Ƴan bindiga a Kaduna sun sace ƴaƴan Sarkin Kagarko

Labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Nabeela Mukhtar Uba and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Albashi zai gagari Amurka biya idan aka hana gwamnati karɓo ƙarin bashi

    Janet Yellen

    Asalin hoton, GETTY IMAGES

    Sakatariyar Baitulmalin Amurka Janet Yellen ta yi gargaɗin cewa matukar aka gaza bai wa gwamnati damar ciyo ƙarin basuka, lamarin na iya yin mummunar illa ga ƙasar.

    Ba tare da an cimma yarjejeniya don ƙarawa gwamnatin tarayya adadin kuɗin da za ta iya karɓowa bashi ba, kuɗi za su iya yankewa a lalitar Amurka nan da farkon watan gobe.

    A wannan yanayi, gwamnatin tarayya ba lallai ne ta iya biyan albashin ma'aikata ba da kula da jin dadin rayuwa da sauran kashe-kashen kuɗaɗe.

    "Aikin majalisa ne ta ƙara adadin kuɗin da gwamnatin za ta iya karɓa bashi. Idan suka gaza yin hakan, za mu shiga cikin bala'in tattalin arziki da harkokin kudi," in ji ta.

    A wata hira da tashar ABC News ranar Lahadi, Misis Yellen ta ce bai kamata a tsaya ana ɓata lokaci wajen tattaunawa a kan batun ƙayyade bashin ba a wannan hali "da Amurkawa ke cikin tsananin matsi."

    Lokaci yana ƙurewa kan wannan yarjejeniya, in ji Sakatariyar Baitulmalin.

    A ranar Talata ne, Shugaba Biden zai gana da shugabannin jam'iyyar Republican inda zai nemi amincewarsu kan ƙara adadin dala tirliyan $31.4 da aka ƙayyade.

    Akasari dai Majalisar Wakilai tana gindaya sharuɗɗa kafin ta amince da ƙara yawan kuɗin da aka ƙayyade ga wasu tanade-tanade a cikin kasafin kuɗi da kuma matakai kan kuɗaɗen da ake kashewa.

  2. Ƙarin ƴan Najeriya kusan 130 sun dawo gida daga Sudan

    .

    Asalin hoton, NIDCOM

    Ƙarin ƴan Najeriya 129 sun dawo gida bayan da suka tserewa yakin da ake gwabzawa a Khartoum, babban birnin Sudan.

    Gwamnain Najeriya dai na ci gaba da ƙarfafa matakan kwashe jama'arta da suka maƙale a ƙasar da ke Arewacin Afirka.

    Bayanai daga gidan Talabijin na Channels sun nuna cewa mutanen sun isa Najeriya ne yau Litinin da ƙarfe 9:15am cikin jirgin Tarco inda suka sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

    Mutanen sun hada da manya 124 sai yara biyar kuma sun samu tarba ne daga jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa NEMA da na hukumar da ke kula da ƴan Najeriya mazauna ƙetare da na ma'aikatar jin ƙai da ma'aikatar harkokin waje sai kuma hukumar kula da shige da fice ta Najeriya.

    Sauran jami'an sun haɗa da na ƴan sanda da hukumar yaƙi da safarar mutane da kuma sojoji.

    Lamarin ya zo ne kusan kwana guda bayan nasarar gwamnati na kwashe kashi na huɗu na ƴan Najeriyar da suka maƙale a Sudan.

    Zuwa yanzu dai sama da ƴan Najeriya 800 ne suka tsere daga Sudan mai fama da rikici.

  3. Yadda rikicin kabilanci ya tarwatsa dubban mutane a Indiya

  4. ECOWAS ta sake yin kiran a murkushe ta'addancin da ke karuwa a tsakiyar Sahel

    .

    Asalin hoton, BUHARI SALLAU

    Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta jaddada buƙatar a ɗauki matakan gaggawa domin magance ƙaruwar hare-haren ta'addanci a tsakiyar Sahel.

    Kwamishinan ECOWAS da ke kula da harkokin siyasa da zaman lafiya da tsaro, Ambasada AbdelFateh Moussa ne ya yi wannan kira a wani taron bayar da horo na yini biyar.

    An yi wa taron taken Tabbatar da ci gaban zaman lafiya: Rawar ƴan sanda da jami'an Jandarma wajen tafiyar da ayyukan ECOWAS wajen wanzar da zaman lafiya.

