoton, Rex/Shutterstuck

    Bayanan hoto, Rahotanni sun ce an binne Prigozhin a kusa da mahaifinsa

    An yi jana'izar shugaban ƙungiyar mayaƙa ta Wagner, Yevgeny Prigozhin, in da aka binne shi a birnin St Petersburg, kamar yadda makusantansa suka bayyana.

    Suka ce an yi jana'izar "a ɓoye" kuma "duk masu son yi masa addu'a za su iya zuwa maƙabartar Porokhovskoye da ke birnin".

    Hukumomi a Rasha sun tabbatar da mutuwar Prigozhin mai shekara 62 ne bayan hatsarin da ya ritsa da shi a kusa da birnin Moscow ranar 23 ga watan Agusta.

    Fadar Kremlin ta Shugaba Putin ta musanta raɗe-raɗin cewa tana da hannu a hatsarin jirgin nasa.

    Sai dai masu sa ido na cewa da ma can Prigozhin "matacce ne a raye" tun bayan da ya yi yunƙurin yin bore a watan Yuni.

  5. Hukumomin agaji sun roƙi Ecowas ta tsame su daga takunkuman Nijar

    Niger Coup

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) da wasu ƙungiyoyin agaji na neman ƙungiyar Ecowas ta ƙasashen Afirka ta Yamma ta cire su daga cikin takunkuman da ta sanya wa Njar sakamakon juyin mulki.

    Suna cewa lamarin yana shafar harkokin kula da lafiyar 'yan ƙasar da dama.

    "Babu hanyar da za a iya shigar da kayan agaji cikin ƙasar," kamar yadda kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito wakilin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta UNHCR, Emmanuel Gignac, yana cewa.

    "Kayan da lamarin ya fi shafa su ne na abinci, daga nan kuma sai magunguna, da ƙwayoyin magani."

    Ya nuna damuwa game da yadda matsalar za ta iya ta'azzara a wuraren da mutane ke dogara da jannareto, sakamakon yanke lantarki da Najeriya ta yi, alhalin kuma ba lallai su iya samun man fetur ba.

    Ƙasashe maƙwabtan Nijar sun rufe iyakokinsu tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum, inda suka daina kowace irin hulɗa da ƙasar bisa umarnin Ecowas.

    • 'Mutane sun wahala a Nijar kuma suna neman wanda za su ɗora wa laifi'
    • Miliyoyin mutane na kwana ba su ci abinci ba a Nijar - Hukumar Abinci
    • Manyan matsalolin tsaro uku da suka addabi Nijar bayan juyin mulki
  6. Kotu ta hana EFCC bincikar hukumar yaƙi da rashawa ta Kano

    Muhuyi Magaji

    Asalin hoton, Facebook/Muhuyi Magaji

    Bayanan hoto, A watan Yunin 2023 Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya mayar da Muhuyi Magaji kan muƙaminsa bayan sauke da gwamnatin Ganduje ta yi

    Babbar kotun tarraya da ke jihar Kano a arewacin Najeriya ta bayar da umarnin dakatar da wasu hukumomin yaƙi da cin hanci, ciki har EFCC daga bincikar hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar da wasu jami’anta.

    Lamarin na zuwa ne yayin da EFCC ta buƙaci hukumar ta Public Complaints and Anti-Corruption Commission ta yi mata bayani game da wasu kuɗaɗe.

    Kazalika ta buƙaci shugaban hukumar, Muhuyi Magaji, ya yi mata bayani game da yadda yake gudanar da ayyukansa.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari rahotan Zahraddeen Lawan daga Kano:

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari rahotan Zahraddeen Lawan daga Kano:
  7. Kotun ƙolin Indiya ta umarci gwamnati ta mayar wa Kashmir matsayinsa na musamman

    Kashmir

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Bayanan hoto, Wasu 'yan sandan yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Indiya ke nan suke fareti a ranar 'yancin kan ƙasar

    Kotun ƙolin Indiya ta umarci gwamnatin ƙasar ta bayyana wani lokaci takamaimai da za ta mayar wa da yankin Kashmir da ke ƙarƙashin Indiyar matsayinsa na jiha.

