Buhari zai tafi taro Ghana

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa and Abdullahi Bello Diginza

  1. Ƙasashe suna rububin kwashe mutanensu daga Sudan

    Sudan evacuation

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Filin jirgin saman birnin ba ya aiki sanadin yaƙin da ya kassara shi.

    An kwashe ƙarin jami'ai da ma'aikatan jakadancin ƙasashen duniya da dama daga Khartoum, babban birnin Sudan, a yayin da sojojin gwamnati da dakaru masu kayan sari na RSF ke ci gaba da gwabza yaƙi.

    Faransa da Jamus da Kanada da Sifaniya da kuma Italiya na cikin ƙasashen baya-bayan nan da suka sanar da cewa sun kai jami'an nasu tudun-mun-tsira.

    Sai dai kuma sauran fararen hula na ƙasashe, sun ce suna fuskantar wahala a yunƙuri da suke yi na fita daga Sudan.

    Wakilin BBC ya ruwaito cewa a bayyane take abu ne mai matuƙar wahala ƙasashe su iya tsarawa tare da kwashe mutanensu a cikin motoci saboda ana faɗa ne a tsakiyar babban birnin ƙasar.

    Ana ta samun kirare-kirayen neman agajin gaggawa daga ɗalibai waɗanda akasarinsu 'yan ƙasashen Afirka da Asiya ne da kuma Gabas ta Tsakiya.

  2. Jama'a, barkanmu da safiya

    Masu bibiyar wannan shafi namu, da fatan kun tashi lafiya.

    Yaya shagulgulan Ƙaramar Salla?

    Sunana Mukhtari Adamu Bawa, idan kuka ci gaba da kasancewa da mu, za mu kawo muku labarai masu armashi da ƙayatarwa game da Najeriya da ma ƙasashe maƙwabta, da kuma sauran sassan duniya.

    Ina yi muku fatan alheri!