Bankwana
Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye da muka shafe tsawon yinin yau muna kawo muku.
Sai kuma gobe Talata - idan Allah ya kai mu.
Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
A'isha Babangida, Rabiatu Kabir Runka and Ahmad Tijjani Bawage
Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye da muka shafe tsawon yinin yau muna kawo muku.
Sai kuma gobe Talata - idan Allah ya kai mu.
Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, METROPOLITAN POLICE
Wata kotu a birnin Landan ta umarci lauyan tsohon gwamnan jihar Delta ya biya kusan dala miliyan talatin da shida saboda ya taimaka masa wajen ɓoye kuɗaɗe.
Kotun ta samu Bhadresh Gohil ne a shekara ta 2010 da laifin karkatar da kuɗaɗe da ke da nasaba da rawar da ya taka wajen taimakawa tsohon gwamnan jihar Delta mai arzikin mai, James Ibori da aka yanke wa hukuncin ɓoye kuɗaɗen da aka samu daga aikata laifuka.
A makon da ya gabata ne wata kotu ta umarci Mista Ibori da ya biya dala miliyan ɗari da talatin na kuɗaɗen da ya sata. Mista Ibori wanda aka sake a shekarar 2016 ya ce zai ɗaukaka kara.
Landan ya yi ƙaurin suna a matsayin cibiyar halasta kuɗin haram. Sai dai ba kasafai kotu ke samun waɗanda ake zargi da laifi ba. Ko da yake akwai batun James Ibori, tsohon gwamnan jihar Delta mai arzikin man fetur da ya sayi kadarori da motoci na miliyoyin daloli a Landan.
Tuni dai shi da lauyansa Bhadresh Gohil suka yi zaman gidan yari a Birtaniya bisa samun su da laifin halatta kuɗin haram. .
Yanzu dai kotunan sun umarce su da su biya miliyoyin kuɗi ko kuma su fuskanci ƙarin ɗauri.
Idan suka miƙa kuɗin kamar yadda kotu ta bayar da umarni – to ya kamata a yi amfani da su wajen samar da ababen more rayuwa a Najeriya.
Akwai yiwuwar cewa idan aka dawo da kuɗin, za su iya shiga cikin aljihun wasu 'yan siyasa a matsayin satar ganima.

Asalin hoton, NATIONAL ASSEMBLY
Majalisar wakilan Najeriya ta goma ta ce za ta sanya batun bunkasa al`umma ta ɓangaren tattalin arziki a cikin manyan manufofinta.
Majalisar ta haɗa manufofin nata ne ta hanyar tattara ra`ayoyi daga `yan majalisar da kuma kwararru.
Majalisar ta ce ta lura da cewa hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka…wanda shi ne ya sa 'yan majalisar da kuma masana daga ɓangarori daban-daban suka haɗu suka kuma dukufa wajen yi wa tafiyar majalisar tsari da daidaita mata manufofi ta yadda za ta yi nasarar cimma su.
A taron, 'yan majalisa da kwararru sun ba da gudummuwa wajen zayyana fannoni daban-daban dangane da ginshikan da ya kamata a gina manufofin majalisar a kan su, inda wasu daga ciki suka bayyana cewa yawan dogaron da Najeriya ta yi a kan man fetur wajen samun kuɗin shigarta, ya wargaza wa ƙasar lissafi, don haka ta na bukatar laluɓo hanyoyi don bunksa tattalin arziki domin gina rayuwar al`umma.
Sun jaddada cewa da wuya a samu kowane irin ci gaba, sai da zaman lafiya, kuma matsalar taɓarɓarewar tsaro na cikin manyan matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
Ginshikai shida ne dai majalisar wakilan ta goma ta yi anniyar gina manufofin nata a kan su, amma kuma suna da 'ya'ya, sun haɗa da bunkasa tattalin arzikin al`umma da faɗaɗa shi, da samar da abubuwan more rayuwa da bunkasa ilimi da lafiya da yin tsari ta yadda gwamnati za ta din ga tafiyar da harkokinta ba wani nuku-nuku.
Ƙasar Chadi ta fara shirin gudanar da zaɓen jin ra'ayin jama'ar ƙasar, da ake sa ran aiwatarwa a ranar 17 ga watan Disamba mai zuwa.
Za a kuri'a a zaben ne da nufin samar da wani sabon tsarin mulki da zai mayar da kasar ga mulkin farar hula.
A yau Litinin ne gwamnatin ƙasar ta kaddamar da wani shiri na bitar kundin sunayen masu zaɓe daga bayanan masu kada kuri'ar da aka tattara a shekara ta 2021.
Za a fara kashin farko na wannan aiki ne daga ranar Litinin zuwa ranar 7 ga watan Agusta, a yankuna bakwai da suka fi yawan jama'a a ƙasar.
Yau ne hukumomin kasar Cadi suka fara aikin rajistar masu zabe a garin Sarh, babban birnin yankin Moyen Chari, daya daga cikin yankuna 23 na kasar.
Wata tawaga da ta kunshi minista mai kula da sha'anin mulkin yankin, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin ƙasa baki ɗaya na shirya zaɓen raba-gardamar, da sauran jami'an gwamnati, sun hallara don kaddamar da fara aikin rajistar.
Kashin farko na aikin rajistar zai ɗauki tsawon kwanaki 15 ana yin sa, daga nan za a yi wasu kwanaki 16 ana aikin a sauran yankuna 16, tun daga karshen watan Agusta har zuwa farko watan Satumban da ke tafe.
Ana sa ran za a wallafa sabon kundin sunayen masu kaɗa kuri'ar ne a ranar 12 ga watan Nuwamba, wanda hakan zai buɗe fagen hada-hadar yakin neman zaɓe.
A ranar 26 ga watan Disamba mai zuwa ne kuma za a bayyana sakamakon zaɓen jin ra'ayin jama'ar.
Cikin watan Yuni ne mafi rinjayen 'yan majalisar gwamnatin rikon kwarya ta ƙasar Chadi suka amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar, wanda aka so yin amfani da shi a mayar da ƙasar bisa turbar tsarin mulkin dimokuraɗiyya, amma kuma sai kakkaifan saɓanin ra'ayi ya kunno kai tsakanin jami'an gwamnatin da 'yan hamayya da kuma kungiyoyin farar hula game da shi.