    Hukuncin na da matuƙar muhimmanci bayan kalubalantar gwamnatin tarayya da ta mayar da yankin ƙarƙashin ikonta a 2019.

    Kotun kolin ta jaddada muhimmancin kasancewar jihar ƙarƙashin mulkin dimokuradiyya.

    Kotun ta kuma buƙaci gwamnatin Indiya ta fayyace dalilin da ya sa ta tuɓe wa yankin na Kashmir matsayin nasa na musamman.

    Sai dai babban mai tattara ƙararraki na gwamnatin ya faɗa wa kotun cewa matsayin yankin na yanzu ba na dindindin ba ne, kuma za a mayar masa da ainahin matsayin nasa na jiha.

  8. Rikicin siyasar Nijar ka iya jefa 'yan ƙasar cikin uƙuba - MDD

    ..

    Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce riKicin siyasar ƙasar Nijar haɗi da takunkuman da aka ƙaƙaba mata sakamakon juyin mulki ya jefa ɗimbin jama'ar ƙasar da ke yankin Sahel cikin "uƙuba".

    A watan da ya gabata kaɗai an samu ƙaruwar rikici da tashe-tashen hankali da suka kai ga raba kimanin mutum 20,000 daga muhallansu, a cewar MDD a ranar Talata.

    Wannan ya haifar da cikas wajen samar da cikakkiyar kariya ga 'yan gudun hijira da masu neman mafaka har ma da waɗanda ke ba su mafakar.

    Hukumar lura da ƙaurar jama'a da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗunkin Duniya, UNHCR, ta ce ta shaida ƙaruwar matsaloli da kashi 50 cikin 100 da suka haɗa da satar jama'a domin neman kuɗin fansa da rikicin cikin gida a kwana biyar da yin juyin mulkin a watan da ya gabata.

    "Dambarwar siyasa da ke ci gaba da faruwa da kuma rashin alamun sasantawa a kusa na ci gaba da haifar da barazana lura da yadda ake yawan samun yawaitar hare-hare daga ƙungiyoyi masu ɗaukar makamai, musamman a kan iyakokin ƙasashen Mali da Burkina Faso", kamar yadda Emmanuel Gignic, jakadan UNHCR a Nijar ya shaida wa manema labarai a birnin Geneva.

    Hukumar ta ce waɗanda rikicin ya shafa sun haɗa da 'yan Nijar 350,000, waɗanda tun asali rikicin cikin gida ya ɗaiɗaita su. A

    Akwai irin wannan adadin na masu neman mafaka da baƙi 'yan gudun hijira da suka fito daga maƙwabtan ƙasashe.

  9. An tono gawar limamin coci bayan shekara 3,000 da binne ta a Peru

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Hukumomi sun ce masu binciken kayan tarihi sun tono wani ƙabari da aka binne tsawon shekara 3,000 a arewacin kasar Peru.

    Masu binciken sun sanya wa mutumin da ke cikin ƙabarin laƙabi da "limamin coci na Pacopampa" saboda alaƙarsa da yankin da aka gano shi.

    Masu binciken sun ce sun tono toka gauraye da bakar ƙasa mai yawa kafin su iya kaiwa ga kwarangwal ɗin gawar, wanda ke dauke da hatimi biyu da wasu abubuwa na musamman.

    A cikin wata sanarwa da ma'aikatar al'adu ta Peru ta fitar ta ce waɗannan hatimai suna nuna cewa mutumin yana da matsayi na musamman.

    Aiki ne na haɗin gwiwa da ya haɗa da masana kimiyyar tarihi na cibiyar National Museum of Ethnology a Japan da kuma Jami'ar Ƙasa ta Peru.

  10. APC ta jefa al'ummar Najeriya cikin uƙuba - PDP

    ...

    Babbar jam`iyyar adawa a Najeriya, wato PDP ta zargi jam`iyyar APC mai mulki karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu da jefa al`ummar ƙasar cikin ukuba.

    Jam`iyyar ta zargi shugaba Tinubu da gazawa wajen inganta rayuwar `yan Najeriya ciki har da janye tallafin man fetur da karya darajar naira da kuma gazawa wajen shawo kan kalubalen da kasar ke fuskanta ta fuskar tabarbarewar tsaro, lamarin da ya jefa al`ummar ƙasar cikin kunci.