    ECOWAS ce ta shirya taron haɗin gwiwa da kwalejin horas da ƙananan jami'an soji ta Najeriya tare da tallafin shirin ECOWAS kan zaman lafiya da tsaro.

    Moussa ya ce ayyukan wanzar da zaman lafiya da aka saba na zama tsohon yayi saboda yanayin rikici a yankin.

  5. Da wahala a iya kawo ƙarshen yaƙin Sudan – Tsohuwar ministar Sudan

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohuwar ministar harkokin wajen Sudan, Mariam al-Sadiq al-Mahdi ta ce tana da shakku kan yiwuwar ɓangarorin da ke rikici da juna a ƙasar su iya cimma sahihiyar yarjejeniyar tsagaita wuta saboda rashin yardar da ke tsakaninsu.

    A hirar da aka yi da ita a shirin BBC Focus on Africa, ta ce jami'an da ke goyon bayan tsohon shugaban ƙasar Omar al-Bashir suna ƙoƙarin tabbatar da cewa yaƙin da sojoji ke yi da dakarun RSF ya ci gaba.

    Miliyoyin mazauna Khartoum, babban birnin ƙasar ta Sudan na ci gaba da fuskantar matsaloli da kuma karancin abubuwa na amfanin yau da kullum.

    Yaƙin ya sa kamfanonin wayoyin hannu da intanet garƙame ofisoshinsu saboda rashin man fetur.

  6. APC ta goyi bayan Akpabio da Tajudden don shugabancin majalisa ta 10

  7. Ƴan bindiga a Kaduna sun sace ƴaƴan Sarkin Kagarko

    .

    Asalin hoton, AFP.

    Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun auka Fadar Sarkin Kagarko a kudancin Kaduna, Alhaji Sa'ad Abubakar, inda suka yi awon gaba da ƴaƴansa tara da jikoki da kuma karin mutum uku a garin.

    Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar yara suka ɗauka wadanda ke tsakanin shekaru 7 zuwa 13 da haihuwa.

    Tun farko Jaridar Daily Trust ta rawaito wani mazaunin garin, na cewa ƴan bindigar sun kutsa yankin ne cikin dare kamar ƙarfe 11:15 na dare inda kuma suka nufi fadar Sarkin.

    "Sun kuma tafi da amaryar sarkin da yaransa tara da jikokinsa amma matar ta kuɓuta, inda ta dawo gida," in ji shi.

    A cewar mazaunin, ƴan bindigar sun kuma yi garkuwa da karin mutum uku ciki har da wata mata, tare da raunata wani Audu Kwakulu na Unguwar Pah wanda a halin yanzu yake samun kulawa a asibiti.

    "Ƴan bindigar sun kuma kashe wani makiyayi a ƙauyen Kuchimi tare da sace kaya a shaguna bakwai a kauyen Janjala duka a karamar hukumar Kagarko - a hanyarsu ta komawa," kamar yadda majiyar ta bayyana.

    Kakakin rundunar ƴan sandan Kaduna, DSP Muhammed Jalige bai amsa kiran da BBC ta yi masa game da wannan labari ba.

    Kaduna dai ɗaya ce daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro a ƙasar.

    Ƴan bindiga sun sha kai hare-hare a sassa daban daban na jihar, yayin da gwamnati ta sha yin alƙawarin magance matsalar.

  8. Abin damuwa ne bashin $800m da gwamnati mai barin gado ta karbo – CISLAC

    Auwal Musa Rafsanjani

    Asalin hoton, OTHER

    Cibiyar sa-ido kan ayyukan majalisar dokokin Najeriya, CISLAC ta koka kan bashin dala miliyan 800 da gwamnatin kasar ta karbo daga Bankin Duniya, domin rage radadin cire tallafin man fetur.

    A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce yin hakan wani bakon abu ne, saboda idan an daina bayar da tallafin tun a watan Afrilu, to kamata ya yi a mayar da kudaden da gwamnatin ta karbo daga babban bankin duniya.

    Shugaban kungiyar ta CISLAC, Awwal Musa Rafsanjani, ya shaida wa BBC cewa a ganinsu, idan aka karɓo bashi kamar yadda doka ta tanada, ya kamata a ce an yi amfani da shi wajen samar da ayyukan da za su amfani ƙasa.

    "Bashi da aka karɓo lokacin da gwamnati za ta miƙa mulki abin damuwa ne saboda ba a san ma ko gwamnatin da za ta zo, ko za ta amince ta ci gaba da waɗannan tsare-tsare ba." in ji Rafsanjani.

