Majalisar Najeriya ta ƙi amincewa da buƙatar a saki Nnamdi Kanu

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Rabiatu Kabir Runka

  1. Ƙasar Singapore za ta zartar da hukuncin kisa karon farko cikin shekaru 20

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Kasar Singapore za ta yanke hukuncin kisa a kan wata mata a karon farko cikin shekaru kusan 20, in ji masu rajin kare haƘƘin bil adama.

    An samu ƴar kasar Singapore Saridewi Djamani mai shekaru 45 da laifin safarar gram 30 na tabar heroin a shekarar 2018.

    Ita ce mutum ta biyu da aka yanke wa hukuncin kisa da za a zaRtar a cikin kwanaki uku masu zuwa.

    A karkashin dokar Singapore, ana iya zartar da hukuncin kisa idan nauyin tabar heroin ya fi gram 15 kuma wiwi ya fi gram 500.

    Ƙasar Singapore tana da wasu tsauraran dokokin yaki da mIyagun kwayoyi a duniya, waɗanda ta ce sun zama wajibi don kare al'umma.

  2. MDD ta yi Allah-wadai da juyin mulki a Nijar

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres "ya yi kakkausar suka ga sauyin gwamnati da aka samu a Nijar ba bisa ka'ida ba," in ji kakakinsa a ranar Laraba.

    Hakan na zuwa ne bayan da sojojin Nijar din suka sanar da juyin mulki a gidan talabijin na kasar, inda suka ce sun jingine aiki da kundin tsarin mulkin kasar, tare da dakatar da dukkan hukumomi da kuma rufe iyakokin ƙasar.

    Mista Guterres ya ce ya damu matuka da tsare Shugaba Mohamed Bazoum kuma ya damu da lafiyarsa, in ji kakakinsa Stephane Dujarric a cikin wata sanarwa.

    Mista Dujarric ya ƙara da cewa "Sakatare-Janar ɗin ya yi kira da a gaggauta kawo karshen duk wasu ayyukan da ke kawo cikas ga tsarin dimokuradiyya a Nijar."

  3. Australiya 1 - 1 Najeriya: An tafi hutun rabin lokaci ana kunnen-doki

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Yanzu haka an tafi hutun rabin lokaci a karawar da ake yi tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya da mai masaukin baƙi Australiya a gasar cin kofin duniya ta mata da ake fafatawa.

    An tafi hutun ne ana kunnen-doki, inda Australiya ta zura ƙwallo ɗaya ita ma Najeriya ta zura ɗaya.

    Ƴar wasa Emily van Egmond ce ta zura ƙwallo a ragar Najeriya a minti 42 da fara wasa, yayin da Najeriya ta zura tata ƙwallon ta ƙafar Uchenna Kanu bayan ƙarin lokaci.

    Ƴan wasan Australiya na murnar ƙwallon da suka zura

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafin hakan dukkanin ɓangaririn biyu sun rinƙa kai wa juna kora.

    Alƙaluma sun nuna cewa Australiya ce ta fi shafa ƙwallo da kashi 60% yayin da Najeriya ke da kashi 40%.

    Ƴan wasan Najeriya na murnar ƙwallon da suka ci

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Putin zai karɓi baƙuncin shugabannin Afirka

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Shugaba Putin zai karɓi baƙuncin shugabannin Afirka a wani taro na musamman da za a yi a birnin St Petersburg anjima.

    Sai dai kadan ne daga cikinsu za su halarci taron saboda wani bangare na damuwa game da mamayar da Moscow ta yi wa Ukraine da kuma matakin da ta dauka na ficewa daga yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta kulla na bayar da damar shigar da hatsi cikin aminci daga tashoshin jiragen ruwa na kudancin Ukraine.

    Kasancewar samar da abinci ya zama babban abin damuwa bayan mamayar Rasha, yarjejeniyar ta taimaka wajen daidaita farashin abinci a duniya.

    Taron farko na Rasha da Afirka a shekarar 2019 ya samu halartar shugabanni 43, a wannan karo 17 ne ake sa ran za su halarta.

    • Wace nasara shugabannin Afirka suka cimma a ziyarar sasanta Ukraine da Rasha?
    • Shugaba Putin ya ce hare-haren martanin Ukraine ba sa nasara a kan Rasha
  5. Za mu kare nasarorin da aka yi gwagwarmayar cimmawa - Bazoum

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Shugaban ƙasar Nijar, Mohamed Bazoum, wanda aka hambarar da gwamnatinsa a wani juyin mulkin da sojoji suka yi, ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa za a kare nasarorin da kasar ta samu.

