Bankwana
Masu bibiyar mu a wannan shafi, ƙarshen rahotannin ke nan a yau Alhamis.
Sai kuma gobe da safe za ku samu ƙarin rahotanni da suka shafi rayuwarku daga sassan duniya.
Badamasi Abdulkadir Mukhtar ne ke maku fatan kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
A'isha Babangida and Rabiatu Kabir Runka
Masu bibiyar mu a wannan shafi, ƙarshen rahotannin ke nan a yau Alhamis.
Sai kuma gobe da safe za ku samu ƙarin rahotanni da suka shafi rayuwarku daga sassan duniya.
Badamasi Abdulkadir Mukhtar ne ke maku fatan kwana lafiya.

Gwamna Uba Sani na jihar Kadunar Najeriya ya gargaɗi sabbin kwamishinoni 14 da ya rantsar kan buƙatar gujewa rayuwar bushasha.
Gwamnan ya kuma ƙaddamar da gidauniyar tallafawa masu ƙaramin ƙarfi a cikin al'umma.
Da yake rantsar da sabbin kwamishinonin, gwamnan ya ce yanzu gwamnatinsa ta haɗa abokan aikinta kuma ta yi aniyar kawo sassauci ga jama'ar jihar, musamman masu ƙaramin ƙarfi.
Uba Sani yanzu lokaci ne na ƙara ɗaura ɗamara kuma “Dole mu ɗauki matakan rage kashe kuɗi wajen tafiyar da gwamnati , dole ne mu ƴan siyasa mu nuna wa jama'ar mu irin rayuwar da ya kamata kowa ya yi ta sadaukarwa don ci gaban ƙasa”

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da wasu matakai da za su taimakawa Amurkawa a wannan lokaci da matsanancin yanayin zafi ya addabi yankuna da dama na ƙasar.
Biranen Boston da Philadelphia da kuma Washington DC sun sanar da dokar ta ɓaci a ranar Alhamis.
Gwamnati ta kuma bayyana cewar a shirye ta ke ta samar da mafita ga ma'aikata musamman waɗanda suke aiki a fili.
Birnin Phoenix, a Arizona ya kwashe kwanki 27 a jere cikin yanayin zafin sama da maki 43 a ma'aunin celsius.
Mr Biden ya ce matakan da za a ɗauka za su mayar da hankali wajen bayar da kariya ga mutanen da suka fi buƙata. .

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Mauritnia sun zargi wata ɗaluba da aikata saɓo ta hanyar cin mutumcin addini, a cikin jarrabawar da ta rubuta.
An kama matashiyar ne a makon da ya gabata kan zargin nuna rashin ɗa'a ga Annabi Muhammad (S.A.W)
Idan dai aka same ta da laifi, za ta fuskanci hukuncin kisa ba tare da tanadin ɗaukaka ƙara ba.
Mauritania ta ƙarfafa tanadin hukunci kan laifin saɓo a ƙasar a shekarun nan, inda ta soke tanadin tsallake hukuncin kisa ga wanda ya nuna nadama bayan an kama shi da laifin aikata saɓo.
Amma duk hakan, shekara 30 kenan ba a taɓa zartar da hukuncin kisa ba a ƙasar.
Kamfanin dillacin labarai na AFP ya ruwaito cewa an kama ɗalubar ne a ranar 18 ga watan Yuli a garin Atar dake arewa maso yammacin ƙasar abisa zargin rashin mutumta Annabi da kuma amfani da kafar sada zumunta wajen cin mutumcin addinin Islama.
Babu dai cikakken bayani kan furucin da ta yi.
Daga baya dai iyalan ɗalubar sun fitar da wata sanarwa inda suka nemi gafara kan abin da ta aikata, sun kuma bayyana cewa tana fama da matsalar taɓin hankali.

