Ƙungiyar Commonwealth ta yaba da yadda zaɓen Najeriya ke tafiya

Asalin hoton, Commonwealth/Twitter
Shugaban kungiyar sa ido kan zaɓen Najeriya ta Commonwealth, Thabo Mbaki ya buƙaci dukkan masu zaɓe da su fito su zaɓi waɗanda suke so domin shugabantar su.
Thabo Mbeki wanda ya kasance tsohon shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, ya bayyana haka ne lokacin da masu sa ido na kungiyar suka ziyarci wasu rumfunan zaɓe a Abuja babban birnin Najeriya.
Kungiyar ta ƙasashe renon Ingila na sa ido ne a daidai lokacin da miliyoyin 'yan Najeriya suka fita rumfunan zaɓe daban-daban da ke faɗin ƙasar domin zaɓan shugaban ƙasa da kuma 'yan majalisar dattawa da kuma wakilai.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X














































