Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ce ta rufe ofishin jakadancinta a ƙasar Sudan.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar ta ce ofishin jakadancin ba zai zama wata matattarar jama'ar da ke son barin birnin Khartoum ba.
Ofishin jakadancin ya ce zai ci gaba da aiki daga birnin Paris na ƙasar Faransa ƙarƙashin kulawar jakadanta a Sudan ɗin.
Sanarwar ta ƙara da cewa ''Faransa na ƙoƙarin ganin an tsagaita wuta, tare da maido da tattaunawar miƙa mulki a Sudan''.
''Faransa na goyon bayan yunƙurin da ƙungiyoyin Tarayyar Afirka, ta ƙasashen gabashin Afirka, da ƙungiyar ƙasashen Larabawa, da ta Tarayyar Turai, da Majalisar Dinkin Duniya, ke gudanarwa wajen kawo zaman lafiya a ƙasar'', in ji sanarwar.
''Faransa na kira ga duka ɓangarorin da ke rikici da juna, da su bari a kai kayayyakin jin-ƙai, da kwashe fararen hula tare da maido ta tattaunawar siyasa a ƙasar'', in ji sanarwar.
Tuni dai ƙasashen duniya suka fara yunƙurin kwashe jami'an diflomasiyyarsu da kuma 'yan ƙasashensu daga ƙasar ta Sudan tun bayan ɓarkewar rikicin ƙasar a ƙarshen makon da ya gabata.