An rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban Amurka na 46

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kan yada ake shirin rantsar da Biden a Amurka da wasu batutuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umaymah Sani Abdulmumin and Mustapha Musa Kaita

  1. Hotunan jawabin karshe na Trump a matsayin shugaban Amurka

    Wadannan wasu ne daga cikin hotunan da aka dauka a sansanin sojin saman Amurka na Andrews Air Base, inda Donald Trump ya yi jawabin karshe a matsayinsa na shugaban kasar a yayin da iyalinsa suke kallonsa.

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

  2. Trump ya yi godiya ga iyali da ma'aikatansa

    Trump da iyalinsa

    Asalin hoton, Reuters

    A jawabin bankwana da ya gabatar a sansanin sojin sama na Joint Base Andrews, inda magoya bayansa suka yi ta tafi da shewa, shugaba Trump ya ce mutane "ba su san aiki tukuru" da iyalansa suka yi a shekaru hudu da ya kwashe a kan mulki ba.

    "Mun yi abubuwan mamaki," a cewarsa, sannan ya bayyana sauyin da ya kawo ga rundunar sojin Amurka.

    Ya gayyaci maidakinsa ta yi tsokaci inda ta ce abin alfahari ne da ta zama matar shugaban kasar Amurka.

  3. Labarai da dumi-dumi, Trump ya fice daga Fadar White House a matsayinsa na shugaban ƙasa

    tr

    Asalin hoton, Reuters

    Donald Trump da matarsa sun yi bankwana da Fadar White House, inda aka yi musu rakiyar karshe a matsayin shugaban ƙasa daga fadar.

    TR

    Asalin hoton, Reuters

  4. Buhari na jagorantar taron majalisar zartarwa karo na farko a 2021

    FEC

    Asalin hoton, TWITTER/BASHIRAHMED

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya na jagorantar taron majalisar zartarwa karo na farko a wannan shekara ta 2021.

    Yayinda taron ya samu halartar mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, da wasu mambobi a fadar gwamnati, sauran mahalarta taron sun shiga taron ne ta intanet.

    Kafin a soma tattaunawa a taron, sai da shugaba Buhari ya ƙaddamar da mambobi uku a hukumar ɗa'ar ma'aikata da mutum guda a hukumar kula da ƴan sanda.

    Mutanen sun hada da Ehiozuwa Ogbonayinma da Babatunde Balogun da Benedict Umeano, sai Onyemuche Nnamani a ɓangaren hukumar ƴan sanda.

    Sannan an gudanar da tsit na minti guda domin girmama tsoffin ministoci biyu da suka rasu kwana nan, wato Jubril Martins-Kuye da Bala Kaoje.

    FEC

    Asalin hoton, TWITTER/BASHIRAHMED

    FEC

    Asalin hoton, TWITTER/BASHIRAHMED

  5. Michael Boulos: Dan Najeriya da zai auri 'yar Donald Trump

    An yi baikon Tiffany Trump, 'yar shugaban Amurka mai barin gado, Donald Trump, da wani fitaccen dan kasuwa dan asalin Lebanon da Najeriya, Michael Boulos.

    Tiffany ta bayyana hakan ne a sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Talata.

    Mr Boulos shi ne daraktan kamfanin SCOA Nigeria tun shekarar 2016.

    An haife shi a Lebanon amma iyayensa sun koma Najeriya lokacin yana karami.

    Ya yi makarantar sakandare a birnin Lagos amma daga bisani ya tafi Ingila inda ya yi digirinsa na farko da na biyu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Mike Pence ba zai halarci bikin yi wa Trump bankwana ba

    Mataimakin shugaban ƙasar Amurka mai barin-gado Mike Pence ba zai halarci bikin bankwana da Trump ya shiryawa kan sa ba a barikin sojojin sama na Andrews da ke Maryland, a ranar Laraba ba.

    Maimakon halartar bikin bankwanan, Mike zai kasance a wurin rantsar da sabon shugaba Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris.

    Masu taimaka masa sun shaidawa Jaridar Washinton cewa zai kasance ƙalubale ga mataimakin shugaban ƙasar ya halarci bukukuwa biyu a lokaci guda.