    A tattaunawarsa da BBC, mataimakin kakakin jam`iyyar PDP na kasa, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya ce lamarin ya jefa ƴan ƙasar fiye da mutum miliyan dari da hamsin cikin hali na yunwa a watanni biyun da suka wuce, wadda ta bayyana a matsayin sakamakon munanan manufofin gwamnatin shugaba Tinubu.

    Sai dai APC ta musanta wannan zargin tana mai cewa adawa ce kawai daga jam'iyyar PDP.

    Daraktan yada labarai na jam`iyyar APC, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa PDP ɗin ce ta jefe Najeriya a mawuyacin halin da ake ciki tun asali.

    Saurari cikakken rahoton a ƙasa:

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifika domin sauraron rahoto
  11. 'Raba mana gwangwanin shinkafa a matsayin tallafi raini ne'

  12. An kai mutum shida kotu game da kuɗi da 'zinaren' da aka kama a wani jirgi

    Treasure

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum 6 daga Zambia da kuma biyar daga Masar sun gurfana a gaban kotu.

    Hakan ya faru ne saboda wani bakon jirgin sama da ya sauka a Lusaka na dauke da zinare na jabu wanda nauyinsa ya haura kilogiram 100, kusan dala miliyan 6, da kuma makamai.

    Wani muhimmin jami'in 'yan sandan Zambia na cikin waɗanda aka kama, ana zarginsa da yin leken asiri.

    Akwai kuma wasu takardu daga kotun da suka ambaci tsohon sojan Masar da kuma wani dan kasuwa.

    Hukumomin Masar sun yi ikirarin cewa jirgin na mutum ne, kuma yana wucewa ne kawai ta Alkahira.

    Sun ƙara da cewa Idan aka same waɗanda aka kama da laifi, , za su iya shan dauri har na tsawon shekaru 30.

  13. Ƴan sanda sun kama fiye da mutum 100 bisa zargin auren luwaɗi

    ...

    Asalin hoton, DELTA POLICE COMMAND

    Bayanan hoto, ...

    Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta bayyana cewa ta kama wasu matasa fiye da 100 bisa zargin su da shirya shagulgulan auren 'yan luwaɗi da maɗigo a wani otal.

    Rundunar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X (Twitter), kuma ta ce nan ba da daɗewa ba za ta gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.

    Rahotanni sun nuna cewa tun bayan sanya hannu kan dokar hana luwaɗi da maɗigo a shekarar 2014, jami’an tsaro sun kama mutanen da ake kyautata zaton ‘yan luwadi ne tare da gurfanar da su gaban shari'a.

    A watan Disambar 2020, rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama mutum 10 da ake zargi da aikata luwadi a wani gidan karuwai.

    A shekarar 2018 kuma, 'yan sanda sun kama wasu maza 57 bisa zargin yin luwadi a otal.

    Haka zalika ma a watan Janairun 2022, an kama wasu mutane takwas da ake zargi su ma da yin luwadi da wani otal.

    Rahotanni dai sun ce dokar hana luwadi a shekarar 2014 ta tanadi daurin shekara 14, ga duk wanda aka samu da laifin yin jima'i da jinsi ɗaya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. An kashe sojan Faransa a Iraqi

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Fadar shugaban kasar Faransa ta bayyana cewa wani soja, Nicolas Mazire ya mutu yayin da yake gudanar da aikin yaki da ta'addanci a Iraƙi.

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya jajantawa iyalan sojan wanda shi ne sojan Faransa na uku da aka kashe a Iraƙi cikin wata guda.

    Macron ya jaddada aniyar kasarsa ta yaƙi da ta'addanci a Iraƙi.

    Kimanin sojojin Faransa 600 ne a halin yanzu suke a Iraki a matsayin wani bangare na kungiyar kasashen da ke aiki tare domin yakar kungiyar IS.