    Shugaban ƙungiyar ya ce sun sha yin kira ga gwamnati game da karɓar basuka, inda suke nusar da gwamnati cewa akwai hanyoyin da suka fi dacewa da za a iya samun kuɗaɗen shiga ya zamana ba kowane lokaci za a karɓi bashi ba.

  9. An kai hari asibiti tare da lalata bankuna a Sudan

    Rahotonni daga Khartoum babban birnin ƙasar Sudan na nuna cewa yawan ɓarnar da aka yi wa birnin ta haddasa matsalar ƙarancin abubuwan buƙatu a ƙasar.

    Wani likita ya shaida wa BBC cewa wasu gungun mutane ɗauke da makaman da suka haɗar da wuƙake da bindigogi, sun yi yunƙurin kutsawa wani asibiti cikin dare, yayin da dakarun RSF ke ci gaba da kai hare-hare domin ƙwace iko da birnin.

    Rahotonni sun ce ana iya ganin yadda dakarun RSF ke lalata bankuna a ƙasar.

    Duka ɓangarorin da ke faɗa da junan na tattaunawar sulhu a birnin Jeddah na ƙasar Saudiyya domin tsagaita wuta, don samar wa fararen hula tallafin jin-ƙai.

    Kuma sun ce a shirye suke domin kawo ƙarshen yaƙin ta hanyar tattaunawar sulhu.

  10. Kotun zaɓen shugaban ƙasa ta ɗage zama zuwa Talata don jin ƙorafin PDP

    Atiku

    Asalin hoton, Atiku/Twitter

    Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya da ke zamanta a Abuja ta ɗage zamanta zuwa gobe Talata domin sauraron ƙorafin babbar jam'iyyar adawa ta PDP, da ɗan takararta Atiku Abubakar, da kuma jam'iyyar APM.

    Hukumar zaɓen ƙasar INEC ce ta ayyana ɗan takarar jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri'a miliyan 8,794,726, bayan da ya kayar da manyan abokan takararsa Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP.

    Bayan da suka yi watsi da sakamakon zaɓen Atiku da Obi sun nufi kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen don ƙalubalantar nasarar Tinubun.

    A zaman sauraron ƙorafe-ƙorafen da ta fara ranar Litinin, kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Haruna Tsammani ta alƙawarta yin adalci ga duka ɓangarorin da ke cikin shari'a.

  11. Ana jimamin mutanen da ambaliya ta kashe DR Kongo

    g

    Asalin hoton, AFP

    Ƙasar Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo ta ayyana zaman makoki a ƙasar, bayan gano gawarwaki fiye da 400 sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasa a gabashin ƙasar.

    Kawo yanzu ba a ga mutane da dama ba kuma ana fargabar cewa suna ƙarƙashin laka da ta mamaye wasu ƙauyuka biyu a gundumar Kalehe.

    An gano wasu gawarwakin ne a kusa da tafkin Kivu.

    Gwamnatin ƙasar ta aike da tawagarta daga Kinshasa babban birnin ƙasar zuwa yankin kwanaki huɗu bayan ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasar.

    Wani likita dan ƙasar, da ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel Denis Mukwege ya soki yadda ake binne waɗanda suka mutu a manyan ƙaburburan bai ɗaya.

    Yana mai cewa mutanen sun cancanci jana`iza ta girmamawa, a maimakon yi musu jana'izar bai ɗaya.

  12. Majalisar dokokin Najeriya ta fara yi wa sabbin mambobinta bita

    Majalisa

    Majalisar dokokin Najeriya ta fara shirye-shiryen yi wa sababbin zaɓaɓɓun 'yan majalisar dattawan majalisa ta 10 bitar ayyukan majalisar.

    Bitar za ta taimaka wajen ilimantar da zaɓaɓɓun 'yan majalisar wajen sanin makamai aikin majalisar.

    Cibiyar kula da ayyukan majalisa da dimokradiyya a ƙasar ta ce bitar na da matuƙar muhimmanci kasancewar fiye da kashi 70 cikin 100, na zaɓaɓɓun 'yan majalisar, karon su na farko kenan da suke zuwa majalisar.

    A cikin watan Yuni mai zuwa ne za a rantsar da majalisar wadda ita ce ta 10 a Najeriya.

  13. Jam'iyyar AA ta janye ƙarar da ta shigar kan zaɓen Tinubu

    Bola Ahmed Tinubu

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Bola Ahmed Tinubu

    Jam'iyyar Action Alliance ta janye ƙorafinta kan zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.