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta bai wa Al-Hilal ta Saudiyya damar tattaunawa da ɗan wasanta Kylian Mbappe kan yiwuwar saye shi kan £259m
Ɗan wasan mai shekara 24, wanda ke da sauran kaka ɗaya a kwantaraginsa da PSG ya ƙi sanya hannu kan sabon kwantaragi, kuma ba ya cikin tawagar ƙungiyar da za ta buga wasannin sada zumunta gabanin fara kaka mai shigowa.
PSG na son ta sayar da Mbappe a yanzu a maimakon barin sa ya tafi a kyauta a baɗi.
Tafiyar ɗan wasa Neymar daga Barcelona zuwa PSG kan kuɗi fan miliyan 200 ita ce cinikin ɗan wasa mafi tsada a tarihi ya zuwa yanzu.

Asalin hoton, Rufa'i Sani Hanga/Facebook
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a jihar Kano ta kori ƙarar da APC ta shigar don ƙalubalantar Sanata Rufa'i Sani Hanga a matsayin wanda ya lashe zaɓen sanatan Kano ta tsakiya.
Abdussalam Abdulkarim da aka fi sani da AA Zaura na jam'iyyar APC ne, ya shigar da ƙarar saboda dalilai da dama ciki har da cewa ba a tura sunan Sanata Rufa’i Sani Hanga zuwa hukumar zaɓe a kan lokaci ba, don haka ya nemi kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.
Sai dai, alƙalin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen, Mai shari'a I.P Chima ya ce bayan nazari kan abubuwan da suka faru tun lokacin da aka fara shari'ar, zuwa yanzu, kotun ta yanke hukuncin korar ƙarar tare da tabbatar da Sanata Rufa'i Hanga a matsayin wanda yayi nasara a zaben.
Mai shari'a Chima ya ce wanda yake ƙara ya gaza tabbatar da hujjojin da ke nuna cewa Sanata Rufa’I Sani Hanga bai shiga zaɓen sanatan Kano ta tsakiya ba, la’akari da hukuncin Kotun Ƙoli da ya ce jam’iyyar NNPP tana da ikon sauya ɗan takara bayan da Malam Ibrahim Shekarau ya ajiye takararsa a jam'iyyar.
Lauyan jam’iyyar APC a Kano, Barista Abdullahi Adamu Fagge ya ce za su yi nazari kan hukuncin ciki da wajensa kafin su san matakin da za su ɗauka a gaba.