Asalin hoton, Reuters
Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da ƙudirin Sanatocin yankin kudu maso gabas na neman a saki Nnamdi Kanu shugaban ƙungiyar ƴan a ware ta Biafra (IPOB).
Sanatan Imo ta Yamma, Osita Izunaso, wanda ya gabatar da ƙudirin, ya ce sakin Kanu zai kawo Ƙarshen umarnin zama a gida da ‘yan bindiga ke aiwatarwa a yankin.
"Lokacin da aka tilasta wa mutane zama a gida da kuma rufe kasuwanci, raguwar kayan aiki da raguwar samun kuɗin shiga, yana shafar rayuwa da ci gaban tattalin arziki," in ji shi.
Sai dai majalisar ta ƙi amincewa da roƙon da ɗan majalisar ya yi, inda a maimakon haka ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da kama waɗanda suka aiwatar da wannan umarni.
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suna aiwatar da umarnin zama a gida duk ranar Litinin tun watan Agustan 2021 duk da cewa IPOB ta nisanta kanta da su.
Tun a watan Yunin 2021 ake tsare da Mista Kanu bayan da kotu ta yi watsi da tuhumar da ake masa kan ta'addanci a watan Oktoban 2022.

Asalin hoton, Reuters
Lauyoyin tsohon shugaban Amurka Donald Trump sun gana da masu gabatar da ƙara na tarayya a yau, lamarin da ke ƙara nuni da shirin gurfanar da shi kan zargin neman murɗe sakamakon zaɓen shigaban ƙasar na 2020.
Kafafen yaɗa labaran Amurka sun ruwaito cewa lauyoyin Mr Trump, John Lauro da Todd Blanche sun gana da mai gabatar da kara na musamman, Jack Smith a ofishinsa dake Washington DC.
Babu dai tabbacin abin da suka tattauna a lokacin taron.
Irin wannan ganawa ta lauyoyi da mai gabatar da ƙara kafin shiga kotu, ba sabon al'amari bane.
A farkon watan nan tsohon shugaban ƙasar ya ce ofishin Jack Smith ya shaida mashi cewa za a gurfanar da shi a kan zargin ya yi yunƙurin murɗe sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.
A cikin watan Yuni ma, tawagar Mr Smith ta gurfanar da Mr Trump a kan zargin ɓoye takardun bayanan sirri.
Shi dai Mr Trump ya sha fitowa ya musanta zargin da ake masa.
Ƙungiyar tarayyar turai, EU ta ce shugaba Vladimir Putin yana ƙoƙarin yaudarar ƙasashen Afirka da alƙawarin kyautar hatsi da ya yi masu.
Kakakin EU, Nabila Massrali ta ce Rasha ba zata cika alƙawarin da ta yi ba, kamar yadda tarihi ya nuna ta saba yi.
Tun da farko a wajen taron Rasha da ƙasashen Afirka, shugaba Putin ya ce zai tura wa ƙasashen Afirka kyautar dubban tan ɗin hatsi a cikin watanni masu zuwa.
Ya ce yana kokari ne don kaucewa samun ''Karancin abinci a duniya''
Kwanan nan Rasha ta fice daga yarjejeniyar fiton abinci ta tekun Bahar Aswad, lamarin da ya janyo fargaba.

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikar yaɗa labaran Zimbabwe ta ce shugaban Rasha Vladimir Putin ya bai wa takwaransa na Zimbabwen kyautar helikwafta.
Shugaba Emmerson Mnangagwa yana halartar taron bunkasa alaƙa tsakanin Rasah da ƙasashen Afirka a birnin St Petersburg tare da sauran shugabannin nahiyar, kuma sanarwar da ma'aikatar yada labaran ta fitar ta ce za a kawo jirgin nan ba da jimaa ba.
Rasha ta kuma yi alƙawarin bayar da hatsi kyauta ga Zimbabwe da wasu ƙasashen Afirka biyar.
Zimbabwe ta daɗe tana ɗasawa da Rasha, tun lokacin da ƙasar ta yi gwagwarmayar neman ynaci daga tsirarun fararen fata da suka mulke ta.
Tana daga cikin ƙasashen Afirka da suka tsaya a matsayin ƴan ba-ruwanmu, a kan yaƙin Ukraine, kuma suka ƙi yin Allah-wadai da kutsen da Rashar ta yi wa Ukraine.