    AA ta bayyana janye ƙorafin nata ne a lokacin fara zaman kararrakin zaɓen shugaban kasa ranar Litinin a Abuja, to sai dai jam'iyyar ba ta bayyana dalilanta na janye karar ba.

    Jagoran lauyoyin jam'iyyar Barista Oba Maduabuchi (SAN), ya ce ya shigar da ƙarar ne tun da farko a madadin jam'iyyar.

    Mai shari'a Haruna Tsammani ya amince da janye ƙorafin bayan jam'iyyar APC da Bola Ahmed Tinubu - waɗanda ake ƙara - sun nuna cewa ba su da ja a kan batun.

  14. Ba zan yi biyayya ga umarnin kotu ba - jagoran adawar Senegal

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Jagoran `yan adawar Senegal, Ousmane Sonko ya ce ba zai yi biyayya ga sammacin kotu ko kuma bai wa hukumomin shari`a haɗin kai ba matuƙar bai samu tabbacin tsaron lafiyarsa ba.

    ''Ba adalci ba ne, wannan tamkar fashi ne a ɓangaren shari`a, shi ya sa na yanke shawarar, ina nan a kan baka ta, ba zan bai wa ɓagaren shari'a haɗin kai ba, ba kuma zan bayyana a gaban kotun ba'', in ji shi.

    Mista Sonko ya ce an aike masa da sammacin kotu har sau biyar, waɗanda duka ya hatarta, in ban da guda daya ,wanda ya ce bai halarta ba bisa dalilai na tsaro, duk kuwa da farfagandar rashin yi wa fannin shari'a biyayya da ya ce ana yaɗa wa a kansa.

    Ya ce a baya an sha fusata shi da muzguna masa tare da yunƙurin kashe shi, bayan sammacin da kotun ta aike masa.

    Mista Sonko na ishara ga ikirarin zargin kashe shi da ya ce jami'an 'yan sanda sun yi a watan Maris, a lokacin da aka tilasta mayar da shari'ar da ake yi masa zuwa kotun birnin Dakar.

    Mista Sonko na fuskantar shari`a biyu na kotu da ka iya hana shi tsayawa takarar shugaban kasa a zaɓen baɗi.

    A cikin wannan watan ne zai fuskanci tuhumar fyade da kuma barazanar kisa da wata ma`aikaciyar gidan gyaran gashi ta shigar da shi a gaban wata kotu.

    Zarge-zargen da duka ya musanta, yana mai cewa bi-ta-da-ƙullin siyasa ne kawai.

    A ranar Litinin ne za a fara sauraren karar da ya shigar gaban wata kotu, yana ƙalubalantar hukuncin da wata kotun ta yanke masa bayan da ta same shi da laifin ɓata sunan ministan yawon buɗe ido na ƙasar.

  15. Mota ta markaɗe mutum takwas a Amurka

  16. An jibge tarin jami'an tsaro a harabar kotun sauraron ƙorafin zaɓen Tinubu

    d

    Asalin hoton, Getty Images

    An ci gaba da zaman sauraron karafin da jam'iyyun adawa suka shigar gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe domin ƙalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC.

    Wakilin BBC da ke harabar kotun ya ce an jibge jami'an tsaro na 'yan sanda a mahaɗar hanyar da za ta sada ka da babbar kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja inda ake zaman sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasar.

    An kuma rufe hanyar da ta bi ta gaban kotun, sannan an hana mutane wucewa sai waɗanda ke aiki a cikin kotun.

    Sannan ba a barin kowa ya shiga cikin kotun harda 'yan jarida, sai dai waɗanda kawai aka tantance.

    Haka kuma akwai tarin 'yan sanda da jami'an tsaron farin kaya na DSS da ke ciki da wajen harabar kotun, domin tabbatar da tsaro a yayin sauraron ƙarar.

  17. Za mu yi wa kowa adalci - Kotun sauraron ƙorafi kan zaɓen Tinubu

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafe kan zaɓen shugaban Najeriya na 2023 ta fara zama a yau Litinin.

    Zaman ya fara ne da misalin ƙarfe 9:15 na safe, inda alƙalin da ke jagorantar zaman kotun, mai shari'a Haruna Tsammani ya gabatar da jawabi.

    Tsammani ya ce kotun za ta yi wa ƙarar adalci sannan ya gargaɗi lauyoyi da su guje wa yin kalamai na harzuƙawa.

    Ya kuma buƙace su da su bai wa kotun haɗin kai domin ganin an kammala shari'ar cikin lokacin da aka ɗiba.