Asalin hoton, Getty Images
Aljeriya ta ce mutum 15 ne suka mutu sakamakon ɓarkewar gobarar daji yayin da ake ci gaba da fuskantar tsananin zafi.
Mutanen sun mutu ne a lardunan Bejala da Bouria da ke kan tsaunuka, inda masu kashe gobara sama da 7,000 ke can suna ƙoƙarin shawo kan wutar.
Zuwa yanzu, an kwashe mutane sama da 1,500 daga yankin.
Hukumar lura da yanayi ta ƙasar ta yi gargaɗin cewa za a ci gaba da samun yanayi da zai kai maki 48 na ma'unin celsius har zuwa karshen wata a yankin arewacin ƙasar.
Hakan ya biyo bayan fuskantar tsananin zafi a faɗin Afrika - wanda ya kai maki 50 a wasu yankuna.
Rahotanni sun bayyana cewa buƙatar wutar lantarki a cikin mutanen Aljeriya ya kai kololuwa da ba a taɓa ganin irinsa ba a tari, tun da aka fara smaun tsananin zafi.

Asalin hoton, Atiku Abubakar/Twitter
Ƴan sanda sun kama wasu mutane guda huɗu da ake zargin suna yunƙurin kai hari ga gidan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar a birnin Yola.
An fara kama ɗaya daga cikin mutanen ne mai suna Jubrila Mohammed, wanda ya amsa cewa shi mamba ne a kungiyar Boko Haram lokacin da suke yunkurin kai harin da misalin karfe 9 na dare ranar Lahadi.
Wata sanarwa da mai taimaka wa tsohon mataimakin shugaban ƙasar Abdul Rasheed Shehu ya fitar, ta ce an kuma samu nasarar kama abokan haɗin bakinsa guda uku.
Sanarwar ta kara da cewa mutanen da ake zargin sun kuma yi yunkurin kai wa kamfanoni masu alaƙa da Atiku Abubakar a Yola da kuma wasu wurare kafin a kama su.
Zuwa yanzu, an miƙa dukkan mutanen da ake zargi hannun sojoji in ji sanarwar domin ci gaba da bincike.

Asalin hoton, Getty Images
Jami`an hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Ɗuniya na wani taro a birnin Rome na ƙasar Italiya don nazarin yadda aka aiwatar da kudurce-kudurcen da aka cimma a baya.
Kazalika suna duba irin cikas ɗin da annobar korona ta yi a shekara ta 2020 da matakan da suka dace a ɗauka don cike giɓin da aka samu wajen samar da abinci a duniya.
Babban jami`in hukumar a Najeriya, Dakta Abubakar Sulaiman wanda ke halartar taron, ya ce taron ya cimma matsaya kan wasu kudurori da suka haɗa bai wa hukumomin MDD a ɓangaren kula da abinci damar su kafa hukuma da za ta bibiyi yadda hiɗimomi suke saboda canza tsarin samar da abinci a duniya.
Ya ce an tattauna yadda hukumomin za su taimaka wa ƙasashe wajen fitar da jadawali da zai canza tsarin yadda abinci yake samu wa a faɗin duniya.
Ku shiga kasa don jin tattaunawar da Ibrahim Isa ya yi da Dakta Abubakar Sulaiman

