An kunna fitilu domin ci gaba da zaɓe a wasu sasssan Najeriya
Wannan shafi zai rinƙa kawo uku abubuwan da ke faruwa game da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokokin tarayya a Najeriya.
Rahoto kai-tsaye
Haruna Kakangi, Buhari Muhammad Fagge, Yusuf Yakasai, Abdullahi Bello Diginza and Nabeela Mukhtar Uba
Rufewa
Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonni kan zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokokin tarayya a Najeriya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabin labarai, musamman kan sakamakon zaɓen da aka gudanar yau.
Haka kuma kar ku manta kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a kowanne lokaci.
Amma yanzu a madadin sauran Abokan aiki, Yusuf Ibrahim Yakasai, Nabeela Muktar Uba tare da Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.
Wasu masu sa-ido sun ce an yi rawar gani a zaɓen Najeriya
Shugaban
gidauniyar MCArthur, Dakta Kole Shettima ya ce sun yaba da yadda hukumar zaɓen
Najeriya ta shirya zaɓen ƙasar.
To sai dai ya ce
duk da haka akwai matsaloli kamar na mutanen da ba su san inda za su yi zaɓe ba
sakamakon sauya wuraren zaɓe da aka yi.
‘’Sannan kuma mun
lura cewa ba duka jam’iyyun ba ne ke da wakilansu a rumfunan zaɓen’’, in ji Dakta
Kole.
Sannan kuma ya ce
akwai matsalar rashin buɗe rumfunan zaɓe a kan lokaci,
Ya ƙara da cewa akwai
matsalar rashin aikin na'urar BVAS kamar yadda ya kamata a wasu wurrare.
Ya kuma yaba da yadda matasa suka nuna jajircewa a zaɓen saboda suna ganin ko ma me a
ke ciki za su jira, ‘’amma kuma duk da haka mun samu labarin cewa wasu sun gaji,
sun kuma bar rumfunan zaɓen’’, in ji shi.
Dakta Kole Shettima
ya ce ya kamata a bai wa mutanen da ba su yi zaɓe ba damar sake yin zaɓe ko a
gobe ne, ko ranar Litinin kasancewar ma’aikatan zaɓen ba su zo da wuri ba.
Dakta Kole Shettima
ya kuma koka kan rashin bai wa mata dama a zaɓen Najeriya.
Sannan ya kuma ce
ya yaba da yadda INEC ke ƙoƙari wajen inganta harkokin zaɓen ƙasar, ba kamar
shekarun baya ba.
Za a ci gaba da zaɓe a jihar Taraba ranar Lahadi
Hukumar zaɓe a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da cewa za a ci gaba da zaɓe a jihar har zuwa gobe Lahadi.
INEC ta tabbatar wa BBC cewa jihar Taraba na cikin jihohin da za a ci gaba da zaɓen har zuwa gobe Lahadi.
Hakan dai baya rasa nasaba da rashin isar kayan zaɓe a kan lokaci wasu rumfunan zaɓen, kuma intanet ɗin na'urar BVAS na dauke wa.
Haka kuma rahotonni sun ce an yi garkuwa da wasu ma'aikatan zaɓen na wucin-gadi guda uku a ƙaramar hukumar Donga.
Wani jami'in hukumar da ya buƙaci a sakaya sunansa ne ya bayyana wa BBC faruwar lamarin.
To sai dai jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar ya ce suna kan gudanar da bincike domin gano yadda lamarin ya faru.
Zaben2023: ICPC ta cafke masu sayen ƙuri'u a jihohi biyar
Asalin hoton, ICPC
Hukumar ICPC mai binciken laifukan cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce ta kama mutum tara saboda laifin sayen ƙuri'u a jihohi biyar na Najeriya.
ICPC ta kama mutanen ne lokacin gudanar da babban zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokoki a jihohin Osun da Ondo da Borno da Akwa Ibom da Sokoto.
A cewar hukumar, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Tuwita, an kama mutum huɗu masu sayen ƙuri'u a jihar Osun, biyu a jihar Sokoto sai kamen da ICPC ta yi a Ondo da Akwa Ibom da Borno inda aka kama mutum ɗaya kowace jiha.
Zuwa yanzu dai hukumar ta ce mutanen da aka kama a Osun na tsare a ofishinta da ke jihar kuma an same su ne da wasu takardu ɗauke da sunaye da kuma lambobin wayoyinsu har da bayanan asusun ajiyar bankinsu.
Yadda hatsaniya ta kaure a wasu mazabu a Kaduna
An samu kaurewar hatsaniya a mazaɓar Rigasa da ke jihar Kaduna yayin da masu zaɓe ke ƙorafin cewa hukumar zaɓe ta ƙi ba su damar jefa ƙuri'unsu a zaɓen Shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokoki.