    Ministan harkokin waje Hassoumi Massoudou ya yi kira ga al'ummar kasar da su yi adawa da kwace ikon da sojoji suka yi.

    Wasu gungun jami’an soji ne suka sanar da juyin mulkin a gidan talabijin na kasar a ranar Laraba da yamma tare da dakatar da dukkan hukumomin gwamnati.

    An dai yi Allah-wadai da juyin mulkin a wajen kasar amma abin da ba a bayyana ba shi ne yadda lamarin zai kasance a Nijar.

    • Duniya na Allah-wadai da yunƙurin juyin mulki a Nijar
  6. Ayyukan ɓangaren kiwon lafiya sun shiga halin ha'ula'i a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Yajin aikin da kungiyar likitocin Najeriya NARD ta fara a ranar Laraba ya saka harkokin kiwon lafiya a cibiyoyin jama'a a fadin kasar cikin halin ha'ula'i.

    Hakan ya zo ne a daidai lokacin da shugaban kungiyar likitocin Dr Orji Emeka Innocent ya shaida wa BBC cewa mambobinsa sun bi duk hanyoyin da suka dace a ƙoƙarinsu na ganin an warware rikicin.

    A asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke jihar Kano, an umarci mutane su mayar da ‘yan uwansu marasa lafiya gida saboda babu likita da zai duba su.

    Wata da lamarin ya shafa maio suna Khadijah Hassan ta shaida wa BBC cewa ta kai mijinta da ya yi hatsarin mota zuwa asibitin da tsakar daren Laraba amma likitoci suka ki zuwa duba shi.

    Al’amarin Khadijah bai bambanta da na Ishiaku Musa ba, wanda ya kai kankansa asibitin daga jihar Yobe saboda ciwon kai da yake fama da shi. Ya shaida wa BBC cewa an ba su takardun magani zu je su siya sai aka ce su fice saboda yajin aikin.

    A Legas kuma, likitoci na ci gaba da kula da majinyatan da aka kwantar da su amma ba su karban sabbin marasa lafiya.

    Likitoci masu neman ƙwarewa wadanda ke da kaso mafi tsoka na likitoci a manyan asibitocin Najeriya, sun ce suna yajin aiki har sai gwamnati ta biya musu bukatunsu na albashi da walwala.

    • Yadda yajin aikin likitoci masu neman kwarewa ya yi tasiri a asibitocin Najeriya
  7. Sabuwar gobarar daji ta ɓarke a ƙasar Girka

    ...

    Asalin hoton, SPYROS BAKALIS / AFP

    Bayanan hoto, ...

    An bai wa al'umma umarnin ficewa daga yankunan da ke kusa da wasu garuruwa biyu na tsakiyar ƙasar Girka da ke fuskantar barazanar ɓarkewar wata sabuwar gobarar daji.

    An gaya wa 'yan ƙasar a yankunan Volos da Lamia da su koma wurin da ya fi kwanciyar hankali yayin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsanancin zafi.

    A halin da ake ciki dai ana ci gaba da samun gobara a tsibirin Rhodes da Corfu da kuma Evia.

    Kasar Girka na daya daga cikin kasashen da a halin yanzu ke fama da gobarar daji, inda sama da mutane 40 suka mutu.

    Mutane biyu ne suka mutu sakamakon sabuwar gobarar daji da ta tashi a kusa da Volos, kamar yadda hukumar kashe gobara ta tabbatar - wani manomi da ya mutu bayan da ya je ya sako tumakinsa domin ya kare su, da wata mata da ke cikin wani gida a Chorostasi.

    Kostas Agorastos, magajin garin Thessaly na ƙasar Girka, wanda ya hada da Volos, ya zargi wasu ma'aikata da tayar da gobarar, a cewar tashar labarai ta Ellada 24.

    • Jiya da yau: Bala'in gobarar dajin da ke addabar duniya
  8. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na kai tsaya a bbc hausa barkan mu da war haka.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a wannan safiya ta Alhamis domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

    Za ku iya lekawa sauran shafukan mu don samun ƙarin labarai.

    Ku biyo mu.