Asalin hoton, Getty Images
Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani shahararren boka ɗan asalin jihar Anambra, mai suna Chinedu Nwangwu a ɗaya daga cikin otel ɗin sa a karamar hukumar Idemili ta Arewa.
Bokan da aka fi sani da Akwa Okuko Tiwaraki, na nufin ‘kwai mai karya kwaran manja’ a turance.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe mataimakansa guda biyu a lokacin da aka yi garkuwa da shi a daren Lahadi.
Wata majiya ta ce mutumin wanda ake kyautata zaton yana ɗaya daga cikin bokaye mafiya karfi a jihar ta Anambra, an yi garkuwa da shi cikin sauki a otal ɗin sa mai suna Triple P Hotel, tare da bindige wasu mukarraban sa guda biyu har lahira.
Ana kuma kallon Akwa Okuko Tiwaraki a matsayin mai maganin gargajiya mafi kuɗi a jihar.
A 2022 ya gina tare da ƙaddamar da otal guda biyu, waɗanda aka ɗauka a matsayin mafi girma a Oba.
Majiyoyi, sun ce sace shi ya janyo ce-ce-ku-ce da kuma raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana ɗaya daga cikin bokaye mafiya karfi.
Hukumomin ƴan sanda a jihar sun tabbatar da faruwar lamarin, inda ma magana da yawunsu, DSP Toochukwu Ikenga ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na dare, sai dai daga bisani an sako bokan da aka sace.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan majalisar Isra'ila sun amince da wata doka mai cike da taƙaddama ta yi wa ɓangaren shari'ar ƙasar garambawul duk da zanga-zangar nuna adawa da matakin.
Dokar ta cire ikon Kotun Koli na yin watsi da matakan gwamnati da take ganin sun saɓa wa hankali. Wannan shi ne na farko da aka amince da shi a jerin sauye-sauyen da ake matuƙar takun-saƙa da su da nufin daƙile karfin kotuna a Isra'ila.
Sauye-sauyen da ake shirin yi sun haifar da zanga-zanga mafi girma a tarihin Isra'ila, inda 'yan adawa suka yi gargaɗin cewa sauye-sauyen na yi wa Isra'ila barazana a matsayinta na ƙasa mai bin tsarin dimokraɗiyya.
Gwamnati ta yin musun cewa matakan sun zama dole don gyara rashin daidaito a tsakanin rassa gwamnati, inda ake ganin kotuna suna ƙara yin katsalandan cikin harkokin siyasa a 'yan shekarun baya-bayan nan.
An amince wa ƙudurin dokar da ake kira "matakin da hankali zai ɗauka 'reasonableness' a Ingilishi" da rinjayen ƙuri'a 64, bayan 'yan adawa sun ƙauracewa kaɗa ƙuri'ar ƙarshe.
A jawabin da ya gabatar wa majalisar wato Knesset, jagoran adawa Yair Lapid ya bayyana matakin da "wani yunƙurin ƙwace mulki daga wasu 'yan tsirarun masu tsattsauran ra'ayi a kan mafi rinjayen 'yan Isra'ila". Sai dai Firaminista Benjamin Netanyahu ya dage a kan cewa kotu za ta ci gaba da kasancewa mai 'yancin cin gashin kanta.
Ya ce ƙudurin dokar ya zama dole ga gwamnati don ta iya "aiwatar da manufofinta kamar yadda suka dace da shawarar mafi rinjayen al'ummar ƙasar".
Ƙuri'ar ta kawo tuƙewar hargitsin watanni, inda shugaban Isra'ila ke gargaɗin shugabannin siyasa a ranar Litinin cewa ƙasar na "cikin yanayi irin na ta-ɓaci".
A ranar Litinin da safe masu zanga-zanga suka toshe wani layi a wajen ginin majalisar dokokin Isra'ila, yayin da 'yan sanda suka yi amfani da tankokin feshin ruwa suka yi ta kwarara musu tare da ture su daga titi a cikin hayaniyar kaɗe-kaɗen ganguna da bushe-bushen usur da ƙahonnin busa.

Asalin hoton, MINISTRY OF SANITATION AND WATER RESOURCES/ FACEBOOK
Ofishin mai shigar da ƙara na musamman a Ghana ya kama tsohuwar ministar tsaftar muhalli da kula da albarkatun ruwa, Cecilia Dapaah bayan wata badaƙalar jibge tsabar kuɗi har dala miliyan ɗaya.
A cewar ofishin mai shigar da ƙarar, an tare jami'ar a gidanta ne ranar Lahadi 22 ga watan Yuli bisa alaƙa da laifukan cin hanci da rashawa da ake zargi bayan rahoton satar maƙudan kuɗi daga gidanta.
Sanarwar ofishin mai shigar da ƙarar ta ce “jami'an ofishin suna yi wa Cecilia Dapaah tambayoyi”.
Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo ya karɓi takardar murabus ɗin minitar bayan kiraye-kirayen jama'a lokacin da aka yi zargin ta jibge tsabar kuɗi sama da dala miliyan ɗaya a gidanta na birnin Accra.
Minista, Cecilia Abena Dapaah, ta yi murabus daga muƙaminta bayan taƙaddama a kan gano cewa ta jibge maƙudan kuɗi a gidanta, wanda aka yi imani wasu 'yan aikinta biyu sun sace.
'Yan Ghana da yawa da kuma masu fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa sun tuhumi inda jami'ar gwamnatin ta samu waɗannan kuɗaɗe da kuma dalilin da ya sa ta ajiye maƙudan kuɗin a gidanta, yayin da ƙasar ke tsakiyar fama da rikicin tattalin arziƙi.
A ranar Juma'a, kafofin yaɗa labaran cikin gida suka ba da rahoton cewa an kai wasu 'yan aikin gidan ministar biyu da ƙarin mutum uku gaban kotun Accra bisa zargin satar $1 miliyan da yuro 300,000 da miliyoyin cedis da kuma wasu kadarori daga gidanta a watan Oktoban 2022.
A cikin sanarwar da ta rubuta wadda a ciki ta bayyana yin murabus daga minista, Cecilia Dapaah ta nunar cewa, “Zan iya ba da tabbacin cewa adadin kuɗin da ake ambatowa ba su yi daidai da abin da ni da mijina muka kai rahoto ga 'yan sanda ba. Ina da matuƙarsanin muhimmancin da irin wannan labarai yake da shi game da mutum mai riƙon muƙami irina.”
An yi zargin cewa 'yan aikin gidan nata sun yi ta facaka da maƙudan kuɗin ne wajen sayen kadarori da motoci da kyautuka masu tsada daga maɓoyarsu.