Masu zaɓen sun ce akwai giɓi a yadda ma'aikatan Inec ke wayar da kan mutane game da sauye-sauyen da aka samu a mazaɓu da kuma wa'adin da aka bayar na kaɗa ƙuri'a.
Wakiliyar BBC ta ruwaito cewa masu zaɓen sun yi ƙorafi kan yadda aka ɓata lokaci duk da cewa sun yi sammako zuwa wuraren kaɗa ƙuri'unsu ba tare da karyawa ba.
An kunna fitilu domin ci gaba da zaɓe a wasu sasssan Najeriya
Har yanzu masu zaɓe na ci gaba da kaɗa ƙuri'a a rumfar zaɓe mai mai lamba ta 108 unguwar Lugbe da ke Abuja babban birnin Najeriya.
Masu kaɗa ƙuri'ar na amfani da fitilu domin haskawa a lokacin gudanar da zaɓen.
Can ma a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin ƙasar rahotonni na cewa har yanzu masu kaɗa ƙuri'ar na kan layi a wata rumfar zaɓe da ke makarantar firamare a Unguwar Galadima.
Haka ma lamarin yake a wata rumfar zaɓe mai lamba 008 a mazaɓar Kauran Namoda shiyyar sarkin Noma da ke jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar, a cewar cibiyar CDD.
Haka kuma a wasu sassan jihar Kano rahotonnin na cewa har cikin wannan dare ana ci gaba da kaɗa ƙuri'a.
Wakilin BBC na wucin-gadi a jihar Borno ya ce an kuma na'urar samar da wutar lantarki a wasu sassan Borno da Yobe domin ci gaba da kaɗa ƙuri'a.
Wannan dai ba ya rasa nasaba da matsalar rashin isar ma'aikata da kayan zaɓen a kan lokaci, kuma a ɗazu ne shugaban hukumar INEC ɗin ya ce duk mutumin da ya hau kan layi kafin ƙarfe 2:30 na rana to doka ta bayar da dama a bar shi ya kaɗa ƙuri'arsa komai dare.
'Yan sanda sun kama mutane kan laifukan zaɓe a Legas
Asalin hoton, Idowu Owohunwa
Kwamishinan 'yan sandan jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya Idowu Owohunwa ya ce rundunarsa ta kama mutane da dama a faɗin jihar kan laifukan da suka shafi zaɓe.
Mista Owohunwa ya bayyana haka ne a wani taron menama labarai da ya gudanar a ranar Asabar, kan zaɓukan ƙasar da aka gudanar.
“Zan iya tabbatar da cewa an kama mutane da dama kan laifukan da suka shafi zaɓe, kuma a yanzu da nake magana da ku muna kan aikin, dan haka ba zan iya cewa ga adadin yawan mutanen da aka kama ba, to amma idan mun kammala za mu iya tantance adadin mutanen da muka kama,'' in ji CP Owohunwa.
To sai dai kwamishinan 'yan sandan jihar ya ce a wasu sassan jihar an samu nasarar gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana.
“Zaɓe ne da aka yi shi cikin kwanciyar hankali da lumana a mafi yawan wurare a jihar, to amma duk da haka mun fusknaci matsaloli na 'yan daba, kuma kamar yadda na faɗa a baya mun kama wasu da dama daga cikinsu'', in ji kwamishinan.
Ana ci gaba da samun sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisa
Bayanai na ci gaba da fitowa kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dattijai da na ƴan majalisar wakilai da aka gudanar ranar Asabar a Najeriya.
Duk da cewa kawo yanzu babu alkaluma da INEC ta fitar a hukumance na sakamakon zaben, sakamakon da ake bayyana wa a mazabu sun cika kafofin sa da zumunta.
BBC ba ta kai ga tantance sahihancin mafi yawncin sakamakon da ake bayyanawa ba.
Tun da misalin karfe 2:30 na yammaci ne aka fara samun sakamakon zaɓen daga rumfuna daban-daban a faɗin Najeriya.
Amma zai yi wuya alkaluman su yi ƙarin haske kan ɗan takarar da yake gaba musamman a zaɓen shugaban ƙasa.
Hukumar zaɓen ƙasar mai zaman kanta ta ce an samu tashin hankali a wasu jihohi da suka hada Edo da Bayelsa da Borno da Legas da Kogi.
Hukumar ta ce za a sake zaɓuka a wasu mazaɓu a jihar Bayelsa ranar Lahadi.
A jawabin da Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi dazun nan, za a buɗe cibiyar tattara sakamakon zaɓe gobe Lahadi da ƙarfe 12 na rana.
