An bai wa ƙasashen Afirka 12 rigakafin Maleriya

Asalin hoton, Getty Images
An ware allurai miliyan 18 na rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na farko (RTS,S) ga kasashen Afirka 12 na tsawon shekaru biyu masu zuwa.
Akalla kasashen Afirka 28 ne suka nuna sha'awar karbar allurar rigakafin cutar maleriyar, amma kasashe 14 ne kawai suka mika buƙata ga ƙungiyar GAVI, kungiyar da ke kula da shirin rigakafin.
Ghana da Malawi da kuma Kenya ne za su kasance kasashe na farko da za su karbi allurar a cikin watannin karshen wannan shekaran. Maleriya na daya daga cikin cututtukan da suka fi kashe mutane a Afirka.
Kusan kowane minti daya, a nahiyar, yaro dan kasa da shekaru 5 na mutuwa sakamakon kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro.
Buƙtar da aka riga aka yi kan allura miliyan18 din da aka ware na maganin RTS, S yana da yawa sosai kuma ya fi ƙarfin abin da ake da shi a ƙasa.
Hukumar lafiya ta duniya (WHO), da ƙungiyar Gavi da sauran abokan hulda sun ce sun yi la'akari da kasashen da suka fi bukata.
Malawi, Ghana da Kenya wadanda tuni suka yi amfani da allurar rigakafin a wani mataki na gwaji ga akalla yara miliyan 1.7, an ware musu allurai miliyan 6.9.
A karon farko, kasashe 8 da suka hada da Benin da Burkina Faso da Burundi da Kamaru, da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Laberiya da Saliyo da Uganda, za su kaddamar da rigakafin a cikin shirye-shiryensu na yau da kullun.
Nijar za ta samu wani bangare na abin da aka yi kasafi. Amma, ƙasashen Mozambik da Sudan ba za su karɓi allurai ba, saboda yawan ficewa da suke yi daga shirye-shiryen rigakafi makamantan wannan.






