Asalin hoton, AFP
Adadin waɗanda suka mutu sakamakon ruftawar wani gini a birnin Douala na Kamaru, sun kai 33 zuwa yanzu, ciki har da wata yarinya ‘yar shekara uku.
Wasu mutane 54 kuma sun jikkata bayan benen mai hawa huɗu ya ruguje kan mutane lokacin da suke barci a unguwar Ndogbong a Douala, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na CRTV ya ruwaito.
Akalla uku daga cikin waɗanda suka jikkata yara ne, a cewar AFP.
Biyar daga cikinsu na cikin mawuyacin hali, in ji ministar gidaje da raya birane, Célestine Ketcha Courte.
Ta ce suna samun kulawa a gundumar Deido da asibitocin Laquintine.
Jami'an agajin gaggawa da makwaɓtan da abin ya shafa na ci gaba da binciken ɓaraguzai domin ceto mutane.
Tawagogin hukumar kashe gobara a Kamaru da kungiyar agaji ta Red Cross da sauran jami'an ceto na ci gaba da aiki a wurin.
Har yanzu dai ba a san abin da ya haddasa ruftawar gijin ba a ranar Lahadi, sai dai ministan ya ce za a tantance dukkan gine-gine a yankin da lamarin ya faru.
Ba a cika samun ruftawar gine-gine ba a Douala da ya kasance cibiyar kasuwancin Kamaru.
A shekarar 2016, wani ruftawar gini ya kashe mutane biyar lamarin da ya sa hukumomi suka fara rusa gidajen da ke da matsalar gine-gine.
Ms Célestine ta ce a yanzu za a ci gaba da korar mutanen da ke zaune a irin waɗannan gine-gine masu haɗari a yankin.
Ta yi nuni da cewa jinkirin samun takardar izinin gini na iya hana a tantance masu gidaje, inda ta bukaci masu unguwanni da su rage wa’adin da aka ba su wajen samun izinin gini.

Asalin hoton, Getty Images
Wata majiyar sojan Somaliya ta shaida wa BBC cewa sojoji 25 sun mutu a lokacin da wani mutum ya tayar da bama-bamai a cikin sojojin da ke cikin jerin gwano a sansanin kwalejin Jale Siad.
Rundunar sojin ƙasar dai ba ta ce komai ba a hukumance kan lamarin.
An ce wasu 48 sun jikkata kuma an kai su asibitoci a Mogadishu.
Mutumin da ya tarwatsa kansa da bam yana sanye ne da kakin soji, ya kuma shiga sansanin da shaidar karya, kamar yadda majiyar sojojin da ba ta so a bayyana sunanta ba ta shaida wa BBC.
Kungiyar al-Shabab ta ce ɗaya daga cikin mayakanta ne ya kai harin, inda ta ce sojoji 73 ne suka mutu sannan 124 suka jikkata.

