Ƴan bindiga a Kaduna sun sace ƴaƴan Sarkin Kagarko

Labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Nabeela Mukhtar Uba and Mukhtar Adamu Bawa

  1. 'Yan bindiga sun kashe ɗan jarida a arewacin Kamaru

    An harbe wani ɗan jarida a yankin arewa maso yammacin Kamaru da ke fama da rikice-rikice.

    Wannan shi ne karo na uku da ake kashe ɗan jarida a wannan shekara a ƙasar.

    Rahotonni sun ce an harbe Anye Nde Nsoh a wata mashaya a birnin Bamenda a lokacin da wasu mahara da ba a san ko su wane ne ba suka buɗe wuta.

    Birnin Bamenda na ɗaya daga cikin wuraren da tashe-tashen hankula masu alaƙa da hare-haren 'yan awaren ƙasar masu magana da Turancin Ingilishi.

    Sauran 'yan jarida biyun da aka kashe a ƙasar cikin wannan shekara, an kashe su ne a birnin Yaoundé.

  2. Shugaban hukumar agaji ta MDD ya isa Saudiyya don tattaunawar sulhun Sudan

    n

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mista Griffiths ya je Saudiyya ne, domin tattauna yadda za a shigar da kayan agaji zuwa cikin Sudan.

    Shugaban hukumar agaji na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths ya isa birnin Jeddah na ƙasar Saudiyya domin fara tattaunawar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin da ke rikici da juna ƙasar Sudan.

    Mai magana da yawun MDD Eri Kaneko ta ce Mista Griffiths ya isa birnin Jeddah ne, domin tattauna yadda za a shigar da kayan agaji zuwa cikin Sudan.

    Tuni wakilan ɓangarorin da ke rikici da juna suka isa Saudiyya domin tattaunawar gaba-da-gaba ta farko tun bayan fara yaƙin.

    A baya dai duka ɓangarorin sun amince da tsagaita wuta domin bai wa fararen hula damar ficewa daga birnin Khartoum, amma ba kawo ƙarshen yaƙin ba.

    Ana sa ran tattaunawar da Saudiyya da Amurka ke jagoranta a Saudiyya za ta kawo ƙarshen yaƙin da aka faro a ƙasar tun tsakiyar watan Afrilu.

  3. Wani abin fashewa ya hallaka sojojin Nijar bakwai

    p

    Asalin hoton, AFP

    Aƙalla sojojin Nijar bakwai ne suka mutu bayan da motarsu ta taka wani abin fashewa a yankin Tillaberi a yammacin ƙasar, da ke fama da ayyukan masu iƙirarin jihadi.

    Rundunar sojin ƙasar ta ce motar na cikin jerin gwanon motocin da ke raka ma'adinan ƙasar da ake haƙowa a ƙauyen Samira da ke kusa da kan iyakar ƙasar da Burkina Faso.

    A baya-bayan nan yankin na fuskantar ƙaruwar hare-haren masu iƙirarin jihadi.

    Ayyukan masu tayar da ƙayar baya a yammacin Nijar na neman zama ruwan-dare, duk kuwa da sintirin da sojoji ke yi a yankin tare da samun goyon bayan dakarun ƙasashen yamma irin su Faransa da Amurka.

  4. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin da Bature ke wa kirari da 'Mande tushen aiki ko da nasara na tsoronki'.

    Abdullahi Bello Diginza ne ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya, za mu fi mayar da hankali musamman kan Najeriya da makwabtan ƙasashe.

    Kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.

    Ku biyo mu....