Gawawwaki fiye da 50 ne ba a gano danginsu ba, bayan hatsarin jirgin Indiya

Asalin hoton, Reuters
Gawawwaki fiye da 50 ne har yanzu ba a gano danginsu ba, wata ɗaya bayan mummunan hatsarin jirgin ƙasan da ya halaka mutane akalla 293 a Indiya.
Hatsarin ya faru ne ranar 2 ga watan Yuni a jihar Odisha da ke gabashin ƙasar, lokacin da wani jirgin ƙasa dauke da fasinja ya yi karo da wani jirgin dakon kaya da ke tsaye.
Mutane sama da 1,000 ne suka jikkata, a abin da ya kasance ɗaya daga cikin hadurran jirgin ƙasa mafi muni da aka taɓa gani a Indiya cikin wannan ƙarni.
Tuni dai aka gyara wurin da hatsarin ya auku, har ma an ci gaba da harkoki, amma iyalai da dama sun ce sun kasa gano gawawwakin 'yan'uwansu.