Asalin hoton, CHINESE LOCAL MEDIA
Mutane 11 sun mutu bayan rufin dakin wasan motsa jiki na makaranta a arewa maso gabashin China ya rufta a lokacin da wata tawagar 'yan wasan kwallon raga ta 'yan mata ke amfani da shi, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.
Da dama daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su kananan yara ne, kamar yadda shaidun gani da ido suka sanar da kafafen yada labaran kasar, duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da hakan a hukumance ba.
Iyayen da ke cikin rikicewa sun yi cincirindo a wani asibiti da ke kusa suna neman ƙarin bayani.
Mutane takwas ne kawai daga cikin 19 da ke cikin dakin motsa jiki a lardin Heilongjiang na masana'antu suka tsira.
Gidan rediyon kasar Sin ya bayyana cewa, an ji mai horar da 'yan wasan kwallon raga na makarantar yana kiran sunayen daliban yayin da tawagar masu aikin ceto suka isa cikin ginin, a birnin Qiqihar don ceto rayukan yaran.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Indiya sun dakatar da neman wadanda suka tsira da ransu kwanaki hudu bayan wata mummunar zaftarewar kasa da ta afku a wani kauye a jihar Maharashtra da ke yammacin kasar.
An gano gawarwaki 27 yayin da mutane 57 suka bace bayan zaftarewar kasar, wadda ta afku a kauyen Irshalwadi da ke gundumar Raigad.
Yunkurin ceton ya samu cikas saboda rashin kyawun yanayi da kuma ruwan sama mai ƙarfi.
An dauki matakin ne bayan tattaunawa da gwamnatin Raigad da sauran hukumomi, in ji wani karamin minista.
Zaftarewar ƙasar wadda ta afku a daren Larabar da ta gabata, ta baje gidaje da dama a kauyen, wanda ke kan hawa zuwa wani tudu mai suna Irshalgad.

Asalin hoton, Edo Civil Society organisaton/Facebook
Ƙungiyoyin farar hula a Edo sun hau kan titunan Benin, babban birnin jihar, domin nuna adawa da karin farashin man fetur da aka yi a baya-bayan nan.
Kafar talabijin ta Channels ta ruwaito cewa masu zanga-zangar sun bi ta wasu manyan tituna suna yin Allah-wadai da karin da kuma tsadar rayuwa a Najeriya.
Masu zanga-zangar dai sun ce abin na ci musu tuwo a kwarya inda suka soki matakin karin farashin man fetur yayin da ake fama da tsantsar talauci.
Masu zanga-zangar na dauke ne da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban, sun kuma yi watsi da shirin tallafin Naira 8,000 da Gwamnatin Tarayya ke yi shirin yi bayan cire tallafin man fetur ɗin.
Zanga-zangar ta zo ne makonni bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa an cire tallafin mai. Tun bayan nan kuma farashin kaya da man fetur suke hauhawa a fadin kasar.
Yayin da gwamnatin tarayya ke cewa matakin an dauka ne don ci gaban kasa, masu suka na ganin zai jefa kasar cikin mawuyacin hali.
A ci gaba da daukar wannan mataki, gwamnatin tarayya ta bayar da shawarar bayar da tallafin Naira 8,000 ga ‘yan Najeriya amma daga baya ta ce za ta sake duba lamarin bayan sukar da shirin ya sha.
Gwamnati ta yi kira ga ƴan Najeriya su yi hakuri kuma ta ce ana daukar matakan rage radadin cire tallafin.

Asalin hoton, Getty Images
Kimanin mutum takwas ne aka tabbatar sun mutu sakamakon fashewar wata tankar dakon mai a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Lamarin ya ƙazance ne yayin da wuta ta kama a daidai lokacin da mazauna garin ke diban mai daga tankar da ta yi hatsarin a daren ranar Lahadi.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta ce motar dakon man ta faɗi ne a kan titi, inda kusan dukkanin abubuwan da ke cikinta ya malale. Bayan haka ne mazauna yankin suka mamaye wurin domin dibar man.
"Motar tankar ta fashe inda ta kashe mutum takwas, ta kuma raunata wasu da dama wadanda aka garzaya da su asibiti, kamar yadda kakakin 'yan sandan ya shaida wa BBC.
Mazauna yankin da shaidun gani da ido sun ce tankar ta fashe ne a wata unguwa da ke kusa da gidan mai, da kuma wani ginin coci amma babu ko daya da gobarar ta shafa.
Najeriya dai na fuskantar karin kusan kashi 400 na farashin man fetur tun watan Yuni bayan cire tallafin man da shugaba Bola Tinubu ya yi, matakin da ya ƙara iza wutar tsadar rayuwa da tsadar kayan masarufi.
Ƙasar wadda ta fi kowacce ƙarfin tattalin arziƙi a Afirka tana shigo da sama da kashi 90 cikin 100 na man da take bukata saboda gaza tace danyen mai a cikin gida saboda lalacewar matatun mai mallakin gwamnati.