Asalin hoton, AFP
Wata babbar kotu a Abuja ta yi watsi da buƙatar da hukumar DSS ta gabatar mata mai neman izinin ci gaba da tsare dakataccen babban bankin Najeriya, Godwin Emefile da kwanaki 14 a bisa ƙarin shaidun da tace ta tattara a kan shi.
Mai shari'a Hamza Muazu ya yi wasi da ƙarar, yana kafa hujja da saɓawa zaman kotu, tare da bayyana cewa kotun bata da hurumin sauraron buƙatar.
A ranar Talata, an samu jayayya tsakanin jami'an DSS da na hukumar kula da gidan gyaran hali ta Najeriya a kan wanda zai ci gaba da tsare Mr Emefiele bayan kotu ta bayar da belinsa.
DSS ta yi Allah-wadai da lamarin, kuma ta sha alwashin gudanar da bincike a kai.
Ita dai DSS tana zargin Mr Emefiele, mai shekaru 61 ne da laifin mallakar bindiga da harsashi ba bisa ƙa'ida ba, zargin da kuma ya musanta.
Za a ci gaba da shari'arsa ne a ranar 14 ga watan Nuwamba.

Asalin hoton, NLC
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi kira ga kungiyoyin kwadago da su kara ba shi lokaci don duba koke-kokensu kafin fara yajin aikin da suke shiryawa ta fadin kasar.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da alamu ke nuna cewa Gwamnatin Tarayya na iya aiwatar da umarnin kotu na hana kungiyoyin kwadagon shiga yajin aikin saboda janye tallafin man fetur a watan Mayu idan har kungiyar ta tabbatar da barazanar fara yajin aiki a ranar 2 ga watan Agusta.
Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, ya bayyana rokon da Tinubu ya yi ga menema labarai a fadar gwamnatin jihar bayan da ya jagoranci wasu jami’an majalisar domin su yi wa shugaban kasa bayanin sakamakon zaman da suka yi da kungiyar Likitoci ta kasa, wadda ta shelanta yajin aikin a fadin kasar.
Abbas ya ce, Tinubu ya roki cewa kasancewar sa sabo a kan muƙamin, yana bukatar lokaci domin tantance batutuwan da ma’aikata suka gabatar a kai wanda har yanzu ba a yi masa bayani ba.
“Har yanzu Tinubu sabo ne a muƙaminsa. Mun roƙe su don Allah su ba shi lokaci kadan."
"Abubuwan da ƴan ƙungiyar suka ambata, bai san su ba, har yanzu ba a yi masa bayanin duk wadannan batutuwa ba."
"An karkatar da hankali ne sosai kan yadda za a hanzarta bin diddigin ayyukan da za su kawo taimako, musamman a kan jigilar jama'a, da rage tashin farashin sufuri."
A ranar Larabar da ta gabata ne ƙungiyar ƙwadago ta bayyana shirin fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai daga 2 ga watan Agustan 2023.

Ɗaruruwan mutane sun yi cincirindo a gaban ginin majalisar ƙasar da ke Yamai, domin nuna goyon baya ga sojoji.
Masu zanga-zangar sun buƙaci Rasha ta kawo masu ɗauki, tare da roƙon dakarun tsaron Faransa da su janye daga ƙasar.
Wasu masu zanga-zangar na ɗauke da tutar Rasha. Sai dai har yanzu babu wata alama da ke nuna wani yunƙurin shiga tsakani da Rasha ta yi.
Masu zanga-zangar sun cinna wa ofishin jami'iyar PNDS Tarayya wuta, wadda kuma ita ce jam'iyar hamɓarraen shugaban ƙasar.

An jinkirta zanga-zangar nuna goyon bayan ga sojoji ne sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka tabka a Yamai din.
Ra'ayoyin ƴan ƙasar ya banbanta, inda wasu ke ganin juyin mulkin abu ne marar kyau, wasu kuma na ganin matakin ya yi daidai.
A ranar Laraba, ɗaruruwan magoya bayan shugaba Mohamed Bazoum, sun yi zanga-zangar adawa da matakin sojin ƙasar, sai dai dakarun tsaro sun tarwatsa su da harbin bindiga.
Magoya bayan shugaba Bazoum sun ce ba za su amince da juyin mulkin ba, sai dai babu tabbacin hanyar da za su bi wajen adawa da juyin mulkin.
Rundunar sojin Nijar ta goyi bayan juyin mulkin da sojoji suka sanar a gidan talabijin na ƙasar, inda hakan ke nuna haɗin kai tsakanin dukkan rundunonin tsaron ƙasar.
Sai dai har yanzu babu tabbacin wanda zai jagoranci gwamnatin sojin.