INEC ta ce tana fatan samun sakamakon ƙarshe cikin ƙanƙanen lokaci, amma ba ta bayyana rana ba.
Dokokin Najeriya sun tanadi cewa dole ne sai ɗan takarar shugaban ƙasa ya samu kashi 25% na yawan ƙuri'un da aka kaɗa a jihohi 24 na Najeriya da Abuja, kafin a samu wanda ya lashe zaɓe.
Yadda harin Boko Haram a Gwoza ya shafi aikin zaɓe
Rahotanni daga jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari a ƙaramar hukumar Gwoza lamarin da ya haifar da jinkirin kaɗa ƙuri'a.
Bayanai na cewa maharan sun afkawa masu zaɓen ne a dai-dai lokacin da ake gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisa a ƙaramar hukumar.
Ɗan majalisar dattijai daga yankin, wanda kuma yake takarar kujerar Ali Ndume, ya tabbatar wa BBC afkuwar harin,inda ya ce lamarin ya sa fargaba a zukatan masu zaɓe har wasu suka koma gida ba tare da kaɗa ƙuri'a ba.
Ya ce Mai Martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Shehu Idrissa Kimta ya bai wa jama'a haƙuri inda kuma ya ba da tabbacin cewa jami'an tsaro sun fatattaki maharan.
"Bayan hatsaniyar, an samu sauƙi, bayan azahar kuma mutanen gari da tawagar ƙaramar hukumar sun tsallaka bayan dutse, sun yi zaɓe an dawo gida lafiya."
A cewarsa, lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 8:30am zuwa 9:00am.
Wasu mata sun koka kan matsalolin da suka fuskanta a ƙoƙarin yin zaɓe a Kaduna.
Bayanan bidiyo, Latsa lasifikar da ke sama domin kallon bidiyon
PDP ta lashe zaɓe a Gidan Gwamnatin Kaduna
Ga sakamakon zaɓe na Gidan Gwamnatin Kaduna:
APC - 40
PDP - 69
LP - 48
INEC ta soke zaɓe a mazaɓu bakwai a Kogi
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta soke zaɓe a wasu cibiyoyin zaɓe na mazaɓar Kogi ta Gabas sakamakon hargitsin da wasu ɓatagari suka haifar a wuraren.
A cewar INEC, an soke zaɓe a rumfunan zaɓe biyu a nyigba sai wasu biyar a yankin Omala na jihar ta Kogi.
Hukumar zaɓen ta bayyana cewa ɓatagarin sun yi ta harbi a iska inda suka tarwatsa masu zaɓen, hakan a cewarta ya saɓa da dokar zaɓe kuma dole ta sa aka soke zaɓe a wuraren da lamarin ya faru.
INEC ta ce lamarin ya sa an dakatar da zaɓe ɓakatatan a rumfunan.
INEC ta ɗage zaɓe a wasu mazaɓu a Bayelsa
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ce ta ɗage zaɓe a wasu mazaɓu 141 a jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya.
Shugaban hukumar farfesa Mahmoud Yakubu ne ya bayyana hakan a jawabin da ya yi manema labarai a ɗakin tattaro sakamakon zaɓen 2023 da ke Abuja babban birnin Najeriya.
Ya ce an ɗage zaɓe a mazaɓun ne saboda tayar da rikici da wasu mutane suka yi.
INEC ɗin ta sanar da cewa za a sake zaɓen a gobe Lahadi.
Na'urar BVAS ta yi wa wasu tagwaye gardama
Asalin hoton, @hussainimk
Bayanan hoto, Hussain Muhammad Kabir
Wani ɗan Najeriya, Hussain Muhammad Kabir ya bayyana damuwarsa saboda rashin samun damar yin zaɓe sakamakon matsalar da ya fuskanta da na'urar BVAS.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Hussain Kabir ya ce hakan ya faru ne saboda abokin tagwaitakarsa, Hassan Muhammad Kabir ya riga shi jefa ƙuri'a abin da ya sa na'urar ta ƙi tantance shi saboda a cewarsa na'urar ba ta iya banbance fuskokinsu ba.
Ya kuma ce ma'aikatan zaɓen sun yi ƙoƙarin tantance shi ta ƴan yatsansa amma hakan ya ci tura.
A cewarsa, ya shafe sa'a huɗu ma'aikatan zaɓen na ta ƙoƙarin tantance shi amma lamarin ya faskara.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Suma wasu ƴan biyu, Hassanah Uthman da Hussainah Uthman sun bayyana cewa sun fuskanci irin wannan ƙalubalen.
A sakon da Hussainah Uthman ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce tasu matsalar ta fi muni kasancewar ma ba su iya samun katin zaɓensu ba saboda kamannin da suke da juna.
