Lil Wayne da Kodak Black na cikin mutanen da Trump ya yi wa afuwa

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump ya yi afuwa ga mutane 73, ciki har da mawaka Lil Wayne da Kodak Black.
Kazalika shugaban kasar ya yi afuwa ga tsohon mai ba shi shawara Steve Bannon.
Shugaban kasar ya sanar da yin afuwar ne sa'o'i kadan gabanin rantsar da sabon shugaban kasar Joe Biden.
Sanarwar ta ce an yi wa mawakan gambara Lil Wayne da Kodak Black da kuma tsohon magajin garin Detroit Kwame Kilpatrick afuwa.
Lil Wayne da Kodak Black na fuskantar shari'a kan mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, yayin da tsohon magajin gari Kwame Kilpatrick ke zaman gidan yari na shekara 28 saboda cin hanci da rashawa.
Kudin gina katanga

Asalin hoton, Reuters
Mista Bannon, wanda a baya yana cikin manyan masu ba Shugaba Trump shawara yayin yakin neman zabensa na 2016, an gurfanar da shi a gaban kotu saboda badakalalar kudaden da aka tara domin gina katangar da ta raba Amurka da Mexico.
Masu shigar da kara sun ce Mista Bannon da wasu mutum uku sun damfari dubban mutanen da suka tara kudade kan batun gina katangar, wanda aka tara fiye da dala miliyan 25.
Kazakila shugaban kasar ya yi sassauci ga hukuncin gidan yari da aka yanke wa mutum 70 .
An saba ganin shugaban kasa mai barin gado yana yin afuwa ga wadanda suka cancanci a yi musu afuwar.
Shugaban Amurka na da ikon yin afuwa ga duk wanda ya so a kan shari'ar da gwamnatin tarayya ke da hurumi.
Yin afuwar na nufin ba za a hukunta su ba, yayin da sassaucin zai rage wa'adin da mutanen za su kwashe a gidan yari.
A watannin baya bayan nan Mr Trump ya yi afuwa ga mutane da dama.
Galibinsu makusantansa ne, wadanda suka hada da tsohon shugaban kwamitin yakin neman zabensa Paul Manafort, da dadadden amininsa Roger Stone da kuma Charles Kushner, mahaifin surukinsa Jared Kushner.