Asalin hoton, EPA
Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayyana aniyar matakinsa na tura wa ƙasashen Afrika shida hatsi kyauta.
Putin ya bayyana hakan ne a wajen taron Rasha da ƙasashen Afrika da ke gudana a birnin St Petersburg.
A wajen taron, shugaba Putin ya ce nan da wasu ƴan watanni masu zuwa ne za su fara tura hatsin kyauta.
Hakan na faruwa ne bayan Rasha ta fice daga yarjejeniyar shiga tsakanin ta Ukraine ta Majalisar Dinkin Duniya.
Putin Ya ce a shirye Rasha take da cike duk wani giɓin hatsi da Ukraine ta haifar.
Ya ce kuma ƙara da cewa, a shirye Rasha take wajen samar da hatsi ga ƙasashen Afrika shida a cikin watanni uku zuwa huɗu masu zuwa.
Ya ce, "watanni uku zuwa huɗu masu zuwa, Rasha za ta tura wa kowace ƙasa tan dubu 25 zuwa dubu 50 na hatsi.
Ƙasashen su ne, Burkina Faso,da Zimbabwe,da Mali,da Somalia, da kuma Afrika ta tsakiya, sai ƙasar Eritrea.
Putin ya ce "Za kuma mu tabbatar an tura hastin kyauta ba tare da biyan koda kuɗin dako ba."
Rundunar sojin Nijar ta goyi bayan juyin mulkin da sojoji suka sanar a gidan talabijin na ƙasar, inda suka tabbatar da hamɓarar da gwamnatin farar hula ta Shugaba Mohammed Bazoum.
Shugaban dakarun ƙasa na kasar ya ce sun goyi bayan juyin mulkin ne saboda guje wa rikici tsakanin rundunonin tsaron ƙasar.
Goyon bayan na sojoji ga masu juyin mulkin na ƙara tabbatar da juyin mulkin.
Sojan da ya jagoranci juyin mulkin, Kanal Amadou Abdramane, ya rushe dukkan shugabannin siyasa.
Yanzu dai sojoji ne ke riƙe da shugabancin ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da kuma Chadi, sai kuma Sudan da yanzu haka ake rikici a ƙasar tsakanin dakarun soji da dakarun RSF.
Akwai yiyuwar ƙawayen Nijar da suka haɗa da Amurka, su mayar da hankali wajen ganin komai ya daidai ta a ƙasar.

Asalin hoton, PRESIDENCY
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godwill Akpabio ya tabbatar da cewa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da sunayen mutum 28 da yake neman a tantance domin naɗawa a muƙaman minista.
Sunayen da shugaban majalisar ya karanta su ne:

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar mata a gasar cin kofin duniya ta mata (Super Falcons) sun yi nasara a karawar da suka yi da Australiya, mai masaukin baƙi.
Najeriyar ta samu nasarar ce bayan ta zura wa Australiya ƙwallo uku, yayin da ƴan wasan na Australiya suka zura ƙwallo biyu.
Wasu daga cikin ƴan wasan na Najeriya sun ɓare da kukan murna bayan da lafari ta hura usur na kammala wasan.
Ƴar wasan Australiya Emily van Egmond ce ta fara zura ƙwallo a 45 bayan fara wasa.
Yayin da Uchenna Kanu ta farke wa Najeriya bayan ƙarin lokaci gab da tafiya hutun rabin lokaci.
Bayan dawowa hutun lokaci ƴan wasan Najeriya Osinachi Ohale ta zura ƙwallon Najeriya ta biyu a minti na 65.
Daga nan sai Asisat Ohoala ta cike wa Najeriya ƙwallo ta uku a minti na 72.
Sai dai gab da tashi wasan, a cikin ƙarin lokaci ƴar wasa Alanna Kennedy ta zura ƙwallo a ragar Najeriya.
Hakan ya san an tashi wasa Australiya na da ƙwallo biyu yayin da Najeriya ke da uku.
Asisat Oshoala ta ci ƙwallon a minti na 72.

Titunan birnin Yamai na ƙasar Nijar, sun yi fayau, babu zirga-zirgar mutane da ababen hawa, tun bayan sanar da juyin mulkin da sojin ƙasar suka yi cikin daren da ya gabata.
Ana cikin hali na rashin tabbas.
Tun farko dakarun tsaro sun rufe dukkan hanyoyin shiga fadar shugaban ƙasar da ke Yamai a ranar laraba.
A ƴan kwanakin nan ƙasashen yammacin Afrika na fama da boren sojoji.
Rasheedat Ajibade ta ci kwallon a minti na 65

Asalin hoton, Getty Images