    Mista Pence ya wallafa wasu jeren hotunan bankwana a shafinsa na twitter - sai dai babu wanda aka ga Trump a ciki.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Sau guda Pence ya hadu da Trump tun ranar 6 ga watan Janairu, da magoya-bayan Trump suka farwa ginin majalisar suna ihu cewa: "A rayata Pence!"

    Mataimakin shugaban ƙasar da matarsa Karen za su wuce gidansu da ke Indiana. Kuma babu cikakken bayyani a kan ko zai sake neman muƙami nan gaba.

  7. Gwamnan Ondo ya mayar wa Buhari martani kan korar makiyaya daga jiharsa

    ONDO

    Asalin hoton, TWITTER/@ROTIMIAKEREDOL

    Gwamnatin Ondo ta ce fadar gwamnatin Najeriya na nuna alamun goyon-baya ga ayyukan Fulani makiyaya.

    Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Donald Ojogo ya shaida hakan ne a lokacin da ya ke mayar da martani kan sanawar fadar gwamnati kan haramcin da jihar tayi na ayyukan fulani makiyaya a dazukanta.

    Mai magana da yawun fadar gwamnati, Malam Garba Shehu ya yi alla-wadai da matakin gwamnatin ondo tare da gargadin cewa ayi biyaya ga umarnin Shugaba Buhari idan ba haka ba za su ɗauki mataki na gaba.

    Sai dai a cewar Ojogo kalaman Garba Shehu na iya haifar da matsala ga kasancewar Najeriya dunkulalliyar kasa guda.

    A makon nan ne gwamnan jihar ta Ondo ya bai wa makiyaya da ke dazukan jihar wa'adin kwanaki bakwai su bar dazukan.

    Gwamna Akeredolu ya ce a matsayinsa na babban mai kula da sha'anin tsaro na jiharsa, ba zai zura ido ba ya bari ana ci gaba da aikata laifuka.

  8. Jawabin bankwanan Trump cikin daƙiƙa 20

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da jawabinsa na bankwana, wanda a ciki yake cewa: "Mun yi abin da ya kawo mu - har ma da kari."

    A wani sakon bidiyo da aka wallafa a YouTube, shugaban ya ce ya "sauke nauyin da aka dora mana, wanda shi ne dalilin da ya sa kuka zabe ni."

    Sai dai har yanzu Mista Trump bai amince da shan kaye a zaben watan Nuwamba ba, zaben da Joe Biden na jam'iyyar Democrat ya lashe

    Za a rantsar da Joe Biden matsayin shugaban Amurka na 46 ranar Laraba.

    Latsa nan domin karanta cikakken labarin.

  9. Biden ya sanar da ayyukan farko da zai yi da zaran ya sha rantsuwa

    Tawagar zaɓaɓɓan shugaban Amurka Joe Biden ta sanar da ayyukan farko da zai aiwatar da zaran an rantsar da shi. Sun hada da;

    • Dakatar da Amurka daga ficewa daga hukumar lafiya ta duniya, WHO.
    • Sake koma wa cikin yarjejeniyar sauyin yanayi na birnin Paris.
    • Soke haramcin shiga ƙasar kan kasashen musulmi da dama
  10. Lil Wayne da Kodad Black na cikin mutanen da Trump ya yi wa afuwa

    trump

    Asalin hoton, Getty Images

    A ɗaya daga cikin ayyukansa na ƙarshe Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump ya yi afuwa ga mutane 73, ciki har da mawaka Lil Wayne da Kodad Black.

    Kazalika shugaban kasar ya yi afuwa ga tsohon mai ba shi shawara Steve Bannon.

    Shugaban kasar ya sanar da yin afuwar ne sa'o'i kadan gabanin rantsar da sabon shugaban kasar Joe Biden.

    Sanarwar ta ce an yi wa mawakan gambara Lil Wayne da Kodak Black da kuma tsohon magajin garin Detroit Kwame Kilpatrick afuwa.

    Shiga nan domin samun wasu bayanan.

  11. Ƙungiyar Afenifere ta caccaki fadar shugaban ƙasa kan batun korar makiyaya a Ondo

    Makiyaya

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar Afenifere ta ‘yan kabilar Yarabawa zalla ta caccaka fadar shugaban Najeriya kan batun wa’adin kwanaki bakwai da gwamnan Ondo, Rotimi Akeredelu ya baiwa makiyaya na su fice daga dazukan jihar.

