Albashi zai gagari Amurka biya idan aka hana gwamnati karɓo ƙarin bashi

Asalin hoton, GETTY IMAGES
Sakatariyar Baitulmalin Amurka Janet Yellen ta yi gargaɗin cewa matukar aka gaza bai wa gwamnati damar ciyo ƙarin basuka, lamarin na iya yin mummunar illa ga ƙasar.
Ba tare da an cimma yarjejeniya don ƙarawa gwamnatin tarayya adadin kuɗin da za ta iya karɓowa bashi ba, kuɗi za su iya yankewa a lalitar Amurka nan da farkon watan gobe.
A wannan yanayi, gwamnatin tarayya ba lallai ne ta iya biyan albashin ma'aikata ba da kula da jin dadin rayuwa da sauran kashe-kashen kuɗaɗe.
"Aikin majalisa ne ta ƙara adadin kuɗin da gwamnatin za ta iya karɓa bashi. Idan suka gaza yin hakan, za mu shiga cikin bala'in tattalin arziki da harkokin kudi," in ji ta.
A wata hira da tashar ABC News ranar Lahadi, Misis Yellen ta ce bai kamata a tsaya ana ɓata lokaci wajen tattaunawa a kan batun ƙayyade bashin ba a wannan hali "da Amurkawa ke cikin tsananin matsi."
Lokaci yana ƙurewa kan wannan yarjejeniya, in ji Sakatariyar Baitulmalin.
A ranar Talata ne, Shugaba Biden zai gana da shugabannin jam'iyyar Republican inda zai nemi amincewarsu kan ƙara adadin dala tirliyan $31.4 da aka ƙayyade.
Akasari dai Majalisar Wakilai tana gindaya sharuɗɗa kafin ta amince da ƙara yawan kuɗin da aka ƙayyade ga wasu tanade-tanade a cikin kasafin kuɗi da kuma matakai kan kuɗaɗen da ake kashewa.