Abin al'ajabin dai ya ja hankalin mutane da dama a shafukan sada zumunta.
Sakamakon zaɓen wasu rumfuna a Legas
Bayan kammala kaɗa kuri'a a wasu sassan Najeriya da dama, a yanzu an fara kirga kuri'u.
Ga yadda sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na mazaɓar Igboho da ke Ikorodu a jihar Legas, yake
A rumfar zaɓe ta 012;
APC - 67
LP - 45
PDP - 9
A rumfar zaɓe ta 013;
APC - 21
LP - 10
PDP - 1
A rumfar zaɓe ta 014
APC - 69
LP - 45
PDP - 11
An fara ƙirga ƙuri'u a wasu rumfunan zaɓe a Kano
Ana ci gaba da ƙidaya
ƙuri’u a wasu rumfuman zaɓe a jihar Kano, yayin da ake ci gaba da zaɓe a wasu
rumfunan kasancewar mutane dai na kan layi
Wakilinmu ya shaida
mana cewa an samu ‘yar hatsaniya a ƙananan hukokmin Shanono da Ƙiru
Kakakin INEC na jihar
ya shaida wa BBC cewa na’urar BVAS tana da inganci, kuma gwajin na’urar da aka
yi a baya ya nuna cewa na’urar ba ta da wata matsala.
Ya kuma tabbatar
da cewa duka inda aka samu tsaiko hukumar ta yi ƙoƙarin ganin cewa an magance
matsalar.
Dangane da
wuraren da ba a fara ƙaɗa ƙuri’ar a kan lokaci ba , duk mutumin da ya hau kan
layi da misalin ƙarfe 2:30 ya ce za a ba shi damar kada ƙuri’arsa.
'Bola Tinubu ya samu nasara a mazaɓarsa'
Babban baturen zaɓe a mazaɓar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana shi a matsayin wanda ya samu nasara a mazaɓar.
Sakamakon zaɓen ya nuna cewa Bola Tinubu ya samu kuri'a 33 a rumfarsa.
Sauran jam'iyyu da suka samu kuri'u sun haɗa da;
APC - 33
LP - 8
PDP - 1
YPP - 1
An tarwatsa wata mazaba an kori mutane a Legas
Rahotanni daga
binin Legos a kudu maso yammacin Najeriya na cewa wasu ‘yan daba sun tarwatsa mutane a wata mazabe a unguwar
Surelere.
Rahotanni sun ce mutanen
da suka je zaɓe sun ringa guduwa don tsira da ransu, a lokacin da ƴan daban suka
ringa harba bindiga.
Bayanai sun ce su
ma jami’an zaɓe sun arce, sun kuma dauke na’urar tantance masu zaɓe BVAS, yayin
da ‘yan bindigar suka ɗauke wasu na’urorin na BVAS.
Wakilin BBC ya ce
an fasa akwatunan zuba ƙuri’u, an kuma kekketa wasu takardun zaben.
Jaridar Daily
Trust ta rawaito cewa an kashe mutum daya a wajen.
Bayanan hoto, Surelere Lagos
Bayanan hoto, Surelere Lagos
Bayanan hoto, Surelere Lagos
Bayanan hoto, Surelere Lagos
Za a sake zabe a wasu mazabu a Edo - INEC
Asalin hoton, INEC/twitter
Bayanan hoto, INEC
A ci gaba da jawabi da yake yi wa manema labarai na yadda zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar tarayya ke tafiya, shugaban hukumar zaɓe farfesa Mahmud Yakubu, ya ce sun samu labaran tayar da rikici a wasu mazaɓu a jihohin Borno da Legas da kuma Bayelsa.
Sai dai, ya ce lamarin ya daidaita.
Mahmud Yakubu ya ce bayan samun matsala ta rashin saka alamar wata jam'iyya a takardar kaɗa kuri'a a wasu mazaɓu biyu na jihar Edo, ya sanya an ɗage zaben sai a ranar 11 ga watan Maris lokacin gudanar da zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jiha.
Ya ce za a yi haka ne saboda kowa doka ta ba shi damar yin zaɓe, don haka INEC za ta yi duk iyawarta na ganin tabbatuwar hakan.
Sannan ya ce a gobe ne za a buɗe karɓan sakamakon zaɓen shugaban ƙasan Najeriya na 2023.
'Atiku Abubakar ya samu nasara a mazaɓarsa'
Babban baturen zabe a mazaɓar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar yace Atikun ya lashe zaɓe a rumfar da ya jefa ƙuri'a.
Sakamakon zaɓen ya nuna cewa Atikun ya samu ƙuri'a 282 a rumfar.