    Sauran alƙalan da za su taimaka wajen gudanar da shari'ar sun haɗa da mai shari'a Stephen Adah da Misitura Bolaji-Yusu da Boloukuoromo Moses Ugo da kuma Abbah Mohammed.

    Gabanin fara zaman, an jibge jami'an tsaro a kan hanyoyin da suke kai wa zuwa kotun.

    Jam'iyyun adawa irin su PDP da LP ne suka shigar da ƙara suna ƙalubalantar nasarar da ɗan takarar jam'iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

    Sakamakon da INEC ta fitar ya nuna cewa Bola Tinubu na APC ya samu ƙuri'u 8,794,726, sai Atiku Abubuakar na jam'iyyar PDP wanda ya samu ƙuri'a 6,984,520, yayin da Peter Obi na jam'iyyar LP ke biye masu da ƙuri'a 6,101,533.

  18. Buhari zai ƙaddamar da matatar man Ɗangote

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai ƙaddamar babbar matatar mai da hamshaƙin ɗan kasuwar ƙasar Aliko Dangote ya gina.

    Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasar Bashir Ahmad ya ce za a ƙaddamar da katafariyar matatar man da aka fara ginawa tun shekarar 2016 nan da mako biyu masu zuwa.

    Kamfanin Aliko Dangote ya gina matatar ne da za ta iya tace gangar mai 650,000 a kowacce rana, da nufin magance shigar da tataccen mai cikin ƙasar, wadda ta fi kowacce ƙasa arzikin man fetur a nahiyar Afirka.

    Bashir Ahmad ya ce Buhari zai ƙaddamar da ke Legas ranar 22 ga watan Mayun da muke ciki, kafin wa'adin saukarsa daga mulki.

    Mai magana da yawun Dangote ya tabbatar da lokacin ƙaddamar da matatar, to sai dai bai yi ƙarin bayani ba.

    Ana tunanin matatar ta laƙume kudi kimanin dala biliyan 19 fiye da yadda aka yi hasashen za ta laƙume tun farkon fara ginata, sakamakon jinkirin shekaru da aka samu wajen ginata.

  19. Hukumar kula da ɗa'ar ma'aikata ta buƙaci Tinubu ya bayyana kadarorinsa

    rr

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da Da'ar Ma'aikata ta Najeriya ta ce dole ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da gwamnonin ƙasar 28 da ke jiran rantsuwa su bayyana kadarorinsu kafin ranar 29 ga watan Mayu.

    Haka kuma hukumar ta ce su ma zaɓaɓɓun 'yan majalisun wakilai da na dattawa za su bayyana nasu kadarorin kafin ranar 5 ga watan Yuni lokacin da za a rantsar da su.

    Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito mai magana da yawun hukumar Mrs Veronica Kato, na cewa bayyana kadarorin, wani ɓangare ne na shirye-shiryen shan ratsuwar kama aiki ga zaɓaɓɓun shugabannin kamar yadda dokar ƙasar ta tanadar.

    Mrs Kato, ta ce da yawa daga cikin zaɓaɓɓun sun fara karɓar fom ɗin bayyana kadarorin a rassan ofisoshin hukumar da ke faɗin jihohin ƙasar, kuma ana sa ran za su mayar da fom ɗin zuwa ofisoshin tare da bayyana kadarorin kafin ranar rantsar da su.

    Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa masu riƙe da muƙaman siyasa su bayyana kadarorin da suka mallaka a lokacin da za su kama aiki da kuma a lokacin da suka kammala wa'adin mulkinsu.

  20. An kama ɗan Najeriya bisa zargin safarar hodar ibilis a Saudiyya

    d

    Asalin hoton, others

    Hukumomin Saudiyya sun kama wani ɗan Najeriya ɗaya da 'yan Saudiyya uku bisa zargin safarar hodar ibilis da ta kai nauyin kilogiram 2.2 a ƙasar.

    Sashen binciken manyan laifuka na rundunar 'yan sandan ƙasar ya ce ya samu nasarar daƙile yunƙurin shigar da hodar ibilis zuwa biranen Riyadh da Jeddah.

    'Yan sandan sun ce mutanen huɗu sun daɗe suna aikata laifin safarar hodar ibilis ɗin tare da sayar da ita a cikin ƙasar ta hanyar amfani da wasu miyagun dabaru.

    Jami'an 'yan sandan sun ce za a gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.

    Safarar ƙwaya dai babban laifi ne a Saudiyya da za a iya yanke wa mutum hukuncin ɗaurin shekaru masu yawa a gidan yari