    A cikin wata sanarwa, kakakin Afenifere, Yinka Odumakin ya ce kodayake ba suyi mamakin matsayin gwamnatin tarayya kan batun ba, amma dai ita kungiyar Afenifere na tare da Gwamna Akeredelu.

    Kungiyar ta yi kira ga sauran gwamnonin jihohin kudu maso yammacin Najeriya su kasance tare da gwamnan Ondo a kan wannan tirka-tirkar.

    A ranar Talata ne fadar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta bayyana cewa matakin gwamnan Ondo na baiwa makiyaya wa’adi ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

    A makon nan ne gwamnan jihar ta Ondo ya bai wa makiyaya da ke dazukan jihar wa'adin kwanaki bakwai su bar dazukan saboda a cewarsa ba zai zura ido ba ya bari ana ci gaba da aikata laifuka.

    Ana zargin makiyaya ne da aikata laifuka ciki hadda garkuwa da mutane domin karbar kundin fansa amma dai shugabannin kungiyar makiyayan sun musanta.

  12. Ministan harkokin wajen Zimbabwe ya rasu

    ZIMBABWE

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin waje na ƙasar Zimbabwe, Sibusiso Moyo, ya mutu.

    Ministan yaɗa labarai Jenfan Muswere ne ya tabbatarwa jaridar ƙasar ta, the Herald, da mutuwar.

    Babu dai wasu bayanai ko karin haske kan musababbin mutuwar kawo yanzu.

    Mr Moyo, wanda manjo janar din soja ne, na cikin sojojin da suka kifar da gwamnatin tsohon shugaba Robert Mugabe.

    A daren da aka cire Mugabe daga Mulki, ya fito ya yi jawabi a kafar talabijin ƙasar inda yake kwantar da hankulan al'umma yana mai cewa mai laifi kawai suke yaƙa.

    Mutuwar Moyo na zuwa ne bayan mutuwar wasu ministocin gwamnatin biyu, Ellan Gwaradzimba da Perrance Shiri, kasa da wata shida. Mr Shiri ya mutu ne sakamakon kamuwa da Covid-19.

  13. 'Fashi da makami ya ragu a jihar Oyo'

    OYO

    Asalin hoton, @RRSLAGOS767

    Rundunar ƴan sanda a Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta ce an samu ragi a aikata fashi da makami da sama da kashi 32 cikin 100 a jihar.

    A bara an samu fashi da makami 123 kasa da 182 da aka fuskanta a 2019, a cewar rahoton ta.

    Rahoton ya kuma ambato cewa an samu ragi wajen aikata muggan laifuka da kashi 40 zuwa kusan 50 cikin 100.

    Ana dai ganin matakan da Gwamna Seyi Makinde ke dauka a fannin tsaro sun taka rawa wajen kawo sauyin da ake gani.

    Sai dai rahoton ya shaida cewa akwai sabon salon sata da garkuwa da mutane da ake zargin mikiyaya da ke kutsawa jihar.

  14. Waƙar Burna Boy na cikin waƙoƙin da za a gwangwaje da su a bikin rantsar da Biden

    BURNABOY

    Asalin hoton, Getty Images

    Waƙar mawaƙin Najeriya Burna Boy na cikin waƙoƙin da za a yi amfani da su a bikin rantsar da zaɓaɓɓan shugaban Amurka, Joe Biden.

    Za a yi amfani da waƙar Destiny na Burna Boy cikin jeren waƙoƙin manyan fitattun mawaƙan duniya a wajen bikin.

    Waƙoƙi 46 aka tsara amfani da su, kuma a cewar kwamitin shirya karbar mulki na Biden, anyi hakan ne domin nuna yaɗa sabuwar Amurka za ta kasance na kowa.

    "Wadanan waƙoƙi da mawaƙan an zaɓosu ne domin shaida wa duniya sabon babbin rayuwa da haɗin-kai da za a ganin a gwamnatin Biden-Harris," a cewar sanarwar.

    Sauran waƙoƙin da ke cikin wannan rukuni akwai 'Find Your Way Back na mawaƙiya Beyonce, da wakar Kendrick Lamar da Mary J. 'Blige's Now ko Never, sai wakar Bob Marley da The Wailers, 'Could You Be Loved.