  15. 'An yanke wa tsohon malamin makaranta hukuncin kisa a Saudiyya'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta ce, kotun hukunta manyan laifuka ta kasar Saudiyya da aka fi sani da kotun yaki da ta'addanci ta yanke hukuncin kisa ga dan kasar Mohammed Al-Ghamdi sanadiyyar wasu abubuwan da ya wallafa a shafinsa na X da kuma ayyukansa a shafin YouTube, inda aka yi amfani da abubuwan da ya wallafa a matsayin shaida a kansa.

    Al-Ghamdi, wanda malami ne wanda ya yi ritaya kuma dan shekara 54, an yanke masa hukuncin kisan ne a ranar 10 ga watan Yuli.

    Takardun kotun da Human Rights Watch ta duba sun nuna cewa dalilin da ya sa aka yanke masa hukuncin kisa shi ne bisa kama shi da laifukan da suka shafi sarki ƙasar da kuma yarima mai jiran gado, kuma laifukan sun tsananta ne saboda kasancewar su a dandalin watsa labarai na duniya wanda ke bukatar hukunci mai tsanani.

    Joy Xia, mai bincike kan al'amuran Saudiyya a kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch, ta bayyana damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin wani sabon mataki mai ban tsoro a Saudiyya inda kotu za ta iya zartar da hukuncin kisa kawai saboda wallafa sako a dandanlin sada zumunta.

    Kawo yanzu dai babu wani martani daga gwamnatin Saudiyya dangane da wannan batu.

  16. An kashe mutum 10 a sabon faɗan da ya ɓarke a ƙasar Habasha

    ....

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ....

    Bayan kwashe tsawon mako guda cikin kwanciyar hankali, faɗa ya sake barkewa a wasu sassan yankin Amhara da ke fama da rikici a kasar Habasha, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula akalla 10.

    Mazauna birnin Debre Tabor na Amhara sun shaida wa BBC cewa an fara gwabza fada tsakanin mayakan sa kai da dakarun gwamnati a karshen mako kuma ya ci gaba har zuwa safiyar Litinin.

    Shaidu sun bayyana cewa an ɓarnata babban asibitin birnin sakamakon manyan bindigogi da aka harba.

    Wani likita a asibitin ya ambaci cewa daga cikin wadanda suka jikkata akwai akalla mutum biyar da suka ziyarci marasa lafiya da fararen hula sama da 20 da ke kusa.

    Kokarin da BBC ta yi na samun bayani daga hukumomin yankin da kuma wani kwamandan da ke kula da dokar ta baci na watanni shida bai yi nasara ba.

    Rahotanni sun kuma nuna cewa an gwabza fada a garuruwan Debre Markos da Fenote Selam da kewaye, da kuma wasu kananan garuruwa da kauyukan yankin.

    Tun a watan Afrilu ne rikici ya barke a yankin na Amhara, sakamakon yanke shawara mai cike da ce-ce-ku-ce ta rusa rundunar sojin yankin.

    A makon da ya gabata majalisar yankin Amhara ta nada sabon shugaban kasa bayan Yilkal Kefale wanda ya jagoranci yankin kusan shekaru biyu ya yi murabus.

    • An ceto jariran da rikicin Sudan ya ritsa da su a gidan marayu
    • Yaƙin Tigray: Ana zargin sojojin Eritrea da yi wa mata fyaɗe duk da yarjejeniyar zaman lafiya
  17. An mayar da ƴan Najeriya 298 gida daga gidajen yarin Libya

    ...

    Asalin hoton, NEMA

    Bayanan hoto, ...

    An mayar da ‘yan Najeriya 298 da suka makale a Libya gida a cikin jiragen haya daban-daban a farkon makon nan.

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta ce an mayar da su ne kai tsaye daga gidajen yarin Libya.

    Galibin waɗanda aka mayar da su dai mata ne da suka shafe lokaci mai tsawo a sansanonin tsare mutane daban-daban a ƙasar da ta arewacin Afirka, wadda ke fama da rikici.

    A cikin wadanda aka mayar gida akwai mata 119, wadanda yawancinsu suna da ciki, tare da yara mata uku da jarirai biyu, sai kuma maza 170, yara maza uku, da jariri namiji daya.

    Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) da Majalisar Dinkin Duniya (UN) ne suka dauki nauyin mayar da su gida a karkashin shirin bayar da Kariya da Taimakon bakin haure.

    • Abin da ya sa ba ma so mu koma gida — ‘Yan gudun hijira
  18. Shugaban gwamnatin sojin Sudan na ziyara a Masar

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Jami'ai a Sudan sun ce babban hafsan sojin ƙasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya bar kasar don ganawa da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi.

    Wannan ne karon farko da ya bar kasar tun bayan barkewar rikici a watan Afrilu tsakanin sojoji ƙasar da dakarun RSF.

    Shugaban Masar ya goyi bayan Janar Burhan a yaƙin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya tilasta wa 'yan Sudan fiye da miliyan hudu barin muhallansu.

    Janar Burhan dai ya kasance a cibiyar sojojin da ke birnin Khartoum har zuwa 'yan kwanaki kadan da suka gabata saboda rikicin da ƙasar ke fama da shi amma yanzu yana Masar, wanda hakan na iya nufin sojojin ba su da matsin lamba kamar da.

    Mai yiwuwa RSF mai hamayya da ita ta yi rauni a babban birnin kasar. Amma a Darfur kungiyar RSF tana da karfi kuma tana kai hare-hare masu nasaba da kabilanci.

    Da yawa daga cikin ƴan Sudan na fatan masu shiga tsakanin na bayan fage za su yi kokarin kawo karshen yakin ta hanyar tattaunawa.

    • Rikicin Sudan: Shugabanni sun ɗauki aniyar kawo ƙarshen rikici
  19. Tinubu ya zabtare yawan jami'an gwamnati da za su halarci taron MDD a Amurka

    ...

    Asalin hoton, TWITTER/@OFFICIALABAT

    Bayanan hoto, ...

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya zabtare yawan mutanen da za su halarci taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a Amurka.

    A ranar Litinin, shugaba Tinubu ya umarci ofishin jakadancin Najeriya a Amurka da kada su bai wa duk wani jami'in gwamnati izinin zuwa taron sai waɗanda kawai suke da alaka da taron, wanda za a yi watan Satumba mai shigowa.

    Haka kuma shugaban ya ce ofishin jakadancin Najeriya a birnin New York kada ya bai wa kowane jami'i izinin shiga taron sai wanda yake da takamaiman abin da zai yi a zauren.

    A wani sako da shugaban ya fityar, ya kuma umarci jami'an Najeriya da za asu halarci taron da su rage yawan masu taimaka musu da za su je da su wurin taron, idan kuma suka gaza yin hakan to su ma za a cire sunayensu daga cikin mahalarta.

    • Mun zaɓo ministoci ne bisa cancanta - Tinubu
    • COP 27 : Dalilin da ya sa yarjejeniyoyin da aka cimma kan sauyin yanayi ba su yi tasiri ba
  20. An rataye mutum uku da suka kai harin bam da ya kashe sama da mutum 300 a Iraƙi

    ...

    Asalin hoton, AFP VIA GETTY IMAGES

    Bayanan hoto, ...

    Kasar Iraƙi ta rataye wasu mutum uku da aka samu da hannu a harin bam da aka kai a birnin Bagadaza.

    Wannan harin bam ya faru ne a cikin shakarar 2016 a cikin watan azumi kuma ya kashe mutane sama da 300 tare da jikkata wasu da dama.

    Wannan dai shi ne harin bam mafi muni da aka kai a Iraki tun bayan mamayar da Amurka ta yi a shekara ta 2003.

    An aiwatar da hukuncin kisan ne a ranar Lahadi ko Litinin, in ji ofishin Firayim Minista Mohammed Shia al-Sudani.

    Amma dai ba a bayyana sunayen wadanda aka kashe ba.

    Firaministan ƙasar ya shaida wa iyalan wadanda abin ya shafa cewa an zartar da hukuncin kisa kan mutanen da ke da hannu a tashin bam din.

    • Jerin mutanen da ke jira a aiwatar musu da hukuncin kisa a Iran
    • Ana tuhumar mutum takwas da laifin tayar da gobarar da ta kashe 'yan ci-rani a Mexico