''Yan sanda sun kama mutanen da suka yi yunkurin kai wa Atiku hari'

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Rabiatu Kabir Runka and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mutane tara sun mutu a hatsarin jirgin saman Port Sudan - sojoji

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Rundunar sojin Sudan ta ce mutane 9 sun mutu a wani hatsarin jirgin sama a filin tashi da saukar jiragen sama na Port Sudan.

    An ce jirgin na farar hula Antonov ya samu matsala a fasaha yayin da yake tashi.

    Jami'an soji hudu na daga cikin wadanda suka mutu. An bayyana cewa wata yarinya ta tsira daga hatsarin.

    Fiye da mutane miliyan uku ne suka rasa muhallansu tun bayan barkewar fada tsakanin sojoji da mayakan RSF a tsakiyar watan Afrilu, inda rikicin ya nuna babu alamun shawo kan lamarin.

    • Hatsarin jirgin Nepal: 'Direban jirgin bai bayar da rahoton komai ba kafin hatsarin'
  2. An canza tambarin manhajar twitter

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Shugaban kamfanin Twitter ya kaddamar da sabon tambarin dandalin sada zumuntar, mai dauke da harafin X, wanda zai maye gurbin shuɗin tsuntsu da ake amfani da shi a baya.

    A cikin wata sanarwa da twitter ya wallafa a safiyar Litinin, babbar jami'ar kamfanin, Linda Yaccarino ta ce "X ya bayyana!"

    Haka zalika Musk ya ce za a daina kiran sakonnin da aka wallafa a twitter da "Tweets" sai dai a riƙa cewa "x's".

    Hamshakin attajirin ya canza hoton shafinsa zuwa sabon tambarin na twitter.

    A ranar Lahadin da ta gabata ne attajirin ya ce yana shirin canza tambarin Twitter, yana mai cewa: "Kuma nan ba da jimawa ba za mu yi bankwana da tambarin twitter na tsutsu da aka saba amfani da shi"

    • Mutum miliyan goma sun yi rijista da dandalin Threads kishiyar Twitter
    • Twitter zai maka mai Facebook a kotu saboda yi masa kishiya
  3. Davido ya goge bidiyon rawa a masallaci bayan ya sha caccaka

    ...

    Asalin hoton, Davido

    Bayanan hoto, ...

    Sanannen mawaki a Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya goge bidiyon waka mai cike da ce-ce-ku-ce na wani yaronsa, Logos Olori, bayan ya fuskanci suka a intanet.

    A ranar Asabar, Davido ya fuskanci suka daga Musulmai da yawa a shafukan sada zumunta saboda ya yada tallar dakika 45 ta bidiyon wakar a shafinsa na Twitter.

    Bidiyon wanda musulmai da dama suka bayyana a matsayin abin takaici, ya nuna wasu gungun maza sanye da sutura irin ta musulmai, suna sallah da addu'o'i, amma ba zato ba tsammani sai suka ɓarke da rawa da waka.

    Sun zargi mawakin da rashin mutunta addinin Islama ta hanyar hada ayyukan addini da waka da raye-raye.

    Sun kuma yi kira gare shi da ya goge bidiyon tare da bayar da hakuri.

    Fitattun ‘yan Najeriya irin su Bashir Ahmad da Ali Nuhu sun tofa albarkacin bakinsu kan hakan.

    Yayin da mawakin ya yi shiru kan lamarin kuma bai bayar da hakuri a hukumance ba, kwanaki biyu bayan ƙorafe-ƙorafen, a karshe Davido bayan ya sha matsin lamba ya goge bidiyon.

    • Ƙasashen Musulmi sun fusata da ƙona Alƙur'ani a Sweden
  4. Rasha ta zargi Ukraine da kai hari kan Moscow

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta zargi Ukraine da kai hari da jirage marasa matuka kan Moscow babban birnin kasar.

    A cikin wani sakon da ya wallafa a manhajar saƙon Telegram, magajin garin Sergei Sobyanin, ya ce jiragen biyu sun faɗo ne ƙasa, inda suka far wa wasu gine-ginen da ba na zama ba - amma ba a samu raunuka ko barna ba.

    Kafofin watsa labaran kasar sun ce an gano wani tarkacen jirgi mara matuki a tsakiyar birnin, nesa kadan da ma'aikatar tsaro.

    Moscow ta fuskanci hare-haren jiragen sama da yawa a wannan shekara, ciki har da wanda ya shafi katangar fadar Kremlin.

    • Shugaba Putin ya ce hare-haren martanin Ukraine ba sa nasara a kan Rasha
    • Amurka ta tabbatar Ukraine na amfani da bam mai 'ya'yan da ta bata
  5. Hotuna gobarar daji a kasar Girka

    Ana ci gaba kwashe dubban mutane daga tsibirin Rhodes da Corfu da Evia na Girka saboda gobarar daji da ta barke a ƙasar tun ranar Talata.

    Ga wasu hotuna daga karshen mako

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Tsibirin Rhodes na fama da gobarar daji tun ranar Talata
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Jiragen yaki na kashe gobara suna zubo da ruwa a kan kauyen Asklipio a Rhodes
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Hayaki na tashi daga tsibirin Corfu a yammacin Lahadi
  6. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi, barkanmu da war haka.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasance da ku a wannan safiya ta Litinin domin kawo muku irin labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman Najeriya da makwabtan ƙasashe.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.

    Ku biyo mu....