  15. INEC za ta wajabta amfani da lambar shaidar zama ɗan ƙasa ta NIN a katin zaɓe

    NIN

    Asalin hoton, NIMC

    Hukumar zaɓe ta kasa a Najeriya, INEC, na duba yiwuwar wajabta amfani da lambar shaidar zama ɗan ƙasa a rajistar katin zaɓe yayinda za a cigaba da yiwa mutanen rajistar katin zaɓe a makonni masu zuwa.

    Wani jami'in hukumar ne ya tabbatar da hakan ga Jaridar The Punch da ke wallafa labaranta a Najeriya.

    Hukumar ta ce amfanin da lambar ɗan ƙasa a rajistar katin zaɓe zai daƙile matsalar yiwa yaran da shekarunsu ba su kai ba katin zaɓe da maguɗi da dai sauransu.

    Nan da ɗan lokaci kaɗan ake saran hukumar ta fito domin sanar da shawarar karshe da ta yanke a cewar Punch.

  16. Biden na gab da shan rantsuwar kama aiki

    An tsaurara matakan tsaro a ginin US Capitol

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An tsaurara matakan tsaro a ginin US Capitol

    A wannan Larabar ake shirin rantsar da Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris a Amurka.

    An garƙame Washington DC na Amurka - ba shiga ba fita gabanin bikin rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban Amurka na 46.

    Sojoji dubu 25 aka girke kan titunan birnin da ke fama da annobar korona da ɓarnar da wasu ɓatagari suka yi wa majalisar dokokin ƙasar.

    Gabianin karbar rantsuwar aiki zaɓaɓɓen shugaban ya jagoranci taron tunawa da Amurkawa dubu dari huɗu da suka mutu sanadin cutar korona.

    Tsaye tare da mataimakiyarsa, Kamala Haris, Biden ya ce abu ne mai mahimmanci a tuna da waɗanda suka mutu sakamakon annobar.

    An kunna fitulu guda dari hudu wadanda ake iya ganin haskensu cikin ruwan da ke kwance a ginin Lincoln Memorial da ke Washington.

    Biden

    Asalin hoton, Getty Images

    Mista Biden ya yi alƙawarin fifita batun tallafin korona da zarar ya karɓi mulki a yau Laraba ƙarƙashin matakan tsaron da ba a taba gani ba a babban birnin ƙasar.

    Wakilin BBC ya ce yanzu Amurka za ta sake shiga yarjejeniyar yanayi ta Paris sannan Biden zai kawo ƙarshen haramcin da Trump ya ƙaƙaba na hana yan wasu ƙasashe akasari na musulmai shiga Amurka

  17. Korona ta kashe karin mutum 15 a Najeriya

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 1,301 da suka kamu da annobar korona a ƙasar ranar Talata.

    A cewar hukumar ta NCDC, mutum 15 ne suka mutu cikin sa'a 24 da ta gabata sannan an sallami mutum 1,261 bayan sun warke daga cutar.

    Bisa sabbin alkaluman hukumar, har yanzu jihar Legas ce ke kan gaba da mutanen da suka kamu da cutar cikin kwana ɗayan inda take da mutum 551.

    Abuja, babban birnin ƙasar ne ke biye wa jihar Legas da mutum 209 sai Oyo mai mutum 83.

    Jihar Plateau na da mutum 65 sai Kaduna mai 64 yayin da a Enugu aka samu ƙarin mutum 61 da suka kamu da cutar ranar Talata.

    Jihar Rivers na da 44 sai Ondo mai 39, Benue kuma tana da 37 inda a Akwa Ibom aka samu mutum 31.

    Kano na da 19 sai Delta da Gombe masu 18 kowace jiha. Ogun na da 16, Edo 15, Kebbi 10, Ebonyi 9.

    Jigawa 4, Osun 3, Zamfara 3, Borno 1 sai Nassarawa 1.

    Yanzu dai kididdigar masu cutar a Najeriya ita ce 113,305 sannan mutum 91,200 sun warke inda kuma mutum 1,464 suka rasu

  18. Budewa

    Masu bibbiyar mu a wannan shafi Barka da safiya da fatan kun wayi gari lafiya. Umaymah Sani Abdulmumin ke fatan kasancewa da ku a wannan rana ta Laraba.

    Shafin zai ke kawo muku bayanai kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma bikin naɗa sabon shugaban Amurka Joe Biden.

    Kar a manta ana iya kasance da mu har a shafukanmu na sada zumunta da Youtube.